2016/02/04

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI saw TA juma'a 26 RABI'U AS-SANIY 1437H daidai da 5 Fabarairu 2016M ta DR. Salah Albudair











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26 /RABI'U AS-SANIY/1437H
daidai da 05/ Fabarairu/ 2016m




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. SALAH XAN MUHAMMADU ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
            Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya ke kwararo alkhairori da kyautayi, ga kowani na nesa daga cikin halittunsa, da na kusa, Ina yin yabo a gare shi da zuciya da gavvai da kuma harshe, kuma ina godiya a gare shi; bayan ya gusar da cuta da zogi, kuma ya kwararo dayawa daga cikin ni'imominSa da kyautatawanSa.    Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke; bashi da abokin tarayya "Mai rahama (Allah) * ya sanar [da Mutum] alqurani * Ya kuma halitta Mutum" [Rahman: 1-3].
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka zave shi daga zavavvu cikin qabilar Ma'ad, da kuma kevantattu daga qabilar Adnan.
            Salaitin Allah da sallamarSa su qara tabbata a gare shi, da kuma ga iyalanSa da sahabbanSa, waxanda suka yaqi varna da kaifin harshe, da kuma harshen takobi.
            Bayan haka;

            Ya ku Musulmai …
            Wanda ya sani sai ya kiyaye, Wanda kuma ya yi kaifin hankali to sai ya yi ta nisantar dauxa,    Wanda kuma ya jahilta to sai kaga yana aukawa cikin kura-kurai, yana dulmuya.  Wanda kuma ya samu taqawar UbangijinSa sai ya rabauta, ba zai yi baqin ciki ba. "Kuma Allah yana tseratar da waxanda suka bi dokokinsa da basu rabo, Mummuna baya shafansu, kuma Su ba za su yi baqin ciki ba" [Zumar: 61].

            Ya ku Musulmai …
Duniya xan lokaci ne, soyayya ce wanda jin daxinta ba ya dogon wanzuwa,    
Ya tave Wanda kawalwalniyarta ta yaudare shi,    
ko abin shanta ya sanya shi maye,   
har ya shiga cikin turvayarta gabanin ya tuba.
Gida ne na yin tsere, Wannan kuma shine fili (da lokacin) aikata hakan,  
Saidai babu mai rigaye daga cikin dawaki a lokacin kowani tseren da ba na wasa ba, face ingarmomi daga cikinsu.
Kuma, kowani Mutum yana da abinda ransa ta gabatar;
Idan ya yi kuskure yana da sakamakon kuskurenSa,
Haka kuma idan ya aikata daidai.

            Ya ku Musulmai …
            Masarautar LARABAWA ta Saudia qasa ce da ta yi matuqar xaukaka da riqo da addini,   Katangunta kuma suka tabbatu a cikin qasa saboda bin shari'a,   Kuma lallai zai tave (ya yi hasara) saboda azamar shugabanninta Wanda ya ke yin gaba da ita,    Kuma zai gagara cin nasara saboda tuben shugabanta da kaiwa harinsa; Jifan waxanda suke husuma da ita. Kuma duk wanda ya nemi qulla kaidodi ga Qasar Masallatan Harami Guda Biyu Maxaukaka, to, lallai Allah zai tuntsurar da shi akan hancinsa, … … Sai sakamakon kaidinsa ya koma akansa.

Ya ku Musulmai …
            Wanzuwa cikin jama'a garkuwa ne,    Rarrabuwar kai shi kuma tozarci ne,    Jama'a (r da take kan sunnah) ita ce: Haqiqanin gaskiya,      Rabuwa da ita kuma shine: Tushen rushewa,    Rarrabuwa shine farkon sharri da tuntuve,  sannan shi ke kaiwa zuwa ga nisantar gaskiya,    Shine ke mayar da abinda aka gina zuwa ga rushewa, AMINCI kuma ya mayar da shi tatsuniya,   kuma rarrabuwa shine Mai yin rauni, Mai yanyankewa.     
Kuma babu wani mai tafiyan da yafi sharri fiye da mai yawo da annamimanci.  Kuma lallai tushen sharri Shine dukkan mai iza faxa a tsakani, wanda ke yawo da al'amari mai muni.

Ya ku Musulmai …
Lallai haqiqa, Wata jama'a vatacciya ta bijire kuma tana fito-na-fito da wannan al'ummar, wassu (ne 'yan qalilan) kamar cikin tafi; waxanda suka vangare (wa jama'a), kuma tuzgaggu vatattu, waxanda basu da wata manufa face qyasa wutar rashin kwanciyar hankali, da ficewa daga xa'ar shugabanni, sai suka bayyanar da savani da rarrabuwa da husuma, suka kuma zaro takkuban fitina, wai kuma suke yin jihadi da savawa ko kishiyantaka da yin akasi,   da wata aqida 'yar jebu (ba ta asali ba), da kuma wassu fahimtoci masu rauni, ko wassu abinda suka hango, amma masu illa. Ra'ayoyi vatattu sun tuntsurar da su a kan turbobi masu vatarwa, da hanyoyi mabanbanta,    Sai suke kafirtawa, suna tsoratarwa,  suna karkashewa, suna qoqqonawa, suke ha'inci, suke warware alqawura;     Su ba su qyale ko suka bar kafiran amana ba, kuma ba Musulmai suka bari cikin lafiya ba,    Sun jefa kayukansu cikin yanayi na kashe kai mai tsanani,   da suna, ko da'awar yin shahada, sun kuma auka cikin mafi munin yanayin bijirewa wa al'umma da kuma shugaba, da yin fito-na-fito da su, da da'awar yin jihadi.    Dabbobi ne marasa tsari; da suke bin dukkan wanda yayi kira, suke kuma tafiya a bayan dukkan wanda ya yi fito (ko fexuwa).     Idan aka kawo musu hujjoji sai su yi ta musu, ko kuma qa'idodi, sai su kawo maganganun da ba a fahimta, suna kuma qoqarin tunkuxe tabbatattun lamuran addini da hujjoji yasassu; (marasa dalilai); waxanda ba za su qara musu komai ba face shakka da ximuwa da rashin nitsuwa.  Mutane ne masu wuce iyaka, da aikata zalunci,   Mutumin da yake yin musu don kare su to kawai yana yin jayayya ne don kare   varna,   Wanda kuma ya taimake su to lallai yana taimakawa ne don a rushe Musulunci.    Kamar kwari ne da suke son aukawa cikin wuta,  Masu qananun shekaru (da rashin sanin yau da gobe), wawaye, ma'abuta sharri.    
Sun sava wa abinda magabata suke, akansa,   Wanda salihan Mutanen baya suka bi shi, a matsayin MANHAJI.  Sai suka bar abinda xaukacin Mutanen yau suka ruwaito shi daga na jiya (na addini), da wanda maruwaita dayawa suka qarvo daga mutane dayawa, da wanda jama'a suka ruwaito daga jama'a, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace:  Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanda ya bijire daga xa'a, kuma ya vangare daga jama'a, sa'an nan ya mutu, to ya mutu mutuwar jahiliyya, Kuma duk wanda ya fita daga cikin al'ummata, ya kuma yi fito-na-fito da al'ummata; yana dukan nagarinsu da fajirinsu, baya kuma cika alqawari ga ma'abucin alqawari, to baya tare da ni", Muslim ya fitar da wannan hadisi.                
            Jama'a ne vatattu,   waxanda suke xauke da zukatan  da suka cike da qiyayya, da kuma qiraza masu hassada,      Ya kasance daga cikin munanan aiyukansu, Mummunan aiki kuma abin kyama, wanda shine laifin: Tada borm a garin Ahsa'i (a masallacin juma'a, ranar juma'ar da ta gabata), wanda hannayen ha'inci, da warware alqawura suka zartar. (Khawarijawa) mummunan tsiro, wanda da sannu za a tuttunvuke su, a cire, Kana jijiyoyi masu varna; waxanda ba za a ragar musu ba; za a tsittsinke su. Yanayin halaka da Lalacewa yana jiransu, aikin azama kuma shi zai girbe su.

            Ya ku Musulmai …
Samartaka, da yarinta, da qarancin shekaru suna haxe da gafala da damar a iya ruxar Mutum, saboda saurayi mai qaramin shekaru yana da qarancin hangen nesa da basira da hikima da gogewa a cikin rayuwa.    Kuma duk lokacin da mai qarancin shekaru yayi abuta da Mutumin da ba a aminta da soyayyarsa, ko aqidarsa da amanarsa da addininsa ba = to sai wannan mutumin mai dauxa ya yaudare shi; cikin rashin sani, ya kuma ciyar da shi mummunan abu; ta inda bai sani ba, ya kuma shayar da shi guba ta inda baya zato,  sa'annan ya sanya shi cikin rundunar da za ta yaqi; addininta, da kuma qasarsa, da iyalansa, da qabilarsa ba tare da ya san yana aikata hakan ba.    
Kuma duk mutumin da ya bar xansa yana kutsawa cikin kwarin da dabbobi masu farauta suke, a cikinsa, yana kuma wargi da wasa cikin namun daji mayunwata, yana tafiya a cikin duhu, yana kuma qetare wuraren halaka; ko cikin qarafu, to haqiqa (irin wannan Uban) ya sayar da xansa, kuma ya tozarta shi, kuma ya sanya shi ya zama abin kwacen ashararan halittu; ta hanyar yaudara,  sa'an nan abin nufa; da buqatunsu munana.     
Kuma duk wanda ya bar yaransa suna kukkutsawa cikin wasanni da savo, suna kai-komo cikin wuraren fitintinu, suna kuma aukawa cikin taron Mutane, ta yadda suke yin nitso cikin yawa-yawan halittu, da cunkoso, Suna yin abuta da duk wanda suka so; ba tare da wata kulawa ba, su kwana a wajen gidaddaji ba tare da wani tsoro ba, suna kuma zama a nesa (da iyaye) ba tare da wata tambaya ba,  (duk wanda ya aikata haka) to haqiqa ya tauye haqqoqinsu kuma ya zalunci su.       Saboda samari –a irin haka- su kan wayi-gari suna ababen farauta ga sautin shexanu, da hudubobin masu tsegumi, da littatafan masu qetare iyaka; mavarnata, da fatawoyin khawarijawa masu qiyayya, da abubuwan qungiyoyi da ake yinsu a sirrance, da irin qungiyoyin da suke kafirta Mutane suna karkashe su, da sauran qungiyoyin ta'asubanci masu shuka adawa da qiyayya a cikin zukatan samarinmu, akan shugabanninmu da malumanmu da qasarmu.

Ya ku Iyaye, da sauran masu jivintar lamarin 'ya'ya …
Ku kiyayi halin sakaci, da shagala, da sako-sako, da gafala.
Kuma ku dasa a cikin rayukan 'ya'yanku, soyayyar addininsu da qasarsu, da so da wala'i ga shuwagabanninsu da jami'an tsaronsu, da malumansu da limamansu.
Kuma hakan ba zai tabbata ba sai ta hanyar kwarara  musu matsanancin tausayi (da bada kulawa a gare su), da sonsu, da bada kyautuka da kyautatawa, da riqansu a matsayin abokai, da rayuwa tare da su da kyautatawa, da karantarwa, da basu kariya.


Ya ku Musulmai …
Khawarijawa (bijirarru 'yan aware) masu savo ne ga Allah da ManzonSa (صلى الله عليه وسلم); suna aiki ne da savanin littafin Allah (Aqlur'ani) da sunnar (Annabi mai karimci),  kuma Su kashi biyu ne; wato: qafon Shexan guda biyu; (Na farkon sune:) ZAUNANNU DAGA CIKINSU. SAI JIKOKINSU MASU YIN HIDIMA;   
Su zaunannun 'yan a-ware (khawarijawa) Su ne suke aikin qawata wa masu qananan shekarun da suka yaudara yin zanga-zanga, da yin fito-na-fito da shugabanni ko bijire musu, kuma sune suke halatta musu aikin hallaka kayukansu, suna yaudararsu da cewa za a gafarta musu, wai kuma za su shiga aljannoni, Suna kuma nuna musu –da fatawowinsu munana- kyan maqala bomabomai a jikinsu; waxanda suke tashi don su halaka Mutane, da tuqa motoci masu bomabomai, da kuma tayar da su ko qona kai a cikin masallatai da gidaddajin ibada, da kasuwanni, da wuraren taruwan Mutane.     
Su kuma JIKOKINSU DA SUKE YIN HIDIMA (suna masu zartar da dukkan abubuwan da shugabannin suka umurce su da shi), suna da qarancin shekaru, da wauta ko qarancin hankali; wannan ya sanya su, suke zartar da abubuwan da shexanu suka tsara musu, suke kuma tayar da wuta da karyayyun itatuwa. 

Ya kai wannan saurayi matashi….
Kada maganar da aka qawata da yaudara da qarya, da kuma kwalliya ta varna ta yaudare ka !        Saboda  da mutumin da ya kira ka don aikata wannan aikin jihadi yake yi, ko ace: Nasiha yake yi, to da shi da kansa ya yi gaggawar aikin tayar da borm a jikinsa gabanin ya maka da'awa ko ya kira ka zuwa ga qona kanka,  (saidai bai aikata hakan ba), Sai ya vatar da kai; ta hanyar saka ka bin son zuciya, Shi kuma ya zavar wa kansa: Jin daxi, da samun dukiya, da rayuwa, da wanzuwa a duniya,    Kai kuma ya zavar maka da: Mutuwa da hallaka da qarewa,
Sai Ka faxaka,
don ka fita daga cikin gafalarka,
Ka kuma tuba daga kan vatar da ka ke, akanta,
Ka dawo izuwa ga shiriyarka,
Ka da ka kasance bala'i da fitina akan kanka, da iyalanka.

Ya kai Wanda ka yi riqo da abaucewa !
Ka kuma kama hanyar tauri, da tsaurin kai !!
Ka ke yin musu, akan zalunci da varna !!!

Ya kai Wanda ka faxi abinda ake jin nauyinsa a kunnuwa,
Ka buxi baki; kake faxin abinda a xabi'a ake jin qyamar faxinsa,

            Ya kai wanda ka  tove biyayyar shugabanni,
            Kuma ka fice tare da sava wa jama'ar musulmai,

Ya kai wanda aka yi masa aikin jinkiri
(wato, Allah bai gaggauta kama shi ba),
Aka yi masa talala,
Aka sanya wa kama shi lokaci,
Aka dakata masa sannu-sannu,
Jinkirin bai qara komai a gare ka ba, face qara karkacewa?
Sarara maka da aka yi bai yi qarin komai ba, face daxa kangarewa?

Ka yanke varnar da kake, a kai,
Ka dawo cikin basirarka,
Ka kuma komo wa gaskiya,
Gabanin a kamo ka, alhalin kumatunka suna haxe da turvaya,
Sannan
A tsayar da kai domin hukunci na adalci, kana qasqantacce,
Kuma, ka tuba, ka gyara, gabanin abinda kake tsoro ya sauka a kanka (Na azaba, ko mutuwa).

Idan kuma, ka qi, ka tuba, da zavinka, to
Sai ka jira takobin gaya-wa-jini na wuce.

            Ya Allah! Ka kare mu daga waswasin shexanu, Ka kuma nisantar da mu daga hanyoyin vatattu masu varna, Ina neman gafarar Allah, kuma ku nemi gafararSa, Mamakin girman rabon masu neman gafara!

HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah; godiyar da ta kai yanayi na cika da qarshensa.  Irin godiyar da take hukunta samun yardarSa, Ya kuma sanya qarin kusanci da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke  bashi da abokin tarayya, shaidawar da muke fatan samun afuwarSa da kuma lafiyarSa da rahamarSa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, kuma annabinSa ne, zavavvenSa, abun ganawanSa, waliyyinSa, abun yardarSa, kuma wanda ya zava.
Allah ka yi daxin salati da sallama a gare shi, da kuma ga iyalanSa da sahabbanSa, da wanda ya yi aiki da sunnarsa, ya kuma shiryu da shiriyarsa.
Bayan haka;

Ya ku Musulmai,,,
Ku kiyaye dokokin Allah; sai a tunkuxe muku musibobi masu girma, Kuma gwargwadon ingancin niyyoyi ne kyaututtuka suke zuwa, kuma sirrin samun gyara da biyayya shine gyaruwan abinda ke voye (cikin zuciya) da na sirri.
"Wannan littafi ne da muka saukar da shi Mai albarka, sai ku bi shi, kuma ku bi dokoki, tsammanin za a yi muku rahama" [An'am: 155].

            Ya ku Musulmai,,,
 Jarabawar Mutanen (garin Madhaya, ta qasar Siria) waxanda maqiyan addini da Sunnah, suka musu qawanyar hana fita da shiga (na tsawon watanni), da haxin bakin manyan-manyan qasashen kafiran duniya, dalili ne da ke nuna qarfa-qarfa, ko kuma kama-karya; wanda ke gudana a duniyarmu ta yau (mai qarfi alkalin qauye), Al'umma ce guda, ake qasqantar da ita, da makamin: yunwantarwa, da tsoratarwa. Da kuma mata da tsofaffi, da yara qanana, waxanda tsoro ya ke samunsu da yunwa da cutuka da sanyi; ba tare da sun samu magani ko abinci ko abin shumfuxi ko mayafai ba; Sun rasa kayan tunkuxe sanyi a cikin tsananin funturu.
Lallai manyan-manyan qasashen duniya, saboda shiru da suka yi, da rashin motsawansu, da qin taimakawa, alhalin suna ganin hotunan da suke tada hankula da tsoratarwa, to suma za a qidaya su daga cikin waxanda suka yi tarayya cikin wannan mummunan aiki na kisa.
Kuma lallai garurrukan Sunnah waxanda ake rurrushe musu masallatansu, da makarantunsu, ake kuma karkashe zavavan mutane da manyan cikinsu, sannan ake qawanyar hana shigi da fici (a garurrukansu), har su mutu = dalili ne da baya barin shakka, kan: Yadda aka haxu don nufan mabiyan Sunnah; da hukumominsu da al'ummarsu (da sharri), yake kuma nuna voyayyen shiri da kuma yadda Su maqiyan wannan al'ummar suka haxu, akan wannan manufar. Ya ke kuma qara, nuna wani salo da ake bi, na qoqarin gutsuttsura qasashe, da qauratar da mutane daga mahallansu, da da'awar za a kawo gyara.  
"Kuma da Allah ya nufa da basu kasha juna ba, saidai Allah yana aikata abinda yake nufi" [Baqarah: 253].

Ya ku Musulmai …
Ku tashi; don taimakon 'yan'uwanku, da duk abinda kuke da iko, na mayafai, da nau'ukan magani, da abubuwan ci.
Kuma wajibi ne akan hukumomin larabawa, dana Musulmai kada su ci-gaba da zama shiru, basa motsi (suna zura ido), akan tsare-tsaren da ake zuwa da su, na nufan qasashensu da sharri, ko yi musu qawanya (da hana su fita).

Ya kai wanda yake almubazzaranci da dukiyarsa,
Ya ke kuma wasa da halal xinsa,

Ya waxanda kuke yi almubazzaranci,
kuke varna cikin abinci (israaf),
kuke wasa da ni'imomin da Allah ya muku

Rahama, ta fice daga zukatanku ne,
Tausayi aka cire daga qirazanku !
Ba kwa ganin abinda ke faruwa da 'yan'uwanku ne?

Ku ji tsoron Allah (ku kiyaye dokokinsa) gabanin azaba da uqubarsa su sauka akanku,,,,,,,,,,,

Sai ku yi salati da sallama ga Manzon shiriya, wanda zai ceci mutane gabaxaya,                                 domin
Duk wanda yayi masa salati guda xaya to Allah zai masa guda goma.

            Zuwa ga Halittu aka turo shi, don ya zama rahama da jin qai,       Ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa.

            Mutanen baya basu rasa wani Mutum da ya kai Muhammadu ba
Kuma babu kwatankwacinsa da za a rasa, har qiyama.

Kuma shin musibar rasa wani wanda ya halaka, ta kai
Irin musibar Rashin, da ta kasance, a ranar da Muhammadu ya rasu?

            Haske ne da ya haskaka wa Mutane gabaxayansu,
Duk wanda aka shiryar zuwa wannan haske mai albarka to ya shiryu,

            Allah ya yi salati, da waxanda suke kewaye da al'arshinSa,
Da halittun kirki akan Mai albarka; Ahmadu,

            Ya Ubangiji, ka haxa mu tare da annabinmu,
A cikin aljannar da take share kanbun bakan masu hassada,

            A cikin aljannar Firdausi, ka rubuta halinmu,
Ya Ma'abucin girma, Ma'abucin xaukaka, da shugabanci.

            Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga annabinmu da shugabanmu; Muhammadu, Kuma Ya Allah! Ka yarda da iyalai da sahabbai, da wanda ya bi su, da wanda ya bi wanda ya bi su, Ka haxa da Mu tare da Su, Ya Mai karimci ya Mai baiwa!
            Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai! 
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai!  !
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai! ! !
Kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai!
Ka kiyaye iyakokin addini!
Kuma ka halakar da azzalumai da masu qetare iyaka!
Kuma, ka taimaki iyalanmu a qasar Sham, da kuma a Falasxinu akan mutane azzalumai, ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka dauwamar wa qasarmu amincinta da wadacinta, da buwayarta da zaman lafiyanta. Kuma ka datar da shugabanmu kuma jagoran lamarinmu; Mai Hidiman Masallatan Harami Guda Biyu Maxaukaka zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, kuma ka kama kansa; ka ja shi zuwa ga aikin biyayya da taqawa, Ya Allah! Ka datar da shi, da na'ibansa biyu zuwa ga abinda a cikinsa akwai amfanin bayi da gyaruwan Musulmai, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka xauke –a qasashen Musulmai- husumomi da jayayya, da yaquka, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka datar da mu don aikata abin da yake yardar da kai, Ka kuma nisantar da mu daga sava maka.
Ya Allah! Ka datar da mu don aikata abin da yake yardar da kai, Ka kuma nisantar da mu daga sava maka.
Kuma ka sanya mu daga cikin waxanda suke jin tsoronka, suke bin dokokinka! Ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka warkar da marasa lafiyan cikinmu, kuma ka bada lafiya ga wanda aka jarraba daga cikinmu, kuma ka warware bautar bayi daga cikinmu, Kuma ka yi rahama wa mamatanmu, ka taimake mu akan wanda yake adawa da mu, Ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka sanya addu'oinmu su zama karvavvu,
Ya Allah! Ka sanya addu'oinmu su zama karvavvu, kuma kiranmu ya zama abun xagawa, YA MAI JI, YA MAKUSANCI, YA MAI AMSAWA !!!

انتهى.  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...