FILM XIN / / /
BIKIN BUXE AIYUKAN FAXAXA
MASALLACIN
HARAMIN MAKKAH, NA GWAMNATIN SAUDIYYA, A KARO NA UKU
(فيلم تدشين التوسعة السعودية الثالثة للحرم
المكي)
AIKIN FAXAXA HARAMIN MAKKAH
MAXAUKAKI
DAGA/
HADIMIN HARAMI BIYU MAXAUKAKA;
SARKI
ABDULLAHI XAN ABDUL'AZIZ ALU-SA'UD
(توسعة
خادم الحرمين الشريفين الملك عبد الله بن عبد العزيز آل سعود للحرم المكي الشريف)
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
"Kawai, Mai raya
masallatan Allah shi ne, Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya tsayar
da sallah, ya bada zakkah, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah, To, akwai
tsammanin Waxannan su kasance daga shiryayyu" [Tauba: 18].
BIKIN BUXE AIYUKAN FAXAXA MASALLACIN HARAMIN
MAKKAH, DAGA DAULAR SAUDIYYA A KARO NA UKU,
RAMADHAN, 1436H
Masallaci
Mai Alfarma (المسجد الحرام)
shine alqiblar Musulmai, kuma wurin da zukatansu suke karkata zuwa gare shi,
kuma suke so.
Harami, Kulawar
Allah, wajen bashi aminci da kula, tana kewaye shi, kuma ana tattaro kayan
marmari izuwa gare shi daga kowani wuri.
Kuma Dauloli da Masarautu (mabanbanta) sun yi
tseren samun tsira wajen aikata aiyukan raya shi (da gina shi) da kuma yin
hidima ga masu ziyartarsa (Mahajjata) a tsawon tarihi.
Kuma a lokacin da Allah ya
qaddara kafuwar Daular Saudiyya -mai albarka- Sai ta rabauta da samun fifiko
wajen yin hidima wa Harami Guda Biyu Maxaukaka, Suka kuma yi gaggawa wajen
aikin gina su da raya su, ta yadda aka samu // AIYUKAN FAXAXAWA A KARO NA
FARKO, a zamanin Sarki Abdul'aziz –Allah yayi rahama a gare shi-.
Wanda kuma aiyukanta suka
ci-gaba a zamanin Sarki Sa'ud, da Sarki Faisal –Allah yayi rahama a gare su-.
Sa'annan sai aikin faxaxa
harabar varayin gabas, wanda ya kasance a zamanin Sarki Khalid –Allah ya yi
rahama a gare shi-.
Sa'annan sai aikin faxaxawa
A KARO NA BIYU; NA DAULAR SAUDIYYA, wacce ta kasance ta vangaren yamma daga
Masallaci, a lokacin Sarki Fahad (Allah yayi rahama a gare shi), Sai kuma ta kammalu
da babban aikin faxaxawa na wurin yin SAFAH da MARWAH (wato: Almas'ah).
A yau kuma (Ramadhan, 1436),
Almasjidul Haram yana rayuwa cikin AIYUKAN FAXAXAWA NA UKU, Wanda Sarki
Abdullahi (Allah yayi rahama a gare shi) ya bada su.
To, Ga nan, aiyukan faxaxawa a karo na-uku, na daular Saudiyya
No comments:
Post a Comment