2016/02/14

LADDUBAN MASALLACIN ANNABI (من آداب المسجد النبوي )







LADDUBAN MASALLACIN ANNABI
(مِن آداب المسجد النبوي)

TANADAR
Ofishin FAXAKARWA DA NUSARWA
Da ke qarqashin
Ofishin WAKILCIN GAMAMMIYAR MA'AIKATA,
DAKE WAKILTAR SHA'ANONIN MASALLACIN ANNABI (s.a.w)




FASSARAR
Abubakar Hamza



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Salati da sallama su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan haka:

Xan'uwana Musulmi!
Ka gode wa Allah Ubangijinka; wanda ya kawo ka Masallacin AnnabinSa (صلى الله عليه وسلم), wanda kuma Allah ya fifita shi, sannan ya sanya yin sallah a cikinsa ya zama yafi salloli dubu a wani masallacin wanda ba shi ba; in banda Masallaci mai alfarma (da ke garin Makkah), kuma ya sanya wanda ya zo wannan masallacin don koyan wani alheri ko ya koyar, a matsayin mai jihadi fiysabili Allah.

Sai ka qara kwaxayi –Ya kai wanda nake xan'uwantaka da shi don Allah- wajen yin sallah a masallacin Annabi, da neman fahimtar addini, ta hanyar halartar halqoqin ilimi, domin ka bauta wa Allah akan basira, sannan ka riqa yin tambayoyi kan dukkan abinda ka jahilta, Allah ta'alah yana cewa:
{فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ} [سورة النحل: 43].
"Kuma ku tambayi ma'abuta ilimi, idan kuka kasance ba ku da sani" [Nahli: 43].

          Ka sani, Wannan Masallacin yana da LADDUBAN da ake kula da su, da wassu HALAYYA; waxanda ake aiki da su.
Anan, Za mu tunatar da kai, sashinsu:

1) Musulmi namiji da musulma mace su zo (Masallacin) cikin nitsuwa da ladabi, da kuma tsarki, da kyakkyawan shiga, da qamshi mai daxi, tare da nisantar nau'ukan wari ababen qi, kamar taba, da albasa, da waninsu, wannan kuma saboda Mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan-Adam suke cutuwa da shi.
2) Idan  za ka shiga Masallacin; Ka gabatar da shigar da qafarta ta hagu, Sai kuma ka ce: "BISMILLAHI, WASSALATU WASSALAMU ALA RASULILLAH, A'UZU BILLAHIL AZIM, WA BI WAJHIHIL KARIM, WA SULXANIHIL QADIM, MINASH SHAIXANIR RAJIM, ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIKA", Daga nan sai ka yi sallah raka'oi biyu, (mai suna) gaisuwar Masallaci. Sai kuma ka yi qoqari wajen ambaton Allah, da ibada, da karatun alqur'ani.
3) Idan ka zo yin sallama wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) Sai ka tsaya ta fiskar qabarin, cikin ladabi, da qanqan da sauti, Sannan ka ce: "ASSALAMU ALAIKA WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU, ASSH'HADU ANNAKA BALLAGTA ARRISALAH, WA ADDAITA AL'AMANAH, WA NASAHTA AL'UMMAH, WA JAHADTA FIY ALLAHI HAQQA JIHADIH, FA JAZAKA ALLAHU ANNIY WA ANIL MUSLIMINA KHAIRAL JAZA'I".
Sa'annan ya yi sallama wa Abubakar da Umar, ta hanyar ambaton sunayensu (رضي الله عنهما).
Sa'an nan ka tafi duk wurin da ka so a cikin wannan masallacin, ka kuma roqi dukkan abinda ka so, daga cikin ababen roqa waxanda suka halatta a shari'a.
Kuma  a cikin zuciyarka ka sanya aqidar cewa, lallai janyo wani amfani da tunkuxe cuta basa kasancewa face daga Allah maxaukaki; Sai ka yi ta neman buqatunka daga wurinsa shi kaxai, na duniya da lahira, ba tare da sanya wani tsani ba, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلْ اللَّهَ وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللَّه".
Ma'ana: "Kuma idan za ka yi roqo ka roqi Allah, haka idan za ka nemi taimako ka nema a wurin Allah".
Kuma ka da ka shafi, ko ka sumbaci katanga ko waninsa.
Kuma ka da ka yi sallama wa qabarin alhalin kana cikin yanayi irin na mai sallah.
Kuma ka da ka yi sallaman alhalin kana nesa da qabarin; saboda hakan savanin abinda magabatan kwarai suka kasance akansa ne (رضي الله عنهم).
4) Ka ribaci samuwarka a wannan masallacin; Idan ka yi sallar nafila sai ka zauna a wurin zamanka, kana TASBIHI wa Allah, kana AMBATONSA, kuma ka yawaita karatun alqur'ani.
Kuma ka zavar wa kanka wurin da ya yi nesa da cunkoso; tsoron ka da ka yi tarayya cikin samar da cunkoson da zai cutar da 'yan'uwanka Musulmai.
5) Yi kwaxayin tottoshe kafa a cikin safu, tare da yin qoqari wajen samun safun farko-farko; domin falalarsu, idan hakan ya yiwu ba tare da haifar da cunkoso ba.
Kuma ka nisanci zama a wuraren shigewa, da mashigan masallaci; don kada ka cutar da 'yan'uwanka Musulmai, ko ka quntata musu.
Kuma kada ka yi gaba da liman, a lokacin da aiwatar da sallah ya kama ka a harabar masallaci (ta gaba).
6) Ka girmama littafin Allah maxaukaki; ka da ka yi rubutu a jikinsa, kada kuma ka riqa wasa da fefofinsa, Sannan ka da ka sanya takalminka a gefensa.
7) Ka kiyaye tsaftar Masallacin, da kuma harabarsa, daga dukkan abinda zai cutar, ko kuma kaki.
Kuma ka karantar da 'ya'yanka ladduban masallaci, ka kuma kiyaye su daga yin wargi da wasa, ko xaxxaga sauti (da shewa).
8) Yi qoqarin rage cunkoso, a lokacin fita daga masallaci; ta hanyar jinkirta fitanka na wani lokaci xan kaxan, har zuwa lokacin da cunkoson zai ragu.
9) Kuma ka sani cewa, lallai masallaci ba wurin barci ba ne, ko yin roqo, ko cikiyar kayayyakin da suka vace.
10)                  Ka da ka yi alwala da ruwan da aka tanada don sha, kuma ka da ka sanya shunfuxan masallaci su zama ababen tada kai (filo), ko mayafan rufuwa; saboda an ajiye su ne a matsayin WAQAFAN da za a riqa sallah a kansu, ba don masallata su riqe su a matsayin shumfuxai ba.
Haka kuma, ka da ka sanya katakon xora qur'anai su zama a qarqashin kanka don tada shi (filo), saboda an ajiye su ne a matsayin WAQAFI don xora Qur'anai kawai.

Daga qarshe kuma; Muna tunatar da kai cewa, lallai taimakawarka ga ma'aikatan da suke masallacin Annabi (s.a.w), da sanar da su, dukkanin abinda yake wurinka na shawarwari, ko gyare-gyare zai taimaka wajen bunqasa irin hidimar da ake aiwatar da ita ga masu ziyarar wannan wuri mai tsarki; Don haka; kada ka yi taraddadi wajen qaddamar da duk abinda ke tare da kai na hakan.

ALLAH YA KARVA MAKA, KUMA YA NINNIKA LADANKA.

Wassalamu alaikum wa rahmatu Allahi wa barakatuhu.

Tanadar: Ofishin FAXAKARWA DA NUSARWA
Da ke qarqashin
Ofishin WAKILCIN GAMAMMIYAR MA'AIKATA,

DAKE WAKILTAR SHA'ANONIN MASALLACIN ANNABI (s.a.w).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...