HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 3/SAFAR/1440H
daidai da 12/OKTOBA/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
AURE DA SHIKA A
ISLAM
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya
kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AURE DA SHIKA A MUSULUNCI,
Wanda kuma a cikinta ya tattauna abubuwa da dama ya ce:
بسم
الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR
FARKO
Yabo ya tabbata ga AllahN da Ya halitta jinsin maza da mata,
daga abinda kasa ke tsirarwa, da kuma cikin Mutane, har da abinda mutane ba su
sani ba. Kuma Allah Mabuwayi da
daukaka ya yi umarni kan yin gyara da kawo gyara, ya kuma yi hani kan barna, a
cikin fadinsa; "Kuma ka kawo gyara,
kada ka bi hanyar mabarnata" [A'araf: 142].
Sannan Allah (تبارك وتعالى) ya shar'anta shari'oi,
domin maslahar bayi da amfani a gare su, kuma domin tunkude barna da dukkan
ababen da suke cutar da Mutane da Aljanu.
Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina
tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa,
Ina kuma
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da
abokin tarayya, Mawadacin da bashi da bukatar talikai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawanSa ne manzonSa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma
manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabadaya.
Bayan haka:
Ku bi Allah da takawa, a asirce da kuma a bayyane, saboda babu mai
samun rabo a cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa, sai da takawa, kuma Mutum ba
zai tabe ba, ya yi hasara, sai ta hanyar bin son zuciya.
Ya ku Mutane
Ku rika tuna mafarin halittarku; (daga Adamu da Hauwa'u), da
yadda mazan cikinku da matanku suka yawaita, alhalin kun samu ne daga rai guda
daya; Wanda Allah ya halitta masa matarsa daga jikinsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya
ku Mutane, ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halitta ku daga rai guda daya,
kuma ya halitta matarsa daga gare shi, kuma daga gare su, ya watsa maza dayawa,
da mata" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Shine wanda ya halitta ku daga
rai guda, kuma ya halitta masa matarsa daga gare shi, domin ya samu natsuwa da
ita" [A'araf: 189].
Sa'annan sai sunnar Allah da shari'arsa suka
gudana, akan kulluwar namiji da mace ta hanyar daurin aure, irin na shari'a,
domin Mutane su iya gina gidan auratayya, kuma domin amsawa ga bukata irin ta
halitta; ta irin sha'awar da take tsakanin Mutane, da bin hanyar aure; ba ta
hanyar zina ba, domin hanyar aure itace, ke haifar da kamewa, da albarka, da
bunkasa, da tsarkaka, da arziki, da lafiyar zukata, da samun doriyar shekaru;
ta hanyar zurriyar Mutum nagari; wato salihai.
Ita kuma hanyar zina tana da dauda, ga janyo cutukan zuciya, da
lalacewar namiji da mace, ga kuma irin kaskancin da sabo ke janyowa, da
matsalolin rayuwa, da tafiyar da albarkar rayuwa, da samun matsaloli cikin
'ya'ya da jikoki, sannan sai azabar lahira, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya gani na
abubuwan al'ajabi, a daren da aka yi isra'i da mi'iraji da shi, Ya ce: "Sa'annan sai ya je ga wasu Mutane, wadanda ake farfasa
kayukansu da dutse, duk lokacin da aka fasa, sai kan ya koma kamar yadda ya ke
daga farko, kuma baza a dena aikata musu hakan ba. Sai ya ce: Su wanene
wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune kayukansu suke yin nauyi akan
halartar sallolin farillai.
Sa'annan
sai ya je ga wasu Mutane, wadanda aka sanya takardu ko fata ta gabansu, da kuma
ta duburarsu, suna kai-komo, kamar yadda rakumi ko dabbobi ke kai-komo, kuma
suna cin kayar rakuma (dari'in), da kuma itaciyar danyan wuta (wato, zakkumin),
da tsakuwa ko duwatsun da aka dafa su da wuta. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya
Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune wadanda ba su bayar da sadakar dukiyarsu
(zakkah), kuma Allah bai zalunce su da komai ba.
Sa'annan
sai ya je ga Mutanen da a gaba gare su akwai dafaffen naman da yake cikin
tukunya, da kuma wani naman danye a cikin wata tukunyar mai dauda, amma sai
gashi suna cin wannan danyen mai dauda, suna barin nunannen mai tsafta, Sai ya
ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wannan Mutum ne daga cikin
al'ummarka, zai kasance yana da mace ta halal, mai tsafta, sai ya je wurin wata
mace mai dauda, sai ya kwana a wurinta, har safiya. Da kuma matar da za ta
tashi daga wurin mijinta na halal mai tsafta, sai ta je wurin wani namiji mai
dauda; ta kwana da shi, har safiya". Ibnu-Jarir ya ruwaito shi a cikin
tafsirinsa.
Gidan aure mafaka ce da take bada kulawa ga zurriya, kuma take tausaya
musu, take damuwa da su, take ilmantar da su.
Kuma uwa da uba sune suke shirya al'umma ('ya'ya da jikoki) domin
su iya daukar nauyin da ke cikin rayuwa, da amfanar da daukacin al'umma, da
bunkasa yara cikin kowane sha'ani, kuma sune suke fadakar da su zuwa ga riko da
kowace dabi'a mai kyau, su kuma yi hani kan aiki da kowace dabi'a abar
aibantawa, kuma su rika bada tarbiyya akan aikin kwarai, domin neman dacewa da
gidan lahira, da kuma rayuwa ta har abada, kuma sai karamin yaro ya yi ta koyi
da irin abinda yake gani a gida, sai kuma ya tasirantu da abinda ya ke gani,
kuma ya ke ji, tun da bashi da ikon karanta tarihi, domin daukar izina daga
cikinsa, da aiki da abin koyi.
Shi kuma daura aure ko kulla shi, alkawari ne mai girma,
kuma igiya ce mai karfi, kuma zumuncin sadarwa mai tsananin muhimmanci, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma
idan kun yi nufin musanya mace, a gurbin wata macen, kuma kun baiwa dayansu
tarin dukiya (na kindari), to kada ku karbi wani abu daga cikinsa, Shin za ku
karbe shi da karya da zunubi bayyananne? * Kuma yaya za ku karbe shi, alhalin,
sashenku ya sadu da sashe, kuma mata sun riki alkawari mai kauri daga gare ku"
[Nisa'i:20-21].
Maluman tafsiri sun fassara alkawari mai kauri da cewa, shine:
Daurin aure.
Daura aure, yana kunsar maslahohi da amfani ga miji da mata, da wasu
amfani da maslahohin na 'ya'ya, da maslahohi da amfani ga makusantan ma'auratan
biyu, da kuma wasu amfani da maslahohin ga daukacin al'umma, da wasu maslahohin na duniya da lahira, wadanda
ba za a iya kididdige wadannan amfanonin ba.
Shi kuma warware wannan alkawarin, da lalata wannan kullin, da
tsinke igiyar auratayya, ta hanyar SHIKA, yana rurrushe wadancan
maslahohin da amfanonin gabadayansu. Sai miji ya auka cikin fitintinun da za su
cutar da shi ga addininsa da duniyarsa da lafiyarsa.
Kuma itama Mace, idan aka sake ta, sai ta auka cikin fitintinun
da suka fi tsanani akan wanda mijin ke aukawa cikinsu, kuma matar da aka sake
ba za ta samu ikon mayar da rayuwarta kamar yadda ta kasance ba, kuma sai ta
rayu cikin nadama, musamman a wannan zamanin wanda a cikinsa mazajen da za su
iya dacewa da halinta suka yi karanci, sai 'ya'yansu su watse, su kuma fiskanci
rayuwa mai matukar tsanani, wacce ta banbanta da wanda suka yi alhalin suna
karkashin inuwa ko kulawar iyaye guda biyu (uwa da uba) a hade, sai kuma su
rasa dukkan dadin da zai sanya rayuwarsu cikin walwala, sai su fiskanci lalacewar
halayya da nau'ukansa mabanbanta, da kuma cutuka iri-iri, sai itama al'umma
gabadayanta, ta cutu, da matsaloli masu cutarwa, wanda suke kasancewa bayan
aukuwar shika, sai ka ga, yanke zumunta ya yawaita.
Kuma duk yadda
aka kai makura wajen kididdige matsalolin da suke cikin shikar aure, to lamarin
ya fi haka.
Kuma, domin ka san barnar da shika take haifarwa, da yawaitar
matsalolinta, kebantattu da masu gamewa, sai ka yi tunani cikin hadisin Jabir (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Lallai Iblisu ya kan dora al'arshinsa ko gadon mulki akan
ruwa (teku), sa'annan ya tura 'yan farautarsa, kuma wanda zai fi su kusancin
matsayi da Iblisu shine wanda yafi tsananin fitina; Sai daya daga cikinsu ya
zo, ya ce: Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce: Ba ka aikata komai ba. Sa'annan
sai daya daga cikinsu ya zo ya ce; Ban bar wane ba, har sai da na raba
tsakaninsa da tsakanin matarsa; Sai Iblisu ya kusantar da shi, yana cewa:
Na'am, Kai ne gogan, Sa'annan kuma ya rungume shi", Muslim ya
ruwaito.
Kuma lallai wasu mutane, sun yi sako-sako da batun shika, sai
suka dauki lamarinsa da sauki, sai suka auka cikin lamura masu hatsari, da
sharrace-sharrace masu tarin yawa, sannan su kan aukar da wasunsu cikin abinda
suka auka a cikinsu.
Hakika shika saboda sabuba masu rauni, ya yawaita a wannan
zamanin, ko saboda dalilai marasa kan-gado.
Kuma SABBUBAN
SHIKA A WANNAN ZAMANIN suna da yawa;
Yana daga MAFI GIRMANSU: JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHIKAN, a
cikin shari'a, da rashin aiki da Kur'ani da sunnah. Saboda shari'ar Musulunci
ta kewaye kullin aure, da dukkan abinda zai bashi kariya da kulawa, kuma ta
kare aure da muhimmiyar katanga, domin bashi kariya; kuma domin kada ya
tsattsage, ya rushe, ya girgiza; a lokacin kadawar guguwar son zuciya.
Kuma domin kasancewar sababin shika yana iya kasancewa daga
miji, ko daga matar, ko daga miji da matar, ko daga wasu daga cikin
makusantansu; Sai shari'a ta magance kowane irin yanayin da ka iya zama sababin
shika;
Sai Allah a
cikin littafinsa ya umarci miji, da ya girmama lamarin aure, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma
kada ku rike mata da cutarwa; har ku kekare iyaka, kuma duk wanda ya aikata
hakan, to ya zalunci kansa, kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili"
[Bakara: 231].
Kuma Allah ya
ce: "Kuma su Mata, suna da kwatankwacin abinda
ke kansu (na hakkoki) da kyautatawa, Kuma su Maza suna da wata daraja akan mata"
[Bakara: 228].
Maluman tafsiri suka ce:
Mace akan Mijinta,
tana da hakkoki, misalin hakkokin mijin da suke kan matarsa, wajen kyautata
zamantakewa, Sai kuma namiji ya samu fifiko akan mace, ta fiskar kasantuwarsa
mai tsayuwa da lamarinta;
Don haka; Wajibi
ne, akan namiji yayi zamantakewa da matarsa cikin abinda aka sani da kuma
kyautatawa, Idan kuma ya kita, to sai ya dau hakuri, la'alla yanayin ya canzu,
izuwa ga wanda yafi kyau, ko la'alla a azurta shi da 'ya'ya salihai tare da
ita, sannan a bashi ladan hakurinsa, Allah (تعالى) ya
ce: "Kuma ku yi zamantakewa da su da
kyautatawa, domin idan kun ki su, to, tana yiwuwa ku ki abu, sai Allah ya sanya
alkhairi mai yawa a cikinsa" [Nisa'i: 19].
Kuma wajibi ne ga miji da matarsa, su rika gyara
lamuran da suke janyo sabani, tun suna farko-farkonsu; domin kada kafar sabanin
ta fadada.
Kuma wajibi ne ga miji da mace; kowannensu ya san
dan'uwansa; sai kowanne ya rika aikata abinda zai fi yardar da sahibinsa, Ya
kuma rika nisantar dukkan abinda dayan baya so, Wannan kuma abu ne mai sauki,
da ba a boye ya ke ba.
YANA DAGA CIKIN SABBUBAN WANZUWAR AURE:
Kokarin yin sulhu a
tsakanin ma'auratan, daga ma'abuta alkhairi, masu sulhuntawa, da kawo gyara,
domin kowanne ya iya samun hakkokinsa na wajibi, wanda ke kan sahibinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma
idan ku ka ji tsoron sabani a tsakaninsu, sai ku tayar da mai hukunci daga
cikin iyalansa, da mai hukunci daga iyalanta, idan sun nufi yin sulhu a
tsakaninsu, to hakika Allah zai daidaita tsakaninsu, Lallai ne Allah ya kasance
Masani Mai bada labari" [Nisa'i: 35].
KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE DA JIN
DADINSA: Hakuri da yin rangwame, domin dacin da ke cikin hakuri, dan kadan, zaki ne
na tsawon zamani ke biyo bayansa, Kuma ba wani abinda ake fiskantar ababen ki
da shi, wanda ya kai hakuri girma, Allah (تعالى) ya
ce: "Kawai, masu hakuri ana cika ladansu, ba
tare da lissafi ba" [Zumar: 10].
Rangwame da yin afuwa, suna kawata rayuwa, kuma
suna sanya ma rayuwa walwala da farin ciki da kyau. Kuma da shi ake warkar da
kurjin da zamantakewa ta haifar. Kuma asali, Yafiya da yin afuwa dole ne a
rayuwa, musamman a tsakanin ma'aurata biyu.
Kuma idan ya kasance cikin lamura ne na karin kwalliya (ba
wajibi ba), Ko kuma cikin lamuran da za a iya jinkirta su, to lallai yin
rangwame a irin wannan, shine mafi alheri ga ma'aurata. Musamman kuma a irin
wannan zamanin, wanda kokarin samar da bukatun rayuwa, ya wahalar da yawa-yawan
mazaje, tare da cewa, wasu ababen ba na lalura ko dole ba ne.
Kuma lallai neman bada dukkan hakkoki, da rashin rangwantawa,
ko yafe wasu hakkokin, yana gadar da guje wa juna da kiyayya a tsakanin
ma'aurata. alhalin shi kuma aure ruhinsa shine, taimakakkeniya, da jin-kan
juna, Allah
(تعالى) ya ce:
"Ya ku wadanda suka yi imani lallai ne wasu daga
matanku da 'ya'yanku makiya ne a gare ku, sai ku kiyaye su, kuma idan kuka yafe
kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne Mai jin
kai", [Tagabun: 14].
Gaba ko kiyayyar da ake nufi a wannan ayar ita ce, sanyaya
guiwar miji ko uba kan aikata alkhairi, ko kuma rashin taimakonsa, ko kuma hana
shi aikata aikhairin.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka
riki abinda ya saukaka, kuma ka yi umarni da alheri, kuma ka kau da kai daga jahilai"
[A'araf: 199].
KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE: MIJI ya yi ta kokarin
gyara abinda ya karkace na halin matarsa, da abinda shari'a ta halatta, kuma ta yi
izini, Allah
(تعالى) ya ce:
"Su salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa ga
gaibi saboda abinda Allah ya tsare. Su kuma wadanda ku ke tsoron bijirewarsu,
to, ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke
su, Idan kuma suka muku da'a, to kada ku nemi wata hanya akansu"
[Nisa'i: 34].
Kuma wajibi ne akan alkalai su rika yin sulhi tsakanin
ma'aurata biyu, cikin
abinda ake kaiwa gare su na kararraki, har a samu ittifaki, a kawar da shika.
Shi kuma HAKKIN MACE AKAN MIJINTA shi ne ya yi zamantakewa da
ita da kyautatawa, ya kuma bata gidan da ya yi daidai da irinta, tare da
ciyarwa da tufatarwa, da bayar da alkhairi, da kamewa ga barin cutar da ita.
Kuma lallai SABABIN SHIKA YANA IYA KASANCEWA DAGA MATAR NE, saboda kaushin harshenta,
ko munin halinta, da jahilcinta, Don haka, wajibi ne akan mace ta rika gyara
halinta, tana mai biyayya ga mijinta, ta yi bakin kokarinta wajen tarbiyyar
'ya'yanta da ingantacciyar tarbiyya, An ruwaito daga Abdurrahman bn Auf (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azuminta na wata,
ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, Sai ace mata: Ki shiga Aljannah,
daga dukkar kofar da ki ka so", Ahmad ya ruwaito shi, kuma
hadisi ne hasan.
Kuma wajibi ne ga mace ta rika hidima ga mijinta, da
kyautatawa, tana mai koyi da sahabbai mata –رضي الله عنهن-.
Kuma abu ne mai kyan gaske ta rika yin tarayya da mijinta cikin
farin cikinsa da bacin ransa, kuma ta kasance mai taimakonsa wajen biyayya ga
Allah Ta'alah.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN SAMUWAR SHIKA: Shisshigin wani daga
dangin miji ko mata, ko kuma danginsu gaba daya, Sai su ji tsoron Allah,
kuma su fadi magata ta daidai. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Allah ya la'anci Mutumin da ya bata matar wani a gare
shi, ko kuma ya bata mijin ga matarsa".
Kuma wajibi ga MACE TA TSAYU WAJEN BADA HAKKIN MAKUSANTAN
MIJINTA, musamman
kuma iyayensa biyu.
Kuma shima
mijin WAJIBI NE YA TSAYU WAJEN BAYAR DA HAKKIN MAKUSANTAN MATARSA; saboda
sakaci kan hakkin makusantan ma'aurata, sau dayawa ya kan zama sababin shikan
aure.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Bibiyar fina-finan da su ke rushe dabi'a, ko
shafukan yanan gizo-gizo (internet) na haram, wadanda suke yada barna.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Fitan mace daga gida ba tare da samun izinin
mijinta ba, kuma baya halatta a gare ta, ta fita ba tare da izininsa ba, domin
miji shine ke da ma'aunin auna lamura.
Kuma idan SABBUBAN ZAMAN AURE SUKA GAGARA To lallai Allah ya
halatta yin shika, tare
dacewa yana kin shikan, saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Halal din da Allah ya fi kinsa, shine shika".
Sai miji ya yi
shika irin na shari'a, bayan tsanaki da bi-sannu-sannu, kamar yadda Allah ya yi
umarni a cikin fadinsa: "Ya kai wannan Annabin
idan za ku saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku kididdige iddar"
[Dalak: 1].
Maluman
tafsiri suka ce:
Sai ya sake ta a cikin tsarkin da bai sadu da ita a cikinsa ba,
shika daya, Idan ya so, sai ya mata kome a cikin wannan iddar. Idan kuma ya so,
sai ya barta har ta gama iddarta, sai ta fita daga mulkinsa.
Kuma lallai
shika ta irin wannan hanyar tana bude kofar fatan yin kome, don wanzar da
auren, ko a sake sabon aure, idan har ta yi tsarki, bayan idda.
Sai ka yi dubi, ga yadda aka karfafa lamarin aure, da yadda
shari'ar gaskiya ta kiyaye shi.
Kuma ka yi dubi kan sakacin mutanen wannan zamanin kan lamarin
shika, da abinda shikan yake janyowa; na kayan bacin rai.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ya
ku wadanda suka yi imani, kada ku bi, hanyoyin shedan, domin duk wanda ya bi
hanyoyin shedan, to lallai shi yana umarni ne da alfasha, da kuma munkari",
[Nur: 21].
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma,
ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na faxi abinda ku ka ji,
kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga
kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,
lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai
rahama Mai jin-kai, ya shar'anta hukunce-hukunce da iliminSa da hikimarSa da
kuma rahamarSa.
Tsarki ya tabbata a gare shi; abin bauta Mai girma.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai
ya ke bashi da abokin tarayya, Masani Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawanSa ne kuma manzonSa,
Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma
manzonka Muhammadu, da iyalanSa, da sahabbanSa, masu riko da shari'arsa
mikakkiya.
Bayan haka
… !!
Ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma ku yi riko a Musulunci
da igiya mai karfi.
Ya ku Bayin Allah
… !!
Allah yana cewa: "Kuma ku taimaki juna akan biyayya da takawar Allah, kada ku
taimaki juna akan sabo da ketare iyaka, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne
Allah Mai tsananin ukuba ne" [Ma'ida: 2].
Ya ku Musulmai,
Shika ya zama wani abinda yake gudana akan harasan wasu samarin
ba tare da tsare ko kula da hakkokin 'ya'yansu, ko wani makusancinsu ba, ko
kuma lura da wani ba,
Kuma hakan yana aukuwa, ta hanyar maimaita shi, a cikin zamani
masu nisa da juna, ko maimaita fadin lafazin shika a majalisa daya, sai kuma Mutum
ya tafi yana ta neman fatawowi, ko ya ce, zai yi wayo, wani lokacin hanyoyi su
kan toshe masa, sai ya yi ta nadamar da ba za ta masa amfani ba, alhalin Allah
kuma yana cewa: "Duk wanda ya ji tsoron Allah,
to zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi, ta yadda baya tsammani"
[Dalak: 2-3].
Kuma duk wanda
ya ji tsoron Allah, cikin lamarin shikansa, ta fiskar da shari'a ta yarda, sai
Allah ya sanya masa mafita.
Kuma duk wanda ya dauki aure da girma, bai yi sako-sako da shi
ba, sai Allah ya sanya masa albarka a cikin aurensa, kuma ya samu kyakkayawar
natija.
Kuma wasu daga cikin na'ukan shika kebantattu, yin shika a
cikin wadannan halayen ya kan kasance laifi ne (sabo), kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa Abu-Ayyub:
"Lallai sake Ummu-Ayyub, laifi ne".
Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
……………………………
No comments:
Post a Comment