HUXUBAR IDI
DAGA MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
LARABA,01/SHAWWAL/1437H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
IDI LOKACI NE NA WALWALA
DA BAYYANAR DA FARIN CIKI
Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh
Al-Subaitiy –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar idin azumi na shekarar 1437H, mai taken: IDI LOKACI NE NA WALWALA
DA BAYYANAR DA FARIN CIKI, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan Yadda idi
yake a musulunci, da abinda yake tattare da sun a walwala da bayyanar da farin
ciki, da jin daxi, da annashwa, kuma a cikin huxubarsa ya bayyana wajabcin aiki
da shari'a, da kuma komawa izuwa ga ma'abuta ilimi a lokacin matsaloli da
fitintinu.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Godiya ta
tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya watan ramadana ya
zama hanya ce ta yin bauta a gare shi, da samun taqawarSa, Ina yin yabo a gare
shi -سبحانه- kuma ina yin godiya a gare shi; irin
yabon da bashi da qarshe, Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya. Kuma da datarwarSa da taimakonSa
ne muka yi salloli da azumi, kuma muka yi sadaka, muka bauta masa. Kuma ina
shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa,
UbangijinSa ya zave shi, kuma ya shiryar da shi. Allah yayi qarin salati a gare
shi da iyalansa da wanda ya jivinci lamarinsa.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Bayan
haka:
Ina
yin wasici a gare ku da ni kaina, da bin dokokin Allah, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku waxanda suka
yi imani ku bi dokokin Allah iyaka bin dokokinsa, kuma kada ku mutu face kuna
musulmai" [Ali-Imrana: 102].
A
kwanakin baya, haqiqa mun shaqi zaqin wani lokaci daga cikin lokutan alkhairi,
wanda yana daga cikin mafi kyan lokutan rayuwa, to shin akwai abin da yafi zaqi
ne, fiye da ganawa da Allah (a cikin sallah), da tsayuwa a gaba gare shi, da
sauraron ayoyinSa waxanda suke da daxi ga kunnuwa, kuma suke tsarkake zukata,
suna kuma qara imani.
Yin
murna ga wanda ya kyautata aiki, da cewa ya samu karvuwa da rabauta da gafara. Cika qidayar ramadana shine
farin cikin da yafi girma, na idi.
Kuma riskar daren lailatul qadari yana yin qari mai yawa a
cikin shekarun rayuwar bawa.
Kuma jikin da zunubansa suka zuzzube ya kan qawata sababbin
tufafi.
Musulmi
a irin wannan lokutan yana bayyanar da farin cikinsa da jin daxinsa, kuma yana
nuna walwala a lokutan walwala da idodi.
Shi
kuma bayyanar da farin ciki yana sanya rai annashwa, yana kuma sabunta ko
jaddada nashaxi, Hasali ma lokutan suna hukunta (musulmai) su rayu cikin farin
ciki a dukkan daqiqoqinsu, da walwala da dukkan ma'anoninta, cikin da'ira ko kewayen shari'a da qa'idodi ko
dokokin addini da halayya.
Kuma
walwalar idi tana bayyana cikin tufafi da ado da kalma daddaxa.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Musulmi ya
kan shiga dimuwa, kuma mamaki ya kan mallake shi, har alqalami ya ximauce,
kalmomi su gaza, saboda girman abinda yake gani, yake ji, musamman lokacin da
fitintinu (na tada boma-bomai) suke isowa garin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da kewayen masallacinsa, a cikin wata mai
girma (na ramadana).
Lallai
abinda ya faru a masallacin Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) da wanin haka, na tashin boma-bomai mai
qona rai, da tattara hanyoyin kisa da rushe-rushe, lamari ne mummuna, kuma
laifi ne abun qyama, kuma kawo varna ne a bayan qasa.
Wannan qungiya,
daga qamus xinta lallai ta yasar da: Girmama wuraren yin bauta wa Allah, da
kuma jin alfarmar masallacin Manzon Allah, wanda ya cika da masallata, masu
azumi da ruku'i da sujjada.
Yaya aka
yi, sakaci da addinin Allah ya kai haka (a wurinsu), da lamarin kashe musulmai
masu azumi da ruku'i da sujjada, a cikin wata mai girma, a kuma gari mai girma
(Madina)? A kewayen masallacin Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم), Wani addini suke yi; su waxannan
mutanen?! Kuma wace aqida suke qudurtawa (a cikin zukatansu)?!
Sun kashe
ran musulmi katangaggiya (ta haram), sun tafiyar da rayukan jami'an tsaro da
suke kwana (ba tare da yin barci ba) wajen kulawa da masu ziyara da umrah, sun
firgitar da amintattu, sun yi yaudara da ha'inci, da kashe kai. Laifuka xaya
bayan xaya, wanda kowani laifi yafi xan'uwansa muni, (suka aikata su) a
makwabtaka da minbarin Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) da mihirabin sallarsa, da xakunan
matansa!
Su waxanda
aka kashe ba su ji ko su ka gani ba, muna roqon Allah ya karve su a matsayin
shahidai, wannan kuma xaukaka ne a gare su, kasancewar duk wanda aka kashe shi
alhalin yana yin sallah, to za a tayar da shi ranar qiyama yana yin sallah.
Wanda aka kashe shi yana yin azumi shi kuma za a tayar da shi ranar qiyama yana
yin azumi.
Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da Muslim daga
hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما)
lallai wani mutum raqumarsa ta jefar da shi, alhalin muna tare da Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم), shi kuma yana cikin harama (da hajji),
Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku yi masa
wanka da ruwa da gabaruwa, ku masa likkafani cikin tufansa guda biyu, kada ku
shafa masa turare, kada ku lulluve masa kansa, saboda Allah zai tayar da shi a
ranar qiyama yana mai yin talbiyyah –LABBAIKALLAHUMMA LABBAIK…-".
Maluma suka ce: Duk wanda ya mutu alhalin yana
aikata wata xa'a, to lallai za a tayar da shi cikin halinsa na aikata wannan
xa'ar.
Suma
waxanda suka halatta zubar da jinin marasa laifi ta hanyar kashe su, lallai za
su tsaya suna masu yin husuma da su a gaban Allah (عز وجل).
Dangane
da halatta yin aika-aika a cikin Madinar Annabi kuma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Madina harami ce tun daga dutsen
Airin har zuwa Saurin, Duk wanda ya yi wata aika-aika a cikinta, ko ya bada
mafaka ga mai laifi, la'anar Allah ta tabbata akansa da ta mala'iku da mutane
gabaxaya, A ranar qiyama ba za a karva masa farilla ba ballantana nafila".
Kuma yana cewa:
"Babu wani da zai yi kaidin makirci
ga ma'abuta Madina face ya zagwanye kamar yadda gishiri ke zagwanyewa a cikin
ruwa".
Na daga
abinda tasirinsa mummuna yayi tsanani ga ma'abuta musulunci; Kasancewar waxanda
suka kunna wutar wannan fitinar ta kai hari a qasarmu: Wasu ne daga 'ya'yan
musulmai waxanda shexanun aljanu da mutane suka zamar da su, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"A qarshen zamani wasu mutane za su
zo, masu qarancin shekaru, masu wauta a cikin hankula, a harshe suna faxan mafi
alherin maganar mutane, saidai kuma suna ficewa daga musulunci kamar yadda
kibiya take ficewa daga dabbar da aka harba, Imaninsu baya qetare maqogoronsu, Duk inda kuka gansu ku kashe su,
saboda cikin kashe su akwai lada ga wanda ya kashe su a ranar qiyama".
Tsoratar
da mutane a zamaninmu da kashe su (me suna: irhabi), wani abu ne da ya
zama ruwan dare gama duniya, kuma shine abinda ake ta magana a kansa, a yanzu,
bashi da wata alaqa da addini ko da wata qasa ko da wata al'umma (a cikin kowa
ana iya samunsa). Kawai tsiro ne da shaixan ke shukawa a cikin tunani ko aqidar
wanda tafiyarsa ta vace, aikinsa kuma ya tozarta. Kuma lallai cutarwar tada
boma-bomai don tsoratarwa ya game duniya, kuma tartsatsin wutarsa ya hauhawa.
Kuma saboda hatsarinsa ne, aka yi kururuwar wajabcin fito-na-fito da shi, da
iyakance ma'anar Kalmar "irhabi", da bayanin karkasuwarsa, da
surorinsa.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Lallai
wannan qasa (ta Saudia) itace cibiya mai nauyi, kuma fitilar yaxa alkhairi a
duniya, kuma zata wanzu a haka, da izinin Allah.
Su kuma
masu kaiwan hari da rushe-rushe da waxanda suke xaure musu gindi, aiyukansu za
su zama uquba ko mummunar makoma akansu, suna masu janyo tavewa da hasara.
Kuma
wannan qasar za ta wanzu tana tabbace wajen fiskantar waxannan hatsarorin, tana
da qarfi cikin imaninta, da izza saboda haxuwar kan 'yan qasan, kuma takobi da
aka tanade shi ga duk wanda yake son raunata amincinsa da zaman lafiyansa. Kuma
duk wanda ya ke son kawo fuji a cikin jikin wannan qasa ko al'umma, ba zai iya
ba.
Wannan
qasa ta tsayu; akan ginshiqai tabbatattu, da manhaji ko tsarin musulunci, kuma
duk wanda yake nufin karya wannan tsari ko raunata shi to ba zai kai ga cimma
manufarsa ba, kuma zai yi hasara.
Mu kuma
muna da tabbacin cewa lallai waxannan ababen (na hare-hare) ba masu tabbatuwa
ba ne; za su gushe, kuma jama'arsu da izinin Allah da sannu za su vuya, saboda
faxakarwa da bayanai da kuma qarfi da takobi.
Kuma
wajibi ne akan musulmai gabaxaya su riqa bayyana wuraren vuyansu, da vatansu.
Kuma haramun ne rufa asirin xaya daga cikinsu. Kuma duk wanda ya basu mafaka,
ko ya ce aiyukansu biyayya ne (ga Allah) to lallai yayi tarayya da su cikin
kashe rayuka katangaggu.
Lallai mu
muna qin waxannan aiyukan kuma muna inkarinsu, wannan kuma shine halin kowani
musulmi, mai hankali, ballantana maluma da xaliban ilimi, saboda al'ummar
gabaxayanta da dukkan vangarorinta suna kan turba xaya, kuma cikin kwale-kwale
xaya. Kuma lallai haxin kan wannan al'umma da wanzuwarta qarqashin tuta xaya
tushe ne na qarfinta da qara samun kariya.
Wajibin da
ke kanmu gabaxaya shine fito-na-fito da waxannan aqidun, ta dukkan hanyoyi da
minbarorin faxakarwa. Da yin taimakakkeniya cikakke tsakanin vangarorin 'yan
qasa da al'umma, domin mu tsaya sahu xaya. Tare da wajabcin haxin kai da
nisantar ababen da ke jawo savani, da yin maganin rarrabewar kai.
Kowa ya
sani, lallai kiyaye lamarin amincin al'umma abu ne da shari'a ta ke nema, kuma
tozarta shi tozarta addini ne da ilimi da rayuka, da mutunci, da arziqi.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Idi wani
lokaci ne daga cikin manya-manyan lokuta na yaxa soyayya, da nashaxantar da
zuciya da ma'anoninta, da kuma kunna garwashin ji –na jika- da kyawawan ababen
da suke nuna soyayya, Kuma haqiqa Musulunci ya sanya soyayya ta zama ginshiqi
na asali wajen gina al'ummai, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yana cewa: "Imanin Xayanku
ba zai cika ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda ya ke so wa kansa".
Soyayya,
tana haifar da samun al'ummai masu son juna, wanda iskar soyayya zata fiskance
ka ta dukkan geffan rayuwarsu, kuma ma'anonin qauna da buwayar rai sune za su
yi musafaha da kai a farfajiyoyinsu. Sai
Miji ya riqa canjin soyayya tare da Matarsa, 'Ya'ya su riqa son iyayensu, Dangi
makusanci ya riqa son makusancinsa, Makwabci ya so makwabcinsa, Mawadaci ya so
faqiri, Babban mutum ya so qarami, Ma'aikaci ya so aikinsa, irin soyayyar da take
qarfafar alaqar zaman gari ko qasa xaya, kuma take haifar da buwaya da kariya
ga wannan al'ummar.
Kuma
irin wannan soyayyar, ita take sanya al'umma, tare da dukkan xaixaikunta su
zama kamar jiki ne guda xaya, wanda idan xayansu ya yi farin ciki sai dukkan
jikin yayi farin ciki, idan kuma xayansu ya koka sai sauran jikin ya koka, suna
masu qarfafar juna da tallafawa, har xaixaikun al'umma, su riqa motsawa wajen
bada gudumawa a lokacin mawuyacin hali da tashin-tashina, da toshe yanayin
talauci da buqata, ko tunkuxe hatsari, ta yadda xan'uwa zai riqa qarfafa wa
xan'uwansa; yana mai yaye baqin cikinsa, yana rufa masa asiri, yana taimakonsa
wajen warware matsalolinsa, yana tarayya da shi cikin farin cikinsa, da xebe
masa kewa da bashi agaji cikin baqin ciki, ya riqa taimakonsa idan ya kasance
wanda aka zalunta, ya masa kamun qafar
shafa'a, ya riqa cike givinsa, yana gyara aibukansa, ya riqa taimakonsa da
dukiyarsa da zancensa, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya ce: "Lallai
mumini yana yin sabo, kuma babu alheri ga mutumin da baya sabo, kuma ba'a
sabawa da shi".
Allah
yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da
KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, ku nemi gafararSa,
lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta
tabbata ga Allah, wanda yake cewa:
"Kuma a yayin da muka sanya xakin ka'aba ya zama
wajen kai-komo, da aminci" [Baqara: 125]. Ina yin godiya a gare shi,
kuma ina yaba masa akan ni'imominsa manya-manya, kuma ina shidawa babu abin bautawa da qaskiya
sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, wanda yake cewa: "Kuma su bauta wa Ubangijin
wannan xaki * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish:
3-4].
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, wanda idan ya ga jinjirin wata
sai yayi addu'a ya ce: "Ya Allah! Ka bayyanar da jinjirin
wata akanmu da aminci da Imani, da kuma salama da musulunci".
Allah
ya yi qarin salati da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, sallama mai
yawa.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Kowace
shekara (fatanmu ita ce) ku riqa son sashinku; so mai yawa (amin), Qasa kuma ta
yi ta xaukaka tana samun bunqasa da ku, Al'ummar musulmai kuma su qara samun
izza da taimakon nasara.
Kowace
shekara hannaye tsarkaka (da fatan) su yi ta yin musafaha. Zukata farare tas
suna yafe wa juna. Rayuka nagartattu da soyayya wa juna suna saduwa (Amin,
Amin)
Sai
ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku
da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati
ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! kayi salati wa Annabi
Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa. Ya
Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu da
iyalansa da sahabbansa masu krimci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya
mafificin masu rahama.
Ya
Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka
musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya
Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini, Ya Allah! Ka sanya
wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya
Allah! Ka karvi azuminmu da sallolinmu da ruku'inmu da sujadanmu, Ya
Allah! Ka sanya mu daga cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu ya
mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka
aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi
gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga
cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri
gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga
cikinsa da wanda ba mu sani ba.
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda
ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna
roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya
Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka
kiyaye su a ko-ina suke, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai
tagaza musu, Ya Allah! Ka karvi wanda ya mutu daga cikinsu yana mai shahada, Ya
Allah! Ka xaukaka darajarsu cikin darajar "illiyuna", Ya Allah! Ka
ninnika kyawawansu, kuma ka yi musu rangwame akan munanansu, kuma ka xinke
karayar iyalansu da danginsu, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Wanda ya nufe mu, ko ya nufi musulmai da mummuna, to ka shagaltar da
shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa Ya mai amsa addu'a.
Ya
Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da
yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Ubangijin halittu.
Ya
Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah!
Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka,
kuma ka bashi lafiya, Ya ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka datar da jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin
hukunci da shari'arka, Ya mafi rahamar masu rahama.
"Ya Ubangijinmu! Mun
zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance
daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
"Ya Ubangijinmu! Ka
bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar
wuta" [Baqarah: 201].
"SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN,
WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA" [].
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment