HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 30/ZULHIJJAH/1437H
Daidai da 30 /SATUMBA / 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
FALALAR HAXIN KAI DA NA ZUKATA
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya
yi hudubar juma'a ta 28 zulhijjah, 1437H, mai taken: FALALAR HAXIN KAI DA NA
ZUKATA,
Wanda a cikinta ya tattauna, kan haxin kai, da na zukata, da riqo da littafi da
Sunnah, Yana mai bayyana falalarsa, da girman tasirinsa, da kasancewarsa sababi
ne na tsiran wannan al'ummar daga fitintinu, yana kuma tsawatarwa kan
rarrabuwar kai da savani da jayayya; saboda abinda su ke sabbabawa na saukar
jarabawa da bala'oi ga musulmai, da rarrabuwar kalmarsu, da kecewar sahunsu.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, saboda taqawar Allah ita ce hanyar
shiriya, sava mata kuma shi ne hanyar tavewa.
Ya ku musulmai …
Allah ya halicci bayi, ya azurta su, yana kuma jujjuya
lamuransu.
kuma Allah ya yi rahama ga
bayi da addinin musulunci, wanda a cikinsa gyaruwar duniyar bayi da lahirarsu
ta ke, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya
bi shiriyata, to ba zai vata ba" –wato: a duniya- "kuma ba zai tave ba" wato: a lahira-[Xaha:
123 ].
Addini ne mai girma (wato: muslunci), wanda yana daga
cikin muhimman ginshiqansa da ababen da ya kevanta da su, da qa'idodinsa masu
girma, KWAXAITARWARSA
AKAN TATTARA MA'ABUTANSA KAN GASKIYA, DA XINKE TSAKANIN ZUKATANSU, kuma wannan (wato, haxin
kai) ni'ima ce mai girma, wanda Allah ya yi baiwa da ita ga bayinsa, Allah yana
cewa: "Shi ne wanda ya qarfafe ka da nasararSa, da kuma muminai * Kuma ya
xinke tsakanin zukatansu, da za ka ciyar da abinda ke cikin qasa gabaxaya, da
baka xinke tsakaninsu ba, saidai Allah Shi ya xinke tsakaninsu, lallai ne shi
Mabuwayi ne Mai hikima[Anfal: 62-63].
Kuma waxannan da su ka tattara akan kalmar musulunci,
waxanda su ke bin Alqur'ani da Sunnah su ne muminai na gaskiya, koda kuwa masu
sava musu sun yawaita ko sun yi qarfi.
Kuma haqiqa manzanni sun haxu (ittifaqi) akan tattara
al'ummominsu a bisa gaskiya, Sai su ka yi umurnin a tsayar da musulunci, da
tsayuwa akansa ta fiskar ilimi da aiki, da aqida da hali, da tattaruwa akan
haka, Allah yana cewa: "Ya shar'anta addini a gare ku, irin abinda
ya yi wasici ga Nuhu, da abinda mu ka yi wahayi izuwa gare ka, da abinda mu ka
yi wasici ga Ibrahima da Musa da Isa; cewa: Ku tsayar da addini, kuma kada ku
rarraba a cikinsa[Shura:
13].
Dukkan Annabawa sun yi kira
izuwa ga a bauta wa Allah shi kaxai, tare da kwaxaitar da mutanensu, akan
haxuwa kan haka, Sai kowani Annabi ya ce wa al'ummarsa: "Ya ku mutanena, ku
bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautan wanda ba shi ba"
[A'araf:
59, 65, 73, 85, Hud: 50, 61, 84, Muminun: 23 ].
Kuma shima Annabi (صلى الله عليه وسلم) an turo shi ga mutanen da suke rarrabe
cikin addininsu, suna masu jayayya ga junansu, a cikin lamuran duniyarsu, "Kowace qungiya da
abinda ke wurinsu, masu alfahari ne" [Muminun: 53, Rum: 32]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi hani, kan yin koyi da su, sannan ya
yi umurni da a haxa kai. Sai lamarin addini ya tsayu, jahiliyya kuma ta kau.
Sai kuma lamuran mutane su ka gyaru sakamakon tsayuwarsu akan addini.
Mutane maslaharsu ta duniya
da ta lahira ba za ta cika ba, face akan tattaruwa akan gangariyan musulunci,
da yin taimakakkeniya, da agaza wa juna.
Kuma saboda muhimmanci, ko wajabcin riqo da musulunci, da
tattaruwan mutane akansa, ya kasance ginshiqi da manzanci ya yi ittifaqi
akansa, kuma ya zama manufa mai girma a cikin dukkan shari'o'i.
Kuma (haxin kai) abu ne na
dole a rayuwar duniya, wanda rayuwa ba za ta gyaru ba sai da shi, kuma ba za a
samu aminci da zaman lafiya ba, matuqar babu haxin kai.
Kuma lamuran bayi a
tsakaninsu ba za su cika ba, kuma maslahohinsu ba za su samu ba, face da shi.
Kuma shi ne hanyar da
al'umma za ta dawo da matsayinta, ta kuma xinke varakarta, ta samu buwaya, da
kariya ga al'ummai.
Kuma haxin kai shi ne hanyar
da ta fi zama daidai wajen tabbatar da burace-buracen musulmai, da tunkuxe
raxaxi a gare su.
Kuma shi ne mahaxa ta gaskiya
da ta kulla tsakanin musulmai.
Kuma da shi ake iya kare
addinin musulunci.
Kuma haxuwa akan addini na gaskiya da tara zukata akansa,
wajibi ne na shari'a akan al'ummah, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya,
kada ku rarraba"
[Ali-Imraan: 103].
Ibnu-Jarir -رحمه الله- ya ce: Yana nufin: "Ku yi riqo da addinin Allah,
wanda ya umurce ku da shi, da kuma alkawarinSa da ya yi da ku, a cikin
littafinsa, na haxe tsakanin zukata da taruwa akan kalmar gaskiya, da miqa wuya
ga lamari ko umurnin Allah".
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada muhimmanci ga wannan lamarin mafi tsananin bada
muhimmanci, sai ya bayyana shi ga sahabbansa, da zance, ya kuma kusanto da shi
ga kwakwalensu da yin zane a qasa, domin wannan lamari mai muhimmanci ya
tabbatu a cikin kwakwalensu, Abdullah ibn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zana mana wani zane, sannan ya ce: Wannan shi
ne hanyar Allah! Sa'annan sai ya zana wasu zanen ta dama da shi da hagu,
sa'annan ya ce: Waxannan hanyoyi ne mabanbanta, akan kowace hanya daga cikinsu
akwai shexanin da ya ke yin kira zuwa gare ta", Sa'annan ya karanta: "Kuma lallai wannan
hanyata ce miqaqqiya, sai ku bi ta, kada ku bi qananan hanyoyi, sai su kautar
da ku daga hanyar Allah [An'am: 153]. Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma Allah ya tunatar da
wannan al'ummar, da wannan ginshiqi mai girma a inda ya ke cewa: "Lallai wannan
al'ummarku ce al'umma guda xaya, Ni kuma nine Ubangijinku, sai ku bauta mini" [anbiya'i : 92].
Cikin haxuwar mutane akan shiriya akwai saukar rahama,
don haka; yana daga cikin sifofin muminai kasancewarsu masu jin qai ga junansu.
Kuma lallai haxin kai
ni'ima ce da Allah ke yin baiwarta ga bayinsa, Allah ya ce: "Kuma ku ambaci
ni'imar Allah akanku, a yayin da ku ka kasance maqiya, sai ya daidata tsakanin
zukatanku, sai kuka wayi gari da ni'imarsa kuna 'yan'uwa", [Ali-Imran: 103].
Kuma Allah ya umurci muminai da haxin kai, ya hane su
savani da rarrabuwar kai, Kuma ya basu labarin cewa, lallai ne waxanda su ka
rigaye su, sun halaka ne da yin jayayya ko husuma a cikin addinin Allah, Allah
(سبحانه) yana cewa: "Lallai waxanda su ka rarrabe addininsu, su
ka zama qungiya-qungiya, baka cikinsu a wani abu, kuma lallai lamarinsu yana ga
Allah, sa'annan ya basu labari akan abinda su ke aikatawa[An'am: 159].
Cikin lazimtar jama'ar musulmai akwai kariya da tsira
daga fitintinu, kuma da aikata haka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi wasici ga musulmai idan fitintinu su ka sauka, Huzaifat
–رضي الله عنه- ya ce: Shin bayan
wannan alkhairin akwai sharri? Sai Annabi –tsira da aminci su qara tabbata a gare
shi- ya ce: ya ce: "E, Masu kira ne akan qofofin jahannama; Duk wanda ya
amsa musu zuwa gare ta, sai su jefa shi a cikinta". Sai Huzaifat –رضي الله عنه- ya ce: "Da me ka ke umurtata idan hakan ya
riske ni? Sai Annabi ya ce: Ka lazimci jama'ar musulmai da shugabansu. Muslim ya ruwaito shi.
Yana daga cikin nasiha ga musulmai: Lazimtar jama'arsu
ta hanyar yin muwafaqa a gare su, cikin ingantacciyar aqida, da aiki na kwarai,
da yin aiki domin daidaita zukatansu,
kuma wanda ya fi mutane
tsarkin zuciya shi ne wanda ya fi su lazimtar gaskiya, tare da jama'ar
musulmai, Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Sifofi uku, zuciyar mutum musulmi bata
xaukar gillu ko qyashi akansu, ikhlasin aiki ga Allah, da nasiha ga jagororin
musulmai, da lazimtar jama'ar musulmai, domin addu'oinsu suna game wanda ke
cikinsu".
Ma'anar wannan shi ne,
lallai addu'ar musulmai ta kewaye su, kuma tana kare su, daga kaidin shexan, da
kuma vacewa –wannan haidsin Tirmiziy ne ya ruwaito.
Haxin kai, yana daga abubuwan da Allah ya yarje wa bayinsa,
shi kuma bawa yana yarda wa kansa, da abinda Allah ya yarda a gare shi, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai ne Allah,
yana yarje muku abubuwa uku, kuma yana qiye muku abubuwa guda uku, Ya yarda
muku, ku bauta masa kada ku haxa shi da kowa, kuma ku yi riqo da igiyar Allah
gabaxaya, kada ku rarraba…". Muslim ya ruwaito shi.
Sheikh Muhammadu bn
Abdulwahhab –رحمه
الله-
ya ce: "Wata matsala bata auku a cikin addinin mutane ko duniyarsu ba,
sai da sababin sakaci akan waxannan abubuwan guda uku, ko sashinsu".
Masu riqo da musulunci daga mavuvvugarsa tatacce; wato: Alqur'ani
da Sunnah, za su ci-gaba da wanzuwa, suna waxanda ake taimakonsu, Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wasu vangare na
al'ummata ba za su gushe ba, akan gaskiya, suna maxaukaka, Wanda zai qi taimaka
musu ba zai cutar da su ba, har sai lamarin Allah ya zo alhalin suna kan haka" . Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma su ne suka fi dukkan mutane rabauta da samun haxewar
zukata, da jin qan juna, da fahimtar juna a tsakaninsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma muminai maza
da muminai mata sashinsu majivinta sashi ne, suna yin umurni dakyakkyawa, suna
yin hani ga mummuna, suna tsayar da sallah, suna bada zakkah, suna yi biyayya
ga Allah da manzonSa, Waxannan lallai Allah zai yi musu rahama, Lallai ne Allah
Mabuwani ne Mai hikima" [Tauba: 71].
Kuma tsakaitawa shine salo ko manhajinsu, basa wuce
iyaka, kuma basa gajartawa, basa yin guluwwi, kuma basa yin jafa'i.
Kuma su ne masu tsira daga bidi'oi da vata, da rarrabuwar
kai, a duniya.
Haka daga halaka, da kuma azaba a lahira. Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma lallai ne
wannan addinin za su rarraba izuwa qungiyoyi saba'in da uku, saba'in da biyu
suna cikin wuta, xayar kuma tana cikin aljannah, wanda kuma ita ce: Jama'a". Abu-dawud ya
ruwaito shi.
A wurin Alhakim kuma, An ce
wa Annabi (صلى اللع عليه وسلم) wacece guda xayan? Sai
ya ce: "Abinda Ni na kasance akansa a yau, da sahabbaina"
Kuma saboda tabbatarwar da Allah ya yi musu, su suna
tabbace akan gaskiya, kuma babu wani banbanci ko savani cikin manhajinsu, koda
an samu tsawon shekaru, kuma duk wanda ya leqa littatafansu da aqidunsu, kuma
ya san tarihinsu, tun daga wanda suka yi rigaye daga cikinsu, da wadanda suka
riski na farkon, zai samu cewa, duka suna kan turba ne guda xaya, kai ka ce
aqidunsu da zantukansu sun fita ne daga zuciya guda xaya, aiyukansu kuma kamar
sun kasance daga jiki guda xaya, savanin abinda wasunsu su ke a kai, domin ('yan
bidi'a) su kan kasance hanyoyinsu nesa da ilimi ko dalili, hujjojinsu kuma suna
da rauni (basu da qarfi), aqidunsu kuma ko zantukansu suna hannun riga da juna;
saboda duk wanda ya bar gaskiya, to sai lamarinsa ya jirkice, addininsa kuma ya
caccakuxe, Allah (سبحانه) yana cewa: "Lallai sun qaryata
gaskiya ne, a lokacin da ta zo musu, don haka, su suna cikin wani al'amari da
ke cakuxe"
[Qaf: 5 ].
A ranar qiyama kuma masu
bin Alqur'ani da sunna za su rabauta, Allah (تعالى) yana cewa: "Ranar da wasu fiskoki za su yi hasken fari,
wasu fiskokin kuma su yi baqi, Amma waxannan da fiskokinsu su ka yi baqi, Shin,
kun kafirce bayan imaninku, to ku xanxani azaba saboda abinda kuka kasance ku
ke yi na kafirci * Amma su kuma waxannan da fiskokinsu suka haskaka, to suna
cikin rahamar Allah, su a cikinta za su dawwama" [Ali-imran: 106-107].
Abdullahi xan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Fiskokin Ahlus-sunnah
wal jama'a za su yi haske, ma'abuta rarrabuwar kai da savani kuma, fiskokinsu
za su yi baqi".
BAYAN
HAKA, YA KU MUSULMAI!
Ya ishi, lamarin haxin kai, xaukaka, kasancewar hannun Allah
yana kan jama'a, kuma Allah ya yarda da haxin kai, kuma a cikinsa akwai
gyaruwan lamura, da alheri.
A cikin rarrabuwar kai kuma,
akwai lalacewan lamura da watsewarsa da halaka.
Shi kuma mai hankali, ba zai yi sakaci kan bin jama'ar da
ta ke bin Alqur'ani da Sunnah ba, koda kuwa ya hangi wasu maslahohi na qashin-kai
cikin barin binta, saboda za su kasance maslahohi ne da basu su ka fi
muhimmanci ba, ko maslahohi. Kuma zai yi farin ciki ne da shiryarwar da Allah
ya masa izuwa ga wannan addinin miqaqqe, sai kuma ya lazimci jama'ar musulmai,
ya kuma riqa da'awar waninsa zuwa ga hakan.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Duk wanda ya sava
wa Manzo, bayan hujjoji sun bayyana masa, kuma ya bi turbar da ba ita ce ta
muminai ba, za mu jivinta masa abinda ya jivinta, kuma mu shigar da shi
jahannama, kuma lallai makoma ta yi muni" [Nisa'i: 115].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA, ya kuma amfanar da ni, da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa
mai hikima, Ina faxan maganata wannan, kuma ina neman gafara wa ni da ku da
sauran musulmai daga dukkan zunubai, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya
kasance Mai gafara Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
"Sunnah" ana gwama ambatonta da "jama'a ko
haxin kai",
Masu yin riqo da sunna kuma sune ma'abuta jama'a, kuma
tafarkinsu guda xaya ne; wanda shine:
Kaxaita Allah cikin bauta, da
ikhlasin addini a gare shi.
Da tabbatar wa Allah
sunayensa da sifofinsa, kamar yadda Allah ya siffanta kansa da su, a cikin
littafinsa, kuma Manzonsa (صلى
الله عليه وسلم) ya siffanta shi da shi, ba tare da canza wani abu, ko korewa
ba, kuma ba tare da faxin yanayin sifa, ko misaltawa ba.
Da kuma tabbatar da rukunin
imani da qaddara, ta hanyar yin imani da kasancewar Allah ya siffanta da sifar
ilimi mai rigaye, ga duk abinda zai kasance, kuma ya rubuta shi a lauhul
mahfuz, kuma Allah ya ke halittarsa, kuma babu wani abu da zai kasance a duniya
face, idan Allah ya nufe shi.
Kuma yana cikin MANHAJIN AHLUS-SUNNAH: Tabbatar da bin Annabi (صلى الله عليه وسلم) da bin shiriyar sahabbansa –رضي الله عنهم-, da koyi da magabatan wannan al'ummar da
bin shiriyarsu.
Tare da gaskiyar riqo da Alqur'ani da Sunnah.
Da neman sani cikin Alqur'ani da Sunnah, da yin aiki da
abinda ke cikinsu.
Kuma haxuwa kan riqo ko aiki da littafin Allah da sunnar
Manzo ginshiqi ne daga ginshiqan Ahlussunnah wal Jama'ah; saboda (أهل السنة والجماعة) suna bin littafin Allah ne, da sunnar
Manzo, kuma suna nisantar fanxarewa, da savani ko rarrabuwa.
Kuma suna kwaxayin ganin
haxin kan musulmai gabaxaya, amma ba tare da an tozarta wata gaskiya ba, ta
hanyar voye ta, ko cakuxa ta da varna.
Kuma suna mu'amalantar waxanda
suka sava musu, da adalci, da rahama, ba tare da qetare iyaka ko zalunci ba.
Kuma wanda aka azurta shi da ilimi mai amfani, da
kuma aiki na kwarai, sai kuma ya nisanci shubuhohi da sha'awowi, to wannan ya
kasance daga cikin bayin Allah masu rabauta.
Sannan ku sani; Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da kuma
sallama ga Annabinsa …
Sai yace, a cikin mafi kyan
littafin da ya saukar: "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yi salati
ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa"
[Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah Ka sanya qasashensu su zama wurin aminci
da zaman lafiya, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka haxa kalmarsu akan
gaskiya da shiriya, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga shiriyarka,
ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Kuma ka datar da xaukacin
jagororin lamuran musulmai zuwa ga aiki da littafinka, da yin hukunci da
shari'arka, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka taimaki rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar
da dugadugansu, Ya Allah! Ka taimake su akan maqiya, Ya Mai qarfi, Ya
Mabuwayi.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya,
ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah Ka karva wa mahajjata hajjinsu, ka mayar
da su, garurrukansu, suna kuvutattu, masu riba, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Bayin Allah!!!
"Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku
wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment