2016/07/10

HUDUBAR IDIN AZUMI DAGA MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) LARABA,01/SHAWWAL/1437H ta AlSubaitiy








HUXUBAR IDI
DAGA MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
LARABA,01/SHAWWAL/1437H







LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
IDI LOKACI NE NA WALWALA DA BAYYANAR DA FARIN CIKI
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar idin azumi na shekarar 1437H, mai taken: IDI LOKACI NE NA WALWALA DA BAYYANAR DA FARIN CIKI, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan Yadda idi yake a musulunci, da abinda yake tattare da sun a walwala da bayyanar da farin ciki, da jin daxi, da annashwa, kuma a cikin huxubarsa ya bayyana wajabcin aiki da shari'a, da kuma komawa izuwa ga ma'abuta ilimi a lokacin matsaloli da fitintinu.


بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya watan ramadana ya zama hanya ce ta yin bauta a gare shi, da samun taqawarSa, Ina yin yabo a gare shi -سبحانه- kuma ina yin godiya a gare shi; irin yabon da bashi da qarshe, Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya. Kuma da datarwarSa da taimakonSa ne muka yi salloli da azumi, kuma muka yi sadaka, muka bauta masa. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, UbangijinSa ya zave shi, kuma ya shiryar da shi. Allah yayi qarin salati a gare shi da iyalansa da wanda ya jivinci lamarinsa.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

Bayan haka:
            Ina yin wasici a gare ku da ni kaina, da bin dokokin Allah, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah iyaka bin dokokinsa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-Imrana: 102].

            A kwanakin baya, haqiqa mun shaqi zaqin wani lokaci daga cikin lokutan alkhairi, wanda yana daga cikin mafi kyan lokutan rayuwa, to shin akwai abin da yafi zaqi ne, fiye da ganawa da Allah (a cikin sallah), da tsayuwa a gaba gare shi, da sauraron ayoyinSa waxanda suke da daxi ga kunnuwa, kuma suke tsarkake zukata, suna kuma qara imani.

            Yin murna ga wanda ya kyautata aiki, da cewa ya samu karvuwa da rabauta da gafara. Cika qidayar ramadana shine farin cikin da yafi girma, na idi.
Kuma riskar daren lailatul qadari yana yin qari mai yawa a cikin shekarun rayuwar bawa.
Kuma jikin da zunubansa suka zuzzube ya kan qawata sababbin tufafi.

            Musulmi a irin wannan lokutan yana bayyanar da farin cikinsa da jin daxinsa, kuma yana nuna walwala a lokutan walwala da idodi.
            Shi kuma bayyanar da farin ciki yana sanya rai annashwa, yana kuma sabunta ko jaddada nashaxi, Hasali ma lokutan suna hukunta (musulmai) su rayu cikin farin ciki a dukkan daqiqoqinsu, da walwala da dukkan ma'anoninta,  cikin da'ira ko kewayen shari'a da qa'idodi ko dokokin addini da halayya.
Kuma walwalar idi tana bayyana cikin tufafi da ado da kalma daddaxa.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

Musulmi ya kan shiga dimuwa, kuma mamaki ya kan mallake shi, har alqalami ya ximauce, kalmomi su gaza, saboda girman abinda yake gani, yake ji, musamman lokacin da fitintinu (na tada boma-bomai) suke isowa garin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da kewayen masallacinsa, a cikin wata mai girma (na ramadana).
Lallai abinda ya faru a masallacin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da wanin haka, na tashin boma-bomai mai qona rai, da tattara hanyoyin kisa da rushe-rushe, lamari ne mummuna, kuma laifi ne abun qyama, kuma kawo varna ne a bayan qasa.
Wannan qungiya, daga qamus xinta lallai ta yasar da: Girmama wuraren yin bauta wa Allah, da kuma jin alfarmar masallacin Manzon Allah, wanda ya cika da masallata, masu azumi da ruku'i da sujjada.
Yaya aka yi, sakaci da addinin Allah ya kai haka (a wurinsu), da lamarin kashe musulmai masu azumi da ruku'i da sujjada, a cikin wata mai girma, a kuma gari mai girma (Madina)? A kewayen masallacin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), Wani addini suke yi; su waxannan mutanen?! Kuma wace aqida suke qudurtawa (a cikin zukatansu)?!
Sun kashe ran musulmi katangaggiya (ta haram), sun tafiyar da rayukan jami'an tsaro da suke kwana (ba tare da yin barci ba) wajen kulawa da masu ziyara da umrah, sun firgitar da amintattu, sun yi yaudara da ha'inci, da kashe kai. Laifuka xaya bayan xaya, wanda kowani laifi yafi xan'uwansa muni, (suka aikata su) a makwabtaka da minbarin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da mihirabin sallarsa, da xakunan matansa!

Su waxanda aka kashe ba su ji ko su ka gani ba, muna roqon Allah ya karve su a matsayin shahidai, wannan kuma xaukaka ne a gare su, kasancewar duk wanda aka kashe shi alhalin yana yin sallah, to za a tayar da shi ranar qiyama yana yin sallah. Wanda aka kashe shi yana yin azumi shi kuma za a tayar da shi ranar qiyama yana yin azumi.
Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da Muslim daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) lallai wani mutum raqumarsa ta jefar da shi, alhalin muna tare da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), shi kuma yana cikin harama (da hajji), Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku yi masa wanka da ruwa da gabaruwa, ku masa likkafani cikin tufansa guda biyu, kada ku shafa masa turare, kada ku lulluve masa kansa, saboda Allah zai tayar da shi a ranar qiyama yana mai yin talbiyyah –LABBAIKALLAHUMMA LABBAIK…-".
Maluma suka ce: Duk wanda ya mutu alhalin yana aikata wata xa'a, to lallai za a tayar da shi cikin halinsa na aikata wannan xa'ar.
            Suma waxanda suka halatta zubar da jinin marasa laifi ta hanyar kashe su, lallai za su tsaya suna masu yin husuma da su a gaban Allah (عز وجل).

            Dangane da halatta yin aika-aika a cikin Madinar Annabi kuma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Madina harami ce tun daga dutsen Airin har zuwa Saurin, Duk wanda ya yi wata aika-aika a cikinta, ko ya bada mafaka ga mai laifi, la'anar Allah ta tabbata akansa da ta mala'iku da mutane gabaxaya, A ranar qiyama ba za a karva masa farilla ba ballantana nafila".
Kuma yana cewa:
"Babu wani da zai yi kaidin makirci ga ma'abuta Madina face ya zagwanye kamar yadda gishiri ke zagwanyewa a cikin ruwa".

Na daga abinda tasirinsa mummuna yayi tsanani ga ma'abuta musulunci; Kasancewar waxanda suka kunna wutar wannan fitinar ta kai hari a qasarmu: Wasu ne daga 'ya'yan musulmai waxanda shexanun aljanu da mutane suka zamar da su,  Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"A qarshen zamani wasu mutane za su zo, masu qarancin shekaru, masu wauta a cikin hankula, a harshe suna faxan mafi alherin maganar mutane, saidai kuma suna ficewa daga musulunci kamar yadda kibiya take ficewa daga dabbar da aka harba, Imaninsu baya qetare  maqogoronsu, Duk inda kuka gansu ku kashe su, saboda cikin kashe su akwai lada ga wanda ya kashe su a ranar qiyama".

            Tsoratar da mutane a zamaninmu da kashe su (me suna: irhabi), wani abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya, kuma shine abinda ake ta magana a kansa, a yanzu, bashi da wata alaqa da addini ko da wata qasa ko da wata al'umma (a cikin kowa ana iya samunsa). Kawai tsiro ne da shaixan ke shukawa a cikin tunani ko aqidar wanda tafiyarsa ta vace, aikinsa kuma ya tozarta. Kuma lallai cutarwar tada boma-bomai don tsoratarwa ya game duniya, kuma tartsatsin wutarsa ya hauhawa. Kuma saboda hatsarinsa ne, aka yi kururuwar wajabcin fito-na-fito da shi, da iyakance ma'anar Kalmar "irhabi", da bayanin karkasuwarsa, da surorinsa.

ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

Lallai wannan qasa (ta Saudia) itace cibiya mai nauyi, kuma fitilar yaxa alkhairi a duniya, kuma zata wanzu a haka, da izinin Allah.
Su kuma masu kaiwan hari da rushe-rushe da waxanda suke xaure musu gindi, aiyukansu za su zama uquba ko mummunar makoma akansu, suna masu janyo tavewa da hasara.
Kuma wannan qasar za ta wanzu tana tabbace wajen fiskantar waxannan hatsarorin, tana da qarfi cikin imaninta, da izza saboda haxuwar kan 'yan qasan, kuma takobi da aka tanade shi ga duk wanda yake son raunata amincinsa da zaman lafiyansa. Kuma duk wanda ya ke son kawo fuji a cikin jikin wannan qasa ko al'umma, ba zai iya ba.
Wannan qasa ta tsayu; akan ginshiqai tabbatattu, da manhaji ko tsarin musulunci, kuma duk wanda yake nufin karya wannan tsari ko raunata shi to ba zai kai ga cimma manufarsa ba, kuma zai yi hasara.
Mu kuma muna da tabbacin cewa lallai waxannan ababen (na hare-hare) ba masu tabbatuwa ba ne; za su gushe, kuma jama'arsu da izinin Allah da sannu za su vuya, saboda faxakarwa da bayanai da kuma qarfi da takobi.
Kuma wajibi ne akan musulmai gabaxaya su riqa bayyana wuraren vuyansu, da vatansu. Kuma haramun ne rufa asirin xaya daga cikinsu. Kuma duk wanda ya basu mafaka, ko ya ce aiyukansu biyayya ne (ga Allah) to lallai yayi tarayya da su cikin kashe rayuka katangaggu.
Lallai mu muna qin waxannan aiyukan kuma muna inkarinsu, wannan kuma shine halin kowani musulmi, mai hankali, ballantana maluma da xaliban ilimi, saboda al'ummar gabaxayanta da dukkan vangarorinta suna kan turba xaya, kuma cikin kwale-kwale xaya. Kuma lallai haxin kan wannan al'umma da wanzuwarta qarqashin tuta xaya tushe ne na qarfinta da qara samun kariya.
Wajibin da ke kanmu gabaxaya shine fito-na-fito da waxannan aqidun, ta dukkan hanyoyi da minbarorin faxakarwa. Da yin taimakakkeniya cikakke tsakanin vangarorin 'yan qasa da al'umma, domin mu tsaya sahu xaya. Tare da wajabcin haxin kai da nisantar ababen da ke jawo savani, da yin maganin rarrabewar kai.
Kowa ya sani, lallai kiyaye lamarin amincin al'umma abu ne da shari'a ta ke nema, kuma tozarta shi tozarta addini ne da ilimi da rayuka, da mutunci, da arziqi.           

ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

Idi wani lokaci ne daga cikin manya-manyan lokuta na yaxa soyayya, da nashaxantar da zuciya da ma'anoninta, da kuma kunna garwashin ji –na jika- da kyawawan ababen da suke nuna soyayya, Kuma haqiqa Musulunci ya sanya soyayya ta zama ginshiqi na asali wajen gina al'ummai, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Imanin Xayanku ba zai cika ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda ya ke so wa kansa".
            Soyayya, tana haifar da samun al'ummai masu son juna, wanda iskar soyayya zata fiskance ka ta dukkan geffan rayuwarsu, kuma ma'anonin qauna da buwayar rai sune za su yi musafaha da kai a farfajiyoyinsu.  Sai Miji ya riqa canjin soyayya tare da Matarsa, 'Ya'ya su riqa son iyayensu, Dangi makusanci ya riqa son makusancinsa, Makwabci ya so makwabcinsa, Mawadaci ya so faqiri, Babban mutum ya so qarami, Ma'aikaci ya so aikinsa, irin soyayyar da take qarfafar alaqar zaman gari ko qasa xaya, kuma take haifar da buwaya da kariya ga wannan al'ummar.
            Kuma irin wannan soyayyar, ita take sanya al'umma, tare da dukkan xaixaikunta su zama kamar jiki ne guda xaya, wanda idan xayansu ya yi farin ciki sai dukkan jikin yayi farin ciki, idan kuma xayansu ya koka sai sauran jikin ya koka, suna masu qarfafar juna da tallafawa, har xaixaikun al'umma, su riqa motsawa wajen bada gudumawa a lokacin mawuyacin hali da tashin-tashina, da toshe yanayin talauci da buqata, ko tunkuxe hatsari, ta yadda xan'uwa zai riqa qarfafa wa xan'uwansa; yana mai yaye baqin cikinsa, yana rufa masa asiri, yana taimakonsa wajen warware matsalolinsa, yana tarayya da shi cikin farin cikinsa, da xebe masa kewa da bashi agaji cikin baqin ciki, ya riqa taimakonsa idan ya kasance wanda aka zalunta,  ya masa kamun qafar shafa'a, ya riqa cike givinsa, yana gyara aibukansa, ya riqa taimakonsa da dukiyarsa da zancensa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai mumini yana yin sabo, kuma babu alheri ga mutumin da baya sabo, kuma ba'a sabawa da shi".

            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda yake cewa:
"Kuma a yayin da muka sanya xakin ka'aba ya zama wajen kai-komo, da aminci" [Baqara: 125]. Ina yin godiya a gare shi, kuma ina yaba masa akan ni'imominsa manya-manya,  kuma ina shidawa babu abin bautawa da qaskiya sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, wanda yake cewa: "Kuma su bauta wa Ubangijin wannan xaki * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].  
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, wanda idan ya ga jinjirin wata sai yayi addu'a ya ce: "Ya Allah! Ka bayyanar da jinjirin wata akanmu da aminci da Imani, da kuma salama da musulunci".
            Allah ya yi qarin salati da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, sallama mai yawa.

ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
           
            Kowace shekara (fatanmu ita ce) ku riqa son sashinku; so mai yawa (amin), Qasa kuma ta yi ta xaukaka tana samun bunqasa da ku, Al'ummar musulmai kuma su qara samun izza da taimakon nasara.

            Kowace shekara hannaye tsarkaka (da fatan) su yi ta yin musafaha. Zukata farare tas suna yafe wa juna. Rayuka nagartattu da soyayya wa juna suna saduwa (Amin, Amin)

            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa.             Ya Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu da iyalansa da sahabbansa masu krimci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini, Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Ka karvi azuminmu da sallolinmu da ruku'inmu da sujadanmu, Ya Allah! Ka sanya mu daga cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka kiyaye su a ko-ina suke, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai tagaza musu, Ya Allah! Ka karvi wanda ya mutu daga cikinsu yana mai shahada, Ya Allah! Ka xaukaka darajarsu cikin darajar "illiyuna", Ya Allah! Ka ninnika kyawawansu, kuma ka yi musu rangwame akan munanansu, kuma ka xinke karayar iyalansu da danginsu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Wanda ya nufe mu, ko ya nufi musulmai da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa Ya mai amsa addu'a.
            Ya Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, kuma ka bashi lafiya, Ya ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya mafi rahamar masu rahama.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN, WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA" [].
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUXUBA DAGA MASALLACIN ANNABI ta DR. ABDULBARIY DAN AWWADH AS-SUBAITIY


HUXUBA DAGA MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
???/???/1437H







LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA



ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
Allah (ta'alah) ya yi wa gavvan mutum ni'ima ta ji da motsowa, sai ya sanya zuciya ta zama ita take mulkan gavvan (sarki). Kuma lallai, Babu wata zuciya da za ta cika da rayuwa, ko kuma ta harba da xebe kewa sai bayan garwashin soyayya ya kunnu a cikinta.
            Ita kuma soyayya ko qauna ita ce, ruhin rayuwa, kuma jagora izuwa ga samun aminci, tana canza abu mai xaci zuwa ga zaqi, zogi kuma waraka, cuta kuma zuwa ga ni'ima. Soyayya arziqi ne da Allah ke bada shi ga zukatan bayinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa a sha'anin Khadijah (رضي الله عنها):
"Lallai ni, an azurta ni da sonta", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma, Allah (سبحانه) ya nufi ya gina rayuwa a tsakaninsa da tsakanin halittunsa a kan ginshiqin soyayya, a inda yake cewa, dangane da mutanen da suka kawar da kai:
"Kuma da sannu Allah zai zo da waxansu mutanen da yake sonsu, suma suke sonsa" [Ma'idah: 54].

            Ita rayuwa, ba za ta tava yin daxi ba, duk yadda zahirinta ya qawatu; ko yayi kyau, matuqar babu soyayya, kuma babban mutum baya wadata ga barin soyayya, haka kuma qarami, saboda idan aka haramta wa mutane son juna, to sai su rayu; rayuwa irin ta rashin sanin juna, da yanke alaqoqi, kuma sai su zama sharri ga sashinsu fiye da dabbobi masu karya qashi, da kuma kwari masu dafi.

            Kuma haqiqa, al'umma gabanin zuwan musulunci, ta kasance cikin ximuwa, a wargaje, ana tunkuxa ta zuwa ga makamin harbi, Sai Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya taso, ya warware dabaibayin yaqi, ya kuma kunce xaurinsa, Sannan ya daddasa dashen aqidar imani a cikin zukata, wanda ya sanya igiyar soyayya ta zama ita ce igiya ta farko, kuma wanda tafi qarfi, Sai yaqukan da wutarsu suke ruruwa suka mutu, suka dusashe, Sai qabilun Aus da Khazraj suka haxe, sannan aka samu 'yan'uwantaka tsakanin waxanda suka yi hijira, da Ansaar (mutanen Madina mataimaka), sai lamarin qabilanci ya yankwane kuma ya bi ruwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Da waxanda suka tanadi gida, da imani gabaninsu suna son waxanda suka hijira izuwa gare su" [Hashr: 9 ].  
Kuma Allah (سبحانه) ya ce:
"Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku a lokacin da kuka kasance maqiyan juna, sai ya daidaita tsakanin zukatanku; sai kuka wayi gari cikin ni'imarsa kuna 'yan'uwan juna" [Ali-imraana: 103].
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya lulluve sahabbansa da soyayyarsa, kuma ya kasance yana yawaita rangwame akansu, mai tausasawa, mai yawaita haquri akansu, Kai, UbangijinSa (صلى الله عليه وسلم) ya umurce shi da cewa, ya riqa yin afuwa a gare su, yana nema musu gafara, yana shawartarsu cikin lamuransu, Sai sahabbai suka yi so wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) irin son da a tarihance ba a tava jin irinsa ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma saboda wata rahama ce daga Allah ka tausasa musu, kuma da ka kasance mai kaushin harshe, mai taurin zuciya to da sun watse daga wurinka, sai ka yi musu afuwa, ka nema musu gafara, ka shawarce su cikin lamari" [Ali-imraana: 159].
 
            Kuma haqiqa Musulunci ya sanya ginshiqi na asali wajen gina al'ummai akan tushe mai qarfi, tatacce garau, kuma mai tsarki cikin ji –irin na jika- da soyayya, wanda ya yi nisa daga xabi'ar son kai ko fifita ta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Imanin Xayanku ba zai cika ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda ya ke so wa kansa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

            Soyayya, tana haifar da samun al'ummai masu son juna, wanda iskar soyayya zata fiskance ka ta dukkan geffan rayuwarsu, kuma ma'anonin qauna da buwayar rai sune za su yi musafaha da kai a farfajiyoyinsu.  Sai Miji ya riqa canjin soyayya tare da Matarsa, 'Ya'ya su riqa son iyayensu, Dangi makusanci ya riqa son makusancinsa, Makwabci ya so makwabcinsa, Mawadaci ya so faqiri, Babban mutum ya so qarami, Ma'aikaci ya so aikinsa, irin soyayyar da ke qarfafar alaqar zaman gari ko qasa xaya, kuma take haifar da buwaya da kariya ga wannan al'ummar.
            Kuma irin wannan soyayyar, ita take sanya al'umma su zama suna iya bada kansu; koda kuwa za su qare wajen sadaukar da rai, da soyayya ta jivinta, kuma sai ya sanya al'ummar, tare da dukkan xaixaikunta su zama kamar jiki ne guda xaya, wanda idan xayansu ya yi farin ciki sai dukkan jikin yayi farin ciki, idan kuma xayansu ya koka sai sauran jikin ya koka, suna masu qarfafar juna da tallafawa, har xaixaikun al'umma, su riqa motsawa wajen bada gudumawa a lokacin mawuyacin hali da tashin-tashina, da toshe yanayin talauci da buqata, ko tunkuxe hatsari, ta yadda xan'uwa zai riqa qarfafa wa xan'uwansa; yana mai yaye baqin cikinsa, yana rufa masa asiri, yana taimakonsa wajen warware matsalolinsa, yana tarayya da shi cikin farin cikinsa, da xebe masa kewa da bashi agaji cikin baqin ciki, ya riqa taimakonsa idan ya kasance wanda aka zalunta,  ya masa kamun qafar shafa'a, ya riqa cike givinsa, yana gyara aibukansa, ya riqa taimakonsa da dukiyarsa da zancensa, kar yana izgili da shi, ko cin namansa (giba),  kada ya munana zato a gare shi. Yana himmatuwa da sha'anoninsa, yana tambayar halin da yake ciki.

A qarqashin inuwar so na gaskiya: Qulle mutum a cikin rai yana narkewa, Hassada kuma tana tafiya, ana kuma watsar da husuma da savani, Sai aminci ya yaxu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Lallai mumini yana yin sabo, kuma babu alheri ga mutumin da baya sabo, kuma ba'a sabawa da shi", Alhakim ya fitar da shi a cikin "Mustadrak".

ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

            Da soyayya ne miji ke tarbiyyantar da matarsa, Matar kuma take iya mallake mijinta, kuma da soyayya ne iyaye guda biyu suke tarbiyyantar da 'ya'yansu, kuma da soyayya ne ake warware matsaloli. Kuma da soyayya ne shugaba ke iya gano ababen da suka vuya daga cikin abinda waxanda ake shugabanta za su iya (na qirqire-qirqire da aiki), sai qirqire-qirqire da aiki su qaru. Kuma da soyayya ake zaburar da bunqasa lamura da gina al'ummah.
            Har ita alaqar da take tsakanin shugaba da wanda ake shugabanta, da mai kiyo da waxanda ake kiyo suna tsayuwa ne akan ginshiqin soyayya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Zavavvun shugabanninku sune waxanda kuke sonsu, suke sonku", Muslim ya ruwaito shi.

            Mu, (musulmai a yau) muna da buqatar gina soyayya; saboda mu iya kashe wutar qiyayya, da kuma son xaukar fansa. Suma duniya (ko sauran mutane) lallai suna da buqatar samar da soyayya, musamman a duniyarmu ta yau, wacce lamuran yaquka wutarsu take qara ruruwa, na kisan jama'a, da xaga mutane marasa laifi daga matsugunansu (gidaje ko garuruka), da yin fyaxe wa mata, da kashe yara, da qona garurruka da gonake, da share gidaje (ko rushe su). 

            Kuma, Duk wanda ya xauki makami ya kashe xan baffansa, ya kuma kafirta sanyin idonsa; wato: Uwarsa, da wanda ya ruguje masallatai da gine-gine, Da wanda ya tara runduna don ya karkashe ko ya qauratar (da bayin Allah), Dukkan waxannan da waxanda suka yi kama da su, to lallai idaniyar soyayya da jin qai sun bushe daga cikin jikinsu, kuma ma'anonin mutuntaka a "qamus" xin rayuwarsu sun fice sun karkace, Sai su ka koma kamar dabbobi masu farauta da karya qashi, ko cin nama, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Wanda ya xauki takobi akanmu baya tare da mu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
???
???
???

            Shiriyar Annabi ta zurfafa soyayya a cikin zukata, kuma ta sanya yaren da ake tattaunawa da shi yana ginuwa akan ginshiqin soyayya, Sai ya koya mana yadda musulmi  zai bayyana soyayyarsa ga xan'uwansa; domin ya watsa lamarin so a cikin ransa, ya kuma jiyar da shi cewa lallai shi, yana cikin wata al'umma ce, wanda soyayya ta dabaibaye ta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Idan Xayanku ya so xan'uwansa, to ya sanar da shi" Tirmiziy ne ya ruwaito da isnadi ingantacce

Tartsati ko haske na soyayya: Watsa sallama da yaxa ta; -cikin faxi ko aiki ko salo na rayuwa- yana tayar da tartsatsin, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin ba zan nuna muku abinda idan ku ka aikata shi za ku so junanku ba? Ku watsa sallama a tsakaninku" Muslim ne ya rawaito shi.

            Sake fuska, murmushi na gaskiya, da tsarkakekkiyar bushasha sako ne (da ake turawa) na soyayya, kuma ma'anansa  qauna; Har Abdullahi xan Harith xan jaz'in yake cewa: "Ban ga wani mutum da ya fi Annabi murmushi ba" Tirmiziy ne ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.

Kyauta tana qara danqon soyayya, kuma tana tsarkake rai, tana kuma gyara zuciya, kuma tana karfafa alaqoqi; Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku yi kyauta don ku so juna'' Bukhariy ya ruwaito a littafin adabul mufrad


Allah mai girma, Allah mai girma,  babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,  Allah mai girma, Allah mai girma, kuma godiya ta tabbata ga Allah!

Wanda yake son ya qarfafa soyayyarsa, ko yake son soyayyarsa ga 'yan'uwansa ta dawwama, to hanyar hakan ita ce: Toshe duk wasu hanyoyi na jita-jita ko annamimanci, da qin biye wa mai aikin yaxa ko yawo da magana, ko yake lalata alaqoqi da wargaza su, Kuma a irin wannan yanayi alqur'ani ya nuna mana matsaya mai girma, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku waxanda suka yi imani ku guji yawan zato, lallai wasu zaton zunubi ne, kuma kar ku yi shisshigi, kuma kar sashinku su riqa gulmar sashi'' [Hujuraat: 12].

Shi masoyi mai hankali, ya kan kasance mai tsakaitawa cikin jiye-jiyen jikinsa (da axifarsa da aiyukansa, wato: kamar fushi, da so, ko qiyayya), Mai hankali  baya israfi ko wuce iyaka, don haka: Baya qetare iyaka idan zai yi so, Haka kuma, baya wuce iyaka idan zai bayyanar da qinsa daga abu, An ruwaito daga Abu-huraira (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa: "Ka so masoyinka a sannu-sannu, wata rana zai iya zama maqiyinka, ka qi maqiyinka a sannu-sannu domin watarana zai iya zama masoyinka" Tirmiziy ya ruwaito shi, da isnadi mai kyau.

Masoyi na iya shiga ko dulmuya cikin abubuwan rayuwa, sai alamomin soyayya su dusashe a cikin kogunan nisanta da kyaliya, Wannan kuma alama ce da take nuna an munana fahimtar yanayin rayuwa, saboda ita rahama (da jin qai) idan har suka samu gindin zama a cikin zukata, to sai Allah ya gyara jiki da su, Wannan ya sanya a lokacin da Aqra'a (رضي الله عنه) ya ce waAnnabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ne, ni ina da 'ya'ya goma ban tava sunbantar ko xaya daga cikinsu ba? Sai ya ce: Ni bana mallaka maka komai! Ko, dai Allah mabuwayi da xaukaka ya tuzge rahama ce daga zuciyarka" Bukhariy a cikin adabul mufrad ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.

Shi Mai so, ana son ya zuba soyayyarsa a mizani na adalci da daidaito, kuma ba a son ya kwarara soyayyarsa ga wani daga cikin tagwaye, ya kuma kyale xayan, wannan kuma domin ya kawo zaman lafiya a cikin iyalansa da aminci, saboda a cikin yin adalci a tsakanin xaixaikun iyalai akwai samun yardarsu, kamar yadda a cikin zalunci kuma akwai janyo qulle mutum a rai da qiyayya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)  ya ce: "Ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin 'ya'yanku" Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Kuma ya ce: "Wanda ya ke da mata biyu sai ya karkata zuwa ga xayan, to zai zo ranan kiyama gefensa xaya a karkace" Abu-dawud ya ruwaito shi da isnadi mai inganci.

            Samun kuskure wajen fahimtar menene ma'anar soyayya, da taqaita ma'anar kan: Karkatar zuci; da ke zuwa ya tafi, ko ga wata sha'awa mai wanzuwa, da bukukuwa na rasar kunya da batsa da tada sha'awa, ko kwana cikin haramun, to, waxannan suna juya ma'anar soyayya daga abu mai falala da matsayi zuwa ga: laifi, haka, daga abu mai daxi izuwa ga azaba da tavewa. Abu na wajibi shine, kada wannan soyayyar ta kai izuwa ga haramun, ko aiyukan da suke fusata Allah, ko wasu halayya waxanda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi hani kan aikata su, kasancewar dayawa kallo, na aukar da Mutum cikin haramun; da aka hana, sai kuma ta gadar wa zuciya wata cuta mai tsayi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ka bibiyi abin da baka da ilimi akansa, Lallai ne, ji, da gani, da zuciya sun kasance abun tambaya ne akansu" [Isra'i: 36].


HUXUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
            Idi wani lokaci ne musamman daga manyan lokuta masu girma; da ake yaxa soyayya, da nashaxantar da zukata da ma'anonin idi, da kyasta garwashin jin ababen cikin idi masu kyau, da tafiya a cikinsa akan shiriyar Annabi (S.A.W) domin qasa ta rayu a cikin falalolin idi, kuma al'umma ta tsinki 'ya'yan itatuwansa.

            Cika qidayar ramadana shine farin cikin da yafi girma, na idi.
Kuma riskar daren lailatul qadari yana yin qari mai yawa a cikin shekarun rayuwa.
Kuma jikin da zunubansu suka zuzzube su kan qawata sababbin tufafi.

            Kowace shekara (fatan ita ce) ku riqa son sashinku da so mai yawa (amin), Qasa kuma ta yi ta xaukaka tana samun bunqasa da ku, Al'ummar musulmai kuma su qara samun izza da taimakon nasara.

            Kowace shekara hannaye tsarkaka (da fatan) su yi ta yin musafaha, Zukata farare tas suna yafe wa juna, Rayuka nagartattu da soyayya wa juna suna saduwa (Amin, Amin)

Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

            Bayan haka;

            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
                Ya Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
                Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
               
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.

,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...