"IDDAH" DA TAKABA A MUSULUNCI
(العدد والإحداد في الشريعة الإسلامية)
ABUBAKAR HAMZA
Domin
bayanin waxannan; wato: "iddah" da
takaba zai kyautu mu dubi mas'aloli da dama, kamar haka:
Mas'alar
farko: Bayani akan "iddah" da dalilai da suka shar'anta ta, da kuma
hikimar yinta:
1-
"Iddah"
a harshen larabci suna ne na "masdari" daga Kalmar "adda,
ya'uddu, addan" wanda aka ciro shi daga "adadi da qididdiga";
saboda "iddah" ta qunshi: adadi qididdigagge
na: jini ko tsarki, da na watanni.
A shari'ar Musulunci kuma "iddah": suna ne na wani
lokaci aiyananne da mace za ta zauna a cikinsa; da nufin bauta ma Allah
mabuwayi da xaukaka, ko don alhinin rasuwar miji, ko don ta tabbatar cewa ba
komai a mahaifarta.
"Iddah" tana kasancewa ne bayan rasuwa ko shika,
kuma don su.
2-
Dalilai
da suka shar'anta yin "iddah": Dalilan
da suka wajabta yin "iddah" sun zo ne a cikin alqur'ani
da sunna, da kuma "ijma'i";
Amma daga alqur'ani; to akwai faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭼ البقرة:
٢٢٨
Ma'ana: (Matan da aka riga aka sake su na zaunar da kansu na
tsawon tsarki uku) [Baqarah: 228]. Da kuma saboda faxinsa:
ﭽ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨﯩ ﯪ ﯫ
ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﭼ الطلاق: ٤
Ma'ana: (Waxanda suka xebe
tsammani daga haila daga cikin matanku, iddansu wata uku ne, haka suma yara
mata da basu fara haila ba. Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shine su
sauke cikinsu) [Xalaq: 4]. Da kuma saboda faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ البقرة:
٢٣٤
Ma'ana: (Waxanda suke rasuwa daga
cikinku, sai su bar mata; zasu zauna –a matsayin takaba- na watanni huxu
da kwana goma) [Baqarah: 234].
Amma dalilin "iddah" daga sunna kuma: Shine hadisin
Almiswar xan Makhramah -t- cewa:
"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ
–رضي الله عنها- نُفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِـلَيَالٍ ، فَجَاءَتِ
النَّبِيَّ r ،
Ma'ana: (Lallai Subai'ah al-aslamiyyah –t- ta haifu
bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi –r- tana
neman izininsa kan ta yi aure, sai ya yi mata izini, sai ta yi aure). Da wassun
waxannan
na daga dalilai.
3-
Hikimar
da ta sanya aka shar'anta "iddah":
Hikimar hakan itace: Domin tabbatar da cewa babu xa
a cikin mahaifar mace; domin kada a samu cakuxar
nasaba. Yana kuma daga cikin hikimar: Bada dama ga mijin da yayi shika ya
waiwaici kansa idan yayi nadama; wannan kuma idan shikan da ya aiwatar ana iya
kome a cikinsa (na xaya da na biyu ne). haka kuma: Lura da haqqin
ciki dana jariri; idan har an rabu, ko an mutu an bar mace da ciki.
Mas'ala
ta biyu: Nau'ukan "iddah":
Iddodin
da mata ke yi sun kasu kashi biyu: (1) Iddan mutuwa (takaba) (2)
Iddan rabuwar aure.
Na
farko: Iddan mutuwa (takaba): Wannan kuma shine: idda da take wajaba
ga matar da mijinta ya rasu ya barta; shi kuma halin wannan matar baya fita
daga xayan halaye guda biyu:
-
Ko wannan
matar ta zama tana da ciki.
-
Ko kuma ta
zama bata da ciki.
Idan har ta kasance tana da ciki: To iddarta zai qare
ne in ta haife abinda ke cikinta; koda kuwa bayan wassu 'yan-dakiqoqi
ne daga rasuwar mijinta; wannan kuma saboda faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﭼ الطلاق:
٤
Ma'ana: (Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shine su
sauke cikinsu) [Xalaq: 4]. Da kuma saboda hadisin Almiswar xan
Makhramata -t-
cewa:
"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ
–رضي الله عنها- نُـفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِلَيَالٍ ، فَجَاءَتِ
النَّبِيَّ r ،
Ma'ana: (Lallai Subai'ah al-aslamiyyah –t- ta haifu
bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi –r- tana
neman izininsa kan ta yi aure, sai yayi mata izini, sai kuma ta yi aure).
Idan kuma ta kasance bata xauke
da wani ciki: To iddanta zai kasance ne tsawon watanni huxu
da kwanaki goma, lallai matar da mijinta ya mutu ya barta ba ciki dole zata yi
wannan takabar; sawa'un ya sadu da ita, ko kuma bai tava
saduwa da ita ba; saboda gamewan faxin
Allah ta'alah:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ
ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭼ البقرة: ٢٣٤
Ma'ana: (Waxanda suke rasuwa daga
cikinku, sai su bar matansu; zasu zauna –a matsayin takaba- na watanni huxu
da kwanaki goma. Idan har suka isa i zuwa ga ajalinsa na takaba to babu laifi a
gare ku cikin abinda suka aikata a cikin kayukansu na komawa ga ado; da
kyautatawa, Allah dangane da abinda kuke aikatawa mai bada labari ne) [Baqarah:
234]. Kuma babu wani dalili da ya zo da kevance
wata mata daga hakan.
Na biyu: Iddar
rabuwar aure: Wannan kuma itace iddar da take wajaba akan matar da ta rabu da
mijinta; ko don saboda raba auren, ko don shika, ko "khul'in" da ya
mata bayan saduwa, lamarin irin wannan ba ya fita daga xayan
waxannan
halaye:
o Ko mijinta ya rabu da ita alhalin tana da ciki.
o Ko babu ciki.
o Ko ya zama bata ganin haila; ko saboda qan-qanta,
ko ta xebe tsammaninsa; saboda tsufa.
In har ta kasance tana da ciki: To iddarta zata qare
ne idan ta haife cikinta; wannan kuma saboda gamewar faxin
Allah ta'alah:
ﭽﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﭼ الطلاق:
٤
Ma'ana: (Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shi ne su
sauke cikinsu) [Xalaq: 4].
In kuma bata da ciki, alhalin kuma wannan matar tana cikin
masu yin haila: To iddarta zata kammalu ne idan ta yi tsarki guda uku, bayan
rabuwansu; wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ
ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﭼ البقرة: ٢٢٨
Ma'ana: (Mata da aka sake suna zaunar da kansu na tsawon
tsarki guda uku, kuma baya halatta a gare su da su voye
abinda Allah ya halitta a cikin mahaifarsu; matuqar
sun yi imani da Allah da kuma ranar qarshe)
[Baqarah:
228].
In kuma ta kasance bata ganin haila; saboda kasancewarta mai
kananan shekaru, ko kuma ta xebe tsammanin
ganinsa saboda yawan shekarunta: To iddarta zai qare
ne idan watanni uku suka shige bayan rabuwansu da mijinta; wannan kuma saboda faxinsa
maxaukaki:
ﭽ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨﯩ ﭼ الطلاق: ٤
Ma'ana: (Waxanda suka xebe
tsammani daga haila daga cikin matanku, iddarsu watanni uku ne, haka suma yara
mata da basu fara haila ba) [Xalaq: 4].
Hukuncin
matar da aka sake ta gabanin saduwa da ita:
Idan miji ya rabu
da matarsa; ko don saboda raba aurensu da aka yi, ko kuma shika gabanin saduwa
da ita: to a nan babu wani idda akanta; wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﭼ الأحزاب:
٤٩
Ma'ana:
(Yaku waxanda suka yi imani idan har kuka auri mata muminai, sa'annan sai
kuka sake su gabanin ku sadu da su, to baku da wata idda da zaku nemi su yi,
sai ku jiyar da su daxi, sai ku sake su shika mai kyau) [Ahzaab: 49].
A
wannan hukunci (rashin idda ga wacce aka rabu da ita alhalin ba a sadu da ita
ba) babu banbancin tsakanin mata muminai da ahlul-kitaabi, kamar yadda maluma
suka yi ittifaqi. Shi kuma ambaton "mata
muminai" a cikin ayar da aka yi don rinjayar da su ne akan sauran.
Mas'ala
ta uku: Haqqoqin da suke cikin idda, da
abubuwan da suke rataya akansa:
1- Iddan shika: Idan
mace ta kasance tana idda ne ga mijinta iddah ta shika; to halinta baya fita
daga xayan lamari guda biyu:
o Shikanta ya kasance na kome ne.
o Shikan da aka yi mata ya zama ba na kome ba ne (ba'inu).
Na farko: Matar
da take idda daga shika da ake iya kome a cikinsa: Wannan matar
hukunce-hukuncen da suke tafe suna rataya akan iddarta:
1. Wajabcin
bata gurin zama tare da mijinta, matuqar
babu wani abinda zai hana haka a shari'ance.
2. Wajabci ciyar da ita,
da tufatar da ita, da makamantansu.
3. Kuma wajibi ne akanta
ta lazimci wajen zamanta; ya zama bata rabuwa da shi, sai dai idan da larura;
wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭼ الطلاق:
٦
Ma'ana: (Ku zaunar da su a wurin da kuke zaune gwargwadon
samunku) [Xalaq: 6]. Da kuma saboda faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭼ الطلاق:
١
Ma'ana: (Kada ku fitar da su daga xakunansu,
kada suma su fita sai sun zo da wata alfasha mabayyaniya) [Xalaq:
1].
4. Haramun ne akanta ta riqa
bijiro da kanta ga wassu mazaje don su nemi aurenta; saboda kasancewarta
killacacciya ga mijinta wannan, domin tana xauke
da hukunci matarsa; saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﭼ البقرة:
٢٢٨
Ma'ana: (Kuma mazajensu su suka fi cancantar dawo da su a
cikin iddar, in har sun nufi yin sulhu) [Baqarah:
228].
Na
biyu: idan kuma ya zama an yi mata shikan da ba kome a cikinsa ne:
To a nan halinta ba zai fita daga lamura guda biyu ba:
o Ta zamto tana da ciki.
o Ko ta zamto ba ta da ciki.
Na xaya:
In ta zama tana da ciki, to a nan hukunce-hukunce da suke
tafe suna rataya kan sake ta:
1. Wajabcin bada wajen zama a gare ta daga mijinta; wannan kuma
saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙﭚ ﭛ ﭜ ﭝﭞ ﭟ ﭠ
ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭼ الطلاق:
١
Ma'ana: (Ya kai wannan annabi idan zaku sake mata to ku sake
su a yanayin da za su fara iddarsu, kuma ku qididdige
iddah, ku ji tsoron Allah Ubangijinku; kada ku fitar da su daga dakunansu, kada
kuma suma su fita, sai dai sun zo da wata alfasha mabayyaniya) [Xalaq:
1].
2. Ciyarwa: Wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭼ الطلاق:
٦
Ma'ana: (Kuma idan suka kasance ma'abota ciki to sai ku riqa
ciyar da su, har su haife cikinsu) [Xalaq:
6].
3. Lazimtar xakinta da take takaba,
da kuma rashin fita daga cikinsa, sai dai in akwai wata buqata;
Allah ta'alah yana cewa:
ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭼ الطلاق:
١
Ma'ana: (Kada ku fitar dasu daga xakunansu,
kada suma su fita) [Xalaq: 1]. Amma dalilin halaccin fitanta kuma daga xakinta;
a lokacin buqata shine: Hadisin Jabir -t-, yace:
"طُلِّقَتْ خَالَتِي، فَأَرَادَتْ
أَنْ تَجُدَّ نَخْلَهَا ، فَزَجَرَهَا رَجُلٌ أَنْ تَخْرُجَ ، فَـأَتَتِ النَّبِيَّ
r، فَقَالَ:
Ma'ana: (Lallai an sake "umata" Sai ta so ta fita
don yanke 'ya'yan dabinonta, sai wani mutum ya tsawatar mata kan fita, sai ta
zo wajen annabi –r-
sai yace: Babu laifi, ta fita ta tsinke 'ya'yan dabinonta; saboda ta yiwu kiyi sadaka,
ko ki aikata wani abu mai kyau da sashi).
Na biyu: Idan
kuma bata da ciki, to a nan shima duk abinda ya tabbata ga mai ciki yana
tabbata a bata su, sai dai ciyarwa, da abinda ke biye masa na tufatarwa; waxannan
kam basa tabbata a gare ta; saboda hadisin Faximah
bnt Qais
- رضي الله عنها-
a lokacin da mijinta ya sake ta sauran shikan nan guda xaya
da ya rage mata, sai Annabi (r)
yace:
Ma'ana: (Ba ki da haqqin
ciyarwa akansa, sai dai in kina da ciki).
2- Iddar matar da mijinta ya rasu ya barta:
Lallai hukunce-hukuncen da suke tafe na lazimtar matar da
take iddar rasuwar mijinta:
1. Wajibi ne akanta ta yi takaba (idda) a gidan da mijinta ya
rasu a ciki, alhalin tana cikinsa, koda kuwa gidan haya ne ko na aro; wannan
kuma saboda faxinsa (r)
ga Furai'ah bnt Malik - رضي الله عنها-:
Ma'ana: (Ki zauna a gidan da labarin mutuwarsa ya zo miki
kina zaune a cikinsa). Kuma baya halatta ta fita daga wannan gidan; ta koma
wani gidan na daban sai idan da akwai uzuri; kamar ta ji tsoron wata matsala in
har ta ci gaba da wanzuwa a cikin wannan gidan, ko kuma a fitar da ita da qarfi,
ko makamancin haka; to a nan ya halatta ta koma gidan da ta so; saboda wannan
larurar.
2. Lazimtar gidanta da take takaba a cikinsa, da kuma haramcin
fita daga cikinsa ko yawo, sai dai in da buqatar
hakan. In kuma da buqatar to yana halatta a gare ta, ta fita daga gidanta ne da rana;
ba da daddare ba; saboda dare lokaci ne da aka fi zaton varna
a cikinsa, don haka baya halatta ta fita a cikinsa sai inda "larura";
savanin
rana; saboda shi lokaci ne na fita biyan buqatu.
3. Wajibi ne akanta ta dena yin ado na tsawon watannin iddah.
Kamar yadda bayani mai faxi zai zo akansa lokacin bayani akan (Ihdaad).
4. Bata da haqqin ciyarwa; saboda
aure na qarewa da aukuwar mutuwa.
Mas'ala
ta huxu: Zaman takaba (Al-ihdaad):
Menene
zaman takaba? da dalilai da suka shar'anta shi:
1- Bayani a kan "ihdaad":
"Ihdaad" a harshen larabci shine
"hanuwa", Ana cewa: "Haa-ddun, Muhiddun" wa mace idan ta
bar amfani da kayan ado, da tirare.
A shari'ar Musulunci kuma: Shine mace ta bar yin ado, da fesa
ko shafa turare, da wassun wannan na daga abubuwan da zasu sanya a yi kwaxayinta,
ya kuma jawo hankali zuwa ga saduwa da ita.
2- Dalilai da suka shar'anta yin "ihdaad":
Yin zaman takaba (Ihdaad) wajibi ne akan matar da mijinta ya
rasu; saboda hadisin Ummu-habibah - رضي الله عنها- lallai Annabi (r) yace:
"لاَ يَحِلُّ لامْرَأَةٍ
تُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَاليَوْمِ الآخِرِ أَنْ تُحِدَّ عَلَى مَـيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثِ
لَيَالٍ، إِلا عَلَى زَوْجٍ
Ma'ana: (Baya halatta ga wata mace da ta yi imani da Allah da
kuma ranar karshe, da ta yi takaba –nisantar ado- ga rasuwar wani mutum na fiye
da kwanaki uku, sai dai ga miji; wata huxu da
kwanaki goma).
Da kuma hadisin Ummu-axiyyah
al-ansaariyyah - رضي الله عنها-
tace:
"كُنَّا نُنْهَى أَنْ نُحِدَّ
عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثٍ إِلا عَلَى زَوْجٍ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ، وَلاَ
نَـكْتَحِلَ
Ma'ana: (Mun kasance ana hana mu muyi takaba ga wani na fiye
da kwanaki uku, sai dai miji; watanni huxu da
kwanaki goma, bama sanya kwalli, bama shafa tirare, bama sanya tufa da aka
rina, sai dai tufan gwado –da aka rina zanensa gabanin a xinka
shi-…).
Matar
da take zaman "Ihdadi" da takaba yana wajaba akanta:
- Ta
nisanci kayan ado da tirare, tare da hanuwa daga sanya tufofi ma'abota
launuka masu qayatarwa,
haka kuma ba za ta sanya tozali ba, ba za ta sanya sarkar ado na zinare ko
azurfa ko wassunsu ba, kamar yadda baya halatta ta sanya wani abu na kayan
da aka rina, saboda hadisin Ummu-salamah - رضي الله عنها-,
daga Annabi (r)
yace:
"الْمُتَوَفَّى عَنْهَا
لا تَلْبَسُ الْمُعَصْفَرَ مِنَ الثِّيَابِ، وَلا الْمُمَشَّقَةَ، وَلا الْحُلِيَّ
وَلا تَخْتَضِبُ وَلا تَكْتَحِلُ"([8]).
Ma'ana: (Macen da mijinta ya rasu a kwanakin takaba bata
sanya kayan da aka rina su da "asfar –launin xorawa-",
da wanda aka rina da "mishqu –wani launi ne
ja", da kayan awarwaro, haka kuma bata yin lalle, ko sanya tozali). Da
kuma saboda hadisin Ummu-axiyyah al-ansaariyyah - رضي الله عنها-, wanda ba da
jimawa ba ya gabata.
- Wajibi
ne ta lazimci gidanta da take idda ko takaba a cikinsa, kuma ba zata fita
daga cikinsa ba sai dai idan akwai buqatar haka; saboda hadisin
Furai'ah bnt Malik - رضي الله عنها-
wanda ambatonsa ya gabata.
Aslm.Ina hukucin yin hidimar fitar TAKABA a musulunci?
ReplyDelete