SHAYARWA DA RENON YARO (WATO HADHANAH)
DA HUKUNCE-HUKUNCENSU A ISLAMA
(الرضاع والحضانة في الشريعة
الإسلامية)
ABUBAKAR HAMZA
MISAU
NA XAYA: SHAYARWA:
A
nan akwai mas'aloli da dama, kamar haka:
Mas'alar
farko: bayani akan menene shayarwa, dalilai da suka shar'anta ta, da
hukuncinta:
1- Bayani akan menene shayarwa:
"Rada'a, ko rida'a"; (shayarwa) shine: Tsotsan nono daga hantsa, ko shan nono
daga hantsa.
A shari'ar Musulunci kuma shayarwa ita ce: Yaron da bai kai
shekaru biyu ba ya tsotsi nonon, da ya samu da sababin ciki. Ko kuma shan nonon xan qasa
da shekaru biyu. (tsotso ko sha ko makamancin haka).
2- Dalilai da suka shar'anta shayarwa:
Lallai an shar'anta shayarwa a cikin faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭼ الطلاق:
٦
Ma'ana: (Idan kuka gagara yin ittifaqi,
to wata mace sai ta shayar masa da yaro) [Xalaq:
6]. Da kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﭼ البقرة:
٢٣٣
Ma'ana: (Idan kuma kuka nemi ku shayar da 'ya'yanku to babu
laifi akanku) [Baqarah: 233].
3- Hukuncin shayarwa: Hukuncin
shayarwa shine irin hukuncin da "dangantaka" ke bayarwa na haramta
auratayya tsakanin wanda tayi shayarwa da wanda aka shayar da shi, tare da
mayar da ita muharramarsa, da kevayya ya halatta da
ita, da kallonta. Don haka: shayarwa na hukunta samar da dangantaka, da kuma yaxa
haramcin auratayya, in an yi shi da sharuxansa.
Dalilin dake nuna ana samun haramcin auratayya sakamakon
shayarwa kuma shine: alqur'ani
da sunna, da ijma'i. Daga cikin dalilan alqur'ani
akwai faxin Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﮎ ﮏ ﮐ
ﮑ ﮒ ﮓ ﭼ النساء:
٢٣
Ma'ana: (Da kuma uwayenku da suka shayar da ku, da
'yan'uwanku ta fiskar reno) [Nisa'i: 23].
Shi kuma dalilin haramcin haka daga sunnah shine: Hadisin
A'ishah - رضي الله عنها-,
lallai tace: Manzon Allah (r)
yace:
Ma'ana: (Lallai shayarwa na haramta abinda haifayya ke
haramtawa).
Da kuma saboda hadisin Ibnu-abbas -t-, yace, Manzon
Allah (r)
ya faxa
dangane da 'yar Hamza -t-:
"إِنَّهَا لا تَحِلُّ لِي،
إِنَّهَا ابْنَةُ أَخِي مِنَ الرَّضَاعَةِ، وَيَحْرُمُ مِنَ الرَّضَاعَةِ مَا يَحْرُمُ
مِنَ الرَّحِمِ"([2]).
Ma'ana: (Lallai aurenta baya halatta a gare ni; saboda
kasancewarta 'yar xan'uwana ne ta fiskar shayarwa; kuma
lallai shayarwa na haramta duk abinda dangantaka ke haramtawa).
Amma dalilin "ijma'i" kuma dangane da mas'alar: to haqiqa
al'umma sun yi ijma'i kan cewa wassu mutane aure a tsakaninsu ya kan zama
haramun sakamakon sabibi na shayarwa.
Mas'ala
ta biyu: Sharuxan shayarwar dake haifar da
haramcin auratayya, da ambaton abubuwan da suke haihuwa saboda dangantaka irin
ta shayarwa:
1-
Menene
sharuxa ga shayarwar dake haifar
da haramcin auratayya?
Shan nonon mace baya haifar da dangantaka, ya kuma yaxa
haramcin auratayya sai idan ya cika sharuxai
guda biyu, kamar haka:
1. Dole shayarwar ta kasance a cikin shekaru biyu na farkon
rayuwar yaro; saboda duk shayarwar da ta kasance bayan yaro ya wuce shekaru
biyu bata da wani tasiri; wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕﯖ ﭼ البقرة: ٢٣٣
Ma'ana: (Uwaye mata su shayar da 'ya'yansu na tsawon shekaru
biyu cikakku, ga mutumin da ke nufin cika shayarwa) [Baqarah:
233]. Tare da faxin Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﭼ لقمان:
١٤
Ma'ana: (Da yaye shi a cikin shekaru biyu) [Luqman:
14]. Da kuma saboda hadisin Ummu-salamah - رضي الله عنها-
tace, Manzon Allah (r):
"لاَ يُحَرِّمُ
مِنَ الرِّضَاعَةِ إِلاَّ مَا فَتَقَ الأَمْعَاءَ فِي الثَّدْيِ، وَكَانَ قَبْلَ الفِطَامِ"([3]).
Ma'ana: (Daga cikin shayarwa babu wanda ke hukunta haramcin auratayya sai wanda ya isa cikin
hanji ya bubbuxe shi, ya kuma kasance gabanin a yi yayen yaro);
Saboda wannan; lallai shayarwar da take hukunta haramcin
auratayya ita ce kawai wanda ta kasance a cikin lokacin yarinta, ta kuma tsaya
a matsayin abinci ga yaro; wannan kuma dole wanda ake shayarwan ya zama jariri
ko yaron da nono ke cike masa yunwar cikinsa, ta kuma tsirar masa da nama a
jikinsa.
2. Dole adadin shayarwar ya kai shayarwa guda biyar masu qosarwa,
ko fiye da haka; wannan kuma saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها-, tace:
"كَانَ فِيمَا نزلَ مِنَ
الْقُرْآنِ: عَشْرُ رَضَعَاتٍ مَعْلُومَاتٍ يُحَرِّمْنَ، ثُمَّ نُسِخْنَ، بِخَمْسٍ
مَعْلُومَاتٍ،
Ma'ana: (Ya kasance yana daga abinda ya sauka na alqur'ani:
Shan nono sau goma ne sanannu ke haramta auratayya, sa'annan sai aka soke su da
shayarwa guda biyar kwarara sanannu, sai manzon Allah –r- ya rasu
alhalin guda biyar xinnan suna cikin abinda ake karantawa a cikin alqur'ani).
Sai dai kuma wannan ayar tana cikin ayoyin da Allah ta'alah
ya soke tilawarta, ya kuma wanzar da hukuncinta.
Da za a qaddara isar nono i zuwa
ga makoshin yaro (cikinsa) ba ta hanyar kame nonon da bakinsa ya tsotsa ba,
misali kamar a xixxiga masa a cikin baki, ko kuma ya sha daga cikin wani masaki, ko
makamancin haka, to a nan hukuncinsa shine hukuncin tsosa kai tsaye da bakinsa,
matuqar
dai adadin shan nonon ya kai "biyar" ko fiye.
2-
Hukunce-hukuncen
da suke bayuwa sakamakon dangantakar shayarwa:
Hukunci iri biyu ne ke rataya kan "dangantakar
shayarwa", kamar haka:
o Hukuncin da ke da alaqa
da haramcin auratayya.
o Hukuncin da ke da alaqa
da halaccin wassu lamurra.
Amma dangane da hukuncin da ke alaqa
da haramci: To lallai shayarwa nada tasirin ta fiskar bada haramcin auratayya;
kwatankwacin abinda "dangantaka ta jini" ke haramtawa; wannan ya
sanya uwar mutum ta vangaren shayarwa duk nisanta ta
sama, da 'yarsa ta fiskar shayarwa duk nisanta ta qasa,
da 'yar'uwarsa ta vangare guda biyu (uwa da uba) ko xaya
daga cikinsu, lallai duka waxannan haramun ne a
samu auratayya a tsakaninka dasu, saboda 'yan'uwatar da ta samu ta hanyar
shayarwa.
Amma dangane da tasirin "dangantakar shayarwa" ta
fiskar halacci: To lallai duk abinda ya halatta a tsakaninka da tsakanin
danginka na jini; kamar uwar mutum da 'yarsa, to ya halatta a tsakaninsa da
tsakanin mutumin da akwai shayarwa a tsakaninsu; don haka ya halatta ya ganta,
ko ya keve da ita; wannan kuma saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها-,
tace, manzon Allah (r)
yace:
Ma'ana:
(Lallai shayarwa na haramta abinda haifayya ke haramtawa).
Mas'ala
ta uku: Hanyoyin tabbatar da shayarwa:
Shayarwa
na tabbata ta hanyar shaidar mace guda xaya
yerjejjiya, wacce aka santa da gaskiya, idan ta yi shaida akanta, ko ga watanta
cewa ta shayar da yaro kaza a cikin shekarunsa guda biyu na farko, shayarwa sau
biyar, wannan kuma saboda hadisin Uqbah xan
Alhaaris -t-
, lallai shi yace:
"تَزَوَّجْتُ امْرَأَةً،
فَجَاءَتِ امْرَأَةٌ فَقَالَتْ: إِنِّي قَدْ أَرْضَعْتُكُمَا، فَأَتَيْتُ النَّبِيَّ
r فَقَالَ: وَكَيْفَ
وَقَدْ قِيلَ! دَعْهَا عَنْكَ"([6]).
Ma'ana:
"Na auri wata mata sai wata matar tazo tace, lallai duk na shayar da ku,
yace: Sai na zo wajen Annabi –(r)-
sai yace: Yaya kuma za a yi, bayan ta riga ta faxa!
Sai ka rabu da matarka".
Za
a karvi
shaidar ta tare da cewa ita xaya a irin wannan mas'alar;
saboda lamarin bada shaida ne akan abinda ya ke voye
(al'aura); wannan ya sanya ake karvar shaidar mata su-kaxai-xinsu,
ba tare da maza ba, sai yayi kama da karvar
shaidarsu a lamurran haihuwa.
NA BIYU: RENON YARO (HADHANAH) DA BAYANIN HUKUNCE-HUKUNCENSA:
A
nan akwai mas'aloli da dama, kamar haka:
Mas'alar
farko: Renon yaro da hukuncinsa, da bayanin mutumin da reno ke kasancewa a
hannunsa:
1- Menene "Hadhanah (reno)":
A harshen larabci "hadhanah" tana nufin tarbiya ma
yaro da bashi kula, an ciro kalmar ce daga "hidnu" mai ma'anar: gefe;
wannan kuma saboda kasancewar mai reno (ko wakilin yaro) ya kan sanya jariri a
gefensa. Shi kuma wanda ake kiransa "haadinu, ko haadinah" shine:
Mutumin da aka bashi karamin yaro don ya kula da shi, ya kuma riqa
tarairayarsa (renonsa).
A shari'ance kuma "hadhanah" itace: Mutum ya tsayu
wajen kula da yaron da bai gama sanin fari-da-baqi
ba, ko kuma ba zai iya cin gashin-kansa ba, da yi masa tarbiyya da irin abinda
zai gyara masa duniyarsa; ta vangaren jikinsa, da kuma
ta vangaren
ma'ana, tare da kare shi daga barin duk abinda zai cutar da shi.
2- Hukuncin "hadhanah":
Hukuncin reno ya kan wajaba akan mai yin hadanar; matuqar
babu wanda zai yi hadanar in banda shi, ko kuma akwai waninsa sai dai kuma
yaron da za a yi ma renon ya qi karvar wani in banda
shi; a nan sai karvarsa ya zama wajibi akansa;
wannan kuma saboda idan har bai karve
shi ba; yaron ka iya halaka, ko kuma alal aqalla
zai cutu; don haka dole ne akansa ya tsamar da shi ko ya kiyaye shi. A wani
lokaci kuma hadhana ka iya zama wajibin da wani zai iya xauke
ma wani (farilla ta kifayah) idan akwai mutanen da za su yi renon, ko a ce
yaron zai karvi mutane da-dama.
3- Wanene
haqqin reno ke tabbata masa?
Reno na iya kasancewa ga mata ko ga mazaje matuqar
dai sun cancanci yinsa; sai dai kuma ana bada fifiko ga mata akan maza; saboda
(mata) sun fi tausayi da sassauta ma yaro. Amma idan matan da ake da su basu da
haqqin
wannan renon to sai lamarin ya juya zuwa ga mazaje; saboda su kuma mazaje sun
fi girman iko wajen kawo abinda zai kare yara, ya kuma tabbatar musu da
maslaha.
Renon yaro na kasancewa a hannun iyayensa guda biyu (uwarsa
da ubansa); matuqar akwai aure a tsakaninsu, amma idan basa tare; saboda shikar
da ta kasance, to a wannan halin "hadhanar" za ta kasance a hannun
uwarsa matuqar bata auri mutumin da bashi da alaqa
(ta kusa ko ta nesa) da mijinta na farko ba, wannan kuma saboda faxinsa
(r)
ga matar da mijinta ya sake ta, sai kuma ya so ya kwace yaronsa daga gare ta:
Ma'ana: (ke ce kika fi cancantar ki rene shi matuqar
ba ki yi aure ba).
Abinda reno ke hukuntawa:
Lallai "hadhanah" na hukunta kiyaye yaron da ake renonsa, da riqe
shi tare da hana shi zuwa ko aikata duk abinda zai cutar da shi, da yi masa
tarbiyya har zuwa girmansa, da aikata duk abinda ke zama maslaharsa; kamar kula
da bada abincinsa, da abin shansa, da tsaftace shi; ciki-da-waje, da kula da
yin barcinsa da tashinsa, da xauke masa dukkan buqatunsa
da abubuwan da ke nema.
Mas'ala
ta biyu: Sharuxan da aka sanya wa mai reno,
da abubuwan da suke hana bada "hadhana":
1- Musulunci: Saboda
ba a bada kafiri renon xa musulmi; domin kuwa Allah ta'alah bai bawa kafirai wata qofa
ko kafa da zasu shugabanci musulmai ba, da kuma saboda tsorace ma yaron da ake
bashi renon cewa kar ya rudu da kafiri ta vangaren
addininsa; har ya iya fitar da shi daga Musulunci i zuwa ga addininsa na
kafirci.
2- Balaga da hankali: Domin yaro qanqani
ba a bashi renon yaro, haka shima mutum mahaukaci ko mai tavin
hankali; wannan kuma saboda basu da ikon juya lamarin waxanda
suke yi musu reno; hasali ma! Su kansu suna buqatar
wanda zai kula da su ya riqa yi musu hadhana.
3- Mai hadhana dole ya zama amintacce ta vangaren
addini, kuma kamamme: Saboda
ba a bada reno ga mutum mai ha'inci, ko fasiqi;
saboda kasancewarsu ba a aminta da su; hasali ma barin yaro a wajensu matsala
ce ga yaron (ma'ana: cutuwa ne) a ransa da kuma dukiyarsa.
4- Dole mai aikin reno ya zama yana da ikon xaukar
nauyin xawainiyar wanda yake reno ta vangaren
buqatunsa na jiki dana kuxi:
Wannan ya sanya cewa duk Mutumin da ya zama ajizi
saboda yawan shekaru ba a bashi reno, ko kuma mai wani aibu kamar bebanta ko
kurumta, haka kuma ba a bada "hadhana" ga talaka futuk (wanda bashi
da sisin kobo), ko kuma mutumin yake da aiyuka da yawa; wanda idan aka bar yaro
a wajensa zai tozarta (ba zai samu wata kula ba).
5- Dole kuma mai renon ya zama ya kuvuta
daga cututtuka da suke yaxuwa daga mutum zuwa
mutum, kamar kuturta, da makamancin haka.
6- Dole mai reno ya zama wanda ya iya jujjuya dukiya:
Saboda ba a bada reno ga wawa mai almubazzaranci; tsoron kar
ya lalata kuxi ko dukiyar yaron da yake renonsa.
7- Dole ne kuma ya zama xa
ba bawa ba: Saboda ba a bada reno ga mutumin da bashi da 'yanci (bawa);
kasancewar "hadhana" shugabanci ne; bawa kuma bashi da shugabanci
akan kowa.
Waxannan
sharuxan sun game mazaje da mata da zasu yi aikin reno, amma ita kuma
mace ana qara sharaxi guda xaya akanta; wanda kuma shine: Kar matar ta zama tana auren
mutumin da babu wata dangantaka tsakaninsa da wanda take reno; saboda a wannan
lokacin zata shagalta da hidima ga mijinta da bashi haqqoqinsa;
da kuma saboda faxinsa (r):
Ma'ana:
(ke ce kika fi cancantar ki rene shi matuqar
baki yi aure ba).
Kuma "hadhana" tana faxuwa
idan aka samu abu guda daga cikin abubuwan da suke iya hana
"hadhanar" waxanda suka gabata, ko kuma idan aka rasa sharaxi
daga cikin sharuxanta.
Mas'ala
ta uku: Wassu daga cikin hukunce-hukuncen da suke rataya akan renon yara
(hadhanah):
-
Idan xaya
daga cikin uwa ko uban yaron da ake renonsa ya yi tafiya, mai tsayi, ba kuma da
nufin cutar da wanda ake renonsa ba, hanyar kuma ta zama amintacciya, to a nan
uban yaro shine ya fi cancantar ya xauki
xawainiyar
renonsa; sawa'un shi uban shine matafiyin, ko shine mazaunin gari da gida;
saboda kasancewar uba shine alhakin tarbiyyar yaro ke wuyansa, don haka idan da
zai zamto a nesa sai xansa ya tozarta.
-
Amma idan
tafiyar xayansu ta kasance ne zuwa ga wani gari da ke kusa-kusa (wanda
nisansa bai kai nisan garin da ake yin sallar qasaru
ba) to a nan "hadhanar" za ta zama a wuyan uwar yaro; sawa'un itace
mai tafiyar ko ita ce a zaune a gida, saboda uwa tafi tsananin tausayin yaro,
kuma uban a irin wannan tafiyar zai iya bincikan halin da yaron ke ciki.
-
Amma idan
tafiyar ta zama tana da nisa, kuma buqata
ce ta hukunta ta, sai kuma hanyar ta zama bata da aminci (ko a-dawo, ko
ba-a-dawo ba) to a nan "hadhanar" yaro zata zama a wuyan mutumin dake
zaune a gida daga cikinsu.
-
"Hadhana"
tana qarewa ne lokacin da yaro ya cika shekaru bakwai, daga nan kuma sai
a bawa xa namiji zavin ya kasance a
wurin ubansa ko wajen uwarsa; sai kuma ya ci gaba da zama a wajen wanda ya zava
daga cikinsu; wannan kuma saboda faxinsa
(r):
"يَا غُلامُ! هَذَا أَبُوكَ
وَهَذِهِ أُمُّكَ؛ فَخُذْ بِيَدِ أَيِّهِمَا شِئْتَ، فَأَخَذَ بِيَدِ أُمِّهِ فَانْطَلَقَتْ
بِه"([9]).
Ma'ana: (Ya kai yaro! Wannan shine ubanka, wannan kuma itace
uwarka; don haka sai ka kama hannun duk wanda ka so daga cikinsu. Sai yaro ya
kama hannun uwarsa, sai ta tafi da shi). Kuma lallai wannan hukuncin na bada zavi
ga yaro Umar da Aliyu -t- suma sun yi hukunci da
irinsa. Ba a bada zavi ma yaro kan mamarsa da babansa har sai idan kowanne daga
cikinsu ya cika sharuxan hadhana da suka gabata.
Abinda yasa kuma aka qayyade bashi wannan zavin
da shekaru (7) shine saboda daga wannan shekaran ake fara umurtar yaro da
sallah. Kuma idan yaro ya zavi ubansa to zai
kasance a wajensa ne dare da yini; domin ya riqa
tarbiyyantar da shi, amma kuma baya halatta ya riqa
hana shi ziyartar uwarsa mahaifiya. Idan kuma uwarsa ya zava
to a nan zai riqa kasancewa ne a wajenta da daddare, ya kuma ci-gaba da
kasancewa a waje ko gidan ubansa da rana; don kula da tarbiyyarsa, kuma saboda
lokacin yini lokaci ne na fita biyan buqatu
da aikata sana'oi.
Amma ita kuma 'ya mace idan ta kai shekaru bakwai (7) to dole
ta kasance a wajen ubanta; saboda shine kawai zai fi kula da ita, kuma shine
mutumin da ya fi haqqin zama waliyyinta (kula da lamarinta har ta kai lokacin aure),
kuma saboda tana kusantar shekarun aure; shi kuma uba shine waliyyinta da za a
nemi aurenta a wajensa, kamar yadda kuma shine ya fi sanin mutumin da zai dace
da ita daga cikin mutanen da za su zo neman aurenta. Sai dai kuma don an ce 'ya
mace ta kasance a wajen ubanta ba za a hana uwarta ziyartat ta ba idan har ta
so hakan; sai dai in akwai abinda ake tsorace mata; na vacin
tarbiyya, ko wanin haka, to a nan kam ya halatta a hana wannan. Amma idan uban
ba zai iya kula da ita ba; ko don saboda aiyukansa, ko don tsufa, ko rashin
lafiya, ko kuma qarancin addininsa, Sai kuma uwar ta
zama ita tafi uban dacewar ta dukkan fiskoki to a nan uwa ita ce ta fi uban
cancantar riqe ta. Haka kuma lamarin yake; idan uban ya auri wata mata, ya
kuma ajiye 'yar tasa a gaban sabuwar matat tasa; sai ba a yi sa'a ba; ta yadda
ta zama tana cutar da ita; ta fiskar zaftare mata wassu haqqoqinta
to a nan ma uwar yarinyar ta haqiqa itace tafi
cancantar ta yi mata hadhana.
-
Kuxin
biyan me reno (hadhana) –sawa'un mai yin hadanar uwa ce ko watanta- za a fitar
da shi daga dukiyar wanda ake renonsa; matuqar
dai yana da kuxi. Ko kuma daga kuxin
waliyyin yaron da duk wanda ciyar da yaron ke kansa; matuqar
yaron bashi da dukiya.
No comments:
Post a Comment