2018/09/26

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم JUMA'A, 18Muharram1440H daidai da 28Satumba 2018M للثببيتي












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/Muharram/1440H
daidai da 28/Satumba/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KA CE: LALLAI SALLATA
قل إنّ صلاتي
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KA CE: LALLAI SALLATA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya karrama jinsin Mutum; sai ya sanya shi ya zama khalifa a bayan kasa, ina yin yabo a gare shi Subhanahu kuma ina gode masa, akan ni'imar imani da falala.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda yin bauta a gare shi itace manufar samar da halitta.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, ya tsawatar daga dabi'ar zage-zage da munanan halaye.
Allah yay i Karin salati a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa, ma'abuta kyawawan zukata.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da ni kaina da takawar Allah, Allah Ta'alah yana cewa:

"Ka ce: lallai ne sallata, da yankena-yankena, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai * bashi da abokin tarayya, kuma da aikata hakan aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa", [An'am: 162-163].
Wannan aya mai karamci, ta zana hadafi da aiki da manufar wannan rayuwa, wanda kuma shine kasancewar Musulmi, da rayuwarsa da mutuwarsa, na Allah ne Ubangijin talikai, na Allah ne Mamallakin ranar sakamako, wanda ya halitta mu, kuma yake azurta mu,  kuma ya bamu kyautar wannan rayuwar.

Tilawar wannan ayar, da yin fadakarwa akanta, da yin tunani a cikin ma'anarta, yana rayar da fahimtoci masu girma, kuma yana jaddada ma'anoni masu tsada, wadanda ya wajaba kada su buya, ko su yi nisa ga kwakwale, ko su bace ta hanyar  fadawa cikin da'irar gafala da mantuwa, wanda kuma su ne: Ya kasance sallar Bawa, da yanke-yankensa, da rayuwarsa da mutuwarsa ga Allah ne, kuma ya kankan-da-kai cikin dukkan sha'anoninsa ga wanda ya halitta shi, kuma yake azurta shi, yake juya lamarinsa. Kuma Bawa a cikin dukkan lamuransa ya fiskanci ko ya nufi fiskar Allah da ikhlasi; har ya zama babu wani abin da Murum yake nufa idan ba Allah ba;
Kuma Mai nufin samun yardar UbangijinSa baya yin magana sai domin UbangijinSa, baya yin wani aiki sai domin UbangijinSa, a darensa da yininsa, da safiyarsa da maraicensa, saboda dukkansu na Allah ne shi kadai bashi da abokin tarayya.

Ayar tana tunatarwa kan samar da matsayi mafi daukaka, wanda shine yin bauta cikin dukkan abinda Musulmi ke aikatawa ko ya bari; yana mai imani da Allah, yana mai tsarkake niyya a gare shi, yana mai son Allah, yana shauki ko begensa, yana mai tsoronsa, yana fatan samun falalarsa, yana mai cin halal, da barin cin haram, da biyayyar iyaye, da sada zumunci, da kyautatawa makwabta, da kyautata halayya, da runtse idanu, da sanya hijabi, da da'awa zuwa ga Allah, da umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna.
Kuma idan bautar Allah ta samu gindin zama a cikin zuciya, to sai Mutum ya 'yantu daga yin bauta ga wanin Allah.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162-163].
"قل إنّ صلاتي".
Ginshiki ne na abubuwan da Bawa yake kusantar Ubangijinsa; Majibincinsa Mabuwayi da daukaka da shi; domi ginshikin ibadodin da suka fi girma shine/ Yin farillan da Allah ya wajabta su ga bayinSa.
Wanda kuma yake neman lada mai yawa, to sai ya karfafi yin farillansa da ibadodin nafilfili da sunnoni, kuma da aikata hakan Mutum zai samu soyayyar Allah, sai ruhinsa ta samu daukaka, ransa kuma ta tsarkaka, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama-: "Lallai ne Allah yana cewa: Wanda ya yi adawa da waliyyina, hakika  ina shelanta yaki da shi, Kuma Bawana bai kusance ni da wani abu wanda yafi soyuwa a gare ni ba, fiye da abinda na farlanta akansa…
Kuma ba zai gushe yana kusantata da nafilfili ba, har sai na so shi, kuma idan na so shi sai in kasance jinsa da yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damka da shi, da kafarsa wanda yake tafiya da ita, kuma idan ya roke ni tabbas zan bashi, idan kuma ya nemi tsarina to lallai ne zan tsare shi", Bukhariy ya ruwaito.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162].
"ونسكي".
Ya nuna cewa lallai yanka domin Allah yana cikin manyan ibadodin da suka fi girma, kuma don haka ne Allah Ta'alah ya gwama ambaton ibadar yanka tare  da sallah a cikin fadinSa: "Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka soke (wato, rakumi)" [Kausar: 2].
Kuma wannan ibada ta yanka, lallai tana da gaya da manufofi, wanda aka shar'anta a cikin kowace shari'a; saboda Allah yana son ibadar yanka, kuma tana da yawan amfani.
Yanka domin Allah Ta'alah yana daga cikin ginshikan imani, kuma lamari ne daga cikin lamuran da tauhidin baya yake bayyanarwa, kuma yanka baya halatta a cikin Musulunci a gabatar da shi, face ga Ubangijin talikai.
Kuma dabbar da aka yanka tana zuwa a ranar Kiyama cikin fatarta da gashinta da kofatonta da dukkan abinda ke tattare da ita, a cikin ma'aunin Bawa, idan har yankan ya kasance domin Allah, ba domin wani abin da ba Allah ba; saboda ba a yin yanka domin gunki, ko bishiya, ko kabari ko waliyyi, kawai ana yin yanka ne domin Allah (سبحانه وتعالى) cikin tsarkin niyya da tauhidi.

Kuma yana daga cikin shirki ga Allah, gabatar da ibadodi da yanke-yanken dabbobin yanka, ba domin Allah Ta'alah ba, Aliyu –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya gaya min kalmomi hudu: "Allah ya la'anci wanda ya yi yanka ga wanin Allah, Allah ya la'anci wanda ya tsine wa iyayensa, Allah ya la'anci wanda ya bada mafaka ga mai bidi'a, Allah ya la'anci wanda ya canza alamomin kasa", Muslim ya ruwaito shi.

Fadinsa: "da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai", [An'am: 162].
"ومحياي ومماتي لله رب العالمين".
Rayuwa ga Allah Ubangijin talikai, itace rayuwa akan addininSa da shari'arSa, da umurninSa da haninSa, a cikin dakikokinta, da bacin ranta da farin cikinta, da darenta da yininta, da kuma dukkan abinda ke cikinta na tsayuwa da zama, da motsawa da natsuwa, da barci da farkawa, da saye da sayarwa, da abinci da abin sha, da koyo da koyarwa, da kwadago da aiki, dukkan wannan, da waninsa, na Allah ne Ubangijin talikai.

Asara dukkan hasara, tana cikin ace Musulmi ya mance da wadannan ma'anonin, ya kuma manta da UbangijinSa, har ya wayi gari a dimauci cikin tafiyarsa, gafalalle daga hadafinsa da manufarsa a cikin rayuwa, sai ya yi shirki wa abin bautarSa Makadaici da UbangijinSa Mafi girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka manta Allah, sai ya mantar da su kayukansu" [Hashr: 19].


Musulmi yana da abin bauta ne guda daya, shine Allah, Mamallakin mulki, wanda ya nufi Mutum ya 'yantu daga dukkan ababen bauta, idan ba Allahn ba, kuma ya nufi rayuwar Bawa ta kasance da ayyukansa da mayar da lamuransa, zuwa gare shi; ba zuwa ga wanin Allah ba; sai ya rayu domin Allah, kuma cikin biyayyar Allah, "Kuma tsarki ya tabbata ga Allah, a lokacin da kuke shiga maraice, da lokacin da kuke shiga safiya * kuma godiya tasa ce, a cikin sammai da kasa, da kuma lokacin zawali" [Rum: 16-17].

Wannan rayuwar idan muka yi ta domin Allah, kuma daidai da ababen da suke yardar da shi, kuma muka so abinda Allah yake so, muka ki abinda Allahn yake ki, muka rika rayar da zukata da ambaton Allah, to lallai tabbas zata kasance rayuwa ce mai dadi da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani, sai zukatansu suka natsu da ambaton Allah, to lallai da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa" [Ra'ad: 28].

Wannan kuma shine halin Musulmi a koyaushe, wato, lokaci ba zai shige alhalin yana nesa da UbangijinSa, da zikirinSa, da bautarSa ba, don haka Musulmi yake sallah, yake azumi, yake hajji, yake fitar da zakkar dukiyarsa, yake auna dukkan ayyukansa da ma'aunin shari'a da imani.

Kuma rayuwa ta kan kasance ta Allah ne Ubangijin talikai, idan aka yi amfani da lokacinta wajen aikin ginawa da bunkasawa, da kuma yin aiki da hankali wajen rayar da Duniya, da sana'a da noma, da gyara rayuwar al'ummai, da tabbatar da aminci da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a lokacin da Ibrahimu ya ce: Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari (na Makkah) amintacce, ka azurta mutanensa, daga 'ya'yan itace, wanda ya yi imani daga cikinsu, da Allah da ranar lahira. Allah ya ce: wanda ya kafirta ma ina jiyar da shi dadi kadan, sa'annan kuma in tilasta shi zuwa ga azabar Wuta, kuma makomar ta munana", [Bakara: 126].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama mai jin-kai. Mamallakin ranar sakamako.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin bautar nafarko da na karshe.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, majibinci masu takawa.
Allah ya yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa gaba daya.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni da bin dokokin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa kuma kada ku mutu face kuna Musulmai ", [Ali-imrana: 102].

Irin wannan Musulmi wanda ke mayar da rayuwarsa gaba dayanta ga Allah: ya kan zama kamar ruwan sama, duk wurin da ya sauka sai ya amfanar, wato, zai rika raya kyakkyawar fata a cikin zukata, ya rika karfafar aminta da Allah, yana yada jin-kai da tausayi a cikin rayuwa, yana barbaza alkhairi, yana ciyar da miskinai, yana tsayuwa akan sha'anonin raunanan Mutane da Marayu da Marasa lafiya, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma wanda ya rayar da wata rai, to lallai kamar ya raya Mutane ne gaba daya", [Ma'idah: 32].
Kuma duk wanda rayuwarsa ta kasance domin Allah, to ba zai jira sakamako ko godiya daga wanin Allah ba, zai cigaba da ayyukansa, ta yadda ba zai iya dakatar da shi ba; wanda ya yi ranga-ranga ga hanya, ko ya ke musa alherinsa ko ya ki godiya a gare shi,
Kamar harshen 'dayansu yana fadin: "suna cewa: Lallai ne mu, muna ciyar da ku ne domin newan yardar Allah, bamu nufin samun wani sakamako daga gare ku, kuma bamu nufin godiya * Lallai ne mu, muna tsoro daga Ubangijinmu wani yini mai gintsewa mai murtukewa * Sai Allah ya tsare musu sharrin wannan yinin, kuma ya hada musu annurin fiska da farin ciki * kuma ya saka musu -saboda hakurin da suka yi- da Aljannah, da tufafin alharir", [Insan: 9-12].

Sai ku yi salati –Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Ubangijinku ya umurce ku da aikata hakan, a cikin littafinsa a inda y ace: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati ga annabi Muhammadu da kuma iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka ga annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Kuma ya Allah, ka yarda da khalifofi guda hudu masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai da iyalan Annabi masu karamci, ka hada mu da su da afuwarka da baiwarka da kyautatawarka Ya mafi jin-kan masu jin-kai!
Ya Allah ka daukaka musulunci da Musulmai



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...