HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24 /JUMADAH AL'ULAH/1437H
Daidai da 04 /Maris / 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu
mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa,
kuma ku yi riqo a Musulunci da igiya mai qarfi (amintacciya).
Ya ku musulmai …
ILIMI yana samun xaukaka da
xaukakar abinda ake neman a sani, Lallai
kuma maxaukakin ilimi da yafi tsarki shine: ILIMIN SANIN ALLAH, kuma buqatuwar
bayi zuwa ga sanin Allah maxaukaki, da girmama shi: Sama yake da kowace buqata,
hasali ma shine tushen dukkan abinda ake da lalurar samu.
Kuma Allah, Ya fitar da
zuriyar Baniy-Adama daga tsatsonsu suna masu yin shaida a kansu cewa lallai
Allah shine: UBANGIJINSU WANDA YA MALLAKE SU, kuma lallai BABU ABIN BAUTAWA DA
GASKIYA SAI SHI. Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma a lokacin da
Ubangijinka ya xauki alkawari daga Xiyan Adam, daga bayayyakinsu, a zuriyarsu,
kuma ya shaidar da su a kan rayukansu, (Ya ce:) Shin ba Ni ne Ubangijinku ba?
Suka ce: Na'am, Mun yi shaida !" [A'araaf: 172].
Kuma lallai ne, ita zuciya an halitta ta ne don ta so
Allah, saboda Allah ya qagi bayinSa a kan sonSa da saninSa, "Halittar Allah, da
ya halitta Mutane a kanta, Babu musanyawa ga halittar Allah" [Rum: 30]. Ma'ana: Kada
ku musanya halittar Allah, ta hanyar canzawa Mutane abinda aka halicce su a
kai. Kuma wannan "Fixrar" ita ce: Miqaqqen addini (haniyfiyyah) wanda
Allah ya halitta bayinSa akanta.
Kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
"Kowani abin
haifuwa ana haifansa ne akan fixirar Musulunci".
Kuma Annabi ya bayyana cewa
Shexanun cikin Aljanu da Mutane suna yin aikin jirkitata (fixrah), Allah yana
faxa cikin HADISIN QUDUSIY: "Lallai ne Ni na halicci bayina akan
miqaqqen addini gabaxayansu, kuma lallai ne Su Shexanu sun zo zuwa gare su, sai
suka juya su daga addininsu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma kowani Musulmi an umurce shi da ya riqa kula da
fixirarsa ta addini; domin wacce ta karkace ta koma kan asalinta, waxanda suke
da imani kuma su qara samun qarfin imani.
Kuma lallai Allah ya tsayar da ayoyinSa don su zamo dalilai
masu nuna RububiyyarSa da UluhiyyarSa, Kuma da ruwan Teku zai kasance tawadar
alqaluman da za a rubuta kalmomin Allah da hukuncinSa da ayoyinSa, waxanda suke
nuni zuwa gare shi, to, da sai ruwan Tekun ya qare, gabanin a gama rubuta
hakan, kai koda an zo da wasu Tekunan waxanda za su riqa qara shi, ana yin
rubutun da su, to da kalmomin Allah basu qare ba "Ka ce: Da teku ya
kasance tawada ne ga rubutun kalmomin Ubangijina, lallai da ruwan tekun ya qare
gabanin kalmomin Ubangijina su qare, kuma ko da mun zo da qarin kwatankwacinsa
don qarawa"
[Kahf: 109].
Su kuma Manzanni gabaxayansu,
an turo su ne don tabbatar da abinda ya kimsu cikin fixirah, da qara kammala shi.
Kuma lallai ne Allah ya
kafa hujja ga waxanda ba su kaxaita shi (cikin UluhiyyarSa) ba, da abinda suka
tabbatar masa na RububiyyarSa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane! Ku
bauta wa Ubangijinku, wanda ya halicce ku, ku da waxanda suka zo gabaninku,
domin ku samu taqawa (da kariya daga shiga azaba) " [Baqarah: 21].
Kuma lallai tauhidin
"Rububiyyah"; ta hanyar kaxaita Allah cikin aiyukanSa dalili ne na
kaxaitakar Allah cikin cancantar bautar bayinsa (wato: Uluhiyyah). Kuma lallai "tauhidin Rububiyyah"
ginshiqi ne daga cikin ginshiqan "imani", kuma xaya ne daga cikin nau'ukan
tauhidi "guda uku", wanda saboda shi Allah (ta'alah) ya halicci bayi.
Kuma yin shirka a cikin wannan tauhidin (na Rububiyya)
shine nau'in shirkar da ta fi girma kuma tafi muni. Kuma babu wanda zai yi
katovara a cikin "Uluhiyyah" sai wanda be baiwa (Tauhidin) Rububiyyah
haqqinsa ba.
Kuma lallai Allah yana da "kamala" a cikin
dukkan "sifofinSa, da aiyukanSa". Kuma yana daga cikin SifofinSa –جل شأنه- Sifar RUBUBIYYAH; kuma bashi da abokin
tarayya a cikinta, kamar yadda bashi da abokin tarayya a cikin
"Uluhiyyah", Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka ce: Shin wanin
Allah nake neman ya zama Ubangiji, alhali shine Ubangijin dukkan komai" [An'am: 164].
Shi kuma HAQIQANIN (tauhidin) RUBUBIYYAH shine:
Kaxaitakar Allah (تعالى) cikin halitta, da
mallaka, da azurtawa, da juya lamari, saboda shi Allah (maxaukaki) shine:
Mahalicci; babu wani mahalicci a tare da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Shin akwai wani
Mahalicci baicin Allah; …" [Faxir: 3].
Kuma shine: Mai kyautata
halittar Sammai da qassai; Wanda ya yi halitta sa'an nan ya daidaita abin
halittar, Ya kuma kyautata dukkan abinda ya halitta, kuma Mai yawan halitta
Masani. "Wannan shine halittar Allah, Sai ku nuna mini Menene waxannan da ba
Shi ba suka halitta?"
[Luqman: 11].
Kuma kamar yadda ya fari
halitta, to Allah zai sake dawo da su ranar qiyamah, kuma sake dawo da su Shine
yafi sauqi a gare shi.
Kuma kowani abin bauta koma-bayan Allah bai cancanci
bauta ba, saboda baya iya yin halitta, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne waxanda kuke bauta musu baicin
Allah ba za su halitta quda ba, ko da sun taru gare shi" [Hajj: 73].
Shi kuma Ubangiji ya
cancanci a yi masa bauta, saboda shi yake halitta, Allah (تعالى) yana cewa: "Shin, Wanda yake
yin halitta yana yin kama da wanda baya yin halitta? Shin ba za ku wa'aztu ba" [Nahl: 17].
Kuma kowani bawa yana
tabbatar da cewa shi halitta ne, Allah kuma shine Wanda ya halicce shi, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma lallai idan ka
tambaye su, wa ya halitta su, Za su ce: Allah ne" [Zukhruf: 87].
Kuma Allah maxaukaki shine MAMALLAKI, kuma mulki nasa ne,
"Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, Waxanda kuke roqo
waninSa, ba su mallakar ko fatar jikin dabino" [Faxir: 13]. Kuma shi ya Mallaki
dukkan halittarSa, "Nasa ne duk abinda yake cikin sammai da qasa" [Baqarah: 255].
Kuma dukkan halittu suna
masu qanqan-da-kai da tasbihi wa Allah, "Sammai bakwai da qasa da waxanda
suke a cikinsu suna yi masa tasbihi. Kuma babu wani abu face yana tasbihi, gami
da gode Masa, Saidai kuma ba ku fahimtar tasbihinsu" [Isra'i: 44].
Hasali ma, dukkaninsu; da
daskararrensu da masu rai daga cikinsu, suna yin sujjada wa Allah, "Kuma ga Allah ne
wanda ke cikin sammai da qasa suke yin sujjada, cikin so da qi" [Ra'ad: 15].
Allah shine shugaba (As-Sayyid), wanda bashi da abokin
tarayya, Dukkan halittu kuma bayinSa ne, "Dukan wanda ke a
cikin sammai da qasa, face zai je wa Mai rahama (Allah) yana bawa" [Maryam: 93].
Yana da MULKI cikakke
dawwamamme, Mamallakin duniya da ranar sakamako, kuma a ranar lahira Allah zai
bayyana, Sai ya ce:
"Mulki ga wa yake a
yau?"
[Gafir: 16]. Sai kuma ya masa wa kansa da faxinSa:
"Yana ga Allah
Makaxaici Mai tilastawa" [Gafir: 16].
Allah maxaukaki ya kevanta da JUJJUYA SHA'ANONIN
HALITTUNSA kuma mallakarSa, saboda lamura dukkansu a hannunSa suke Shi kaxai, "Ku saurara! Na
(Allah ne) halittu da Umurni" [A'araf: 54].
(Allah) yana yin umurni, yana kuma hani, yana halitta,
yana azurtawa, yana bayarwa yana hanawa, yana dankwafarwa yana xaukakawa, yana
buwayarwa kuma yana qasqantarwa, yana
rayarwa yana kashe wa, "Yana shigar da dare akan yini, kuma yana
shigar da yini akan dare, kuma ya hore rana da wata" [Zumar: 5]. "(Allah) yana fitar da
rayayye daga matacce, yana kuma fitar da matacce daga rayayye, kuma yana raya
qasa bayan mutuwarta"
[Rum: 19]. Kuma yana fitar da abinda yake a voye, a cikin sammai da qasa.
Kuma dukkan halittu suna qarqashin rinjayenSa da
zartarwarSa, kuma zukatun bayi da makwarkwaxarsu suna hannunSa, kuma linzamin
lamura yana qulle ne da hukuntawarSa da qaddarawarSa, kuma al'amari nasa ne
gabanin komai da bayansa, Yana tsaye akan kowace rai game da abinda take
aikatawa, kuma sama da qasa suna tsaye ne da umurninSa, "Kuma yana riqe da
sama domin kada ta rikito akan qasa, face da izininSa" [Hajj: 65 ]. Kuma
lallai Allah "Yana riqe da sammai da qasa domin kada su gushe" [Faxir: 41].
Kuma dukkan halittun cikin sammai da qasa suna roqonSa,
"Kowani yini Shi, yana cikin wani sha'ani (da aiki)" [Rahman: 29].
Kuma yana daga
"SHA'ANONINSA" kasancewar yana gafarta zunubai, yana kuma shiryar da
vatacce, yana yaye baqin ciki, yana kwaranye vacin rai, yana gyara karaya, yana
kuma wadata faqiri, yana amsa addu'ar mabuqata, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ba mu kasance masu gafala; mu kyale
halittu ba"
[Muminuna: 17].
UmurninSa na bibiye wa-juna, NufinSa kuma shike zartuwa, don
haka; Duk abinda ya nufa sai ya kasance, abinda bai nufa ba kuma baya
kasancewa, yana halitta abinda ya so, yana kuma aikata abinda ya nufa, kuma
al'amarinSa ya kasance abin qaddarawa tabbatacce, Babu mai hana abinda ya
bayar, kuma babu mai bayar da abinda ya hana, kuma babu mai cin gyaran
hukuncinSa, kuma babu mai mayar da abinda ya hukunta, kuma babu mai tunkuxe
nufinSa, kuma babu mai canza kalmominSa, Ya qaddara abubuwan da ya qaddara wa
halittu gabanin halittar sammai da qasa da shekaru dubu hamsin.
Kuma da halittu za su
tattara akan wani abu da Allah bai rubuta shi ba, domin su sanya ya zama mai
kasancewa, to, ba za su samu iko akan haka ba, Da kuma za su taru akan abinda
zai kasance don su hana aukuwarsa, to, ba za su sami iko akansa ba. Kuma da
al'umma zata haxu akan cutar da wani bawa wanda kuma Allah bai nufe shi da
cutuwa ba, to, ba za su iya cutar da shi ba. Idan kuma da al'ummar za su haxu
akan su amfanar da shi, Sai kuma Allah bai yi izinin ya samu amfani ba, to, baza su amfane shi ba. Babu mai mayar da
azabarSa idan ta zo sauka, babu kuma mai tunkuxe ta idan ta auku. Yana shiryar
da wanda ya nufa –da falalarSa-, yana kuma vatar da wanda ya nufa da adalcinSa.
umurninSa da zance suke kasancewa, kuma ababen aiki ne da su. Idan ya nufi
kasancewar wani abu kawai ya kan ce da shi: Ya kasance, sai ya kasance. Kuma
cikin dukkan aiyukanSa babu wani da zai tambaye shi "Ba a tambayarSa ga
abin da yake aikatawa, alhali su ana tambayarsu" [Anbiya'i: 23].
MaganarSa itace mafi kyan zance, KalmominSa basu da farko,
kuma basa qarewa, "Kuma da dai duk abinda ke cikin qasa duka; na itatuwa
(bishiyoyi) ya zama alqaluma, kuma teku yana yi masa tawada, a bayansa da
waxansu tekuna bakwai, to lallai da kalmomin Allah ba su qare ba" [Luqman: 27].
Kuma iliminSa (maxaukakin sarki) ya yalwaci kowani abu, saboda
Allah ya san duk abinda ya kasance, da abinda bai kasance ba, da abinda ba zai
kasance ba, kuma ya san abinda halittu za su aikata shi a gaba-gare su, da duk
abinda suka aikata shi, "Kuma ya san abinda yake tudu da teku, kuma
wani ganye ba ya faxuwa face ya san shi" [An'am: 59].
Kuma daidai da kwayar zarra bata motsawa a cikin duniya face da
izininSa, Babu wani abu da yake vuya a gare shi a cikin qasa ko a cikin sama,
kuma ya san abinda yake vuya a gare mu na abubuwan da suke aukuwa da al'ummai,
da kuma abinda ya bayyana, kuma ya san abinda rayuka ke waswasinsa, da abinda
zukata suke voyewa da sirrace-sirrace. Kuma ya san abinda mace take xauke da
shi a cikinta, da abinda qasa take fitarwa, "da abinda yake
sauka daga sama, da abinda yake hawa zuwa gare ta" [Saba'i, 2, da
Hadid, 4 ].
"Gwargwadon zarra
bata nisanta daga gare shi, a cikin sammai, da cikin qasa" [Saba'i, 3 ].
Kuma "Mabuxan gaibi (a
wurinsa suke) babu wanda ya ke saninsu face shi" [An'am: 59].
Ilimin dukkan halittu
gabaxayansa kamar kwayar ruwa ne guda xaya daga tekun ilimimnSa, "Kuma basa kewayawa
da kome daga iliminSa, face da abinda ya so" [Baqarah: 255].
(Wata-rana) wani tsuntsu ya
xauki ruwan teku da bakinsa, Sai Alkhadir yace wa Musa (عليهما السلام):
"Ilimina da
iliminka be tauye komai daga ilimin
Allah ba, sai kamar yadda wannan tsuntsun ya tauye daga wannan kogin", Muslim ya ruwaito
shi.
(Allah) yana jin kowani sauti a duniya, ya faxa dangane
da kansa: "Ina ji kuma ina gani" [Xaha: 46].
jinSa ya game dukkan
sautuka; ba su sassavawa a gare shi, kuma ba su cakuxa, "Ko suna zaton
lallai Mu, ba mu jin abinda suke asirtawa da ganawarsu" [Zukhruf: 80].
Wata mata ta zo izuwa ga
Annabi (صلى الله عليه وسلم) alhalin tana qarar
mijinta, A'isha kuma tana vangaren wannan xakin, Ta ce:
"Lallai ne
Ni ina jin magananta, shashinsa kuma yana vuya a gare ni, Allah kuma a saman
sammai guda bakwai ya ji maganarta, ban farga ba sai ga (Mala'ika) Jibrilu (عليه السلام)
ya sauka da wannan ayar: "Haqiqa Allah ya ji zancen matar da take maka jayayya game da
mijinta, kuma tana kai qara ga Allah, Shi kuma Allah yana jin muhawararku" [Mujadilah: 1]".
Kuma duk wani motsi a bayan duniya (Allah) yana ganinsa;
saboda ganinSa ya game dukkan ababen gani, yana ganin motsawan tururuwa baqa
akan kurman dutse a cikin dare mai duhu. Kuma aiyukan bayi a cikin duhun dare
basa vuya a gare shi "Wanda yake ganinka lokacin da kake tashi tsayuwar dare
* da jujjuyawarka a cikin masu sujjada" [Shu'ara'i: 218-219].
Kuma dukkan aiyukan bayi
Ubangijinmu yana jiransu a madakata, "Kuma lallai ne Ubangijinka yana nan
a madakata"
[Fajr: 14].
Kuma saboda kasancewar halittun duka halittarSa ce, to,
hukunci nasa ne; shi kaxai, Allah (تعالى) yana cewa:
"Babu hukunci face
na Allah"
[Yusuf: 40]. Kuma hukunce-hukuncenSa da haddodinSa da shari'oinSa sune mafi
alherin hukunce-hukunce, Kuma babu wanda ya fi shi kyan hukunci "Kuma shine mafi
alherin mahukunta"
[Yusuf: 80].
Baya karkatar da hukunci,
kuma baya zaluntar kowa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ashe, ba Allah ba
ne mafi kyawon hukuncin masu hukunci?" [Attin: 8].
Yana yin hukunci "babu mai bincike ga
hukuncinSa, kuma shi Mai gaggawar hisabi ne" [Ra'ad: 41].
Amma dangane da rahamar Allah kuma, to, lallai haqiqa babu
mai rahama irin tasa, (Allah) ya yaba wa kansa da faxinSa:
"Shine mafi rahamar
masu rahama"
[Yusuf: 64]. Kuma shine "Mafi alherin masu tausayi" [Muminuna: 109 ].
Yafi tausayawa fiye da Uwa
ga Xanta, saboda wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ga wata mata cikin waxanda aka kamo; fursunan yaqi, tana ta
neman xanta, Sai kuwa ta samu yaron, ta xauke shi, ta manna shi da jikin
cikinta, ta shayar da shi, Sai yace wa SahabbanSa: "Shin kuna
ganin wannan matar zata iya jefa xanta a cikin wuta? Sai suka ce: A'a! Sai
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): To, lallai ne Allah yafi tsananin
tausayi fiye da wannan matar ga xanta", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Wannan kuma saboda Allah
(maxaukaki) ya halitta rahama guda xari, Sai ya saukar da guda xaya, wanda da
ita ne, halittu a bayan qasa suke tausaya wa junansu, Sai kuma ya riqe yanki
casa'in da tara a wurinSa. Kuma rahamarSa ta game kowani abu, Kuma Mala'ikun da
suke xauke da al'arshi da waxanda suke kewaye da shi suna cewa:
"Ya Ubangijinmu, ka
yalwaci kowani abu da rahama, da kuma ilimi" [Gafir: 7 ].
Kuma rahamarSa a miqe take,
har zuwa ga lahira.
(Allah) Mai karimci ne da kyauta, babu wanda yafi shi
kyautayi, yana son kyautatawa da baiwa ga halittunSa, kuma yana azurta su daga
samansu da kuma qasansu, "Ka ce: Wanene yake azurta ku daga sama da
qasa?"
[Yunus: 31 ].
FalalarSa tana da girma,
kuma taskokinSa ba su qarewa, kuma hannayenSa a cike suke; Aikin ciyarwa ba su
tauye su, suna yin baiwa da dare da yini, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"shin Ba ku
ga abinda ya ciyar ba ne tun lokacin da ya halicci sammai da qasa, kuma yin
hakan be tauye abinda yake hannunSa ba".
Baya mayar da addu'ar da bayi suka yi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina
suka tambaye ka game da Ni, to, lallai ne Ni Makusanci, Ina amsa addu'ar mai
addu'a idan ya roqe ni" [Baqarah: 186].
Babu wata buqata da take
masa girman ya bayar da ita, koda kuwa dukkan bayi; Na farkonsu da na
qarshensu, da Mutanensu da aljanunsu za su haxu akan qasa xaya, Sai su roqe
shi, Sai ya baiwa kowani xaya daga cikinsu abinda ya roqa, to hakan ba zai
tauye abinda yake wurinSa ba, sai kamar yadda allura idan aka shigar da ita
teku zata tauye shi. Kuma ya xauki xawainiyar baiwa kowace halitta arziqinta,
daga cikin mutane da aljanu, musulminsu da kafirinsu, da dukkan dabbobi, saboda
"Babu wata dabba ga qasa face akan Allah ne arziqinta yake" [Hud: 6].
Kuma baiwar Allah ya kan yi
ta, ba tare da yin gori ba. Shine mafi alherin masu azurtawa. Ya buxe qofofin
baiwanSa ga bayinSa; sai ya hore tekuna, ya kuma gudanar da koguna, ya kuma
malalar da arziqi, ya baiwa bayinSa arziqi mai yawa alhalin ba su roqe shi ba,
haka kuma ya ba su daga kowani abu suka roqe shi. Kuma yana bijiro wa bayinSa
lamarin su riqa roqonsa, a inda yake cewa:
"Wanene zai
roqe Ni, sai in bashi".
Dukkan alkhairi daga
wurinSa ne, "Kuma duk abinda ke tare da ku; na ni'ima to daga Allah ne" [Nahl: 53].
Kuma ya isar zuwa ga kowace
halitta arziqinta; Sai ya azurta xan tayi alhalin yana cikin cikin
mahaifiyarsa, da tururuwa a cikin raminta, da kuma tsuntsu a cikin sararin samaniya,
da kifaye a cikin gulbin ruwa, "Kuma, dayawa daga dabbobi basa iya xaukar
abincinsu, Allah yake ciyar da su, tare da ku" [Ankabut: 60].
Mai karimci ne, baya yarda
a xaukaka buqatu izuwa ga waninSa, kuma duk wanda ya qi ya roqe shi, to, sai ya
yi fushi akansa. Kuma lallai marashin rabo shine wanda yake rataya kwaxayinsa
izuwa ga wanin Allah. Kuma babu wanda yafi tsananin haquri akan cutarwar da
yake ji, fiye da Allah; (halittu) suna yin shirka a gare shi, kuma suna jingina
masa haifar xa, amma shi kuma yana basu lafiya yana azurta su.
Kuma yana yin farin ciki da tuban bawanSa, da yafi
tsanani, fiye da mutumin da yake cikin dokar daji, sai abun hawansa ya gudu ya
bar shi, har ya xebe tsammani, ya zo jikin wata bishiya, sai ya kwanta a
qarqashin inuwarta, bayan ya xebe tsammani daga samun abin hawansa, Yana nan
cikin wannan halin sai ga abin hawansa a tsaye a wurinsa, Sai yace, saboda
tsananin farin ciki: "Ya Allah kai ne bawa na, Ni kuma nine
Ubangijinka, wato: yayi kure saboda tsananin farin ciki".
Ya datar –da falalarSa da karimcinSa- ma'abuta yi masa
biyayya, kuma ya basu lada bayan dacen ya musu, Shine: Mai yin godiya; wanda
yake bada lada akan abu kaxan, ya kuma gwavava sakamako akan aiki mai yawa; mai
kyau guda xaya ya ninninka ta har sau goma, ko ninkin ba-ninkiya masu yawa.
Kuma ya yi tanadi wa bayinSa a gidan aljannah da abinda ido bata tava gani ba,
kunne shima bai tava jin labarinsa ba, kuma bai tava xarsuwa a cikin zuciyar
wani Mutum ba, Kuma ya ce:
"Lallai haqiqa
wannan arzurtawarmu ce, bata qarewa" [Sad: 54].
Kuma Ubangiji ba zai gushe
ba, yana neman bayinSa su yarda da abinda yake basu; ya riqa cewa:
"Shin kun
yarda? Sai su ce: Me yasa ba za mu yarda ba, alhalin ka bamu abinda ba ka baiwa
wani daga cikin halittunka ba, Sai yace: Ni zan baku abinda yafi hakan falala?
Sai su ce: Ya Ubangiji, Menene kuma yafi hakan falala? Sai yace: Zan saukar da
yardata akanku; ba zan tava fishi da ku ba; har abada", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Mawadaci ne da zatinSa, Abun nufi ne; Wanda halittu ke
nufansa cikin buqatunsu, kuma Shugaba ne, Cikakke, don haka bashi da tunbi (balle
yaci abinci), "Bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba * Kuma babu wani da ya kasance
kwatankwacinSa"
[Ikhlas: 3-4].
Kuma babu wani abin bautawa
tare da shi, "kuma bai riqi mata ba, kuma bai riqi xa ba" [Jinn: 3]. "Kuma abokin tarayya
bai kasance a gare shi ba, cikin mulkinSa, kuma wani majivinci daga qasqanci
bai kasance a gare shi ba" [Isra'i: 111].
Kuma babu wani abin bautawa
tare da shi.
Ba a yi masa xa'a da biyayya
sai da falalarSa.
Ba a kuma sava masa sai da
iliminSa.
Mawadaci ne ga barin
halittunSa.
Kuma kowani abu yana tsaye
ne, da Shi, kuma (kowani abu) mabuqaci ne izuwa gare shi, "Ya ku mutane,
lallai ku ne mabuqata zuwa ga Allah, Shi kuma Allah shine Mawadaci Abin godiya" [Faxir: 15].
Biyayyar masu biyayya bata
masa amfani, haka savon masu savo baya cutar da shi, "Idan kuka kafirta, to,
lallai ne Allah wadatacce ne daga barinku" [Zumar: 7 ].
Kuma da mutane da aljanu za
su kasance akan zuciyar wanda yafi taqawa daga cikinsu, to da hakan bai qara
komai akan mulkin Allah ba. Kuma da za su kasance akan zuciyar wanda yafi
fajirci daga cikinsu, to da hakan bai tauye komai akan mulkin Allah ba. Kuma
bayi ba za su kai ga amfanar da shi ba, balle su amfane shi. Kuma ba za su kai
ga cutar da shi ba, balle su cutar da
shi.
Yana tsaye da kanSa, Mai
girma ne Babba, Mai qarfi, Buwaya itace kwarjallenSa, Girma kuma mayafinSa, Mai
mulki ne bashi da abokin tarayya, Makaxaici ne bashi da kishiya, Mawadaci ne;
bashi da mataimaki, Maxaukaki ne; bashi da abin buga misali, "Kowani abu mai
halaka ne, baicin fiskarSa" [Qasas: 88: ].
Kuma kowani mulki mai
gushewa ne in banda mulkinSa, kuma kowace falala zata yanke in banda falalarSa,
yana kewaye da kowani abu, amma babu wani abu da yake kewaye da shi, "Gannai basa iya
riskarsa, Shi kuma yana riskar gannai" [An'am: 103 ].
"Kuma Qasa duka
damqarSa ce, a ranar qiyama, kuma sammai ababen naxewa ne ga damanSa" [Zumar: 67 ].
"Zai
sanya sammai a ranar qiyama akan yatsa xaya, qasa akan yatsa xaya, duwatsu akan
yatsa xaya, bishiyoyi akan yatsa xaya, da ruwa da turvaya akan yatsa xaya,
sauran halittun kuma akan yatsa xaya, Sa'an nan sai ya jijjiga su, ya ce: Ni ne
Mai mulki"
Bukhariy ya ruwaito shi.
Ba a yin magiya da shi a wajen wani daga cikin
halittunSa, kuma babu wani da zai yi ceto a wurinSa face da izininSa, savanin
halittunSa; waxanda ake iya samun cetonsa ba tare da izininsu ga manema ceton
nasu ba.
Kujerar mulki (Kursiyyun Allah)
-wanda wurin ajiye qafofi ne- ta yalwaci sammai da qasa (a girma).
Amma shi kuma kursiyyun
idan aka kwatanta girmansa da na al'arshi ba a bakin komai yake ba, sai kamar
zoben qarfe da aka jefa shi cikin wani babban fili, kuma shi al'arshi shine
yafi dukkan halittu girma, Mala'ikun da suke xauke da shi, tsakanin fatar
kunnen xayansu da kafaxarsa kamar tafiyan shekaru xari bakwai ne.
Allah kuma, Ya daidaita a
saman al'arshinsa, kamar yadda ya dace da matsayinSa, kuma lallai ne shi ya
wadata daga al'arshin, da duk abinda ke qasa da shi (na halittu).
"Kuma sammai suna
kusa su tsattsage, saboda shi" [Maryam: 90]. Ma'ana: Su tsattsage saboda
tsoron Allah.
Kuma idan ya furta wahayi
sai wata girgiza ko tsawa mai tsanani ta kama sammai, Sai kuma ma'abuta sammai
su suma, su faxi suna masu sujjada.
Rayayye ne, Tsayayye;
Gyangyaxi baya kama shi haka kuma barci, "kuma baya
dacewa a gare shi ya yi barci, yana saukar da adalci kuma yana xaga shi, Ana
xagawa zuwa gare shi aiyukan dare gabanin na yini, da kuma aiyukan yinin
gabanin na dare, Abinda ya hana ganinSa (shamaki) shine haske, da zai yaye shi
da sai hasken fiskarSa ya qona dukkan abinda ganinSa ya kai zuwa gare
shi".
Shi ne Na
farko; babu wani abu gabaninSa, shine Na qarshe; babu wani abu a bayanSa, kuma
shine Maxaukaki; babu wani abu a samanSa, kuma shine voyayye; babu komai da
yake hana saninSa".
Mai iko ne akan kowani abu, babu abinda yafi shi tsananin
qarfi, Mutanen ADAWA sun ruxu da qarfin da suke da shi "Sai suka ce: Wanene
ya mafi tsananin qarfi daga gare mu? Ashe ba su gani cewa lallai Allahn da ya
halitta su, shine mafi qarfi daga gare su" [Fussilat: 15].
Kuma, Allah yafi qarfin
iko, akan halittarSa, fiye da ikon da shugaba yake da shi akan bawansa. Ya faxa
–dangane da kanSa-:
"Lallai ne qarfi ga
Allah yake gabaxaya"
[baqarah: 165].
Babu wani abu da yake
gagaranSa a cikin qasa da sama; ya halitta sammai da qasa a cikin yini guda
shida, kuma wata gajiya bata tava shi ba.
Duk wanda Allah ya taimake
shi to babu mai rinjayarsa, kuma babu dabara (ko kauce wa savo) babu kuma qarfi
ga halittu sai da Allah.
lamarinSa kamar walqawar
gani, ko kuma mafi kusa.
Kuma yana da rundunonin da
babu wanda ya sansu sai Shi kaxai.
Kuma idan lamarin duniya ya
zo qarewa to sai ya girgiza qasa girgizawa, ya kuma dake ta; rushewa, ya kuma
tafiyar da duwatsu tafiyarwa, ya kuma sheqe su sheqewa.
Kuma da busa xaya ne
halittu za su firgita, ida kuma aka sake wata sai su mutu, Idan kuma aka yi ta
uku sai su tashi zuwa filin da za a tattara su.
Kuma idan (Ubangiji) zai
sauka saboda yin hukunci sai sama ta kekkece, sai ta kasance lugu-lugu kamar
man shafawa.
Mai tsarkaka ne Mai tsarki,
wanda ya kuvuta da kowani aibi da naqasa, Yana da mafi xaukaka daga jinsin
kamala, daga cika da kyau kuma, (Allah) yana da mafi haske, bashi da kishiya,
kuma bashi da misali, bashi da takwara, kuma bashi da tsara, "Babu wani abu da
yake tamkarSa, kuma shi ne Mai ji Mai gani" [Shura: 11].
BAYAN
HAKA, YA KU MUSULMAI!
Shin ba zai zama wajibi akanmu mu SO Ubangijinmu wanda waxannan
sune sifofinSa da aiyukanSa ba?
Kuma mu yi GODIYA a gare
shi, muna masu kevance shi da ibada da IKHLASI?!
Kuma duk wanda ya so Allah,
ya kuma yi bauta a gare shi, to Sai Allah ya so shi, kuma duk wanda ya so Allah
sai ya riqa aikin kusanci zuwa gare shi, yana mai qanqan da-kai a gare shi,
yana miqa wuya, tare da xebe kewa da shi, da samun nitsuwa, ya kuma yi fatan
samun ladanSa, ya kuma ji tsoron uqubarSa, Sai kuma ya riqa sauke buqatunsa
zuwa gare shi, yana yin tawakkali akansa (dogara ga Allah).
Kuma duk wanda ya yi godiya wa Allah, ya kuma yawaita
yabo a gare shi, to, sai ya xaukaka;
Saboda babu wani da yafi Allah son yabo, saboda haka ne ya yaba wa kanSa.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Ba su girmama Allah
yadda ya cancanci a girmama shi ba, lallai ne Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [Hajj: 74].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA. …
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Yabo kuma nasa ne
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Duk wanda ya yi shirka ga Allah, ya kuma roqi waninSa,
daga cikin halittu da matattu to, haqiqa ya tauye haqqin Allah; Ubangijin
talikai, kuma ya munana zato a gare shi, kuma ya daidaita waninSa tare da shi.
Shi kuma shirka yana ruguza
dukkan aiyuka, kuma ba a gafarta wa ma'abucinsa, kuma (sahibinsa) ba zai shiga
aljannah ba, kuma Shi a cikin wuta yana daga masu tabbata. Kuma shirka shine
mafi munin canjin da yake tava fixrah, kuma shine mafi girman fasadi da varna a
bayan qasa, kuma shine asali ko tushen kowani bala'i, kuma matattarar kowace
cuta, cutarwarsa yana da girma, kuma hatsarinsa yana da muni.
Suma dangogin savo
mabanbanta shu'umcinsu yana da girma, saboda suna haxuwa ga bawa; su halaka
shi, kuma su shamakance tsakanin bawa da zuciyarsa.
Kuma gwargwadon yadda
zunubi ke yin qaranta a ido (n bawa), to, gwargwadon yadda yake yin girma a
wajen Allah Kenan.
Kuma kada ka yi dubi zuwa
ga qarantar savo, A'a, (ana son) ka yi dubu zuwa ga girma (Allan) da ka sava
masa.
Sannan ku sani; Lallai
Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa
Sai yace, a cikin mafi kyan
abinda aka saukar:
"Lallai Allah da
Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah! Ka mayar da su izuwa ga addininka,
mayarwa mai kyau.
Ya Allah! Ka sanya qasashensu su zama garurrukan
aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi!
Ya Allah! Ka tabbatar da rundumarmu, Ya Allah! Ka
tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka daidaita jifansu, kuma ka azurta
su da yi don kai (ikhlasi), Ya Ma'abucin girma da Baiwa.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu, kuma ka sanya aikinsa ya
zama cikin yardarka. Kuma ka datar da sauran jagororin Musulmai wajen yin aiki
da littafinka, da hukunta shari'arka, Ya ma'abucin girma da yin baiwa.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya,
ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah! Lallai ne Mu muna roqonka ilimi mai
amfani da kuma aiki mai kyau.
Ya Allah! Lallai kai ne abin bautawa; Babu wani
abin bauta face kai, Kai ne Mawadaci, mu kuma mune Faqirai, Ka saukar mana da
ruwan sama kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka
bamu ruwan sama!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!!
"Ya Ubangijinmu lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan
har baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, za mu kasance daga cikin masu
hasara"
[A'araf: 23].
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci,
kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da
fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment