2016/02/09

FADAKARWA DA NASIHOHI GA MAZIYARTA MASALLACIN ANNABI MATA (توجيهاتونصائح لزائرات المسجد النبوي الشريف)







FAXAKARWA DA NASIHOHI
GA
MAZIYARTA MASALLACIN ANNABI MATA
(توجيهات ونصائح لزائرات المسجد النبوي)


TANADAR
Ofishin Faxakar Da Mata Da Nusar da Su, 1434h




FASSARAR
Abubakar Hamza



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Salati da sallama su qara tabbata ga shugaban manzanni, da kuma iyalanSa da sahabbanSa gabaxaya.
Ya wacce ta ziyarci masallacin Annabi !
Ya wanda Allah ya yi baiwa a gare ki da ziyartar masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) domin yin salla, da zikiri, da ibada.
Zuwa gare ki nake fiskantar da waxannan wasiyyoyin da faxakarwa:
Muna faxakar da ke, kuma muna cewa:
Ke (a yau), kina masallacin Annabi ne (صلى الله عليه وسلم), Masallacin da zukatan muminai suke begen zuwansa, kuma rayukansu suke cike da begen gamuwa da shi.
Tayin murnar samun damar sallah da kika yi a cikinsa; saboda yin sallah a cikin wannan masallacin yana daidai da yin sallah dubu (1000) a waninsa, kamar yadda ya zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa:
((صلاةٌ في مسجدي هذا خيرٌ من ألف صلاةٍ فيما سواه، إلا المسجدَ الحرامَ)).
Ma'ana: ''Sallah a masallacina wannan yafi salloli dubu alheri; a waninsa in banda masallaci mai alfarma", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Taya ki murnar samuwarki a wannan bagiren mai albarka; bagiren da imani ke fakewa a cikinsa, kamar yadda macijiya ke fakewa a cikin raminta, Imamul Albukhariy –Allah yayi rahama a gare shi- ya fitar da hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) cewa lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), yace:
((إنَّ الإيمان ليَأْرزُ إلى المدينة كما تأرز الحَيَّةُ إلى جُحْرها)).
"Lallai imani zai tattara a garin Madina kamar yadda macijiya take tattara a cikin raminta".
            Taya ki murnar halartar halqoqin ilimi; waxanda suke cikin wannan masallaci (mai albarka); domin ki samu ladan Mai yin jihadi fiysabil Allah, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه), ya ce: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:  
((مَن جاء مسجدي هذا لم يأتِهِ إلا لخيرٍ يتعلَّمُه أو يُعلِّمُه، فهو بمنزلة المجاهدِ في سبيلِ الله، ومَن جاء لغير ذلك فهو بمنزلة الرجل يَنظرُ إلى مَتاعِ غيره)).
Ma'ana: "Wanda ya zo masallacina wannan; bai zo masa ba sai don wani alherin da zai koye shi, ko ya koyar da shi, to yana da matsayin mai jihadi fiysabil Allah. Wanda kuma ya zo ba da wannan manufar ba to kamar mutumin da yake kallon kayan waninsa ne". Ibnu-majah ya ruwaito shi. Kuma Albaniy ya inganta shi.
            Taya ki murnar samun damar yin sallah a raudha, wanda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yake faxa a kanta:
((ما بين بيتي ومِنبري روضةٌ من رياضِ الجنّة)).
Ma'ana: ''Tsakanin gidana da minbarina dausayi ne daga cikin dausayin aljanna'', Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
             Taya ki murnar jiran sallah, bayan sallah a wannan masallaci (mai albarka), domin ki samu ladan mutumin da yake aikin ribaxi fiysabil Allah, kamar yadda Imamul Muslim –Allah yayi rahama a gare shi- ya fitar da hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) lallaiManzon Allah (صلى الله عليه وسلم), ya ce:
«ألا أدلُّكم على ما يمحو الله به الخطايا، ويرفع به الدرجات؟ قالوا: بلى يا رسول الله. قال: إسباغ الوضوء على المكاره، وكثرة الخُطى إلى المساجد، وانتظار الصلاة بعد الصلاة، فذلكم الرباط».
"Shin ba zan nuna muku abin da Allah ke share kura-kurai da shi ba, kuma ya xaukaka darajoji da shi? Sai suka ce: Na'am, Ya ma'aikin Allah! Sai ya ce: Cika alwala, a lokacin qi (sanyi), da yawan taku izuwa masallatai, da kuma jiran sallah bayan sallah; Wannan kuma kamar yin ribaxi ne".
          Taya ki murnar samun sallar gawa (jana'iza); saboda a cikin yin ta akwai lada mai girma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
((مَن شَهِد الجنازة حتى يُصلَّى عليها فله قيراطٌ، ومَن شهد حتى تُدفن كان له قيراطان. قيل: وما القيراطان؟ قال: مثل الجبلين العظيمين)).
"Duk wanda ya halarci sallar janaza har aka yi mata sallah, to yana da qiyraxi guda xaya, Kuma duk wanda ya halarce ta har zuwa a bunne ta zai samu qiyraxi guda biyu. Sai aka ce, menene qiyraxi biyu? Sai ya ce: Misalin duwatsu guda biyu masu girma ", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

            YA KE WANDA TA ZIYARCI MASALLACIN ANNABI Yi qoqarin, zuwan da kika yi don ziyara ya zame miki dama ta yin hisabi wa kanki, da samun qarin imani, da yawaita aiyyukan xa'a.
   Kuma ki yi kwaxayin aikata kyakkyawan aiki, da neman lada, da yin ikhlasi ga Allah ta'alah cikin dukkan aiyukanki.
   Ki kasance Mai girmama wuraren bauta wa Allah na harami guda biyu; saboda taqawar Allah itace take sanya a riqa  girmama waxannan wuraren, kuma duk zuciyar da ta ke girmama Allah, to zata bada dalili ne akan ita mai taqawar Allah ne ta hanyar girmama wuraren da Allah ya nemi a girmama su, Allah ta'alah yana cewa:
{ذَلِكَ، وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ} [الحج 32].
"Saboda, Duk wanda ya girmama wuraren bautan Allah, to lallai hakan yana daga cikin taqawar zukata" [Surat Alhajj: 32].
   Kuma kada ki riqa xaga sauti a cikin masallacin, ta yanayin da za ki takura wa sauran mutane, kuma ahir xinki da yin tafi, da guxa a cikin masallaci, saboda yin haka mummunan aiki ne abun kyama.
    Abu ne mai kyau, ki girmama wannan masallacin; ta hanyar rufe wayar hannu, a lokacin sallah; don kada ki takura wa 'yan'uwanki masallata da qarar waya; sai ki tafiyar musu da kushu'insu.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama wannan masallacin da rashin shagaltuwa da xauke-xauken hotunan sasaninsa da vangarorinsa; saboda ba ki yi dogon tafiya kika zo wannan garin ba, sai don ki samu lada mai yawa, ki kuma amfana da alkhairi mai yawa.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama masallacin; ta hanyar kiyaye tsaftarsa; wannan kuma zai tabbatu ta hanyar nisantar yin rubutu akan katangun masallacin da abubuwan da ake sanyawa don hana shigewa. Kuma kada ki yi amfani da ruwan da aka tanada don a riqa sha; wajen yin alwalanki, a cikin wannan masallacin, saboda aikata hakan zai tauye ko rage ruwan da aka tanadar ga masu ziyara don sha, tare da abinda zai janyo na cutar da mutumin da ya bi ta kansa; alhalin kuma banxakai da kuma wuraren da aka tanada don yin alwala suna nan, a kusa, kuma suna xauke da dukkan abinda zaki iya buqatarsa.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama masallacin a yayin tafiyanku zuwa ga Raudha; ta hanyar tafiya cikin nitsuwa da kwanciyar hankali, kuma ki kasance cikin rufi da cikakken yanayi na sutura.
    Kuma abu ne mai kyau, ki koyar da xanki LADDUBAN MASALLACI,             kina mai shuka son masallaci da girmama alamomin da ake yin bautar Allah a wurinsu, a cikin zuciyarsa.
Sannan ki sani cewa, lallai wurin karatun da aka tanada wa yara (laburarin yara) ya himmatu wajen karantar da yara ladduban da suke da alaqa da masallatai da wassunsu, sai ki yi qoqarin xanki ya samu rabonsa na ziyartar wannan laburaren.

            Sai kuma ki yi qoqari wajen cike lokutanki a wannan masallacin da yin tilawar littafin Allah (Alqur'ani), da ambatonsa maxaukakin sarki, da halartar halqoqin ilimi. Kuma ki yi guzuri, ki amfana da littatafan da aka ajiye wa masu ziyara a laburaren da suka kevanci Su, da kuma muhadarorin da aka yi rakodin, daga ofishin xaukan karatu cikin sauti, tare da kuma amfana da littatafan da ake bayar da su kyauta ga masu ziyara.
            Kuma ki yi qoqari, wajen daidaita sahun mata masu sallah; saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
((سَوُّوا صفوفكم؛ فإنَّ تسوية الصفوف مِن إقامة الصلاة))
Ma'ana: "Ku daidaita sahu; saboda daidaita sahu yana daga tsayuwar sallah", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma hadisi   ya zo daga Jabir xan Samurah (رضي الله عنه) ya ce:
«أَلَا تَصُفُّونَ كَمَا تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا؟ فَقلنا: يَا رَسُولَ اللهِ! وَكَيْفَ تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبّها؟ قَالَ: يُتِمُّونَ الصّفَّ الْأُوَلَ، وَيَتَرَاصُّونَ فِي الصَّفِّ».
Ma'ana: "Shin ba za kuna yin sahu kamar yadda Mala'iku ke yin sahu a wajen Ubangijinsu ba? Sai muka ce: Ya ma'aikin Allah! Ta yaya Mala'iku ke yin sahu a wajen Ubangijinsu? Sai ya ce: suna ciccika sahun farko sai wanda ke biye da shi, kuma suna hadewa; sashinsu zuwa sashi a cikin sahu", Muslim ne ya ruwaito shi.

            Kuma abu ne mai kyan gaske, ki zama babbar misali da ke aiki da musulunci wajen kyautata mu'amalantar tsare-tsaren da aka sanya ga mata masu ziyartar masallacin Annabi; waxanda ba don komai aka sanya su ba sai don kowa ta yi aikin ziyararta cikin qoshin lafiya, tun daga lokacin shigowarki ta qofofin masallacin, har zuwa fitarki daga wannan masallacin.

            Kuma abu ne mai kyan gaske, ki siffanta da halaye masu kyau, da ladduban musulunci. Kuma ki taimaki 'yan'uwanki mata masu ziyara, a lokacin cunkoso. Sai kuma ki ji, kana ki bi, faxakarwar masu nusantarwa; waxanda suke aikin faxakarwa zuwa ga abinda alkhairi ya ke a cikinsa.

             Ya wacce muke fatan kariyar Allah a gare ta ! Tafiyarki zuwa ga Raudha ya zama da tsanaki da nitsuwa, ba tare da ke kin wahala ba, ko kuma sauran masu ziyara sun wahala ba. Kuma ki sani, lallai tafiya raudha, da yin sallah a cikinsa alheri ne da lada, in sha Allah. Saidai kuma ba wajibi ba ne, kuma bashi da alaqa da umrarki da hajjinki, don haka kada ki tsananta wa kanki, wajen shiga wurin da ya yi cunkoso.

Ya wacce muke fatan kariyar Allah a gare ta ! Lallai addinin musulunci addini ne cikakke, da ya game dukkan maslahohinmu na duniya da lahira, kuma ya zo da alkhairori ga musulmai; mazansu da matansu. Kuma lallai ya bada muhimmanci ga mace, ya kuma sanya ta a wurin karramawa da girmamawa; matuqar ta yi riqo da shiriyarsa, ta kuma yi ado da siffantuwa da falalolinsa.
Yana kuma daga cikin haka: Lallai musulunci ya mata izinin halartar masallatai, domin ta yi tarayya da mutane cikin alkhairi, da yin sallar jam'i, da halartar majalisosin ambaton Allah (zikiri); cikin wassu dokoki da qa'idodi waxanda za su nisantar da ita daga fitina, su kuma kiyaye mata mutuncinta. Allah ta'alah yana cewa:
{يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورا رحيما} [الأحزاب 59].
"Ya kai wannan Annabin! Ka gaya wa matanka da 'ya'yanka mata, da matan muminai su kusantar da jilbabinsu qasa, wannan shi yafi kusa da a sansu ba za a cutar da su ba, Kuma Allah ya kasance Mai gafara Mai rahama" [Ahzab: 59].
Ya zo daga Ummu-Salmah (رضي الله عنها) ta ce:
((Yayin da ayar
{يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن}.
Ta sauka (wato, ayar umurnin matan muminai da sanya hijabi), Tace: Sai matan Al'ansaar, kai ka ce akan kayukansu akwai hankaku, na daga tufafi)), Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.

            Ya budurwar da take rayuwa cikin musulunci! Ki sani! Lallai shi hijabi yana kare mace daga idanun mutanen banza.
Kuma lallai waxanda suka xanxani xacin bayyanar da ado da ballagaza, suka kuma quna da wutar qazantar cakuxuwar maza da mata sun tabbatar da hakan.
Kuma ki yi kwaxayin nesantar yin ado da sanya turare a lokacin fitanki daga gidanki; Ya zo daga Zainab matar Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله عنه) ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya gaya mana:
«إِذَا شَهِدَتْ إِحْدَاكُنَّ الْمَسْجِدَ فَلاَ تَمَسَّ طِيبًا».
"Idan xayanku za ta halarci masallaci to kada ta shafa turare", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ki yi kwaxayin nisantar cakuxuwa da maza akan hanya; saboda ya zo daga Hamza xan Abiy-Usaidu Al'ansaariy, daga Babansa (رضي الله عنه), lallai shi ya ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) alhalin yana fita daga masallaci, sai Maza suka cakuxa da Mata, a hanya, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
«اسْتَأْخِرْنَ؛ فَإِنَّهُ لَيْسَ لَكُنَّ أَنْ تَحْقُقْنَ الطَّرِيقَ، عَلَيْكُنَّ بِحَافَاتِ الطَّرِيقِ». فَكَانَتِ الْمَرْأَةُ تَلْتَصِقُ بِالْجِدَارِ، حَتَّى إِنَّ ثَوْبَهَا لَيَتَعَلَّقُ بِالْجِدَارِ مِنْ لُصُوقِهَا بِهِ.
Ma'ana: "Mata Ku koma qarshe; saboda ba haqqinku ba ne ku kasance a tsakiyar hanya, Ina horonku da bin geffan hanya", Daga nan Mace sai ta kasance tana mannewa da katanga, har ya zama tufafinta yana maqalewa da katanga; saboda yadda ta ke mannewa da shi . Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya ce: hadisi ne hasan.

            Me ya fi kyau, kuma me yafi xaukaka, fiye da ki kasance abar koyi ga wassunki, wajen aiki da ladduban shari'a, waxanda suka zo a cikin littafin Allah mabuwayi da xaukaka, da sunnar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم).

            Muna roqon Allah, ya karva miki aiyukanki na kwarai, ya kuma datar da ke zuwa ga dukkan alkhairi; wanda ma'auninki zai nauyaya da su; don ki kasance cikin rayuwa yardaddiya; a ranar tashin qiyamah; ranar da mutane za su tashi zuwa ga Ubangijin talikai.
30/04/1437h
Wanda ya yi daidai da
09/fabarairu/2016m

A Madinar Manzon Allah (SAW)

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...