HUXUBA DAGA MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
???/???/1437H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL
HAMD
Allah
(ta'alah) ya yi wa gavvan mutum ni'ima ta ji da motsowa, sai ya sanya zuciya ta
zama ita take mulkan gavvan (sarki). Kuma lallai, Babu wata zuciya da za ta
cika da rayuwa, ko kuma ta harba da xebe kewa sai bayan garwashin soyayya ya
kunnu a cikinta.
Ita
kuma soyayya ko qauna ita ce, ruhin rayuwa, kuma jagora izuwa ga samun aminci, tana
canza abu mai xaci zuwa ga zaqi, zogi kuma waraka, cuta kuma zuwa ga ni'ima.
Soyayya arziqi ne da Allah ke bada shi ga zukatan bayinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa a sha'anin Khadijah (رضي الله عنها):
"Lallai ni, an azurta ni da sonta",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma,
Allah (سبحانه) ya nufi ya gina
rayuwa a tsakaninsa da tsakanin halittunsa a kan ginshiqin soyayya, a inda yake
cewa, dangane da mutanen da suka kawar da kai:
"Kuma da sannu Allah zai zo da waxansu
mutanen da yake sonsu, suma suke sonsa" [Ma'idah: 54].
Ita
rayuwa, ba za ta tava yin daxi ba, duk yadda zahirinta ya qawatu; ko yayi kyau,
matuqar babu soyayya, kuma babban mutum baya wadata ga barin soyayya, haka kuma
qarami, saboda idan aka haramta wa mutane son juna, to sai su rayu; rayuwa irin
ta rashin sanin juna, da yanke alaqoqi, kuma sai su zama sharri ga sashinsu
fiye da dabbobi masu karya qashi, da kuma kwari masu dafi.
Kuma
haqiqa, al'umma gabanin zuwan musulunci, ta kasance cikin ximuwa, a wargaje,
ana tunkuxa ta zuwa ga makamin harbi, Sai Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya taso, ya warware dabaibayin yaqi, ya
kuma kunce xaurinsa, Sannan ya daddasa dashen aqidar imani a cikin zukata,
wanda ya sanya igiyar soyayya ta zama ita ce igiya ta farko, kuma wanda tafi
qarfi, Sai yaqukan da wutarsu suke ruruwa suka mutu, suka dusashe, Sai qabilun
Aus da Khazraj suka haxe, sannan aka samu 'yan'uwantaka tsakanin waxanda suka
yi hijira, da Ansaar (mutanen Madina mataimaka), sai lamarin qabilanci ya
yankwane kuma ya bi ruwa, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Da waxanda suka tanadi gida, da imani
gabaninsu suna son waxanda suka hijira izuwa gare su" [Hashr:
9 ].
Kuma Allah (سبحانه) ya
ce:
"Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku a lokacin
da kuka kasance maqiyan juna, sai ya daidaita tsakanin zukatanku; sai kuka wayi
gari cikin ni'imarsa kuna 'yan'uwan juna" [Ali-imraana: 103].
Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya lulluve sahabbansa da soyayyarsa, kuma
ya kasance yana yawaita rangwame akansu, mai tausasawa, mai yawaita haquri
akansu, Kai, UbangijinSa (صلى الله عليه وسلم) ya
umurce shi da cewa, ya riqa yin afuwa a gare su, yana nema musu gafara, yana
shawartarsu cikin lamuransu, Sai sahabbai suka yi so wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) irin son da a tarihance ba a tava jin
irinsa ba, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma saboda wata rahama ce daga Allah ka
tausasa musu, kuma da ka kasance mai kaushin harshe, mai taurin zuciya to da
sun watse daga wurinka, sai ka yi musu afuwa, ka nema musu gafara, ka shawarce
su cikin lamari" [Ali-imraana: 159].
Kuma
haqiqa Musulunci ya sanya ginshiqi na asali wajen gina al'ummai akan tushe mai
qarfi, tatacce garau, kuma mai tsarki cikin ji –irin na jika- da soyayya, wanda
ya yi nisa daga xabi'ar son kai ko fifita ta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Imanin Xayanku
ba zai cika ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda ya ke so wa kansa",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Soyayya,
tana haifar da samun al'ummai masu son juna, wanda iskar soyayya zata fiskance
ka ta dukkan geffan rayuwarsu, kuma ma'anonin qauna da buwayar rai sune za su yi
musafaha da kai a farfajiyoyinsu. Sai
Miji ya riqa canjin soyayya tare da Matarsa, 'Ya'ya su riqa son iyayensu, Dangi
makusanci ya riqa son makusancinsa, Makwabci ya so makwabcinsa, Mawadaci ya so
faqiri, Babban mutum ya so qarami, Ma'aikaci ya so aikinsa, irin soyayyar da ke
qarfafar alaqar zaman gari ko qasa xaya, kuma take haifar da buwaya da kariya
ga wannan al'ummar.
Kuma
irin wannan soyayyar, ita take sanya al'umma su zama suna iya bada kansu; koda
kuwa za su qare wajen sadaukar da rai, da soyayya ta jivinta, kuma sai ya sanya
al'ummar, tare da dukkan xaixaikunta su zama kamar jiki ne guda xaya, wanda
idan xayansu ya yi farin ciki sai dukkan jikin yayi farin ciki, idan kuma
xayansu ya koka sai sauran jikin ya koka, suna masu qarfafar juna da tallafawa,
har xaixaikun al'umma, su riqa motsawa wajen bada gudumawa a lokacin mawuyacin
hali da tashin-tashina, da toshe yanayin talauci da buqata, ko tunkuxe hatsari,
ta yadda xan'uwa zai riqa qarfafa wa xan'uwansa; yana mai yaye baqin cikinsa,
yana rufa masa asiri, yana taimakonsa wajen warware matsalolinsa, yana tarayya
da shi cikin farin cikinsa, da xebe masa kewa da bashi agaji cikin baqin ciki,
ya riqa taimakonsa idan ya kasance wanda aka zalunta, ya masa kamun qafar shafa'a, ya riqa cike
givinsa, yana gyara aibukansa, ya riqa taimakonsa da dukiyarsa da zancensa, kar
yana izgili da shi, ko cin namansa (giba),
kada ya munana zato a gare shi. Yana himmatuwa da sha'anoninsa, yana
tambayar halin da yake ciki.
A qarqashin inuwar so na gaskiya: Qulle mutum
a cikin rai yana narkewa, Hassada kuma tana tafiya, ana kuma watsar da husuma
da savani, Sai aminci ya yaxu, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya ce:
"Lallai mumini yana yin sabo, kuma
babu alheri ga mutumin da baya sabo, kuma ba'a sabawa da shi",
Alhakim ya fitar da shi a cikin "Mustadrak".
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL
HAMD
Da
soyayya ne miji ke tarbiyyantar da matarsa, Matar kuma take iya mallake
mijinta, kuma da soyayya ne iyaye guda biyu suke tarbiyyantar da 'ya'yansu,
kuma da soyayya ne ake warware matsaloli. Kuma da soyayya ne shugaba ke iya
gano ababen da suka vuya daga cikin abinda waxanda ake shugabanta za su iya (na
qirqire-qirqire da aiki), sai qirqire-qirqire da aiki su qaru. Kuma da soyayya
ake zaburar da bunqasa lamura da gina al'ummah.
Har
ita alaqar da take tsakanin shugaba da wanda ake shugabanta, da mai kiyo da
waxanda ake kiyo suna tsayuwa ne akan ginshiqin soyayya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Zavavvun
shugabanninku sune waxanda kuke sonsu, suke sonku",
Muslim ya ruwaito shi.
Mu,
(musulmai a yau) muna da buqatar gina soyayya; saboda mu iya kashe wutar
qiyayya, da kuma son xaukar fansa. Suma duniya (ko sauran mutane) lallai suna
da buqatar samar da soyayya, musamman a duniyarmu ta yau, wacce lamuran yaquka
wutarsu take qara ruruwa, na kisan jama'a, da xaga mutane marasa laifi daga matsugunansu
(gidaje ko garuruka), da yin fyaxe wa mata, da kashe yara, da qona garurruka da
gonake, da share gidaje (ko rushe su).
Kuma,
Duk wanda ya xauki makami ya kashe xan baffansa, ya kuma kafirta sanyin idonsa;
wato: Uwarsa, da wanda ya ruguje masallatai da gine-gine, Da wanda ya tara
runduna don ya karkashe ko ya qauratar (da bayin Allah), Dukkan waxannan da
waxanda suka yi kama da su, to lallai idaniyar soyayya da jin qai sun bushe
daga cikin jikinsu, kuma ma'anonin mutuntaka a "qamus" xin rayuwarsu sun
fice sun karkace, Sai su ka koma kamar dabbobi masu farauta da karya qashi, ko
cin nama, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Wanda ya xauki takobi akanmu baya
tare da mu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
???
???
???
Shiriyar
Annabi ta zurfafa soyayya a cikin zukata, kuma ta sanya yaren da ake tattaunawa
da shi yana ginuwa akan ginshiqin soyayya, Sai ya koya mana yadda musulmi zai bayyana soyayyarsa ga xan'uwansa; domin
ya watsa lamarin so a cikin ransa, ya kuma jiyar da shi cewa lallai shi, yana
cikin wata al'umma ce, wanda soyayya ta dabaibaye ta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Idan
Xayanku ya so xan'uwansa, to ya sanar da shi" Tirmiziy
ne ya ruwaito da isnadi ingantacce
Tartsati ko haske na soyayya: Watsa sallama
da yaxa ta; -cikin faxi ko aiki ko salo na rayuwa- yana tayar da tartsatsin, Annabi
(صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin ba zan
nuna muku abinda idan ku ka aikata shi za ku so junanku ba? Ku watsa sallama a
tsakaninku" Muslim ne ya rawaito shi.
Sake
fuska, murmushi na gaskiya, da tsarkakekkiyar bushasha sako ne (da ake
turawa) na soyayya, kuma ma'anansa qauna;
Har Abdullahi xan Harith xan jaz'in yake cewa: "Ban ga wani
mutum da ya fi Annabi murmushi ba" Tirmiziy ne ya ruwaito shi da
isnadi ingantacce.
Kyauta tana qara danqon soyayya, kuma
tana tsarkake rai, tana kuma gyara zuciya, kuma tana karfafa alaqoqi; Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku yi
kyauta don ku so juna'' Bukhariy ya ruwaito a littafin adabul mufrad
Allah mai girma, Allah mai girma, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah mai girma, Allah mai girma, kuma godiya
ta tabbata ga Allah!
Wanda yake son ya qarfafa soyayyarsa, ko yake
son soyayyarsa ga 'yan'uwansa ta dawwama, to hanyar hakan ita ce: Toshe
duk wasu hanyoyi na jita-jita ko annamimanci, da qin biye wa mai aikin yaxa ko
yawo da magana, ko yake lalata alaqoqi da wargaza su, Kuma a irin wannan yanayi
alqur'ani ya nuna mana matsaya mai girma, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku waxanda suka
yi imani ku guji yawan zato, lallai wasu zaton zunubi ne, kuma kar ku yi
shisshigi, kuma kar sashinku su riqa gulmar sashi'' [Hujuraat:
12].
Shi masoyi mai hankali, ya kan kasance mai
tsakaitawa cikin jiye-jiyen jikinsa (da axifarsa da aiyukansa, wato: kamar fushi,
da so, ko qiyayya), Mai hankali baya
israfi ko wuce iyaka, don haka: Baya qetare iyaka idan zai yi so, Haka kuma, baya
wuce iyaka idan zai bayyanar da qinsa daga abu, An ruwaito daga Abu-huraira (رضي الله عنه),
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)
cewa: "Ka so masoyinka a sannu-sannu, wata rana zai iya zama maqiyinka,
ka qi maqiyinka a sannu-sannu domin watarana zai iya zama masoyinka" Tirmiziy
ya ruwaito shi, da isnadi mai kyau.
Masoyi na iya shiga ko dulmuya cikin abubuwan
rayuwa, sai alamomin soyayya su dusashe a cikin kogunan nisanta da kyaliya, Wannan
kuma alama ce da take nuna an munana fahimtar yanayin rayuwa, saboda ita rahama
(da jin qai) idan har suka samu gindin zama a cikin zukata, to sai Allah ya
gyara jiki da su, Wannan ya sanya a lokacin da Aqra'a (رضي الله عنه) ya ce waAnnabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ne, ni ina da 'ya'ya goma
ban tava sunbantar ko xaya daga cikinsu ba? Sai ya ce: Ni bana mallaka maka
komai! Ko, dai Allah mabuwayi da xaukaka ya tuzge rahama ce daga
zuciyarka" Bukhariy a cikin adabul mufrad ya ruwaito shi da isnadi
ingantacce.
Shi Mai so, ana son ya zuba soyayyarsa a
mizani na adalci da daidaito, kuma ba a son ya kwarara soyayyarsa ga wani daga
cikin tagwaye, ya kuma kyale xayan, wannan kuma domin ya kawo zaman lafiya a
cikin iyalansa da aminci, saboda a cikin yin adalci a tsakanin xaixaikun iyalai
akwai samun yardarsu, kamar yadda a cikin zalunci kuma akwai janyo qulle mutum
a rai da qiyayya, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya
ce: "Ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin 'ya'yanku" Bukhariy
ne ya ruwaito shi.
Kuma ya ce: "Wanda ya ke
da mata biyu sai ya karkata zuwa ga xayan, to zai zo ranan kiyama gefensa xaya
a karkace" Abu-dawud ya ruwaito shi da isnadi mai inganci.
Samun
kuskure wajen fahimtar menene ma'anar soyayya, da taqaita ma'anar kan: Karkatar
zuci; da ke zuwa ya tafi, ko ga wata sha'awa mai wanzuwa, da bukukuwa na rasar
kunya da batsa da tada sha'awa, ko kwana cikin haramun, to, waxannan suna juya
ma'anar soyayya daga abu mai falala da matsayi zuwa ga: laifi, haka, daga abu
mai daxi izuwa ga azaba da tavewa. Abu na wajibi shine, kada wannan soyayyar ta
kai izuwa ga haramun, ko aiyukan da suke fusata Allah, ko wasu halayya waxanda
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
yi hani kan aikata su, kasancewar dayawa kallo, na aukar da Mutum cikin
haramun; da aka hana, sai kuma ta gadar wa zuciya wata cuta mai tsayi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ka bibiyi abin da baka da ilimi
akansa, Lallai ne, ji, da gani, da zuciya sun kasance abun tambaya ne akansu"
[Isra'i: 36].
HUXUBA TA BIYU
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Idi wani
lokaci ne musamman daga manyan lokuta masu girma; da ake yaxa soyayya, da nashaxantar
da zukata da ma'anonin idi, da kyasta garwashin jin ababen cikin idi masu kyau,
da tafiya a cikinsa akan shiriyar Annabi (S.A.W) domin qasa ta rayu a cikin
falalolin idi, kuma al'umma ta tsinki 'ya'yan itatuwansa.
Cika qidayar ramadana shine farin
cikin da yafi girma, na idi.
Kuma riskar daren
lailatul qadari yana yin qari mai yawa a cikin shekarun rayuwa.
Kuma jikin da
zunubansu suka zuzzube su kan qawata sababbin tufafi.
Kowace
shekara (fatan ita ce) ku riqa son sashinku da so mai yawa (amin), Qasa kuma ta
yi ta xaukaka tana samun bunqasa da ku, Al'ummar musulmai kuma su qara samun
izza da taimakon nasara.
Kowace
shekara hannaye tsarkaka (da fatan) su yi ta yin musafaha, Zukata farare tas
suna yafe wa juna, Rayuka nagartattu da soyayya wa juna suna saduwa (Amin,
Amin)
Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin
alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi,
da tunatarwa mai hikima, Ina faxar
maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
Bayan
haka;
Sai ku yi
salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da
aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin
salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi,
da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! kayi salati wa Annabi
Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi
Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa,
kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne,
Mai girma.
Ya
Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da Iyalan annabi da sahabbansa masu
karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
Ya
Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka
musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya
Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan
qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
"Lallai Allah yana yin umurni da
adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da
abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku
gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma,
kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment