AIYUKAN FAXAXA MASALLACIN HARAMI
TARE DA BAYANIN
AIKIN FAXAXAWA SABO DA AKE ZARTARWA
(توسعات
المسجد الحرام، ومشروع التوسعة الجديدة)
AIKIN FAXAXA HARAMIN MAKKAH MAXAUKAKI
DAGA/ HADIMIN HARAMI BIYU MAXAUKAKA;
SARKI ABDULLAHI XAN ABDUL'AZIZ ALU-SA'UD
(توسعة
خادم الحرمين الشريفين الملك عبد الله بن عبد العزيز آل سعود للحرم المكي الشريف)
TANADAR
OFISHIN SHA'ANONIN MASALLACI MAI
ALFARMA DA MASALLACIN ANNABI
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Allah ya
halitta Mutum domin ya raya wannan duniyar, ya kuma kevance wani kwari mai
girma dakasancewa wurin da ya fi tsarki; wanda shine: MAKKAH.
Kuma a
cikin garin Makkah akwai XAKI NA FARKO da aka gina a bayan qasa, don bautar
Allah Shi kaxai.
Matakai dayawa
Xakin Allah mai alfarma ya bi ta kansu, har zuwa, ganin Hadimin Masallatan
Harami Guda Biyu; (Wato: Sarki Abdullahi) don shima –a tarihance- ya dangwala
hannunsa (wajen yin hidimar qara faxaxa Masallacin), kuma don ya bar wata alama
da zata dawwama, wacce 'ya'ya da jikoki za su riqa tuna shi da ita, suna kuma addu'ar
sakayya da lada a gare shi (su riqa, shi masa albarka).
Cikakkiyar
surar da zata nuna muhimmacin wannan lokacin zata bayyana ne idan aka xauko bayanin;
daga farkon aikin faxaxawa da aka yi wa MASALLACI MAI ALFARMA, a zamanin khalifancin
Alfaruq; khalifa Umar xan Alkhaxxab (رضي الله
عنه);
a lokacin da ya iyakance filin masallacin
harami ta hanyar gina katanga wacce tsayinta shine: qafa shida (6, wato: qama
xaya), a shekara ta goma sha bakwai (17) daga hijira.
Bayan
kaman shekaru takwas (8) kuma, Sai Khalifa Usman xan Affan (رضي الله عنه) ya qirqiro wani qarin na daban, wanda ya
qara wax akin Allah kwar-jini, da xaukaka.
Sa'an
nan Sai gwamna Abdullahi xan Az-zubair (رضي الله
عنه) ya qara faxaxa wurin sallah da xawafi ta vangaren gabas.
Haka kuma
khalifan daular Abbasiyya; mai suna: Abu-Ja'afar Almansur shima ya qara wani
fili wa masallacin ta vangaren arewa da yamma.
Haka kuma,
Xansa; Muhammadu Almahdiy shima ya bi mahaifin, ta hanyar qara wani filin ta
kowani vangare (gabas da yamma, kudu da arewa).
Sa'an
na sai khalifa mai suna: Mu'utadhid shima ya yi wani qarin ta arewa.
Amma
shi kuma sarki Muqtadir, a shekara ta 306 na hijira shi kuma ya yi qarinsa ne
ta yamma.
Kuma da
haka ne, faxin masallacin Makkah, da kuma filin xawafi; wanda daxaxxun runfunan
da aka yi a zamanin khalifancin daular Abbasiyya suke kewaye da shi = suka
tabbatu akan wannan yanayi har tsawon shekaru 1069, Wanda a cikinsu babu wani
qarin gini da aka yi a masallacin haramin Makkah, Saidai aiyukan gyare-gyare da kwaskwarima (a
lokuta mabanbanta), da kuma sanya qubbobi akan waxannan rumfunan, a lokaci, da kuma
umurnin sarkin daular Usmaniyya; Salim Na-biyu.
A ZAMANIN
SARAUTAR SAUDIYYA, Sai (Wanda muke neman gafarar Allah a gare shi) wanda kuma
shine ya assasa daular saudiyya; wato: Sarki Abdul'aziz, Alu-Sa'ud = ya dasa
harsashen fara aiyukan qarin farko na daular Saudiyya; kuma shine farkon qarin da ya haxe wurin
sa'ayi (na Safa da Marwa); ya kuma jona shi da masallaci mai alfarma, kamar
yadda aka qara hawan sama (na beni) wanda ya ninka faxin masallacin gabaxaya,
tare kuma da samar da masallacin cikin qasa. Kuma a nan ne, aka qara wurin yin
xawafi, kamar yadda ya ke a yanzu.
Sa'an nan
sai sarki Sa'ud xan Abdul'aziz, da sarki Faisal (Allah ya yi rahama a gare su) suka
qarisa abinda babansu wanda ya assasa daular saudiya ya farar.
A lokacin qarin
da daular saudiya na biyu kuma ga haramin Makkah maxaukaki a zamanin mulkin mai
hidimar harami guda maxaukaka; wato sarki Fahad xan Abdul'aziz (Allah yayi
rahama a gare shi) sai aka yi qarin wani wuri daga vangaren yanma, wanda aka
haxa shi da harami, sannan aka daidaita su har ta fiskar tsari ko yanayin gini.
Kamar yadda
aka shirya saman rufin masallacin, ga masu sallah, aka kuma faxaxa harabar da
ta kewaye masallacin domin haramin Makkah maxaukaki ya xauki masu sallah kamar
Mutane dubu xari shida (600, 000) da dukkan qare-qaren da aka yi masa.
Saidai a
shekarun qarshe-qarshe an samu qaruwar da ba a tava samun irinta ba; na adadin
mahajjata da masu umrah da ziyara, saboda ci-gaban da aka samu da bunqasa a
hanyoyin tafiye-tafiye, da kuma qaruwar yawan musulmai wannan ya sa masallacin
ya wayi gari cikin matsananciyar buqatar neman qari, Sai qoqarin warware
matsalar da samar mata da mafita ya zama babban abinda mai hidimar harami biyu maxaukaka
ya himmatu da shi (Sarki Abdullahi), Sai kuma ya bada aikin faxaxa wurin sa'ayi
(na Safah da Marwah); wanda aka gama aikinsa a shekarar da ta wuce, ta yadda
faxinsa ya ninku har zuwa sau huxu. Sai
kuma aka qara wani hawan, a sama, da kuma wani a cikin qasa, tare kuma da ninka
filin sa'ayi; daga mita 20 zuwa mita 40, domin sabon wurin Safah da Marwah ya
ishi qarin masallata kamar 70000. Sai kuma
aikin qara nazari mai zurfi na yadda za a warware matsalar cunkoson ya ci-gaba,
wanda ya haifar da bada umurnin bunqasa masallacin; wanda a tarihi ba a tava
yin irinsa ba wajen girma, ta yadda idan an gama ta, a dunqule; filin
masallacin harami, tare da wannan qarin zai wayi gari ya kai ninki ukun girman
filin a yanzu, don sabon qarin shi kaxai xinsa ya iya xaukar masallata kimanin
Mutane miliyan xaya (1000000), shi kuma masallacin gabaxaya ya iya xaukar
masallata fiye da Mutane miliyan xaya da dubu xari shida (1,600,000), ba a
kwanakin cunkoso ba. Amma a lokacin hajji
da sauran kwanakin tsananin cunkosu nan kuma sabon qarin zai xauki adadin mahajjata
da masu umrah wanda yafi haka. Wannan kuma sharar fage ne ga wassu qare-qaren
da suke tafe (nan gaba), don su zama hidima wa garin Makkatul makarramah da
kuma baqin (Allah) mai rahama.
Kuma shi
wannan qarin da yafi na bayansa girma, zai kasance ne ta vangaren arewacin
masallacin harami, kuma wannan aikin zai qunshi: abubuwa guda shida manya; (1)
Ginin sabon qari. (2) Filayen wajen masallaci (harabobi). (3) Gadodi (4) Ginin
sama (harabar sama, mai gangarowa), (5) Wuraren shigewan masu tafiyar qafa (6)
da kuma nau'ukan gine-gine don hidimomi dayawa mabanbanta, waxanda sun haxa da:
Cibiyoyin lafiya, da ofishin 'yan
kwana-kwana, da asibiti, da cibiyar tashar sanyaya iska (A C), da kuma samar ko
bada wutan lantarki (ihtiyaxi;
kar-ta-kwana, na wucin gadi). Waxannan vangarori (guda shida) sashinsu
yana qarfafa ko kammala sashi ne, don samar da masallaci na zamani wanda yake
da gamewa, da kuma yin amfani da mafi kyan kayayyakin zamani da takanolaji, don
kawo aminci da hutu ga mahajjata da masu umrah, da kuma isowarsu cikin sauri da
sauqi zuwa masallaci mai alfarma.
Tunanin
kama wannan aikin wanda ya fara da rushe ko shishirya vangaren da ake kiransa:
Almanxiqatu As-shamiyyah (da ke arewa) na aikin qarin gini wa masallacin
haramin Makkah ya xauki
shakali ne irin na haske, wanda ya fara daga: cibiyar Ka'abah ta dukkan vangarorin gabaxaya, domin fiskantar
da xaukacin masallata gabaxaya zuwa ga vangaren alqiblah.
Kuma wannan
wurin da ake aikin ginin qara shi a jikin masallaci ta qunshi babbar qofa, mai
suna: QOFAR SARKI ABDULLAHI, wanda a saman qofar akwai hasumiya manya-manya
guda biyu, domin hasumiyoyin harami su wayi gari sun zama guda goma sha xaya (11).
Kuma saboda
sauqaqe kai-komon masallata, ta hanyar da ta fi tsari, da yawan aminci, da kuma
saboda kai-komon nasu cikin jagoranci, da taqaita cunkoso Sai aka qara yawan gadodi;
waxanda za su qulle tsakanin harabar da
take sama ta arewa da kuma ginin harami na yanzu, wanda kuma su gadodin za su
tsaga; kana su bi ta cikin ginin sabon qari gabaxayansa. Tare da shirya harabar
qasa da take tsakanin sabon masallacin da aka qara da kuma harabar sama da take
a can baya, wanda za ta xauki sahu masu yawa na qarin masallata.
Wannan tsararren
wurin da aka gina ta vangaren arewa, a cikin harabarsa manya-manyan lemomin da ake
buxe su da na'urori suna qawata shi, Wannan
kuma don su bada kariya ga masallata daga zafin rana, da kuma ruwan sama.
A qarqashin
harabobi kuma an samar da banxakai da wuraren alwala, da kuma wassu wurare da
ofisoshi masu gamammen amfani.
A wajen samar
da harabobin sama da suke vangaren arewa, ta can baya kuma, an lura da matakai
guda shida da suke bin juna, waxanda suke dacewa da yanayi ko xabi'ar duwatsun
da suka kewaye wurin, wanda kuma za a yi amfani da rufinsu a matsayin qarin
wuraren da za a riqa yin sallah, a wani yanayi mai qayatarwa.
Kuma, a
qasan waxannan harabobin sama: An samar da banxakai, da wuraren alwala, qari
akan xakunan kunne-kunne da ofisoshi, da kuma cibiyoyin lafiya.
Kuma
hanyar da ta yi zobe (ring road) wa masallacin harami ta farko, tana kutsawa ta
cikin ginin harabar baya, wacce take sama ta arewa, daga gabas zuwa yamma. Tare
da qulluwa da tashoshin motocin… da aka tanada don kai-komo, domin sauqaqe
lamarin shigi da fici zuwa ginin sabon masallaci. Qari akan hanyoyin shigewan
masu tafiyan qafa; waxanda suke faraway daga harabar qasa na masallaci, suke
kuma tafiya vangaren arewacin masallaci mai alfarma; inda aka tanadi asibiti da
gine-ginen 'yan sandan kar-ta-kwana, da jami'an tsaro, a ta wannan vangaren.
Haka nan
kuma, ginanniyar hanyar cikin qasa (NAFAQU KHIDIMAAT) itama take kutsawa ta
cikin ginin harabar baya da take sama, don ta haxe babbar tashar motoci da kuma
masallacin harami.
Daga Qofar
Mai Hidimar Harami Biyu Maxaukaka (sarki Abdullahi) muke shiga ginin sabon
masallaci, domin mu samu mashiga maxaukaki mai girma (الممر الشرفي) wanda qubba mai girma da take buxewa tana
qawata shi.
A geffan wannan qubbar kuma guda biyu akwai wani
hol (قاعة) don yin sallah, wanda aka yi shi akan
matakai huxu waxanda tsakiyansu ya sha banban, a hawa na xaya da na biyu,
waxanda kuma suka kasu zuwa manya-manyan hol da qanana, tsakaninsu kuma akwai
filaye ta ciki, a tsawon wannan ginin, wanda kuma aka yi aikin rufin kansu da
rufi na gilashi mai buxewa, da kuma qubbobi guda huxu waxanda basa motsawa.
Wannan
shine zamanin wannan sarki (sarki Abdullahi) Mai Hidimar Masallatan Harami Biyu
Maxaukaka, wanda yak e cika abinda ya alqawarta wa al'ummarsa na cika abinda
khalifa shiryayye; Umar xan Alkhaxxabi (رضي الله
عنه) ya fara (Na aiki a masallacn harami).
Kuma
abin mamaki ba ne, a wurinku irin wannan kyautayin da masarautar larabawa ta
Saudiya take rayuwa a cikinsa, a irin wannan mataki da masallacin harami yake rayuwa
a cikinsa, wanda tarihinsa ya sha banban.
Ya
Mai Hidimar Masallatan Harami Guda Biyu, da irin umurnin da kuka bayar ne
maxaukaki mai karamci, Wannan aiki na-azo a gani yake wanda kuka yi umurnin a kammala
aikinsa, a cikin shekaru biyu masu zuwa, da izinin Allah maxaukaki da sannu
aikin ganin an qare shi zai ci gaba tuquru, dare da rana.
"Ya ku waxanda suka yi imani idan kuka
taimaki Allah sai ya taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku" [Muhammadu:
7].
No comments:
Post a Comment