BIDIYO FILM; DAKE BAYANIN AIYUKAN "HADIMIN
MASALLATAN HARAMI BIYU"
CIKIN SHEKARU 20 DON FAXAXA DA SAKE GINA MASALLACIN ANNABI MAXAUKAKI
TANADAR
OFISHIN SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA DA
MASALLACIN ANNABI
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
"Kawai, Mai raya
masallatan Allah shi ne, Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya
tsayar da sallah, ya bada zakkah, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah, To,
akwai tsammanin Waxannan su kasance daga shiryayyu" [Tauba:
18].
Yana
faranta mini rai; Na sanar da ku, -daga Madinar Manzo Mai karimci (Salati da
sallama su qara tabbata a gare shi)-, kan wata buqata matsananciya da ta
dabaibaye zuciyata, Wanda kuma itace Na karvi jagorancin wannan qasa
Maxaukakiya, Tare da canza laqabin da za a riqa kirana da shi; daga SAHIBUL
JALALAH (wato: shugaba ma'abucin girma), zuwa wani Laqabin da Nake sonsa, kuma
amfani da Shi zai xaukaka Ni, Shine: MAI HIDIMAR MASALLATAN HARAMI BIYU
MAXAUKAKA (khadimu alharamaini as-sharifaini).
(Sarki Fahad)
Masallacin
Annabi Maxaukaki; Wato masallacin Manzon Allah; (صلى الله عليه وسلم) wanda ya ke garin Madinatul Munawwarah: Ya
samu babban matsayi a zukatan Musulmai, da Maluman tarihi.
Sai mu
koma, ga kwanakin da tarihi ya rubuta, Don mu yi qoqarin gano farkon yadda garin Madinatul Munawarah
ya fara, wanda ta bi matakai masu sauqi wajen bunqasarta, har zuwa lokacin da
aka fari aikin ginin Masallacin Annabi maxaukaki, -kamar yadda za a gani cikin
zanen misaltawa- don Madinatul Munawwarah ta wayi gari, a matsayin cibiyar da
take jagorantar Musulmai, kuma take tsara duk sha'anoninsu, na lamuran da za su
tabbatar da walwalar duniya, da samun ni'imar lahira.
A shekarar
farko ta hijira: Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya tsayu wajen gina MasallacinSa
maxaukaki, Sai aka yi aikin rufinsa da tankar Dabino.
Sa'annan
sai aka yi aikin faxaxa shi, a shekara ta bakwai bayan hijira, a inda
Masallacin ya wayi-gari, yana da kusurwa guda huxu, Tsayinsa kuma kusan zira'i
xari, Wanda kuma ya qunshi: Gurbin Sallan Annabi, da MinbarinSa, da Raudha
maxaukakiya.
Daga nan,
sai Himmar khalifofi, da sauran jagororin Musulmai na aikin faxaxa Masallacin
Annabi Maxaukaki, ta biyo baya.
Haka, masu
sarauta da sarakunan musulmai, suma suka biyo bayansu; Ta yadda suka qara, hasumiyoyi,
da qubbobi, aka kuma shafa zinari a jikin katangu, da usxuwanoni, da qofofi, a
wani yanayin da yake nuna gwanancewar musulmai a fannin aikin gini mai kyau.
A qarshen
shekarun daular Usmaniyyah, Sai aka qawata wannan masallaci da aikin qara shi;
Wanda khalifan daular Usmaniyyah mai suna: As-sulxan Abdulmajid, ya aiwatar,
wanda ya kai kimanin mita 2293, a lissafin murabba'i. Kuma ya gama wannan aikin, a shekarar hijira
ta 1277h, a inda aka canza qubbobi, a rufin masallacin, maimakon katakai.
Shekaru
kamar 90 sun shige, bayan qarin da khalifan daular Usmaniyya; As-sulxan
Abdulmajid, ya yi, Sai Musulmai su ka yi mubaya'a wa shugaban da ya haxe wannan
qasa; mai suna Abdul'aziz xan Abdurrahman; Alu-Sa'ud, Sai ya baiwa masallatan
harami guda biyu maxaukaka muhimmanci, a tsawon mulkinsa; kuma ya yi umurnin
ayi masa qarin daular Saudia ta farko, a shekarar hijira ta 1372h, Sai aka sayi
gidajen da suka kewaye da Masallacin, aka rushe su, aka kuma daidaita su da
qasa, Sai kuma aka sadar da qarin da daular Saudia ta farko ta yi, da wanda
As-sulxan Abdulmajid ya yi, a wani yanayi da yake nuna gwanancewa a fannin
gini, mai kyau.
Wannan
qarin da aka yi, wanda kuma aka kamala shi a shekarar hijira ta 1375h, ya kai
mita 6024 a lissafin murabba'i.
Sai faxi
ko girman Masallacin, da dukkan aikin faxaxa shi da aka yi ta yi, (lokaci bayan
lokaci) ya fi mita 16327 a lissafin murabba'i.
A farkon
zamanin mulkin HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya
kiyaye shi- sai ya tafi akan takun Mahaifinsa; wanda ya assasa wannan qasa, Jagora;
Abdul'aziz xan Abdurrahman (Allah yayi
masa rahama) wajen bada kulawa ga masallatan harami biyu maxaukaka.
Kuma a
cikin shekaru ashirin (20) na bunqasawa da samar da manyan aiyuka, a dukkan
vangarorin rayuwa, Batun masallatan harami guda biyu suna daga abu na farko da
basu muhimmanci (Allah ya daxa kare shi).
Mai
HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- ya xora tubulin farko, na qara aikin faxaxa
Masallacin Annabi maxaukaki, a garin Madinatul Munawwarah, ranar Juma'a, 9 ga
watan Safar, ta shekarar 1405 daga hijira, domin Madinatul Munawwara ta ga,
Shima Masallacin na Annabi, ya samu mafi girman aikin faxaxawa, da ya tava
samu, a tsawon tarihi.
Sai aikin
rurrushe ginin da suke kewaye da masallacin ya fara, bayan an gama biyan
waxanda aka saya daga wurinsu.
Daga nan,
sai aikin ginin faxaxawan da yafi girma ya fara, wanda faxinsa shine: mita
82000 a lissafin murabba'i, domin a wannan karon, faxaawan yafi duk abin da ya
gabace, ta fiskar kyautata gini, da faxi, da qarfi, da kyale-kyale, Tare da
sanya ko riskar da duk abinda Masallacin zai buqata, saboda an samar da kayan
aiki na qarshe, wanda ilimin fannin gine-gine da qere-qere, ya kai izuwa gare
su; kamar QUBBOBI masu motsi; waxanda ake aiki da su, a karo na farko, da kuma
manya-manyan LEMOMI waxanda aka qirqiro, kuma babu irinsu, da MATAKALAI na
lantarki a tsakanin hawan beni da na qasansa; waxanda suke saukake kai-komon
dubban xarurrukan Mutane, da wassu irin RUMFUNA ko LEMOMI da suka qunshi dubban
FILOLI, da dogayen HASUMIYOYI, wanda sune mafi tsawo da aka tava yi a tsarihin
musulunci, da kuma HARABA mai faxi, wanda ba a tava samun irinsa ta fiskar faxi
ba, a tsawon tarihi, waxanda kuma aka shumfuxe kasansa da blok xin fulon da ya
ke tsote zafin rana, da kuma HIDIMOMI mabanbanta na gyaran abinda ya lalace,
madawwami wanda baya yankewa, qarqashin kulawan Babban ofishin sha'anonin
masallatan haramin Makkah da na Annabi. Da kuma sauran wassu abubuwan na daban;
waxanda za su sanya masallacin Annabi maxaukaki, ya zama wata alama ce
bayyananniya akan doron qasa.
HADIMIN
MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- ya bada kansa da dukiyarsa domin hidiman
masallatan harami guda biyu maxaukaka, da kuma kula da mahajjata da masu ziyara
da masu umrah.
Don, kuma
a kiyaye lamarin addini da yanayinsa, Sai (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi-
ya yi umurnin ayi amfani da tsare-tsare da suka dace, da yadda aka gina
masallacin annabi da irin yanayin ginin musulunci. Sannan ya yi umurnin a zrtar
da wannan aikin faxaxawan tare da ci-gaba da gudanar ibada a cikin masallacin;
ba tare da aikin da ke gudana ya tsayar da komai ba.
Harsashin da
aka gina qarin da (Sarki Fahad) mai hidimar masallatai guda biyu maxaukaka, ya
yi wa masallacin Annabi maxaukaki, sun dogara ne akan FILOLI guda 8500 masu
dungu uku na FOLABIY,
wanda aka kafa sashinsu a cikin qasa, kamar tsawon kimanin MITA 30 zuwa 50.
Kuma idan aka haxe waxannan filolin tsayinsu
zai kai, kamar KILO MITA 30.
Kuma a
wajen gino harsashin masallacin (faundation) an yi amfani da kusan buhun siminti
musallah 100000.
Kuma haqiqa an qulle filoli na FOLABIYYA da qarfen yin fila da manara da tushe, wanda yawansu ya kai
tushe guda 1877. Tsayuwansu kuma akan mita 70000 ne na fila mai dungu uku,
wanda aka yi shi da siminti musallah.
Faxin
ginin da (Sarki Fahad) mai hidiman masallatai biyu ya qara, a masallacin Annabi
= ya kai mita 82000 na lissafin murabba'i. Wannan faxin kuma zai baiwa
Mutane kusan 170000 damar yin sallah.
Kuma an shirya saman wannan ginin don a iya yin sallah a kansa, da faxin da aka
qaddara shi da mita 67000 na lissafin murabba'i, wanda kuma Mutane 90000 za su
iya yin sallah.
Kuma
wannan qarin da ya yi, ya haxa da, tanada ko shirya harabar da take kewaye da
wannan masallacin, wanda faxinsa ya kai mita 235000 da lissafin murabba'i.
Sai
faxin cikin masallacin Annabi maxaukaki, bayan wannan qarin, idan aka dunqule
shi ya wayi gari, ya kai mita 98500, a lissafin murabba'i, wato: qarin kawai,
ya kai ninkin tsofon Masallacin Annabi (gabanin qarin) har sau biyar.
A, haka,
sai wuraren da za a iya yin sallah ya zama kusan gurbin masu sallah mutum
miliyan xaya (1000000), a watan ramadana mai albarka, da kuma lokacin hajji.
Qarin
hadimin masallatan harami guda biyu (Sarki Fahad), wanda ya aiwatar a
masallacin Annabi, Ya haxa da RUMFUNA; waxanda suka qunshi fiye da FILOLI guda
2100, waxanda su kuma a samansu, akwai wasu baka; waxanda a lokacin sana'anta
su, da tsatsara su an kula da tsarin da zai kawo daidaito ko ya sanya su, su
zama abu xaya tare da qarin da ake masa laqabin: Qarin daular Saudia na farko.
Shi kuma
rufin wannan qarin ya kasu har zuwa yanki 95, waxanda aka lulluve su
gabaxayansu. In banda yanki guda 27 waxanda su kuma aka keve su da QUBBOBI masu
motsi.
Qarin da
mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) ya yi, ya samar
da sabin HASUMIYA guda shida akan hasumoyoyin da ake da su a masallacin Annabi
maxaukaki; waxanda tsayin kowannensu shine:
mita 104.
Kuma guda
huxu daga cikinsu, suna nan ne a kusurwan wannan qarin guda huxu, su kuma
sauran guda biyun suna jikin mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, ta vangaren
arewa.
Kuma a
saman hasumiyoyin akwai hoton jinjirin wata, wanda aka leleye shi da ruwan zinari,
nauyin kowani xaya daga cikinsu shine ton huxu.
Sai yawan
hasumiyoyin gabaxaya su ka zama guda goma (10), suna haskaka sararin samaniyar
Madina da alamar Imani, wacce ta cika da kevantacciyar alama ta kyau.
Qarin ginin
da mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka yayi wa masallacin annabi,
ya qunshi MASHIGA GUDA BAKWAI manya-manya, ta vangaren gabas, da arewa da
yamma, kuma kowani mashiga yana da qofofi guda biyar a kusa, da kusa, tare kuma
da wassu qofofin guda biyu a ta gefensu.
Sannan
kuma akwai manya-manyan mashiga guda biyu ta vangaren arewa na wannan qarin,
kowanne daga cikinsu yana da qofofi guda uku a wuri xaya, a ta gefensu kuma
akwai qofofi guda huxu.
Kamar
yadda wannan qarin ya qunshi qofofi guda goma (10), a matsayin mashiga da
mafitan matakalai masu motsi na lantarki; domin yin hidima ga hawa na sama na
wannan qarin. Qari akan matakalai guda goma sha takwas (18 ba masu motsi ba) ta
cikin masallaci.
Kuma a
qarshen arewacin masallacin akwai qubbobi guda bakwai (7) da hasumiya guda biyu
a saman mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, domin wannan mashigan ya banbanta
da sauran, kuma domin ya yi nuni kan zanen kalmomin musulunci masu kyau.
Kuma a
saman ginin da mai hidimar masallatan harami guda biyu (sarki Fahad) ya yi,
akwai qubbobi guda 27 masu motsi, Nauyin kowanne xaya daga cikinsu ton 80 ne,
tsayinsa ta sama kuma mita uku ne da rabi (3 1/2) daga
tudun rufin, kuma fiye da mita 16 daga kan qasa. Kuma faxin qubba xaya shine
mita 14 da uku bisa huxun mita (3/4), kuma an yi amfani
da ton 40 ne wajen sana'anta kowace qubba. Kuma ana bubbuxe qobbobin ko a rufe
su ne ta hanyar na'ura; domin a amfana da iska ta xabi'a a wassu yanayin da
suka dace.
Mai
hidiman masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye
shi- shi da kansa, da kuma tunaninsa ya ke bibiyar matakan zanen aikin da
qirqiransa, da zartar da shi, a inda ya riqa miqa dukkanin abinda zai sauqaqe
aikin, musamman idan wani abu ya gitta ko ya so ya tsaya a gaban wannan aiki
mai xan karen girma na wahalhalu ko abinda zai hana ruwa gudu.
Kamar yadda ya bada muhimmanci mai girma –Allah ya
qara kiyaye shi- wajen yin hidima da kawo kwanciyar hankali ga masu ziyartar
masallacin annabi maxaukaki; Sai aka qirqiri lemomi guda 12 don kare masallata
daga zafin rana, a wurin da ake ce masa, HASWATU BIYU, daga cikin wuraren da aka
qara, a lokacin qarin ginin da daular Saudia ta farko ta gabatar. A matsayin misalin da bashi da
makamanci.
Kuma ana
bubbuxe waxannan lemomin, ana kuma rurrufe su da na'ura, duk da girman kowanne
daga cikinsu. Kamar yadda a lokacin sana'anta su an lura da abinda zai kawo
haske, da kyautata iska, da kawo sanyi a jikinsu. Kuma girman kowace lema ya
kai mita 306. Sannan ana sana'anta lemar daga sejintiplon wanda gobara ko wuta bata qona shi, haka
kuma, da wassu layukan na haske qanana; waxanda da ido kawai ba za a iya
ganinsu ba.
Su kuma
gine-gine da hadimin masallatan harami biyu maxaukaka ya yi don hidimomi
mabanbanta ya haxa da; Gini guda 15, wanda kowannensu ya qunshi: hawa huxu (a
cikin qasa); Kuma a cikin waxannan gine-ginen akwai: wuraren alwala guda 6214,
da kuma banxakai guda 2432, da mataka guda 116 na latarano wanda aka yi su, a
wurare talatin mabanbanta (30), qari akan matakalolin da basa motsawa suma guda
talatin (30).
Kuma wannan
qarin ya qunshi gini guda 27 don wassu kevantattun hidimomi; kamar cibiyoyin
lafiya, da cibiyoyin kunne-kunne, da kashe-kashe (control), da cibiyoyin gyaran
na'urori, da cibiyan kashe gobara, da
xakin kula da aiyukan tsaro.
Qarin da
mai hidiman masallatan harami maxaukaka ya yi, ya qunshi: Kevantacciyar tashan
wutan lantarki, domin samar da wutan wucin gadi ko kar ta kwana , wanda mashuna ko injuna guda biyar
suke yin aiki a cikin wannan tashar; don su iya wadatar da vangarorin da aka
qara na masallacin, da kuma wani injin guda xaya na daban don ya bada wuta a
wuraren fakin xin motoci. Sannan sai aka qaro wassu injunan guda biyu; domin
wutan da ake samu idan aka haxa shi, ya iya kaiwa wanda zai haskaka birni guda
cikakke.
Shi kuma
aikin kawo sanyi (A C) a masallacin Annabi maxaukaki yana dogara ne, akan
cibiyoyin kawo sanyi guda shida (6), wanda suke aiki da injunan wuta; qarfin
xaya daga cikinsu qisan
dubu bakwai (7000) ne, Kuma a cikinsu akwai babban abin sanyaya ruwa, a duniya.
Kuma tashar sanyayawar ta qunshi galan 17000 na ruwan da ake sanyaya shi a
kowani minti xaya. Kuma tafiyan ruwan da aka sanyaya shin yana farawa ne daga
tashar sanyaya shi; wanda nisanta –zuwa da komawa- shine: kilomita bakwai daga
masallacin Annabi, kuma ruwan ya kan kasance ne, cikin wani hanyar tiyo na
musamman, wanda ya ke bi ta cikin hanyar da aka yi a cikin qasa; wacce aka mata
suna da NAFAQUL KHADAMAAT.
Kuma a nan
za mu ga cewa, hanyar wannan aiki da aka bunqasa, wajen kawo sanyi, wanda bashi
da makamanci a duk duniya, Ta yadda a cikinsa ake: Tace iskar da za a riqa shaqarta,
tare da sanyaya ta, sai watso ta, ta wassu kafofi ko vuli-vulin da aka samar da
su a jikin qasan filolin masallaci; wannan kuma ba don komai ba; sai domin
yanayi mai sanyi (da daxi) ya game xaukacin masallacin Annabi maxaukaki.
(Ruwan
zamzam): Shi kuma ruwan zamzam ana xauko shi ne, daga cibiyar tashar da ake
cika gorunan zamzam; wacce take Makkatul mukarramah, zuwa cibiyar tashar
sanyayawa ta garin Madinatul munawwarah. Kuma aikin dako, ko xauko ruwan zamzam
yana ci-gaba a cikin wassu tankunan da aka tabbatar da su akan motoci, a tsawon
duka kwanakin shekara.
No comments:
Post a Comment