MA'AIKATAR BUGA ALQUR'ANI MAI GIRMA
TA SARKI FAHAD, A MADINAR ANNABI (s.a.w)
(مجمع الملك فهد لطباعة المصحف الشريف
بالمدينة النبوية)
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Alqur'ani
(littafi abin karantawa)
Mafi
girman littafin da Allah ta'alah ya saukar da shi, cikamakon littatafan da suka
sauka daga sama, littafi gagara koyo (mu'ujiza) madawwamiya ga wannan al'ummar,
wanda Allah mabuwayi da xaukaka ya xauki nauyin kiyaye shi da bashi kariya. Wannan
littafin duk wanda ya karanta shi (ko ya haddace shi) to lallai Allah zai
xaukaka darajojinsa, kuma duk wanda ya karanta wannana maganar to ga kowani harafi
da ya karanta yana da kyakyawa "lada", ita kuma ladan za a ninninkata
da kwatankwacinta guda goma.
Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) a zamaninsa ya yi
kwaxayin kada Mutane su riqa rubuta komai face alqur'ani (shi kaxai), kuma ya
kasance yana karantar da su yadda ake karanta alqur'ani karantawa, kuma sun
kasance suna sauraro, kuma ya sanya wassu daga cikin Sahabbai suka zama masu
karantar da alqur'ani, mahaddata, ta yadda Mutane ke komawa i zuwa gare su;
idan suka yi mantuwa, ko suka yi kuskure. Kuma da irin haka aka kiyaye littafin
Allah mabuwayi da xaukaka.
Yayin
da ya kasance Alq1ur'ani yana da irin wannan muhimmanci da matsayi, Sai ya zama
aikin buga shi, da kuma kula da rubuta shi da zana shi ya kasance yana da
matsayi mai girma a wajen musulmai; tun rasuwar Manzon Allah har zuwa yau, tun
zamanin Abubakar; yayin da ya yi aikin tattara Alqur'ani a cikin takardun
Mus-haf, kuma tun lokacin Usman; yayin da ya sake aikin tara shi. Sa'annan
waxanda suka zo a bayansa; kamar zamanin daular Umawiyyawa da Abbasiyyawa, da
wassunsu, dukkaninsu sun kasance suna bada muhimmanci mai girma ga littafin
Allah (mabuwayi da xaukaka), kuma sun kasance suna rigaggeniya wajen buga shi,
da yaxa shi.
Bayan
haka;
Sai
muka zo wannan zamanin, wanda muka samu wani mataki; wanda shima za a xauka
yana daga cikin matakai masu muhimmanci a tarihance, wajen bada kulawa ga
littafin Allah (mabuwayi da xaukaka).
(A
yanzu) Za mu tafi mu yi ziyarar WATA MA'AIKATA, wanda aka assasa ta gabanin
gomman shekaru, Wato a zamanin Sarki Fahad (Allah ya yi masa rahama), wanda
aka assasa wannan MA'AIKATAR sukutum don ta kevanta da bada kula ga littafin
Allah (mabuwayi da xaukaka); ta fiskar zana shi, da buga shi, da kuma aikin raba
shi ga duniya gabaxaya.
Wannan
ita ce ma'aikatar da ta xauki nauyin buga littafin Allah maxaukaki.
Kuma
dai, akwai wassu ma'aikatun buga littafin Allah (Alqur'ani), a qasashe ko
birane masu yawa, saidai wannan (ma'aikatar) tana daga cikin waxanda suka fi
yin fice; Don haka ne, za mu xauke ku, mu kewaya da ku cikin wannan ma'aikatar,
domin mu gane wa idonmu yadda Musulmai suka bada muhimmanci ga littafin Allah (mabuwayi
da xaukaka).
Tambaya:
Mun
san cewa, wannan ma'aikatar tana aikin buga littafin Allah (Alqur'ani), Saidai
ina zaton buga Alqur'ani yana bin matakai dayawa gabanin ya fito, don haka, Ya
kai shehinmu! Muna so mu san irin gudumawar da kuke bayarwa, wajen buga wannan
alqur'anin?
Amsa
(Daga
Bakin: Aliyu xan Abdurrahman Alhuzaifiy, Limami, kuma mai huxuba a Masallacin
Manzon Allah –S.A.W- kana shugaban komitin bitar Alqur'ani):
Lallai
aikin buga Alqur'ani mai karimci aiki ne mai girma, kuma aiki ne da yake cikin
aiyuka masu tsananin wahala, ba wai saboda wahalarsa ba, A'a, Saidai don a
samu, Alqur'ani ya kuvuta daga kowani irin kuskure, saboda yin kuskure a cikin rubuta alqur'ani –koda kuwa ba a yi gangancin
sa ba-, ba daidai ya ke da yin kuskure a wani littafin na daban; wanda ba
alqur'ani ba. Su kuma matakan mabanbanta waxanda lajanar ilimi ta ke bin su, a
lokacin bitar Mus-haf xin Maxina, a farkon aikin ne, da kuma qarshensa; Na
farkon shine:
A
lokacin da Mai zana ko kuma rubuta Mus-hafi ya rubuta shi ba tare da ya yi wasalinsa
ko sanya masa xigo ba; Sai wannan komitin ta yi bitarsa, a cikin wannan halin, har
su samu tabbacin cewa lallai abinda aka rubuta na Alqur'ani; babu ragi, babu
wani abu (na qari).
Mataki
kuma na qarshe, shine: Ba za a yi izini, ko a rubuta rubutun xaukar matakin
cewa: Wannan mus-haf xin za a iya buga shi, ko a yaxa shi ba, har sai ya bi
mataki na "TAHAJJIY"; Shi kuma wannan matakin –Muna gode wa Allah-
komitin ilimi ne suka qirqiro shi, don yin bitar "Mus-hafin Madina",
Kuma wannan mataki ne wanda akwai tabbaci a cikinsa, saboda ya zama ba a samu
wani kuskure ba cikin rubuta "Mus-haf" da falalar Allah mabuwayi da
xaukaka. Misalin wannan matakin shine: Ayar:
"Bismillahir rahmanir rahim",
Sai a karanta ta da cewa:
Harafin "Ba" qarqashinsa
akwai "kasrah", Shi kuma "Siyn" a samansa akwai
"Sukun", "Miymun" kuma a qarqashinsa akwai "kasrah".
… To, haka za a bi, dukkan alqur'ani.
Wato:
Ya Sheikh! Haka za a yi ta yi, "harafi" bayan "harafi"?
E,
Haka za a yi ta yi, "harafi"
bayan "harafi" har sai "Mus-hafin" ya qare, da
wannan hanyar, daga farkonsa har zuwa qarshensa. To daga nan ne, sai a bada
izinin a buga ko a yaxa wannan "Mus-hafin".
A
yau muna tare da Baqonmu mai karamci, kuma xan'uwa mai matsayi, wato: Sheikh
Usman Xaha, wanda kuma shine ya rubuta da hannunsa –Allah ya yi mata
albarka- ko ya zana, wannan "Mus-hafin" da a yau a cikin
duniya Miliyoyin xarurruka suka yi haddar alqur'ani ko suke yi da shi. Muna
miqa gaisuwarmu, Sheikh Xaha!
Allah
yayi
maka albarka!
Ya
Sheik, Ko za ka taimaka ka yi mana magana ko bayani, kan "Wannan Mus-haf"
wanda ka rubuta Shi da rubutun hannunka?
Kowani
Musulmi mai yin rubutu da hannunsa (wato: Khaxxax) idan har ya koyi wannan aiki
(na gwanancewa cikin rubutu da zane), zaka samu yana mafarkin ya ga ya rubata
"Mus-hafi maxaukaki", To, Nima, (tun ina yaro) na yi ta
qoqarin na gwanance a wannin fanni na zane, mai kyau, domin daga baya (a cikin
rayuwata) na rubata "Mus-hafi maxaukaki", Kuma lallai na yi ta
bitar hanyoyin da malaman zane suke bi wajen rubuta "Mus-hafai",
Daga nan sai nima na qirqiro, wata hanya wacce ta kevanci mai zane; Usman
Xaha, a wannan fannin. Yanzu haka, zanena ya shahara, kuma ya yi fice, ya
kuma banbanta da sauran, wajen kyautata rubuta "kalmah" da "harafi",
da kuma alaqar "wasali" da harafin da yake biye da ita. To daga
qarshe sai na zo, qasar masarautar larabawa ta Saudiya, kuma sai aka qaddara
min matsayin mai zana alqur'ani da rubuta shi a ma'aikatar Sarki Fahad na buga
"Mus-haf maxaukaki" –Allah ya yi masa rahama-.
No comments:
Post a Comment