HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10 /JUMADAH AL'ULAH/1437H
daidai da 19/ Fabarairu/ 2016m
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya karrama Mutum, kuma
ya sanya shi, ya zama khalifa a bayan qasa, Ina yin godiya a gare shi kuma ina
yaba masa, a kan ni'imar imani da ta falala. Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, kuma yin
bauta a gare shi Shine manufar samar da halittu.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa; Ya tsarkake mu
daga qulle mutane a rai, da hassada, kuma yansa zukatanmu suka zama lafiyayyu.
Allah ya yi qarin salati a
gare shi da sallama, Shi iyalansa, da sahabbansa; waxanda suka kasance a kan
mafi alherin xabi'a.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da
Ni kaina da bin dokokin Allah, Allah
maxaukaki yana cewa:
"Ya ku waxanda suka
yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna
Musulmai"
[Ali-imrana: 102].
Kuma Allah; Allah yana
cewa:
"Kuma a lokacin da
Ubangijinka yace wa Mala'iku: Lallai ne Ni zan sanya wani halifa a doron qasa" [Baqarah: 30].
Lallai yana daga HIKIMAR ALLAH -wanda ya baiwa kowani abu
halittarsa sannan ya shiryar- Sanya Mutum ya zame halifarSa, a doron qasa; Don
ya tsayar da addininSa, ya kuma bayyanar da ababen mamakin da suka qunsu cikin
halittarSa (Allah), da sirrace-sirracen da suke cikin halittarSa, da kyawawan
hikimominSa, da nau'ukan amfanin da suke cikin hukunce-hukuncenSa.
Kuma, shin akwai wata alama ko aya bayyananniya; da ta ke
nuna kamalar Allah (تعالى), da yalwar iliminSa
fiye da WANNAN MUTUM; wanda Allah ya halitta shi cikin mafi kyan halitta? (Amsar itace: A, a!).
RAHAMAR ALLAH DA SUNNARSA CIKIN HALITTUNSA Sun hukunta ya
bada mayewa a kan doron qasa, ga wanda ya nufa daga cikin bayinsa "Lallai ne qasa ta
Allah ce, yana gadar da ita ga wanda ya nufa daga cikin bayinSa" [A'araf: 128].
Kuma lallai ne bada mayewa a doron qasa (halifanci)
jarraba, ce, Allah (تعالى) yana cewa:
"Akwai tsammanin
Ubangijinku ya halaka maqiyanku, sai ya baku mayewa a doron qasa, don ya gani
yaya za ku aikata!"
[A'araf: 129].
Kuma yana gaje qasa ne, Wanda ya kyautata tsayuwa da
abinda khilafanci ya wajabta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai ne
haqiqa Mun rubuta a cikin littatafai, baicin alqur'anin, cewa Lallai ita qasa
bayiNa salihai ne, su ke gadonta" [Anbiya'i: 105].
MAYEWA A BAYAN QASA (ko halifanci): Yana hukunta: Yin
bauta wa Allah, da aiki da tsarin Allah (wato, shari'arSa), da gyaruwa da kawo
gyara, da rayar da qasa, da kuma gina rayuwa da zantuka da aiyuka, da
sana'antawa, da neman ilimi, da ilmantarwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Suna yin bauta a
gare Ni; basa haxa komai da Ni" [Nur: 55 ]. Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah ya yi
alqawari ga waxannan da suka yi imani daga cikinku, kuma suka aikata aiyukan
kwarai, lallai zai shugabantar da su a doron qasa" [Nur: 55].
Kuma lallai haqiqa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya buga misalin Mutum MUMINI, da itaciyar
dabino; kowani abu a jikinta mai amfani ne. Su kuma muminai fiskokin amfaninsu
da amfanarwarsu, da kuma tasirunsu a cikin al'umma suna banbanta; daga mutum
zuwa mutum, Allah (تعالى) yana cewa:
"Shin ba ka gani ba,
yadda Allah ya buga wani misali; Kalma mai kyau, kamar bishiya ce mai kyau;
tushenta yana tabbatacce, Ressanta kuma suna cikin sama * Tana bayar da abin
cinta, a kowani lokaci da izinin Ubangijinta" [Ibrahim: 24-25].
Shi mumini dukkansa alkhairi ne, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"A kan
kowani Musulmi akwai sadaka, Sai aka ce: To idan bai samu ba fa? Sai ya ce:
Yayi aiki
da hannayensa; sai ya amfanar da kansa, ya kuma yi sadaka.
Sai ya ce:
To idan bai samu iko ba fa? Sai ya ce: Ya taimaki ma'abucin buqata; wanda aka
zalunta.
Ya ce: Sai
aka ce masa: To idan bai samu iko ba fa?
Sai yace:
Ya yi umurni da kyakkyawa, ko da alkhairi.
Ya ce: To
idan bai aikata ba fa? Sai ya ce: Sai
ya kame daga aikata sharri; don yin hakan sadaka ne".
Shi kuma Musulmin da ya karvi musulunci a matsayin
addini: Saqon da yake xauke da shi zai wayi-gari: Aiki ne da wannan addinin, da
yin da'awa ko kiran mutane izuwa gare shi, da amfanar da halittu.
Kuma da aikata haka ne
kawai Musulmi zai kasance mutum mai amfani; wanda ya ke haifar da alkhairi, ya
ke kuma fiskantar abu mai daraja; na biyayya. Ya kuma wayi-gari yana haskakawa
da wani haske, yana zuwa da albarka; saboda zuciyarsa tana cike da qauna, Harshensa
kuma shatab yake da bayyanar da soyayya, Hannunsa ya shumfuxa ni'ima da shi, Yana bada ni'ima kuma ya shumfuxa fiska ga duk
wanda ya haxu da shi. (irin wannan) ana fatan samun alkhairinsa, tare da
amintuwa daga sharrinsa.
MUSULMI yana rayuwa ne
saboda wani saqo mai girma, da wata manufa maxaukakiya, yana yin rayuwarsa don
ita, yana iya fiskantar kowani abu a hanyarsa ta tabbatar da ita, yana kuma
tabbatar da gamammen maslaha, kuma yana jiran samun aminci a qarqashin haka,
(Musulmi) yana aikinsa saboda saqon da ya ke xauke da shi; ba wai don kuxi ba,
kuma ya kan yi hidima daga cibiyar aikinsa, yana mai rayar da saqonsa, kuma
yana yin rayuwa da shi.
Kana iya ganin Mutum mai
lafiyayyen jiki, mai cikakken qira, saidai kuma yana cikin ximuwa a rayuwa;
saboda babu wata manufa da yake tafiya da ita, ko wani aikin da yake aikata
shi, haka kuma, Bashi da wani saqon da yake ji da shi ko yake sadaukar da ransa
don ganin tabbatuwansa. Imam As-Shafi'iy (رحمه الله) yana cewa:
"Idan har
baka shagaltar da ranka da gaskiya ba, sai ta shagaltar da kai da varna".
Kuma daga tunbin
"zaman banza" ake kyankyasar "munanan halaye".
Wanda yake xauke da "Saqo" ya kan fara qoqarin
gyara kansa, da yi mata hisabi, saboda duk wanda ya yi watsi da kansa, ya bar
"hisabi a gare ta", sannan ya doge cikin gafala, ya runtse idanuwansa
daga sakamakon da zai kasance a qarshen lamura, ya shantake kan faxin "Allah
Mai afuwa ne", to sai ya bijirar da kansa ga halaka.
(Daga nan), Sai "Saqon da Musulmi" ke xauke da
shi ya tafi zuwa ga: xoruwar amfani, da qoqarin gyara wani, ko wassu, tare da
basu kulawa, cikin gaya ko manufa maxaukakiya, da babbar himma, ta bada kariya
ga addini, da yin hidima ga al'ummah, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Lallai ne
Allah (تعالى) yana son lamura maxaukaka masu girma,
kuma yana qin qananan lamura".
Wanda yake xauke da wani saqo: Yana tarbiyyantar da kansa
akan qarfin nufin aiki da umurnin Allah, da tsayuwa da abinda ya wajabta, da
rashin qetare iyakokinSa, yana kuma nisantar bin son zuciyarsa da sha'awowinsa.
SHUGABA MUSULMI Saqonsa a cikin rayuwa shine,
qoqarin tabbatar da maslahohin waxanda yake shugabanta; ta hanyar tsayar musu
da adalci, da tabbatar da gaskiya. Kuma shugaba (wajibi ne akansa) ya yi
qoqarinsa wajen aikata duk abinda zai amfani talakawansa, da tunkuxe musu
abinda zai cutar da su a cikin addininsu da duniyarsu, Sa'an nan ya kame
hannayen wawayen Mutane da fasiqai, ya tsawatar da su aikata savo da zalunci da
aikin kara-zube.
MALAMAI Saqonsu a cikin rayuwa yana da girma;
saboda sune halifofin Manzanni, kuma magada annabawa. Kuma wajibi ne akan
ma'abuta ilimi su kare al'umma daga cutar jahilci, ko rugujewar aqidu da
lalacewansu. Sannan su riqa haskaka hanyoyi(wa Mutane); ta hanyar yaye musu
shubuhohi (da abubuwan da suka shige musu duhu), suna ilmantar da Mutane
lamuran addininsu; Saboda shi malami yana gyara abinda Mutane suka vata ne,
yana kuma faxakar da su izuwa ga alkhairi, yana yin umurni da kyakkaya, yana
hani kan munkari da abin kyama, yana kuma yin haquri kan cutarwa.
MAI BADA TARBIYYA MUSULMI Shi kuma
xawainiyar da take wuyansa itace: Ya zana misali ingantacce, na Musulmin kirki;
ta hanyar gyara halin da ake ciki, da tarbiyya wa 'ya'ya da jikoki, ko aikin misalta
mai halayya maxaukaka; domin saqonsa ya isa izuwa ga kowace zuciya, kuma ya
tsaftace aqidu da tunani, da busa sabuwar rayuwa gangariya cikin rayuwa; saboda
halayen mai bada tarbiyya ababen koyi ne, aiyukansa kuma adalci ne da hikima,
matsayoyinsa kuma, abu ne mai falala.
ITA KUMA MACE MUSULMA Saqonta a cikin rayuwa
shine: Kula da kyawawan halaye a cikin al'umma; wajen gina su (a cikin zukatan
yara) da basu kariya, da kuma samar da al'umma ta gari, kamar mata, da uwa
tagari; ta yadda matar za ta kasance nitsuwa ce da kwanciyar hankali da aminci
ga mijinta, Sannan ta sanya gida ya zama mazaunin walwala, kana matabbatar
qauna da tausasawa; tana mai bada kula ga 'Ya'ya da tausasawarta da kuma
soyayyarta.
Mace musulma tana
tarbiyyantar da yaranta ne akan manufofin Musulunci, da kyawawan halaye, ta kan
hakaito musu da qissoshin annabawa, da manyan mutanen da aka yi a tarihin Musulunci,
tana kuma fahimtar da su addini, tana kuma bayyana musu shiriyar shugaban Manzanni
(S.A.W).
SHI KUMA SAURAYI MUSULMI ; yana jin buwaya da Musuluncinsa,
yana kuma qarfafa imaninsa, yana fahimtar addininsa, tare da tafiya akan
karantarwarsa, yana katange hankalinsa, yana kuma yin aiki don gyara kansa,
yana kuma kiyaye zaman lafiyan al'ummarsa da amincinsu, ya tsaftace zuciyarsa,
ya kuma gyara aibukansa, yana kuma fahimtar ababen da suke aukuwa ko wakana,
tare da sanin cewa yana da saqon da yake xauke da shi, da kuma gudumawar da zai
bayar a cikin rayuwa. Yana kwasar ilimi daga mavuvvugarsa, a cikin kowani
fannin ilimi da (تخصص).
SHI KUMA MUSULMI A GARURRUKAN DA BA NA MUSULMAI BA:
Xawainiyar da take wuyansa tana da girma: Ta fiskar ya bada misalin Musulunci
cikin aiki da halayya, da kuma hukunce-hukuncensa, ya kuma gabatar da hoton Musulunci
mai haske, da sauqinsa mai shiryarwa, a cikin aqida da halaye; saboda su Musulmai
(a ko-yaushe) sune mafi alherin Mutane ga Mutane, kuma sune Mutanen da suka fi dukkan
Mutane tausayi.
HANYOYIN SADARWA NA MUSULMAI Saqon da suke
xauke da shi yana da girma, saboda girman tasirin kafafen, da yadda suke isa ga
Mutane dayawa; (Suna da babban aiki) wajen isar da saqon Musulunci, da bayyanar
da abubuwan da ya ginu akansu, tare da
baiwa Musulunci kariya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai Manzo! Ka
isar da abinda aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, idan baka aikata ba to
baka isar da saqonsa ba, Kuma Allah zai tsare ka daga Mutane. Lallai ne Allah
baya shiryar da Mutane kafirai" [Ma'idah: 67].
Hanyoyin sadarwa suna yin
hidima wa Musulunci; cikin zance da aiki, suna yaqar karkacewa da ilhadi da
munanan aiyuka, suna kare hankali da ruhi da zuciya daga munanan halaye, da
dauxar ficewa daga karantarwar addini, da kuma bayanin jinsin vatan da suke
cikin karkatattun aqidu.
SAQON GARRURUKA KO AL'UMMAR MUSULMAI
zuwa ga duniya saqon aminci ne da tausasawa, da zaman lafiya.
Kuma lallai (As-Salam; wato:
Mai bada aminci) suna ne daga cikin sunayen Allah masu kyau.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zo don ya zama aminci da rahama; kuma
don tsamar da Mutane daga duffai izuwa ga haske, Kuma ya xaukaka su zuwa ga
martabobi maxaukaka a cikin halayya; kamar cika alqawari, da hana zalunci da
qetare iyaka, da tsayar da adalci, da tunkuxe zalunci.
Kuma lallai ne al'umma zata gaza sauke saqon da ke
wuyanta a lokacin da suke shantaqewa cikin wadaci da ni'imomi da wuraren wargi
(da wasa), suka kuma dulmuya cikin sha'awowinsu da jin daxinsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Sunnar Allah ne ga
waxannan da suka shuxe gabaninka, kuma ba zaka samu wani canji ba ga sunnar
Allah"
[Ahzab: 62].
Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai
girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa
mai hikima, Ina faxar maganata
wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran
Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai * Mai rahama mai jin qai * Mamallakin ranar sakamako.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, abun bautan na farko da na qarshe.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, majivincin masu
taqawa.
Allah yayi daxin salati da
sallama a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa gabaxaya.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da
Ni kaina da bin dokokin Allah, Allah
maxaukaki yana cewa:
"Ya ku waxanda suka
yi Imani ku bi dokokin Allah, kuma ku faxi Magana ta daidai *
Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, Kuma wanda ya
yi biyayya wa Allah da ManzonSa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71 ].
Yana daga abubuwan da suke
hana musulmi sauke saqon da yake wuyansa: TUNKUXUWA A BAYAN ABABEN DA SUKE YIN
RUXI A RAYUWAR DUNIYA, DA FITINTINUNTA, Kuma babu wani abin da yafi lalata
zuciya fiye da rataya zuciya ga duniya, da karkata izuwa gare ta, da fifita ta
akan lahira.
Ruxin duniya, da aukawa cikin tarkonta yana zaunar da Musulmi
daga zaquwa zuwa ga lahira, da yin aiki don ita, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane, lallai
ne alkawarin Allah gaskiya ne; kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma kada mai
ruxi (Shexan) ya ruxe ku daga Allah" [Luqman: 33]. Kuma Allah (تعالى) ya ce: "A'aha! Ba haka ba,
Kuna son mai gaggawa ce (wato: Duniya) * Kuma kuna barin gidan qarshe; (Lahira)" [Qiyamah: 20-21].
Kuma yana daga abubuwan da suke hana Musulmi sauke saqon
da yake wuyansa: Zama da ma'abuta wargi, da kuma kutsawa cikin mas'alolin ilimi
masu tsaurin fahimta, ko kuma cikin mas'alolin da basu auku ba, saboda neman tayar
da fitina. Alhasan Albasariy (رحمه
الله):
"Ashararen bayin Allah sune waxannan da suke bin mas'aloli
masu sharri, suna makantar da bayin Allah da Su". Kuma
Al'auza'iy yana cewa:
"Lallai ne
Allah idan ya nufi ya hana wani bawansa albarkar ilimi, to sai ya jefa
mas'aloli marasa fa'ida (magalix) akan harshensa. Kuma lallai na ga irin
waxannan Mutane su ne Mutanen da suka fi qarancin ilimi".
انتهى.
Sai ku yi salati, -Ya ku
bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a
cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa
suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a
gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! kayi salati wa Annabi
Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi
Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa,
kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne,
Mai girma.
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu
shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu
da Aliyu, da Iyalan annabi da
sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin
masu rahama.
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya
Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da
kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah!
Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen
musulmai.
Ya Allah! Lallai mu muna roqonka aljanna, da
abinda yake kusantarwa zuwa gare ta, na zance ko na aiki, kuma muna neman
tsarinka daga wuta, da kuma abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko na
aiki.
Ya Allah! Lallai mu muna roqonka mabuxan alkhairi
da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, kuma muna
roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shine
kariya ga al'amarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta rayuwarmu
take, kuma ka gyara mana lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, ka sanya
rayuwa ta zama qarin alkhairi ne a gare mu, mutuwa kuwa ka sanya ta hutu ne a
gare mu daga kowani sharri. Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Lallai mu muna roqonka shiriya da taqawa
da kamewa da wadaci da arziqi.
Ya Allah! Ka taimake mu kada ka taimaki wassu
akanmu, ka bamu nasara kada ka bada nasara ga wassu akanmu, ka qulla mana, kada
ka qulla ma wassu akanmu, ka shirye mu, kuma ka sauqaqe shiriyarka a gare mu,
kuma ka taimake mu akan wanda ya yi zalunci akanmu.
Ya Allah! Ka sanya mu zama masu ambatonka, masu
yin godiya a gare ka, masu qanqan da kai a gare ka, masu yin kuka da mayar da
al'amari zuwa gare ka.
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, ka
tabbatar da hujjojinmu, kuma ka daidaita harshenmu, ka zare dauxar zukatanmu.
Ya Allah! Lallai mu muna neman tsarinka daga
gushewar ni'imarka, da canzuwar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma
dukkan abinda zai sanya ka fushi.
Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da
rahamarka da falalarka da arziqinka.
Ya Allah! Ka yi mana albarka cikin shekarunmu, kuma ka
sanya mana albarka cikin matanmu, da 'ya'yanmu, da zurriyarmu, da aiyukanmu da
shekarunmu, ka sanya mu; mu zama masu albarka a duk inda muke, Ya Ubangijin
talikai.
Ya Allah! Lallai mu muna roqonka tabbatuwa cikin
lamarin addini, da kuma azama akan aikin shiriya, da ribatar kowace biyayya, da
kuvuta daga kowani savo, da rabauta da aljanna, da kuvuta daga wuta.
Ya Allah! Ka taimaki wanda ya taimaki addini, kuma
ya Allah ka tavar da duk wanda ya tavar da musulunci da musulmai, Ya Allah!
Ka taimaki addininka da littafinka da sunnar annabinka da kuma bayinka muminai.
Ya Allah! Ka kasance wa musulmai… a kowani wuri,
Ya Ubangjin talikai, Ya Allah! ka kasance wa musulmai… a qasar Sham Ya
mafificin masu jin qai, Ya Allah! Ka kasance musu Mai qarfafawa, Mai
taimako, Mai tallafawa, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ubangijin gaskiya, Ya Allah wanda ya
saukar da littatafai, mai gudanar da gajimare, wanda ya rusa rundunoni, ka
kwace nasara daga maqiyanka; maqiyan addini, kuma ka taimaki musulmai akansu,
Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi! Ka taimaki
musulunci da ma'abotansa, a kowani wuri.
Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada
lafiya ga majinyatanmu, ka yaye baqin cikinmu, ka sunce fursunoninmu, ka
jivinci lamarinmu, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka yi dace wa shugabanmu da abinda kake
so, kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shugabanmu mai hidimar harami
guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, ka datar da shi zuwa ga
shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu,
Kuma ina roqonka ka datar da na'ibansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma
ka yarda, lallai kai mai iko ne akan
komai.
Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai gabaxaya
wajen yin aiki da littafinka, da yin aiki da shari'arka, Ya mafificin rahamar
masu rahama.
Ya Allah! Kai ne abin bauta; babu abin bautawa da
gaskiya sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma faqirai, ka saukar mana da ruwan sama,
kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya
Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah!
Shayarwar rahama, ba shayarwar azaba ko bala'i ko rusau, ko dulmuya ba, Ya
Allah! Ka rayar da garurruka da shi, ka bada ruwan sama ga bayi, ka sanya
shi ya kai birni da qauye, Ya mafificin rahama masu rahama.
"Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka
yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu
da imani, kada ka sanya a cikin zuciyarmu wani qulli ga waxanda suka yi imani;
Ya Ubangijinmu lallai kai ne Mai tausasawa ne Mai rahama" [Hash,ri: 10].
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau
a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].
"Lallai Allah yana yin umurni
da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha
da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,