2018/10/12

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 3 SAFAR 1440H Dr Huzaifiy daidai 12 Oktoba2018












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 3/SAFAR/1440H
daidai da 12/OKTOBA/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
AURE DA SHIKA A ISLAM
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AURE DA SHIKA A MUSULUNCI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna abubuwa da dama ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga AllahN da Ya halitta jinsin maza da mata, daga abinda kasa ke tsirarwa, da kuma cikin Mutane, har da abinda mutane ba su sani ba. Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya yi umarni kan yin gyara da kawo gyara, ya kuma yi hani kan barna, a cikin fadinsa; "Kuma ka kawo gyara, kada ka bi hanyar mabarnata" [A'araf: 142].
Sannan Allah (تبارك وتعالى) ya shar'anta shari'oi, domin maslahar bayi da amfani a gare su, kuma domin tunkude barna da dukkan ababen  da suke cutar da Mutane da Aljanu.
        Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa,
Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mawadacin da bashi da bukatar talikai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabadaya.

Bayan haka:
Ku bi Allah da takawa, a asirce da kuma a bayyane, saboda babu mai samun rabo a cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa, sai da takawa, kuma Mutum ba zai tabe ba, ya yi hasara, sai ta hanyar bin son zuciya.

Ya ku Mutane
Ku rika tuna mafarin halittarku; (daga Adamu da Hauwa'u), da yadda mazan cikinku da matanku suka yawaita, alhalin kun samu ne daga rai guda daya; Wanda Allah ya halitta masa matarsa daga jikinsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya ku Mutane, ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halitta ku daga rai guda daya, kuma ya halitta matarsa daga gare shi, kuma daga gare su, ya watsa maza dayawa, da mata" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Shine wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta masa matarsa daga gare shi, domin ya samu natsuwa da ita" [A'araf: 189].
        Sa'annan sai sunnar Allah da shari'arsa suka gudana, akan kulluwar namiji da mace ta hanyar daurin aure, irin na shari'a, domin Mutane su iya gina gidan auratayya, kuma domin amsawa ga bukata irin ta halitta; ta irin sha'awar da take tsakanin Mutane, da bin hanyar aure; ba ta hanyar zina ba, domin hanyar aure itace, ke haifar da kamewa, da albarka, da bunkasa, da tsarkaka, da arziki, da lafiyar zukata, da samun doriyar shekaru; ta hanyar zurriyar Mutum nagari; wato salihai.
Ita kuma hanyar zina tana da dauda, ga janyo cutukan zuciya, da lalacewar namiji da mace, ga kuma irin kaskancin da sabo ke janyowa, da matsalolin rayuwa, da tafiyar da albarkar rayuwa, da samun matsaloli cikin 'ya'ya da jikoki, sannan sai azabar lahira, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya gani na abubuwan al'ajabi, a daren da aka yi isra'i da mi'iraji da shi, Ya ce: "Sa'annan sai ya je ga wasu Mutane, wadanda ake farfasa kayukansu da dutse, duk lokacin da aka fasa, sai kan ya koma kamar yadda ya ke daga farko, kuma baza a dena aikata musu hakan ba. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune kayukansu suke yin nauyi akan halartar sallolin farillai.
Sa'annan sai ya je ga wasu Mutane, wadanda aka sanya takardu ko fata ta gabansu, da kuma ta duburarsu, suna kai-komo, kamar yadda rakumi ko dabbobi ke kai-komo, kuma suna cin kayar rakuma (dari'in), da kuma itaciyar danyan wuta (wato, zakkumin), da tsakuwa ko duwatsun da aka dafa su da wuta. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune wadanda ba su bayar da sadakar dukiyarsu (zakkah), kuma Allah bai zalunce su da komai ba.
Sa'annan sai ya je ga Mutanen da a gaba gare su akwai dafaffen naman da yake cikin tukunya, da kuma wani naman danye a cikin wata tukunyar mai dauda, amma sai gashi suna cin wannan danyen mai dauda, suna barin nunannen mai tsafta, Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wannan Mutum ne daga cikin al'ummarka, zai kasance yana da mace ta halal, mai tsafta, sai ya je wurin wata mace mai dauda, sai ya kwana a wurinta, har safiya. Da kuma matar da za ta tashi daga wurin mijinta na halal mai tsafta, sai ta je wurin wani namiji mai dauda; ta kwana da shi, har safiya". Ibnu-Jarir ya ruwaito shi a cikin tafsirinsa.

Gidan aure mafaka ce da take bada kulawa ga zurriya, kuma take tausaya musu, take damuwa da su, take ilmantar da su.
Kuma uwa da uba sune suke shirya al'umma ('ya'ya da jikoki) domin su iya daukar nauyin da ke cikin rayuwa, da amfanar da daukacin al'umma, da bunkasa yara cikin kowane sha'ani, kuma sune suke fadakar da su zuwa ga riko da kowace dabi'a mai kyau, su kuma yi hani kan aiki da kowace dabi'a abar aibantawa, kuma su rika bada tarbiyya akan aikin kwarai, domin neman dacewa da gidan lahira, da kuma rayuwa ta har abada, kuma sai karamin yaro ya yi ta koyi da irin abinda yake gani a gida, sai kuma ya tasirantu da abinda ya ke gani, kuma ya ke ji, tun da bashi da ikon karanta tarihi, domin daukar izina daga cikinsa, da aiki da abin koyi.

Shi kuma daura aure ko kulla shi, alkawari ne mai girma, kuma igiya ce mai karfi, kuma zumuncin sadarwa mai tsananin muhimmanci, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan kun yi nufin musanya mace, a gurbin wata macen, kuma kun baiwa dayansu tarin dukiya (na kindari), to kada ku karbi wani abu daga cikinsa, Shin za ku karbe shi da karya da zunubi bayyananne? * Kuma yaya za ku karbe shi, alhalin, sashenku ya sadu da sashe, kuma mata sun riki alkawari mai kauri daga gare ku" [Nisa'i:20-21].
Maluman tafsiri sun fassara alkawari mai kauri da cewa, shine: Daurin aure.

Daura aure, yana kunsar maslahohi da amfani ga miji da mata, da wasu amfani da maslahohin na 'ya'ya, da maslahohi da amfani ga makusantan ma'auratan biyu, da kuma wasu amfani da maslahohin ga daukacin al'umma, da  wasu maslahohin na duniya da lahira, wadanda ba za a iya kididdige wadannan amfanonin ba.

Shi kuma warware wannan alkawarin, da lalata wannan kullin, da tsinke igiyar auratayya, ta hanyar SHIKA, yana rurrushe wadancan maslahohin da amfanonin gabadayansu. Sai miji ya auka cikin fitintinun da za su cutar da shi ga addininsa da duniyarsa da lafiyarsa.
Kuma itama Mace, idan aka sake ta, sai ta auka cikin fitintinun da suka fi tsanani akan wanda mijin ke aukawa cikinsu, kuma matar da aka sake ba za ta samu ikon mayar da rayuwarta kamar yadda ta kasance ba, kuma sai ta rayu cikin nadama, musamman a wannan zamanin wanda a cikinsa mazajen da za su iya dacewa da halinta suka yi karanci, sai 'ya'yansu su watse, su kuma fiskanci rayuwa mai matukar tsanani, wacce ta banbanta da wanda suka yi alhalin suna karkashin inuwa ko kulawar iyaye guda biyu (uwa da uba) a hade, sai kuma su rasa dukkan dadin da zai sanya rayuwarsu cikin walwala, sai su fiskanci lalacewar halayya da nau'ukansa mabanbanta, da kuma cutuka iri-iri, sai itama al'umma gabadayanta, ta cutu, da matsaloli masu cutarwa, wanda suke kasancewa bayan aukuwar shika, sai ka ga, yanke zumunta ya yawaita.
Kuma duk yadda aka kai makura wajen kididdige matsalolin da suke cikin shikar aure, to lamarin ya fi haka.
Kuma, domin ka san barnar da shika take haifarwa, da yawaitar matsalolinta, kebantattu da masu gamewa, sai ka yi tunani cikin hadisin Jabir (رضي الله عنه)  daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Lallai Iblisu ya kan dora al'arshinsa ko gadon mulki akan ruwa (teku), sa'annan ya tura 'yan farautarsa, kuma wanda zai fi su kusancin matsayi da Iblisu shine wanda yafi tsananin fitina; Sai daya daga cikinsu ya zo, ya ce: Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce: Ba ka aikata komai ba. Sa'annan sai daya daga cikinsu ya zo ya ce; Ban bar wane ba, har sai da na raba tsakaninsa da tsakanin matarsa; Sai Iblisu ya kusantar da shi, yana cewa: Na'am, Kai ne gogan, Sa'annan kuma ya rungume shi", Muslim ya ruwaito.

Kuma lallai wasu mutane, sun yi sako-sako da batun shika, sai suka dauki lamarinsa da sauki, sai suka auka cikin lamura masu hatsari, da sharrace-sharrace masu tarin yawa, sannan su kan aukar da wasunsu cikin abinda suka auka a cikinsu.
Hakika shika saboda sabuba masu rauni, ya yawaita a wannan zamanin, ko saboda dalilai marasa kan-gado.
Kuma SABBUBAN SHIKA A WANNAN ZAMANIN suna da yawa;
Yana daga MAFI GIRMANSU: JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHIKAN, a cikin shari'a, da rashin aiki da Kur'ani da sunnah. Saboda shari'ar Musulunci ta kewaye kullin aure, da dukkan abinda zai bashi kariya da kulawa, kuma ta kare aure da muhimmiyar katanga, domin bashi kariya; kuma domin kada ya tsattsage, ya rushe, ya girgiza; a lokacin kadawar guguwar son zuciya.
Kuma domin kasancewar sababin shika yana iya kasancewa daga miji, ko daga matar, ko daga miji da matar, ko daga wasu daga cikin makusantansu; Sai shari'a ta magance kowane irin yanayin da ka iya zama sababin shika;
Sai Allah a cikin littafinsa ya umarci miji, da ya girmama lamarin aure, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku rike mata da cutarwa; har ku kekare iyaka, kuma duk wanda ya aikata hakan, to ya zalunci kansa, kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili" [Bakara: 231].
Kuma Allah ya ce: "Kuma su Mata, suna da kwatankwacin abinda ke kansu (na hakkoki) da kyautatawa, Kuma su Maza suna da wata daraja akan mata" [Bakara: 228].
        Maluman tafsiri suka ce:
Mace akan Mijinta, tana da hakkoki, misalin hakkokin mijin da suke kan matarsa, wajen kyautata zamantakewa, Sai kuma namiji ya samu fifiko akan mace, ta fiskar kasantuwarsa mai tsayuwa da lamarinta;
Don haka; Wajibi ne, akan namiji yayi zamantakewa da matarsa cikin abinda aka sani da kuma kyautatawa, Idan kuma ya kita, to sai ya dau hakuri, la'alla yanayin ya canzu, izuwa ga wanda yafi kyau, ko la'alla a azurta shi da 'ya'ya salihai tare da ita, sannan a bashi ladan hakurinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku yi zamantakewa da su da kyautatawa, domin idan kun ki su, to, tana yiwuwa ku ki abu, sai Allah ya sanya alkhairi mai yawa a cikinsa" [Nisa'i: 19].
        Kuma wajibi ne ga miji da matarsa, su rika gyara lamuran da suke janyo sabani, tun suna farko-farkonsu; domin kada kafar sabanin ta fadada.
        Kuma wajibi ne ga miji da mace; kowannensu ya san dan'uwansa; sai kowanne ya rika aikata abinda zai fi yardar da sahibinsa, Ya kuma rika nisantar dukkan abinda dayan baya so, Wannan kuma abu ne mai sauki, da ba a boye ya ke ba.
      
        YANA DAGA CIKIN SABBUBAN WANZUWAR AURE: Kokarin yin sulhu a tsakanin ma'auratan, daga ma'abuta alkhairi, masu sulhuntawa, da kawo gyara, domin kowanne ya iya samun hakkokinsa na wajibi, wanda ke kan sahibinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan ku ka ji tsoron sabani a tsakaninsu, sai ku tayar da mai hukunci daga cikin iyalansa, da mai hukunci daga iyalanta, idan sun nufi yin sulhu a tsakaninsu, to hakika Allah zai daidaita tsakaninsu, Lallai ne Allah ya kasance Masani Mai bada labari" [Nisa'i: 35].

        KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE DA JIN DADINSA: Hakuri da yin rangwame, domin dacin da ke cikin hakuri, dan kadan, zaki ne na tsawon zamani ke biyo bayansa, Kuma ba wani abinda ake fiskantar ababen ki da shi, wanda ya kai hakuri girma, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, masu hakuri ana cika ladansu, ba tare da lissafi ba" [Zumar: 10].
        Rangwame da yin afuwa, suna kawata rayuwa, kuma suna sanya ma rayuwa walwala da farin ciki da kyau. Kuma da shi ake warkar da kurjin da zamantakewa ta haifar. Kuma asali, Yafiya da yin afuwa dole ne a rayuwa, musamman a tsakanin ma'aurata biyu.
Kuma idan ya kasance cikin lamura ne na karin kwalliya (ba wajibi ba), Ko kuma cikin lamuran da za a iya jinkirta su, to lallai yin rangwame a irin wannan, shine mafi alheri ga ma'aurata. Musamman kuma a irin wannan zamanin, wanda kokarin samar da bukatun rayuwa, ya wahalar da yawa-yawan mazaje, tare da cewa, wasu ababen ba na lalura ko dole ba ne.
Kuma lallai neman bada dukkan hakkoki, da rashin rangwantawa, ko yafe wasu hakkokin, yana gadar da guje wa juna da kiyayya a tsakanin ma'aurata. alhalin shi kuma aure ruhinsa shine, taimakakkeniya, da jin-kan juna, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani lallai ne wasu daga matanku da 'ya'yanku makiya ne a gare ku, sai ku kiyaye su, kuma idan kuka yafe kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Tagabun: 14].
Gaba ko kiyayyar da ake nufi a wannan ayar ita ce, sanyaya guiwar miji ko uba kan aikata alkhairi, ko kuma rashin taimakonsa, ko kuma hana shi aikata aikhairin.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka riki abinda ya saukaka, kuma ka yi umarni da alheri, kuma ka kau da kai daga jahilai" [A'araf: 199].

KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE: MIJI ya yi ta kokarin gyara abinda ya karkace na halin matarsa, da abinda shari'a ta halatta, kuma ta yi izini, Allah (تعالى) ya ce: "Su salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abinda Allah ya tsare. Su kuma wadanda ku ke tsoron bijirewarsu, to, ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke su, Idan kuma suka muku da'a, to kada ku nemi wata hanya akansu" [Nisa'i: 34].

Kuma wajibi ne akan alkalai su rika yin sulhi tsakanin ma'aurata biyu, cikin abinda ake kaiwa gare su na kararraki, har a samu ittifaki, a kawar da shika.

Shi kuma HAKKIN MACE AKAN MIJINTA shi ne ya yi zamantakewa da ita da kyautatawa, ya kuma bata gidan da ya yi daidai da irinta, tare da ciyarwa da tufatarwa, da bayar da alkhairi, da kamewa ga barin cutar da ita.
Kuma lallai SABABIN SHIKA YANA IYA KASANCEWA DAGA MATAR NE, saboda kaushin harshenta, ko munin halinta, da jahilcinta, Don haka, wajibi ne akan mace ta rika gyara halinta, tana mai biyayya ga mijinta, ta yi bakin kokarinta wajen tarbiyyar 'ya'yanta da ingantacciyar tarbiyya, An ruwaito daga Abdurrahman bn Auf (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azuminta na wata, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, Sai ace mata: Ki shiga Aljannah, daga dukkar kofar da ki ka so", Ahmad ya ruwaito shi, kuma hadisi ne hasan.

Kuma wajibi ne ga mace ta rika hidima ga mijinta, da kyautatawa, tana mai koyi da sahabbai mata –رضي الله عنهن-.
Kuma abu ne mai kyan gaske ta rika yin tarayya da mijinta cikin farin cikinsa da bacin ransa, kuma ta kasance mai taimakonsa wajen biyayya ga Allah Ta'alah.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SAMUWAR SHIKA: Shisshigin wani daga dangin miji ko mata, ko kuma danginsu gaba daya, Sai su ji tsoron Allah, kuma su fadi magata ta daidai. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Allah ya la'anci Mutumin da ya bata matar wani a gare shi, ko kuma ya bata mijin ga matarsa".

Kuma wajibi ga MACE TA TSAYU WAJEN BADA HAKKIN MAKUSANTAN MIJINTA, musamman kuma iyayensa biyu.
Kuma shima mijin WAJIBI NE YA TSAYU WAJEN BAYAR DA HAKKIN MAKUSANTAN MATARSA; saboda sakaci kan hakkin makusantan ma'aurata, sau dayawa ya kan zama sababin shikan aure.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Bibiyar fina-finan da su ke rushe dabi'a, ko shafukan yanan gizo-gizo (internet) na haram, wadanda suke yada barna.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Fitan mace daga gida ba tare da samun izinin mijinta ba, kuma baya halatta a gare ta, ta fita ba tare da izininsa ba, domin miji shine ke da ma'aunin auna lamura.

Kuma idan SABBUBAN ZAMAN AURE SUKA GAGARA To lallai Allah ya halatta yin shika, tare dacewa yana kin shikan, saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Halal din da Allah ya fi kinsa, shine shika".
Sai miji ya yi shika irin na shari'a, bayan tsanaki da bi-sannu-sannu, kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin fadinsa: "Ya kai wannan Annabin idan za ku saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku kididdige iddar" [Dalak: 1].
Maluman tafsiri suka ce:
Sai ya sake ta a cikin tsarkin da bai sadu da ita a cikinsa ba, shika daya, Idan ya so, sai ya mata kome a cikin wannan iddar. Idan kuma ya so, sai ya barta har ta gama iddarta, sai ta fita daga mulkinsa.
Kuma lallai shika ta irin wannan hanyar tana bude kofar fatan yin kome, don wanzar da auren, ko a sake sabon aure, idan har ta yi tsarki, bayan idda.

Sai ka yi dubi, ga yadda aka karfafa lamarin aure, da yadda shari'ar gaskiya ta kiyaye shi.
Kuma ka yi dubi kan sakacin mutanen wannan zamanin kan lamarin shika, da abinda shikan yake janyowa; na kayan bacin rai.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku bi, hanyoyin shedan, domin duk wanda ya bi hanyoyin shedan, to lallai shi yana umarni ne da alfasha, da kuma munkari", [Nur: 21].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai rahama Mai jin-kai, ya shar'anta hukunce-hukunce da iliminSa da hikimarSa da kuma rahamarSa.
Tsarki ya tabbata a gare shi; abin bauta Mai girma.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masani Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalanSa, da sahabbanSa, masu riko da shari'arsa mikakkiya.

Bayan haka … !!
Ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi.

Ya ku Bayin Allah … !!
Allah yana cewa:  "Kuma ku taimaki juna akan biyayya da takawar Allah, kada ku taimaki juna akan sabo da ketare iyaka, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai tsananin ukuba ne" [Ma'ida: 2].

Ya ku Musulmai,
Shika ya zama wani abinda yake gudana akan harasan wasu samarin ba tare da tsare ko kula da hakkokin 'ya'yansu, ko wani makusancinsu ba, ko kuma lura da wani ba,
Kuma hakan yana aukuwa, ta hanyar maimaita shi, a cikin zamani masu nisa da juna, ko maimaita fadin lafazin shika a majalisa daya, sai kuma Mutum ya tafi yana ta neman fatawowi, ko ya ce, zai yi wayo, wani lokacin hanyoyi su kan toshe masa, sai ya yi ta nadamar da ba za ta masa amfani ba, alhalin Allah kuma yana cewa: "Duk wanda ya ji tsoron Allah, to zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi, ta yadda baya tsammani" [Dalak: 2-3].
Kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, cikin lamarin shikansa, ta fiskar da shari'a ta yarda, sai Allah ya sanya masa mafita.
Kuma duk wanda ya dauki aure da girma, bai yi sako-sako da shi ba, sai Allah ya sanya masa albarka a cikin aurensa, kuma ya samu kyakkayawar natija.

Kuma wasu daga cikin na'ukan shika kebantattu, yin shika a cikin wadannan halayen ya kan kasance laifi ne (sabo), kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم)  ya ce wa Abu-Ayyub: "Lallai sake Ummu-Ayyub, laifi ne".

Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
……………………………

2018/09/26

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم JUMA'A, 18Muharram1440H daidai da 28Satumba 2018M للثببيتي












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/Muharram/1440H
daidai da 28/Satumba/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KA CE: LALLAI SALLATA
قل إنّ صلاتي
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KA CE: LALLAI SALLATA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya karrama jinsin Mutum; sai ya sanya shi ya zama khalifa a bayan kasa, ina yin yabo a gare shi Subhanahu kuma ina gode masa, akan ni'imar imani da falala.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda yin bauta a gare shi itace manufar samar da halitta.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, ya tsawatar daga dabi'ar zage-zage da munanan halaye.
Allah yay i Karin salati a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa, ma'abuta kyawawan zukata.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da ni kaina da takawar Allah, Allah Ta'alah yana cewa:

"Ka ce: lallai ne sallata, da yankena-yankena, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai * bashi da abokin tarayya, kuma da aikata hakan aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa", [An'am: 162-163].
Wannan aya mai karamci, ta zana hadafi da aiki da manufar wannan rayuwa, wanda kuma shine kasancewar Musulmi, da rayuwarsa da mutuwarsa, na Allah ne Ubangijin talikai, na Allah ne Mamallakin ranar sakamako, wanda ya halitta mu, kuma yake azurta mu,  kuma ya bamu kyautar wannan rayuwar.

Tilawar wannan ayar, da yin fadakarwa akanta, da yin tunani a cikin ma'anarta, yana rayar da fahimtoci masu girma, kuma yana jaddada ma'anoni masu tsada, wadanda ya wajaba kada su buya, ko su yi nisa ga kwakwale, ko su bace ta hanyar  fadawa cikin da'irar gafala da mantuwa, wanda kuma su ne: Ya kasance sallar Bawa, da yanke-yankensa, da rayuwarsa da mutuwarsa ga Allah ne, kuma ya kankan-da-kai cikin dukkan sha'anoninsa ga wanda ya halitta shi, kuma yake azurta shi, yake juya lamarinsa. Kuma Bawa a cikin dukkan lamuransa ya fiskanci ko ya nufi fiskar Allah da ikhlasi; har ya zama babu wani abin da Murum yake nufa idan ba Allah ba;
Kuma Mai nufin samun yardar UbangijinSa baya yin magana sai domin UbangijinSa, baya yin wani aiki sai domin UbangijinSa, a darensa da yininsa, da safiyarsa da maraicensa, saboda dukkansu na Allah ne shi kadai bashi da abokin tarayya.

Ayar tana tunatarwa kan samar da matsayi mafi daukaka, wanda shine yin bauta cikin dukkan abinda Musulmi ke aikatawa ko ya bari; yana mai imani da Allah, yana mai tsarkake niyya a gare shi, yana mai son Allah, yana shauki ko begensa, yana mai tsoronsa, yana fatan samun falalarsa, yana mai cin halal, da barin cin haram, da biyayyar iyaye, da sada zumunci, da kyautatawa makwabta, da kyautata halayya, da runtse idanu, da sanya hijabi, da da'awa zuwa ga Allah, da umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna.
Kuma idan bautar Allah ta samu gindin zama a cikin zuciya, to sai Mutum ya 'yantu daga yin bauta ga wanin Allah.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162-163].
"قل إنّ صلاتي".
Ginshiki ne na abubuwan da Bawa yake kusantar Ubangijinsa; Majibincinsa Mabuwayi da daukaka da shi; domi ginshikin ibadodin da suka fi girma shine/ Yin farillan da Allah ya wajabta su ga bayinSa.
Wanda kuma yake neman lada mai yawa, to sai ya karfafi yin farillansa da ibadodin nafilfili da sunnoni, kuma da aikata hakan Mutum zai samu soyayyar Allah, sai ruhinsa ta samu daukaka, ransa kuma ta tsarkaka, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama-: "Lallai ne Allah yana cewa: Wanda ya yi adawa da waliyyina, hakika  ina shelanta yaki da shi, Kuma Bawana bai kusance ni da wani abu wanda yafi soyuwa a gare ni ba, fiye da abinda na farlanta akansa…
Kuma ba zai gushe yana kusantata da nafilfili ba, har sai na so shi, kuma idan na so shi sai in kasance jinsa da yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damka da shi, da kafarsa wanda yake tafiya da ita, kuma idan ya roke ni tabbas zan bashi, idan kuma ya nemi tsarina to lallai ne zan tsare shi", Bukhariy ya ruwaito.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162].
"ونسكي".
Ya nuna cewa lallai yanka domin Allah yana cikin manyan ibadodin da suka fi girma, kuma don haka ne Allah Ta'alah ya gwama ambaton ibadar yanka tare  da sallah a cikin fadinSa: "Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka soke (wato, rakumi)" [Kausar: 2].
Kuma wannan ibada ta yanka, lallai tana da gaya da manufofi, wanda aka shar'anta a cikin kowace shari'a; saboda Allah yana son ibadar yanka, kuma tana da yawan amfani.
Yanka domin Allah Ta'alah yana daga cikin ginshikan imani, kuma lamari ne daga cikin lamuran da tauhidin baya yake bayyanarwa, kuma yanka baya halatta a cikin Musulunci a gabatar da shi, face ga Ubangijin talikai.
Kuma dabbar da aka yanka tana zuwa a ranar Kiyama cikin fatarta da gashinta da kofatonta da dukkan abinda ke tattare da ita, a cikin ma'aunin Bawa, idan har yankan ya kasance domin Allah, ba domin wani abin da ba Allah ba; saboda ba a yin yanka domin gunki, ko bishiya, ko kabari ko waliyyi, kawai ana yin yanka ne domin Allah (سبحانه وتعالى) cikin tsarkin niyya da tauhidi.

Kuma yana daga cikin shirki ga Allah, gabatar da ibadodi da yanke-yanken dabbobin yanka, ba domin Allah Ta'alah ba, Aliyu –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya gaya min kalmomi hudu: "Allah ya la'anci wanda ya yi yanka ga wanin Allah, Allah ya la'anci wanda ya tsine wa iyayensa, Allah ya la'anci wanda ya bada mafaka ga mai bidi'a, Allah ya la'anci wanda ya canza alamomin kasa", Muslim ya ruwaito shi.

Fadinsa: "da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai", [An'am: 162].
"ومحياي ومماتي لله رب العالمين".
Rayuwa ga Allah Ubangijin talikai, itace rayuwa akan addininSa da shari'arSa, da umurninSa da haninSa, a cikin dakikokinta, da bacin ranta da farin cikinta, da darenta da yininta, da kuma dukkan abinda ke cikinta na tsayuwa da zama, da motsawa da natsuwa, da barci da farkawa, da saye da sayarwa, da abinci da abin sha, da koyo da koyarwa, da kwadago da aiki, dukkan wannan, da waninsa, na Allah ne Ubangijin talikai.

Asara dukkan hasara, tana cikin ace Musulmi ya mance da wadannan ma'anonin, ya kuma manta da UbangijinSa, har ya wayi gari a dimauci cikin tafiyarsa, gafalalle daga hadafinsa da manufarsa a cikin rayuwa, sai ya yi shirki wa abin bautarSa Makadaici da UbangijinSa Mafi girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka manta Allah, sai ya mantar da su kayukansu" [Hashr: 19].


Musulmi yana da abin bauta ne guda daya, shine Allah, Mamallakin mulki, wanda ya nufi Mutum ya 'yantu daga dukkan ababen bauta, idan ba Allahn ba, kuma ya nufi rayuwar Bawa ta kasance da ayyukansa da mayar da lamuransa, zuwa gare shi; ba zuwa ga wanin Allah ba; sai ya rayu domin Allah, kuma cikin biyayyar Allah, "Kuma tsarki ya tabbata ga Allah, a lokacin da kuke shiga maraice, da lokacin da kuke shiga safiya * kuma godiya tasa ce, a cikin sammai da kasa, da kuma lokacin zawali" [Rum: 16-17].

Wannan rayuwar idan muka yi ta domin Allah, kuma daidai da ababen da suke yardar da shi, kuma muka so abinda Allah yake so, muka ki abinda Allahn yake ki, muka rika rayar da zukata da ambaton Allah, to lallai tabbas zata kasance rayuwa ce mai dadi da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani, sai zukatansu suka natsu da ambaton Allah, to lallai da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa" [Ra'ad: 28].

Wannan kuma shine halin Musulmi a koyaushe, wato, lokaci ba zai shige alhalin yana nesa da UbangijinSa, da zikirinSa, da bautarSa ba, don haka Musulmi yake sallah, yake azumi, yake hajji, yake fitar da zakkar dukiyarsa, yake auna dukkan ayyukansa da ma'aunin shari'a da imani.

Kuma rayuwa ta kan kasance ta Allah ne Ubangijin talikai, idan aka yi amfani da lokacinta wajen aikin ginawa da bunkasawa, da kuma yin aiki da hankali wajen rayar da Duniya, da sana'a da noma, da gyara rayuwar al'ummai, da tabbatar da aminci da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a lokacin da Ibrahimu ya ce: Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari (na Makkah) amintacce, ka azurta mutanensa, daga 'ya'yan itace, wanda ya yi imani daga cikinsu, da Allah da ranar lahira. Allah ya ce: wanda ya kafirta ma ina jiyar da shi dadi kadan, sa'annan kuma in tilasta shi zuwa ga azabar Wuta, kuma makomar ta munana", [Bakara: 126].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama mai jin-kai. Mamallakin ranar sakamako.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin bautar nafarko da na karshe.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, majibinci masu takawa.
Allah ya yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa gaba daya.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni da bin dokokin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa kuma kada ku mutu face kuna Musulmai ", [Ali-imrana: 102].

Irin wannan Musulmi wanda ke mayar da rayuwarsa gaba dayanta ga Allah: ya kan zama kamar ruwan sama, duk wurin da ya sauka sai ya amfanar, wato, zai rika raya kyakkyawar fata a cikin zukata, ya rika karfafar aminta da Allah, yana yada jin-kai da tausayi a cikin rayuwa, yana barbaza alkhairi, yana ciyar da miskinai, yana tsayuwa akan sha'anonin raunanan Mutane da Marayu da Marasa lafiya, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma wanda ya rayar da wata rai, to lallai kamar ya raya Mutane ne gaba daya", [Ma'idah: 32].
Kuma duk wanda rayuwarsa ta kasance domin Allah, to ba zai jira sakamako ko godiya daga wanin Allah ba, zai cigaba da ayyukansa, ta yadda ba zai iya dakatar da shi ba; wanda ya yi ranga-ranga ga hanya, ko ya ke musa alherinsa ko ya ki godiya a gare shi,
Kamar harshen 'dayansu yana fadin: "suna cewa: Lallai ne mu, muna ciyar da ku ne domin newan yardar Allah, bamu nufin samun wani sakamako daga gare ku, kuma bamu nufin godiya * Lallai ne mu, muna tsoro daga Ubangijinmu wani yini mai gintsewa mai murtukewa * Sai Allah ya tsare musu sharrin wannan yinin, kuma ya hada musu annurin fiska da farin ciki * kuma ya saka musu -saboda hakurin da suka yi- da Aljannah, da tufafin alharir", [Insan: 9-12].

Sai ku yi salati –Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Ubangijinku ya umurce ku da aikata hakan, a cikin littafinsa a inda y ace: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati ga annabi Muhammadu da kuma iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka ga annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Kuma ya Allah, ka yarda da khalifofi guda hudu masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai da iyalan Annabi masu karamci, ka hada mu da su da afuwarka da baiwarka da kyautatawarka Ya mafi jin-kan masu jin-kai!
Ya Allah ka daukaka musulunci da Musulmai



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...