2016/03/17

HUXUBAR MASALLACIN ANNABI, ta 09/ JUMADAH AL'AKHIRAH /1437H Daidai da 18 /MARIS /2016M, Kan addu'a








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله علي وسلم)
 JUMA'A, 09/JUMADAH AL'AKHIRAH/1437H
Daidai da 18 /MARIS /2016m




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin qasa da sama, Mai amsa addu'a, Wanda ke fararwa bayinSa da ni'imomi, Kuma yake yaye munana da bala'oi,
Ina yabon UbangijiNa, kuma ina godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare Shi, ina neman gafararSa, Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,  Ma'abucin buwaya da girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne; wanda aka turo shi da shrai'a cikakkiya, mai haske.
Ya Allah! Ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa masu rigaye zuwa ga aiyukan biyayya ababen godiya.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, iyakar kiyayewa, saboda duk wanda yayi riqo da taqawa to sai Allah ya haxa masa alkhairi a duniyarsa da lahirarsa. Wanda kuma ya nisanci taqawa to sai ya tave a qarshen lamuransa, ko da kuwa duniyarsa ta fiskance shi.

Ya ku Musulmai!!
Lallai haqiqa Allah (تعالى) ya qaddara sabbuban alkhairori, da samun rabo a duniya da lahira, Kuma ya qaddara sabbuban sharrukan duniya da lahira, saboda haka; Duk wanda ya yi riqo da sabbuban alkhairi da rabauta to sai Allah ya lamunce masa samun gyaruwan rayuwarsa ta duniya, A lahira kuma zai kasance yana da kyakkyawan makoma, yana mai dawwama cikin aljannonin ni'imah, tare da rabauta da samun yardar Ubangiji Mai rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba komai ba ne sakamakon kyautatawa face kyautatawa" [Suratur Rahman: 60].
            Wanda kuma yayi aiki da sabbuban sharri, to sai ya girbe sakamakon aikinsa, a rayuwarsa ta duniya, da kuma bayan mutuwa. Allah yana cewa:
 "…Wanda ya aikata mummunan aiki za a saka masa da shi, Kuma ba zai sami wani masoyi ba, baicin Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba" [Suratun Nisa'i: 123].

            Ku saurara!
            [Yin addu'a] Lallai yana daga cikin sabbuban gyaruwa da kawo gyara, da rabauta, da yawaitar samuwan alkhairori, da tunkuxe fitintinun da suke sauka, da uqubobi, da xauke musibun da ake cikinsu, da baqin ciki: YIN ADDU'A da ikhlasi, da zuciya da take halarce, tare da yin naci, Saboda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka yana son a riqa yin addu'a, kuma yayi umurni da shi. Shi kuma addu'a yana yin amfani akan abinda ya sauka, da wanda bai sauka ba (na musibobi), Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roqe ni zan amsa muku, Lallai waxannan da suke kangarewa daga bauta mini, za su shiga jahannama qasqantattu" [Ghafir: 60].
            Kuma addu'a shine Bauta, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annu'uman xan Bashir (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), Ya ce:
"Addu'a shine bauta (ibada)", Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu wani abu wanda yafi matsayi a wurin Allah fiye da yin addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
            Kuma Addu'a abun kwaxaitarwa ne akansa a kowani lokaci, kuma Shi ibada ne wanda Allah ya ke bada sakayya akansa da mafi girman sakamako, Kuma addu'a yana tabbatar da ababen nema gabaxayansu; kevantattu, da waxanda albarkarsu take gamewa, na addini, da na duniya, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa.
Kuma saboda amfanin da addu'a yake da su masu girma Allah ta'alah ya shar'anta yinsa a cikin ibadodin da aka farlanta, a matsayin wajibi, ko a matsayin mustahabbi, saboda rahamar Ubangijinmu da karramawa da yin baiwa, domin bayi muyi aiki da wannan sababin; da Allah ya sanar da mu Shi. Kuma da Allah bai sanar da mu yin addu'a ba, to da lallai kwakwalenmu basu shiryu izuwa gare shi ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma aka ilmantar da ku, abinda Ku da ubanninku baku sani ba" [Suratul An'am: 91].
Don haka; Yabo da godiya na Allah ne, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma kamar yadda Ubangiji ya yarda.

            Kuma buqatar yin addu'a a ko-da-yaushe ta kan yi tsanani, Musamman a wannan zamanin, Wanda fitintinu suka bayyana, kuma suka yawaita, tare da saukar bala'oi da annoba masu halakarwa, da kuma saukar ababen baqanta rai, ga Musulmai, da bayyanar qungiyoyin bidi'a; waxannan da suke rarrabe kan Musulmai, kuma suke halatta zubar da katangaggen jini, da kwasar dukiya ta haramun, suke kuma kyamar ilimi da ma'abutansa, kuma suke yin fatawa da jahilci, da kuma vata. A lokacin da maqiyan Musulunci suke taruwa don qoqarin murqushe shi, suke kuma shisshirya makirce-makirce akan masu imani, (A ta xaya vangaren) kuma su Musulman suke tavar da junansu, suke rarrabewa, suke savani, a tsakaninsu. A kuma lokacin da dangogin cutuwa suka riski kowanne daga cikin xaixaikun Musulman da aka fitar da su, daga gidajensu, da zalunci, kuma cutuka suka shafe su, samun buqatunsu ya zame musu da wahala, ,,,,,, Lallai a irin waxannan halaye masu tsanani; waxanda Musulmai suke quna da wutansu a garurrukan da fitintinu suka kunnuBuqatuwar yin addu'a tana qara yawaita.

            Kuma lallai haqiqa Allah yayi yabo akan waxanda suke roqonSa, suke kuma qanqan-da kai izuwa gare shi Mabuwayi da xaukaka; IDAN har manyan lamura  ko tsanani suka sauka akansu, Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayenMu guda biyu (Adamu da Hauwa'u عليهما السلام):
 "Suka ce: Ya Ubangijinmu! lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana kayi rahama a gare mu ba, to lallai zamu kasance daga cikin masu hasara" [Suratul A'araf: 23]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya cikin dukiya da rayuka da 'ya'yan itatuwa, Kuma ka yi bishara ga masu haquri * Waxannan da idan musiba ta same su, sai su ce: Lallai Mu daga Allah muke, kuma lallai Mu zuwa gare shi masu komawa ne * Waxannan akansu akwai albarku daga Ubangijinsu, da wata rahama, Kuma waxannan sune shiryayyu" [Suratul Baqarah: 155].
kuma Allah mabuwayi da xaukaka ya faxa dangane da annabi Yunus (عليه السلام):
"Kuma annabi Yunus (wanda kifi ya haxiye) sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu quntata masa ba, sai yayi kira a cikin duffai, cewa: babu abin bautawa face kai, tsarki ya tabbata a gare ka, lallai Ni kasance daga azzalumai" [Suratul Anbiya'i: 87].
Hadisi ya zo daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Addu'ar annabi Yunus wanda kifi ya haxiye, a lokacin da ya roqi Allah alhalin yana cikin kifi, babu wani Mutum Musulmai da zai yi roqo da shi, face Allah ya amsa masa addu'ah", Ahmad ya ruwaito shi, da Attirmiziy, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.

            Kuma a yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kirayi qabilar Saqifu zuwa ga Musulunci, sai suka qi karvar da'awarsa, sannan suka jefe shi da duwatsu, har qafofinsa guda biyu suka fitar da jini, sai ya roqi Ubangijinsa yana mai cewa:
"Ya Allah ina koka raunin qarfina zuwa gare ka, da qarancin dabarata, da qasqancin da nake da shi a wurin Mutane, Ya mafi rahamar masu rahama; izuwa ga Wa; zaka jivintar da Ni; zuwa ga maqiyin da yake xaure min fiska, ko kuma izuwa ga wani maqiyin da ka mallaka masa lamarina, Idan baka yi fushi da ni, ba; to bani da damuwa, Saidai kuma  lafiyarka ita tafi yalwa a gare ni. Ina neman tsari da hasken fiskarka wanda ya haskaka duffai, kuma lamarin duniya da lahira suka gyaru da shi, kada fushinka ya sauka akaina, Komawa naka ne, har sai ka yarda, Babu dabara babu qarfi face daga wurinka".

            Da yin addu'oi ne, ake fiskantar tsanani da ababen vacin rai, na abubuwan da Mutum ba zai iya tunkuxe maka su ba; saboda Yazo daga Sauban (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu abinda ke tunkuxe qaddara sai addu'a, kuma babu abinda yake qara tsawon rai sai xa'a ga iyaye da sada zumunci, Kuma lallai Mutum ana haramta masa arziqi saboda wani zunubin da ya aikata", Ibnu-Hibbana ya rawaito shi a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), yace:
"Lallai addu'a yana amfani daga abinda ya sauka, da kuma wanda bai sauka ba, Ya ku bayin Allah; Sai ku lazimci yin addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim.
An ruwaito daga Abu-Hurairata (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah (تعالى) yana cewa:
"Ni, Ina yadda bawana ke zatona, kuma Ni ina tare da shi idan ya roqe ne", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma lallai wannan lada da falala ya kai yadda ya kai (A ce, Allah yana tare da bawanSa; idan ya roqe shi!).

            Kamar yadda Allah yayi zargi ga waxanda  suke barin roqon Allah ko addu'a a lokacin da uqubobi suka sauka, ko bayyanar fitintinu; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun kama su, da azaba, saidai basu qanqan da kai ga Ubangijinsu ba, kuma ba sa yin tawali'u" [Suratul Muminuna: 76].
Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yace:
"Kuma lallai mun aika zuwa ga al'ummai daga gabaninka, sai muka kama su da tsanani da cuta, tsammaninsu za su qanqan da kai * To, don me a lokacin da tsananinmu ya je musu basu yi tawali'u ba, Sai zukatansu suka qaiqashe, kuma Shexan ya qawata musu abinda suka kasance suke aikatawa" [Suratul An'am: 42-43]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma ba mu aika wani annabi a cikin wata alqarya (sai suka qaryata shi) ba, face mun kama mutanenta da azaba, da cuta, tsammaninsu za su qasqantar da kai" [Suratul A'araf: 94].

            Kuma lallai qin yin addu'a, a lokacin tsanani dogewa ne, akan zunubai, da kuma raina lamarin kamu ko damqar Ubangiji mai tsanani, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai damqar Ubangijinka mai tsanani ce" [Suratul Buruj: 12]. Da kuma faxinSa Allah mabuwayi da xaukaka:
"Kuma kamar wancan ne, kamun Ubangijinka, idan ya kama alqaryoyi alhali kuwa suna masu zalunci, Lallai kamunSa mai raxaxi ne, mai tsanani" [Suratu Hud: 102].

            Kuma lallai shi addu'a sababi ne mai girma na sauqar alkhairori da albarkoki, da tunkuxe sharri, ko xauke shi, daga mai yin addu'ar.
            Kuma yin addu'a shine sababin da ya fi qarfi domin fita daga sharrin da ya auku, da mummunan yanayin da ake ciki, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma kai ne mafi rahamar masu tausayi * Sai muka amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na cuta, Kuma muka kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama daga gare mu, da tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne ya ke amsawa mai buqata, idan ya roqe shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun Naqml: 62]. Ai, Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma Allah (سبحانه) yace:
"Ka ce Wane ne yake tsirar da ku daga duffan tudu da ruwa, kuna roqonsa bisa ga qanqan da kai, kuma a voye; Lallai ne idan ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu kasance masu godiya * Ka ce: Allah ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da kuma dukan baqin ciki, Sa'annan sai ku kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul An'am: 62-63].

            Shi Musulmi wajibi ne akansa ya riqa addu'a da kwaxayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabaxaya, yana mai xaga buqatunsa zuwa ga UbangijinSa gabaxayansu, ya riqa roqonSa kowani abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kuvuta daga aukawa wuta, Allah (تعالى) yana faxa a cikin hadisin Qudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma shine: Ku roqe ni shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara. Ya Allah lallai ne Mu muna roqonka shiriya da tufa da abinci da gafara, kuma muna roqonka, da ka ba mu daga falalarka mai girma.
Kuma ya zo a cikin hadisi cewa:
"Xayanku ya riqa roqon UbangijinSa koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da gishirin abincinsa".

          Kuma dayawa, addu'a ta kan canza abinda yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga alheri, ko kuma daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi Ibrahim (عليه الصلاة والسلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo, daga gare su, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karantar da su wannan littafin da hikima, kuma yana tsarkake su, lallai ne kai, kai ne Mabuwayi Mai hikima" [Suratul Baqara: 129]. An ruwaito daga Abu-Umamah (رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene farkon lamarinka? Sai yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma busharar annabi Isah, Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga gare ta, wanda har ya haskaka benayen qasar Sham", Ahmad ya ruwaito shi. 
Kuma saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima; Musulmai suka kasance cikin alheri madawwami, kai, dukkan duniya itama wannan addu'ar ta shafe su.
            Haka, addu'ar da annabi Nuhu (عليه الصلاة والسلام) itama ta kasance alheri ga muminai masu tauhidi, sharri ga mushirkai.
            Haka addu'ar da annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) zai yi; shi da sahabbansa waxanda za a killace su a jikin dutsen AXXUR, a qarshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai, sa'annan halaka ga YAJUJU da MAJUJU, waxanda suke kamar farar da za ta game dukkan qasa (ko duniya) da sharri, saboda sune mafi sharrin halitta, masu tsananin varna da qetare iyaka da qirman kai,  saboda Ya zo a cikin hadisin Annawas xan Sam'an (رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU AD-DAJJAL:
"Sai Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi, waxanda wani bashi da ikon yaqarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen Ax-xur. Sai Allah ya tayar da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga kowani tudun qasa; Sai na farkonsu su shige ta jikin wani qaramin teku na xabariya, sai su shanye dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na qarshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To, sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa; har sai ya kasance kan Saniya yafi alheri ga xayansu, fiye da dinari xari ga xayanku a yau, to daga nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu, kamar mutuwar rai guda xaya. Sa'annan sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su sauka kan qasa, saidai kuma ba za su sami daidai da taqi xaya ba, a doron qasa face gawar Ja'ajuju da ma'ajuju da warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya turo da wassu tsuntsaye, waxanda suke kama da wuyan raqumi, sai su tattare su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma addu'ar da Annabi (صلى الله عليه وسلم) shugaban halitta,  yayi; shi da sahabbansa, a lokacin yaqin badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har abada, kuma tavewa ce, ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke neman agajin Ubangijiku sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan taimaka muku da dubu daga cikin Mala'iku, a jere" [Suratul Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen yin addu'ar a Badar, har sai da mayafinsa ya faxi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce:  Yadda kake yin magiya wa Ubangijinka, ya isa, ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda ya yi maka alkawari. Sai yace: Ina maka albishir ya kai Abubakrin! Saboda ga nan Mala'ika Jibrilu (عليه السلام) yana sauka yana jagorantar Mala'iku ,,,,, . Kuma Mala'iku ba su tava yin yaqi tare da wani ba'annabe ba, gabaninSa. An kevance shi da wannan saboda cikar falalarSa (عليه السلام), da qarfin yaqininSa, da kuma ikhlasin sahabbanSa (ضي الله عنهم).  

            Kuma lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da rugujewar varna, yana daga nasiha ga Allah da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran Mutane.

            Kuma babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai qaurace masa face wanda ya tozarta rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na haqqin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin Musulmai ba to baya cikinsu".

            Kuma da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idodin addu'a da albarkokinsa, da alherorinsa, da natijojinsa, daxaxa, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan yayi tsayi. Saidai abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
           
            Kuma lallai addu'a yana da SHARRUXA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharruxan addu'a: Cin abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه):
"Ka kyautata abincinka; sai a amsa addu'arka".

Kuma yana daga cikin sharruxansa: Riqo da Sunnah, da kuma amsawa Allah (تعالى); ta hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar abubuwan da yayi hani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da ni, tsammaninsu za su shiryu" [Suratul Baqara:186]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma yana amsawa waxannan da suka yi imani,  suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma yana qara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26]. Amma Mutumin da aka zalunce shi kuma to shi kam ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa kafiri ne, ko xan bidi'a.

            Kuma yana daga cikin sharruxansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da yin naci, wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roqi Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kuwa mushirkai sun qi" [Suratul gafir: 15].
Ya zo cikin hadisi cewa, "Allah baya karvar addu'a daga zuciya rafkananniya mai wargi".
           
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Kada ya yi, addu'a da savo, ko yanke zumunta, kuma kada ya qetare iyaka, cikin addu'a.
            Kuma yana daga cikin sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالى) da sunayensa mafiya kyau, da sifofinsa maxaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum yana cewa:
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka , da shaidawata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, Makaxaici, Wanda ake nufi da biyan buqata, wanda bai haifu ba, kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da wani wanda yake daidai da shi, Sai yace: Lallai ne, ka roqi Allah da sunanSa da yafi girma; wanda idan aka roqe shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka yi addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya ruwaito shi, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله عنه).
An kuma ruwaito daga Fadalah (رضي الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai wani Mutum ya shigo yayi sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ka gafarta mini, ka yi mini rahama, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah, Idan ka zo sallah; sai ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abinda ya cancance shi, San'annan sai ka yi min salati, Sa'annan sai ka roqi Allah", Ahmad ya ruwaito shi, da Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A cikin wani hadisin kuma:
"Lallai addu'a yana rataye tsakanin sama da qasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".

            Kuma yana daga cikin ladduban addu'a da sharruxan karvarsa: Kada ya yi gaggawar amsawa, A'a yayi haquri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a amsa wa xayanku matuqar bai yi gaggawa ba; yace: Na roqa, na roqa, amma ba a amsa mini ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita shi), a tare da shi akwai amsawa, saboda ya zo a cikin wani hadisi, cewa: "Babu wani Musulmi a bayan qasa, wanda zai roqi Allah da wata addu'a, face Allah ya bashi ita, ko kuma ya tunkuxe masa wani mummunan kwatankwacinta, matuqar bai roqi sabo, ko yanke zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita! Sai yace: Allah zai fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadisi ne, hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar Abiy-Sa'id, sa'annan ya yi qari a cikinsa: Ko kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.

            Kuma ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
Wace addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace: "Ta qarshe dare, da bayan sallolin farilla", Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah. Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu yana sauka zuwa ga saman duniya, a cikin xaya bisu ukun dare na qarshe; Sai ya ce: Wa zai yi roqo sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai nemi gafarata sai na gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga hadisin Abu-hurairah.

            Da kuma tsakanin kiran sallah da yin iqamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya zo cikin hadisi cewa:
"Lokacin da bawa yafi kasancewa kusa da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku yawaita addu'a", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.

            Da kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukar ruwa, da hali na buqatuwa, da bayan khatamar alqur'ani gabaxaya, da bayan yin sadaka.

            Ka yi mamakin girman rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga Allah (تعالى); yana roqonSa, yana fatanSa, yana kuma dogara akanSa, yana neman taimakonSa, ,,,,,, .
            Da kuma tavewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake roqon kabari, ko yake neman agaji daga Annabawa (عليهم الصلاة والسلام), da waliyyai, ko yake roqonsu koma bayan Allah (تعالى), ko yake xaga buqatunsa zuwa ga wani Mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali; saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام) sun zo ne, don kiran Mutane, cewa su keve Allah (تعالى) da yin roqo a gare shi, sa'annan su kaxaita shi da bauta shi kaxai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu riqa yin aiki irin nasu, sa'annan mu so, su, kuma aka hane mu, kan roqonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai masallatai na Allah ne, kada ku roqi wani tare da Allah"[suratul Jinn: 18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce: Kawai ni, ina roqon Ubangijina ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn: 20].       
Kuma wanda baya halarce, da matattu babu wani daga cikinsu da yake amsa addu'a; saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah Mabuwayi da xaukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kiran gaskiya nasa ne, Waxanda kuma suke roqa baicinsa basa amsa musu da komai, face kamar mai shumfuxa tafukansa zuwa ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face a cikin vata" [Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Babu wanda ya fi vata fiye da wanda ke roqon wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har ranar qiyama, alhalin (waxanda ake roqan) sun gafala da kiran masu kiransu * Kuma idan aka tattara mutane, za su kasance abokan gaba a gare su, kuma za su kasance masu kafircewa ga bautan da suka yi a gare su" [Ahqaf: 5-6].
Kuma Allah (تعالى) yace, alhalin yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar da dare a cikin yini, kuma yana shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da rana; kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma waxanda kuke roqa waninSa basa mallakar ko da fatar kwallon dabino * Idan kuka roqe su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun ji to ba za su amsa muku ba, kuma a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani", [Faxir: 13-14].
            Kuma lallai Allah bai yi izinin a roqi waninSa ba, duk irin kusancin da yake da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku; lallai ne duk wanda ya yi shirka da Allah to, lallai Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa itace wuta, kuma babu wassu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72]. Kuma Allah yace:
"Kuma ba ya yin umurni a gare ku da ku riqi Mala'iku da Annabawa ababen Bauta, Shin zai umurce ku da kafirci ne, a bayan kun riga kun kasance musulmai" [Ali-imrana: 80].
Ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu alhalin yana roqon wani koma bayan Allah ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله عنه).

            Ya kai Musulmi!!
            Wannan shine littafin Allah, da hadisan ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A shine BAUTA, kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka shine kawai ya kevanta da addu'a, ba a yinsa sai ga Allah maxaukaki, kuma duk wanda ya haxa wani da Allah a cikin addu'a to wannan mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin vata da shirka; saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da sababin taqalidanci, da bin mutane vatattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin wancan, shine mafi zama alheri ga liyafa, ko kuma itaciyar zaqummi * Lallai Mu mun sanya ta fitina ga azzalumai * Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita daga asalin wutar jahima * Fudarta, kai kace kayukan shexanu ne * Lallai su haqiqa masu ci ne daga gare ta, sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta * Sa'annan suna da wani gauraye a kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai makomarsu izuwa ga wutar jahimu take * Lallai su, sun iske Ubanninsu suna vatattu *  Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa" [As-safat: 62-70].
Kuma Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku roqi Ubangijinku da qanqan da kai, da kuma a voye, Lallai ne shi, baya son masu qetare iyaka, * Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyaruwanta. Kuma ko roqe Shi cikin tsoro da tsammani, lallai ne rahamar Allah a kusa take daga masu kyautatawa" [A'araf: 55-56].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA, KUMA YA AMFANAR DA NI DA KU DA ABINDA KE CIKINSA NA AYOYI DA WA'AZI MAI HIKIMA, INA FAXAN MAGANATA WANNAN, KUMA INA NEMAN GAFARAR ALLA WA NI DA KU, SAI KU NEMI GAFARARSA, LALLAI SHI MAI GAFARA NE MAI RAHAMA.

HUXUBA TA BIYU
            Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin qai, Mabuwayi Mai hikima, Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi maxaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukakin da Yafi xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne Zavavve.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu taqawa.
Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku aikyukanku, sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan komawa izuwa ga makoma.

Ya ku Bayin Allah!
            Ku kasance, masu bayyanar da kwaxayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roqo a gare shi (da yawaitawa); saboda Duk wanda ya roqi Allah baya tavewa, wanda kuma ya yi fatan samun Allah ba a hana shi.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ni, Ina yadda bawana ke zatona". Kuma an karvo daga Umar (رضي الله عنه) lallai shi yana cewa:
"Lallai ne ni bana xaukar damuwar amsa addu'a, kawai ina xaukar damuwar aiwatar da addu'an ne, saboda matuqar an mini ilhamar yin addu'ar, to lallai Allah ya lamunce min batun amsawar".
Kuma kowani Mutum yana da buqatun da suke sabuntuwa, da ababen nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roqi UbangijinSa, duk abinda ya san alheri ne, kuma ya riqa addu'a ga Musulmai waxanda ake zaluntarsu saboda addininsu, kuma ake fitar da su daga gidaddajinsu. Ya kuma nemi tsarin Allah duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roqo shine neman samun yardar Allah, da kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abinda ake neman tsari daga gare shi, shine wuta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar roqon abinda ya dame shi, daga wajen UbangijinSa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci, Abun godiya, Mai yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-qarshenku, da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya roqe ni, sai in bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin ruwan teku", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa: "Duk wanda baya roqon Allah, to zai yi fushi da shi".
            Kuma mustahabbi ne, Musulmi ya riqi addu'oi masu gamewa, waxanda suka zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), kamar faxinsa maxaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].  
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka aljanna da abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".

            Ya ku bayin Allah!
             "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin amintarwa" [Ahzab: 56].

            Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Duk wanda yayi salati xaya a gare ni, to Allah zai yi masa guda goma.
            Sai ku yi salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Kuma ka yi musu sallama; tsiratarwa mai yawa.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya, da waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai,
            Ya Allah ! ka fahimtar da mu addini, Ya Allah ka bamu fahimta da sauran Musulmai a cikin addini.
            Ya Allah ! ka ilmantar da mu abinda zai amfane mu, kuma ka amfanar da mu da abinda ka ilmantar da mu, ya Ubangijin talikai!
Ya Allah !
Ya Allah!
Ya Allah! .
Ya Allah!
Ya Allah!
Ya Allah!  
            Ya Allah! Ka yi salati
            Ya Allah! Ka yi
     "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...