2016/02/04

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI saw TA juma'a 26 RABI'U AS-SANIY 1437H daidai da 5 Fabarairu 2016M ta DR. Salah Albudair











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26 /RABI'U AS-SANIY/1437H
daidai da 05/ Fabarairu/ 2016m




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. SALAH XAN MUHAMMADU ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
            Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya ke kwararo alkhairori da kyautayi, ga kowani na nesa daga cikin halittunsa, da na kusa, Ina yin yabo a gare shi da zuciya da gavvai da kuma harshe, kuma ina godiya a gare shi; bayan ya gusar da cuta da zogi, kuma ya kwararo dayawa daga cikin ni'imominSa da kyautatawanSa.    Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke; bashi da abokin tarayya "Mai rahama (Allah) * ya sanar [da Mutum] alqurani * Ya kuma halitta Mutum" [Rahman: 1-3].
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka zave shi daga zavavvu cikin qabilar Ma'ad, da kuma kevantattu daga qabilar Adnan.
            Salaitin Allah da sallamarSa su qara tabbata a gare shi, da kuma ga iyalanSa da sahabbanSa, waxanda suka yaqi varna da kaifin harshe, da kuma harshen takobi.
            Bayan haka;

            Ya ku Musulmai …
            Wanda ya sani sai ya kiyaye, Wanda kuma ya yi kaifin hankali to sai ya yi ta nisantar dauxa,    Wanda kuma ya jahilta to sai kaga yana aukawa cikin kura-kurai, yana dulmuya.  Wanda kuma ya samu taqawar UbangijinSa sai ya rabauta, ba zai yi baqin ciki ba. "Kuma Allah yana tseratar da waxanda suka bi dokokinsa da basu rabo, Mummuna baya shafansu, kuma Su ba za su yi baqin ciki ba" [Zumar: 61].

            Ya ku Musulmai …
Duniya xan lokaci ne, soyayya ce wanda jin daxinta ba ya dogon wanzuwa,    
Ya tave Wanda kawalwalniyarta ta yaudare shi,    
ko abin shanta ya sanya shi maye,   
har ya shiga cikin turvayarta gabanin ya tuba.
Gida ne na yin tsere, Wannan kuma shine fili (da lokacin) aikata hakan,  
Saidai babu mai rigaye daga cikin dawaki a lokacin kowani tseren da ba na wasa ba, face ingarmomi daga cikinsu.
Kuma, kowani Mutum yana da abinda ransa ta gabatar;
Idan ya yi kuskure yana da sakamakon kuskurenSa,
Haka kuma idan ya aikata daidai.

            Ya ku Musulmai …
            Masarautar LARABAWA ta Saudia qasa ce da ta yi matuqar xaukaka da riqo da addini,   Katangunta kuma suka tabbatu a cikin qasa saboda bin shari'a,   Kuma lallai zai tave (ya yi hasara) saboda azamar shugabanninta Wanda ya ke yin gaba da ita,    Kuma zai gagara cin nasara saboda tuben shugabanta da kaiwa harinsa; Jifan waxanda suke husuma da ita. Kuma duk wanda ya nemi qulla kaidodi ga Qasar Masallatan Harami Guda Biyu Maxaukaka, to, lallai Allah zai tuntsurar da shi akan hancinsa, … … Sai sakamakon kaidinsa ya koma akansa.

Ya ku Musulmai …
            Wanzuwa cikin jama'a garkuwa ne,    Rarrabuwar kai shi kuma tozarci ne,    Jama'a (r da take kan sunnah) ita ce: Haqiqanin gaskiya,      Rabuwa da ita kuma shine: Tushen rushewa,    Rarrabuwa shine farkon sharri da tuntuve,  sannan shi ke kaiwa zuwa ga nisantar gaskiya,    Shine ke mayar da abinda aka gina zuwa ga rushewa, AMINCI kuma ya mayar da shi tatsuniya,   kuma rarrabuwa shine Mai yin rauni, Mai yanyankewa.     
Kuma babu wani mai tafiyan da yafi sharri fiye da mai yawo da annamimanci.  Kuma lallai tushen sharri Shine dukkan mai iza faxa a tsakani, wanda ke yawo da al'amari mai muni.

Ya ku Musulmai …
Lallai haqiqa, Wata jama'a vatacciya ta bijire kuma tana fito-na-fito da wannan al'ummar, wassu (ne 'yan qalilan) kamar cikin tafi; waxanda suka vangare (wa jama'a), kuma tuzgaggu vatattu, waxanda basu da wata manufa face qyasa wutar rashin kwanciyar hankali, da ficewa daga xa'ar shugabanni, sai suka bayyanar da savani da rarrabuwa da husuma, suka kuma zaro takkuban fitina, wai kuma suke yin jihadi da savawa ko kishiyantaka da yin akasi,   da wata aqida 'yar jebu (ba ta asali ba), da kuma wassu fahimtoci masu rauni, ko wassu abinda suka hango, amma masu illa. Ra'ayoyi vatattu sun tuntsurar da su a kan turbobi masu vatarwa, da hanyoyi mabanbanta,    Sai suke kafirtawa, suna tsoratarwa,  suna karkashewa, suna qoqqonawa, suke ha'inci, suke warware alqawura;     Su ba su qyale ko suka bar kafiran amana ba, kuma ba Musulmai suka bari cikin lafiya ba,    Sun jefa kayukansu cikin yanayi na kashe kai mai tsanani,   da suna, ko da'awar yin shahada, sun kuma auka cikin mafi munin yanayin bijirewa wa al'umma da kuma shugaba, da yin fito-na-fito da su, da da'awar yin jihadi.    Dabbobi ne marasa tsari; da suke bin dukkan wanda yayi kira, suke kuma tafiya a bayan dukkan wanda ya yi fito (ko fexuwa).     Idan aka kawo musu hujjoji sai su yi ta musu, ko kuma qa'idodi, sai su kawo maganganun da ba a fahimta, suna kuma qoqarin tunkuxe tabbatattun lamuran addini da hujjoji yasassu; (marasa dalilai); waxanda ba za su qara musu komai ba face shakka da ximuwa da rashin nitsuwa.  Mutane ne masu wuce iyaka, da aikata zalunci,   Mutumin da yake yin musu don kare su to kawai yana yin jayayya ne don kare   varna,   Wanda kuma ya taimake su to lallai yana taimakawa ne don a rushe Musulunci.    Kamar kwari ne da suke son aukawa cikin wuta,  Masu qananun shekaru (da rashin sanin yau da gobe), wawaye, ma'abuta sharri.    
Sun sava wa abinda magabata suke, akansa,   Wanda salihan Mutanen baya suka bi shi, a matsayin MANHAJI.  Sai suka bar abinda xaukacin Mutanen yau suka ruwaito shi daga na jiya (na addini), da wanda maruwaita dayawa suka qarvo daga mutane dayawa, da wanda jama'a suka ruwaito daga jama'a, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace:  Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanda ya bijire daga xa'a, kuma ya vangare daga jama'a, sa'an nan ya mutu, to ya mutu mutuwar jahiliyya, Kuma duk wanda ya fita daga cikin al'ummata, ya kuma yi fito-na-fito da al'ummata; yana dukan nagarinsu da fajirinsu, baya kuma cika alqawari ga ma'abucin alqawari, to baya tare da ni", Muslim ya fitar da wannan hadisi.                
            Jama'a ne vatattu,   waxanda suke xauke da zukatan  da suka cike da qiyayya, da kuma qiraza masu hassada,      Ya kasance daga cikin munanan aiyukansu, Mummunan aiki kuma abin kyama, wanda shine laifin: Tada borm a garin Ahsa'i (a masallacin juma'a, ranar juma'ar da ta gabata), wanda hannayen ha'inci, da warware alqawura suka zartar. (Khawarijawa) mummunan tsiro, wanda da sannu za a tuttunvuke su, a cire, Kana jijiyoyi masu varna; waxanda ba za a ragar musu ba; za a tsittsinke su. Yanayin halaka da Lalacewa yana jiransu, aikin azama kuma shi zai girbe su.

            Ya ku Musulmai …
Samartaka, da yarinta, da qarancin shekaru suna haxe da gafala da damar a iya ruxar Mutum, saboda saurayi mai qaramin shekaru yana da qarancin hangen nesa da basira da hikima da gogewa a cikin rayuwa.    Kuma duk lokacin da mai qarancin shekaru yayi abuta da Mutumin da ba a aminta da soyayyarsa, ko aqidarsa da amanarsa da addininsa ba = to sai wannan mutumin mai dauxa ya yaudare shi; cikin rashin sani, ya kuma ciyar da shi mummunan abu; ta inda bai sani ba, ya kuma shayar da shi guba ta inda baya zato,  sa'annan ya sanya shi cikin rundunar da za ta yaqi; addininta, da kuma qasarsa, da iyalansa, da qabilarsa ba tare da ya san yana aikata hakan ba.    
Kuma duk mutumin da ya bar xansa yana kutsawa cikin kwarin da dabbobi masu farauta suke, a cikinsa, yana kuma wargi da wasa cikin namun daji mayunwata, yana tafiya a cikin duhu, yana kuma qetare wuraren halaka; ko cikin qarafu, to haqiqa (irin wannan Uban) ya sayar da xansa, kuma ya tozarta shi, kuma ya sanya shi ya zama abin kwacen ashararan halittu; ta hanyar yaudara,  sa'an nan abin nufa; da buqatunsu munana.     
Kuma duk wanda ya bar yaransa suna kukkutsawa cikin wasanni da savo, suna kai-komo cikin wuraren fitintinu, suna kuma aukawa cikin taron Mutane, ta yadda suke yin nitso cikin yawa-yawan halittu, da cunkoso, Suna yin abuta da duk wanda suka so; ba tare da wata kulawa ba, su kwana a wajen gidaddaji ba tare da wani tsoro ba, suna kuma zama a nesa (da iyaye) ba tare da wata tambaya ba,  (duk wanda ya aikata haka) to haqiqa ya tauye haqqoqinsu kuma ya zalunci su.       Saboda samari –a irin haka- su kan wayi-gari suna ababen farauta ga sautin shexanu, da hudubobin masu tsegumi, da littatafan masu qetare iyaka; mavarnata, da fatawoyin khawarijawa masu qiyayya, da abubuwan qungiyoyi da ake yinsu a sirrance, da irin qungiyoyin da suke kafirta Mutane suna karkashe su, da sauran qungiyoyin ta'asubanci masu shuka adawa da qiyayya a cikin zukatan samarinmu, akan shugabanninmu da malumanmu da qasarmu.

Ya ku Iyaye, da sauran masu jivintar lamarin 'ya'ya …
Ku kiyayi halin sakaci, da shagala, da sako-sako, da gafala.
Kuma ku dasa a cikin rayukan 'ya'yanku, soyayyar addininsu da qasarsu, da so da wala'i ga shuwagabanninsu da jami'an tsaronsu, da malumansu da limamansu.
Kuma hakan ba zai tabbata ba sai ta hanyar kwarara  musu matsanancin tausayi (da bada kulawa a gare su), da sonsu, da bada kyautuka da kyautatawa, da riqansu a matsayin abokai, da rayuwa tare da su da kyautatawa, da karantarwa, da basu kariya.


Ya ku Musulmai …
Khawarijawa (bijirarru 'yan aware) masu savo ne ga Allah da ManzonSa (صلى الله عليه وسلم); suna aiki ne da savanin littafin Allah (Aqlur'ani) da sunnar (Annabi mai karimci),  kuma Su kashi biyu ne; wato: qafon Shexan guda biyu; (Na farkon sune:) ZAUNANNU DAGA CIKINSU. SAI JIKOKINSU MASU YIN HIDIMA;   
Su zaunannun 'yan a-ware (khawarijawa) Su ne suke aikin qawata wa masu qananan shekarun da suka yaudara yin zanga-zanga, da yin fito-na-fito da shugabanni ko bijire musu, kuma sune suke halatta musu aikin hallaka kayukansu, suna yaudararsu da cewa za a gafarta musu, wai kuma za su shiga aljannoni, Suna kuma nuna musu –da fatawowinsu munana- kyan maqala bomabomai a jikinsu; waxanda suke tashi don su halaka Mutane, da tuqa motoci masu bomabomai, da kuma tayar da su ko qona kai a cikin masallatai da gidaddajin ibada, da kasuwanni, da wuraren taruwan Mutane.     
Su kuma JIKOKINSU DA SUKE YIN HIDIMA (suna masu zartar da dukkan abubuwan da shugabannin suka umurce su da shi), suna da qarancin shekaru, da wauta ko qarancin hankali; wannan ya sanya su, suke zartar da abubuwan da shexanu suka tsara musu, suke kuma tayar da wuta da karyayyun itatuwa. 

Ya kai wannan saurayi matashi….
Kada maganar da aka qawata da yaudara da qarya, da kuma kwalliya ta varna ta yaudare ka !        Saboda  da mutumin da ya kira ka don aikata wannan aikin jihadi yake yi, ko ace: Nasiha yake yi, to da shi da kansa ya yi gaggawar aikin tayar da borm a jikinsa gabanin ya maka da'awa ko ya kira ka zuwa ga qona kanka,  (saidai bai aikata hakan ba), Sai ya vatar da kai; ta hanyar saka ka bin son zuciya, Shi kuma ya zavar wa kansa: Jin daxi, da samun dukiya, da rayuwa, da wanzuwa a duniya,    Kai kuma ya zavar maka da: Mutuwa da hallaka da qarewa,
Sai Ka faxaka,
don ka fita daga cikin gafalarka,
Ka kuma tuba daga kan vatar da ka ke, akanta,
Ka dawo izuwa ga shiriyarka,
Ka da ka kasance bala'i da fitina akan kanka, da iyalanka.

Ya kai Wanda ka yi riqo da abaucewa !
Ka kuma kama hanyar tauri, da tsaurin kai !!
Ka ke yin musu, akan zalunci da varna !!!

Ya kai Wanda ka faxi abinda ake jin nauyinsa a kunnuwa,
Ka buxi baki; kake faxin abinda a xabi'a ake jin qyamar faxinsa,

            Ya kai wanda ka  tove biyayyar shugabanni,
            Kuma ka fice tare da sava wa jama'ar musulmai,

Ya kai wanda aka yi masa aikin jinkiri
(wato, Allah bai gaggauta kama shi ba),
Aka yi masa talala,
Aka sanya wa kama shi lokaci,
Aka dakata masa sannu-sannu,
Jinkirin bai qara komai a gare ka ba, face qara karkacewa?
Sarara maka da aka yi bai yi qarin komai ba, face daxa kangarewa?

Ka yanke varnar da kake, a kai,
Ka dawo cikin basirarka,
Ka kuma komo wa gaskiya,
Gabanin a kamo ka, alhalin kumatunka suna haxe da turvaya,
Sannan
A tsayar da kai domin hukunci na adalci, kana qasqantacce,
Kuma, ka tuba, ka gyara, gabanin abinda kake tsoro ya sauka a kanka (Na azaba, ko mutuwa).

Idan kuma, ka qi, ka tuba, da zavinka, to
Sai ka jira takobin gaya-wa-jini na wuce.

            Ya Allah! Ka kare mu daga waswasin shexanu, Ka kuma nisantar da mu daga hanyoyin vatattu masu varna, Ina neman gafarar Allah, kuma ku nemi gafararSa, Mamakin girman rabon masu neman gafara!

HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah; godiyar da ta kai yanayi na cika da qarshensa.  Irin godiyar da take hukunta samun yardarSa, Ya kuma sanya qarin kusanci da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke  bashi da abokin tarayya, shaidawar da muke fatan samun afuwarSa da kuma lafiyarSa da rahamarSa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, kuma annabinSa ne, zavavvenSa, abun ganawanSa, waliyyinSa, abun yardarSa, kuma wanda ya zava.
Allah ka yi daxin salati da sallama a gare shi, da kuma ga iyalanSa da sahabbanSa, da wanda ya yi aiki da sunnarsa, ya kuma shiryu da shiriyarsa.
Bayan haka;

Ya ku Musulmai,,,
Ku kiyaye dokokin Allah; sai a tunkuxe muku musibobi masu girma, Kuma gwargwadon ingancin niyyoyi ne kyaututtuka suke zuwa, kuma sirrin samun gyara da biyayya shine gyaruwan abinda ke voye (cikin zuciya) da na sirri.
"Wannan littafi ne da muka saukar da shi Mai albarka, sai ku bi shi, kuma ku bi dokoki, tsammanin za a yi muku rahama" [An'am: 155].

            Ya ku Musulmai,,,
 Jarabawar Mutanen (garin Madhaya, ta qasar Siria) waxanda maqiyan addini da Sunnah, suka musu qawanyar hana fita da shiga (na tsawon watanni), da haxin bakin manyan-manyan qasashen kafiran duniya, dalili ne da ke nuna qarfa-qarfa, ko kuma kama-karya; wanda ke gudana a duniyarmu ta yau (mai qarfi alkalin qauye), Al'umma ce guda, ake qasqantar da ita, da makamin: yunwantarwa, da tsoratarwa. Da kuma mata da tsofaffi, da yara qanana, waxanda tsoro ya ke samunsu da yunwa da cutuka da sanyi; ba tare da sun samu magani ko abinci ko abin shumfuxi ko mayafai ba; Sun rasa kayan tunkuxe sanyi a cikin tsananin funturu.
Lallai manyan-manyan qasashen duniya, saboda shiru da suka yi, da rashin motsawansu, da qin taimakawa, alhalin suna ganin hotunan da suke tada hankula da tsoratarwa, to suma za a qidaya su daga cikin waxanda suka yi tarayya cikin wannan mummunan aiki na kisa.
Kuma lallai garurrukan Sunnah waxanda ake rurrushe musu masallatansu, da makarantunsu, ake kuma karkashe zavavan mutane da manyan cikinsu, sannan ake qawanyar hana shigi da fici (a garurrukansu), har su mutu = dalili ne da baya barin shakka, kan: Yadda aka haxu don nufan mabiyan Sunnah; da hukumominsu da al'ummarsu (da sharri), yake kuma nuna voyayyen shiri da kuma yadda Su maqiyan wannan al'ummar suka haxu, akan wannan manufar. Ya ke kuma qara, nuna wani salo da ake bi, na qoqarin gutsuttsura qasashe, da qauratar da mutane daga mahallansu, da da'awar za a kawo gyara.  
"Kuma da Allah ya nufa da basu kasha juna ba, saidai Allah yana aikata abinda yake nufi" [Baqarah: 253].

Ya ku Musulmai …
Ku tashi; don taimakon 'yan'uwanku, da duk abinda kuke da iko, na mayafai, da nau'ukan magani, da abubuwan ci.
Kuma wajibi ne akan hukumomin larabawa, dana Musulmai kada su ci-gaba da zama shiru, basa motsi (suna zura ido), akan tsare-tsaren da ake zuwa da su, na nufan qasashensu da sharri, ko yi musu qawanya (da hana su fita).

Ya kai wanda yake almubazzaranci da dukiyarsa,
Ya ke kuma wasa da halal xinsa,

Ya waxanda kuke yi almubazzaranci,
kuke varna cikin abinci (israaf),
kuke wasa da ni'imomin da Allah ya muku

Rahama, ta fice daga zukatanku ne,
Tausayi aka cire daga qirazanku !
Ba kwa ganin abinda ke faruwa da 'yan'uwanku ne?

Ku ji tsoron Allah (ku kiyaye dokokinsa) gabanin azaba da uqubarsa su sauka akanku,,,,,,,,,,,

Sai ku yi salati da sallama ga Manzon shiriya, wanda zai ceci mutane gabaxaya,                                 domin
Duk wanda yayi masa salati guda xaya to Allah zai masa guda goma.

            Zuwa ga Halittu aka turo shi, don ya zama rahama da jin qai,       Ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa.

            Mutanen baya basu rasa wani Mutum da ya kai Muhammadu ba
Kuma babu kwatankwacinsa da za a rasa, har qiyama.

Kuma shin musibar rasa wani wanda ya halaka, ta kai
Irin musibar Rashin, da ta kasance, a ranar da Muhammadu ya rasu?

            Haske ne da ya haskaka wa Mutane gabaxayansu,
Duk wanda aka shiryar zuwa wannan haske mai albarka to ya shiryu,

            Allah ya yi salati, da waxanda suke kewaye da al'arshinSa,
Da halittun kirki akan Mai albarka; Ahmadu,

            Ya Ubangiji, ka haxa mu tare da annabinmu,
A cikin aljannar da take share kanbun bakan masu hassada,

            A cikin aljannar Firdausi, ka rubuta halinmu,
Ya Ma'abucin girma, Ma'abucin xaukaka, da shugabanci.

            Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga annabinmu da shugabanmu; Muhammadu, Kuma Ya Allah! Ka yarda da iyalai da sahabbai, da wanda ya bi su, da wanda ya bi wanda ya bi su, Ka haxa da Mu tare da Su, Ya Mai karimci ya Mai baiwa!
            Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai! 
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai!  !
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da Musulmai! ! !
Kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai!
Ka kiyaye iyakokin addini!
Kuma ka halakar da azzalumai da masu qetare iyaka!
Kuma, ka taimaki iyalanmu a qasar Sham, da kuma a Falasxinu akan mutane azzalumai, ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka dauwamar wa qasarmu amincinta da wadacinta, da buwayarta da zaman lafiyanta. Kuma ka datar da shugabanmu kuma jagoran lamarinmu; Mai Hidiman Masallatan Harami Guda Biyu Maxaukaka zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, kuma ka kama kansa; ka ja shi zuwa ga aikin biyayya da taqawa, Ya Allah! Ka datar da shi, da na'ibansa biyu zuwa ga abinda a cikinsa akwai amfanin bayi da gyaruwan Musulmai, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga!
            Ya Allah! Ka taimaki rundunarmu a bakin daga Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka xauke –a qasashen Musulmai- husumomi da jayayya, da yaquka, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah! Ka datar da mu don aikata abin da yake yardar da kai, Ka kuma nisantar da mu daga sava maka.
Ya Allah! Ka datar da mu don aikata abin da yake yardar da kai, Ka kuma nisantar da mu daga sava maka.
Kuma ka sanya mu daga cikin waxanda suke jin tsoronka, suke bin dokokinka! Ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka warkar da marasa lafiyan cikinmu, kuma ka bada lafiya ga wanda aka jarraba daga cikinmu, kuma ka warware bautar bayi daga cikinmu, Kuma ka yi rahama wa mamatanmu, ka taimake mu akan wanda yake adawa da mu, Ya Ubangijin talikai!
Ya Allah! Ka sanya addu'oinmu su zama karvavvu,
Ya Allah! Ka sanya addu'oinmu su zama karvavvu, kuma kiranmu ya zama abun xagawa, YA MAI JI, YA MAKUSANCI, YA MAI AMSAWA !!!

انتهى.  

2016/02/02

BIDIYO FILM DAKE BAYANIN AIYUKAN HADIMIN MASALLATAN HARAMI BIYU (SARKI FAHAD) NA KARIN MASALLACIN ANNABI MADAUKAKI






BIDIYO FILM; DAKE BAYANIN AIYUKAN "HADIMIN MASALLATAN HARAMI BIYU"
CIKIN SHEKARU 20 DON FAXAXA DA SAKE GINA MASALLACIN ANNABI MAXAUKAKI




TANADAR
 OFISHIN SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA DA MASALLACIN ANNABI




TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
"Kawai, Mai raya masallatan Allah shi ne, Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya tsayar da sallah, ya bada zakkah, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah, To, akwai tsammanin Waxannan su kasance daga shiryayyu" [Tauba: 18].



Yana faranta mini rai; Na sanar da ku, -daga Madinar Manzo Mai karimci (Salati da sallama su qara tabbata a gare shi)-, kan wata buqata matsananciya da ta dabaibaye zuciyata, Wanda kuma itace Na karvi jagorancin wannan qasa Maxaukakiya, Tare da canza laqabin da za a riqa kirana da shi; daga SAHIBUL JALALAH (wato: shugaba ma'abucin girma), zuwa wani Laqabin da Nake sonsa, kuma amfani da Shi zai xaukaka Ni, Shine: MAI HIDIMAR MASALLATAN HARAMI BIYU MAXAUKAKA (khadimu alharamaini as-sharifaini).

(Sarki Fahad)


Masallacin Annabi Maxaukaki; Wato masallacin Manzon Allah; (صلى الله عليه وسلم) wanda ya ke garin Madinatul Munawwarah: Ya samu babban matsayi a zukatan Musulmai, da Maluman tarihi.
Sai mu koma, ga kwanakin da tarihi ya rubuta, Don mu yi qoqarin  gano farkon yadda garin Madinatul Munawarah ya fara, wanda ta bi matakai masu sauqi wajen bunqasarta, har zuwa lokacin da aka fari aikin ginin Masallacin Annabi maxaukaki, -kamar yadda za a gani cikin zanen misaltawa- don Madinatul Munawwarah ta wayi gari, a matsayin cibiyar da take jagorantar Musulmai, kuma take tsara duk sha'anoninsu, na lamuran da za su tabbatar da walwalar duniya, da samun ni'imar lahira.

A shekarar farko ta hijira: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya tsayu wajen gina MasallacinSa maxaukaki, Sai aka yi aikin rufinsa da tankar Dabino.

Sa'annan sai aka yi aikin faxaxa shi, a shekara ta bakwai bayan hijira, a inda Masallacin ya wayi-gari, yana da kusurwa guda huxu, Tsayinsa kuma kusan zira'i xari, Wanda kuma ya qunshi: Gurbin Sallan Annabi, da MinbarinSa, da Raudha maxaukakiya.

Daga nan, sai Himmar khalifofi, da sauran jagororin Musulmai na aikin faxaxa Masallacin Annabi Maxaukaki, ta biyo baya.
Haka, masu sarauta da sarakunan musulmai, suma suka biyo bayansu; Ta yadda suka qara, hasumiyoyi, da qubbobi, aka kuma shafa zinari a jikin katangu, da usxuwanoni, da qofofi, a wani yanayin da yake nuna gwanancewar musulmai a fannin aikin gini mai kyau.

A qarshen shekarun daular Usmaniyyah, Sai aka qawata wannan masallaci da aikin qara shi; Wanda khalifan daular Usmaniyyah mai suna: As-sulxan Abdulmajid, ya aiwatar, wanda ya kai kimanin mita 2293, a lissafin murabba'i.  Kuma ya gama wannan aikin, a shekarar hijira ta 1277h, a inda aka canza qubbobi, a rufin masallacin, maimakon katakai.

Shekaru kamar 90 sun shige, bayan qarin da khalifan daular Usmaniyya; As-sulxan Abdulmajid, ya yi, Sai Musulmai su ka yi mubaya'a wa shugaban da ya haxe wannan qasa; mai suna Abdul'aziz xan Abdurrahman; Alu-Sa'ud, Sai ya baiwa masallatan harami guda biyu maxaukaka muhimmanci, a tsawon mulkinsa; kuma ya yi umurnin ayi masa qarin daular Saudia ta farko, a shekarar hijira ta 1372h, Sai aka sayi gidajen da suka kewaye da Masallacin, aka rushe su, aka kuma daidaita su da qasa, Sai kuma aka sadar da qarin da daular Saudia ta farko ta yi, da wanda As-sulxan Abdulmajid ya yi, a wani yanayi da yake nuna gwanancewa a fannin gini, mai kyau.
Wannan qarin da aka yi, wanda kuma aka kamala shi a shekarar hijira ta 1375h, ya kai mita 6024 a lissafin murabba'i.
Sai faxi ko girman Masallacin, da dukkan aikin faxaxa shi da aka yi ta yi, (lokaci bayan lokaci) ya fi mita 16327 a lissafin murabba'i.

A farkon zamanin mulkin HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- sai ya tafi akan takun Mahaifinsa;  wanda ya assasa wannan qasa, Jagora; Abdul'aziz  xan Abdurrahman (Allah yayi masa rahama) wajen bada kulawa ga masallatan harami biyu maxaukaka.
Kuma a cikin shekaru ashirin (20) na bunqasawa da samar da manyan aiyuka, a dukkan vangarorin rayuwa, Batun masallatan harami guda biyu suna daga abu na farko da basu muhimmanci (Allah ya daxa kare shi).
Mai HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi-  ya xora tubulin farko, na qara aikin faxaxa Masallacin Annabi maxaukaki, a garin Madinatul Munawwarah, ranar Juma'a, 9 ga watan Safar, ta shekarar 1405 daga hijira, domin Madinatul Munawwara ta ga, Shima Masallacin na Annabi, ya samu mafi girman aikin faxaxawa, da ya tava samu, a tsawon tarihi.
Sai aikin rurrushe ginin da suke kewaye da masallacin ya fara, bayan an gama biyan waxanda aka saya daga wurinsu.
Daga nan, sai aikin ginin faxaxawan da yafi girma ya fara, wanda faxinsa shine: mita 82000 a lissafin murabba'i, domin a wannan karon, faxaawan yafi duk abin da ya gabace, ta fiskar kyautata gini, da faxi, da qarfi, da kyale-kyale, Tare da sanya ko riskar da duk abinda Masallacin zai buqata, saboda an samar da kayan aiki na qarshe, wanda ilimin fannin gine-gine da qere-qere, ya kai izuwa gare su; kamar QUBBOBI masu motsi; waxanda ake aiki da su, a karo na farko, da kuma manya-manyan LEMOMI waxanda aka qirqiro, kuma babu irinsu, da MATAKALAI na lantarki a tsakanin hawan beni da na qasansa; waxanda suke saukake kai-komon dubban xarurrukan Mutane, da wassu irin RUMFUNA ko LEMOMI da suka qunshi dubban FILOLI, da dogayen HASUMIYOYI, wanda sune mafi tsawo da aka tava yi a tsarihin musulunci, da kuma HARABA mai faxi, wanda ba a tava samun irinsa ta fiskar faxi ba, a tsawon tarihi, waxanda kuma aka shumfuxe kasansa da blok xin fulon da ya ke tsote zafin rana, da kuma HIDIMOMI mabanbanta na gyaran abinda ya lalace, madawwami wanda baya yankewa, qarqashin kulawan Babban ofishin sha'anonin masallatan haramin Makkah da na Annabi. Da kuma sauran wassu abubuwan na daban; waxanda za su sanya masallacin Annabi maxaukaki, ya zama wata alama ce bayyananniya akan doron qasa.

HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi-  ya bada kansa da dukiyarsa domin hidiman masallatan harami guda biyu maxaukaka, da kuma kula da mahajjata da masu ziyara da masu umrah.
Don, kuma a kiyaye lamarin addini da yanayinsa, Sai (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- ya yi umurnin ayi amfani da tsare-tsare da suka dace, da yadda aka gina masallacin annabi da irin yanayin ginin musulunci. Sannan ya yi umurnin a zrtar da wannan aikin faxaxawan tare da ci-gaba da gudanar ibada a cikin masallacin; ba tare da aikin da ke gudana ya tsayar da komai ba.

Harsashin da aka gina qarin da (Sarki Fahad) mai hidimar masallatai guda biyu maxaukaka, ya yi wa masallacin Annabi maxaukaki, sun dogara ne akan FILOLI guda 8500 masu dungu uku na FOLABIY, wanda aka kafa sashinsu a cikin qasa, kamar tsawon kimanin MITA 30 zuwa 50.
Kuma idan aka haxe waxannan filolin tsayinsu zai kai, kamar KILO MITA 30.
Kuma a wajen gino harsashin masallacin (faundation) an yi amfani da kusan buhun siminti musallah 100000.
Kuma haqiqa an qulle filoli na FOLABIYYA  da qarfen yin fila da manara da tushe, wanda yawansu ya kai tushe guda 1877. Tsayuwansu kuma akan mita 70000 ne na fila mai dungu uku, wanda aka yi shi da siminti musallah.
            Faxin ginin da (Sarki Fahad) mai hidiman masallatai biyu ya qara, a masallacin Annabi = ya kai mita 82000 na lissafin murabba'i. Wannan faxin kuma zai baiwa Mutane  kusan 170000 damar yin sallah. Kuma an shirya saman wannan ginin don a iya yin sallah a kansa, da faxin da aka qaddara shi da mita 67000 na lissafin murabba'i, wanda kuma Mutane 90000 za su iya yin sallah.
            Kuma wannan qarin da ya yi, ya haxa da, tanada ko shirya harabar da take kewaye da wannan masallacin, wanda faxinsa ya kai mita 235000 da lissafin murabba'i.
            Sai faxin cikin masallacin Annabi maxaukaki, bayan wannan qarin, idan aka dunqule shi ya wayi gari, ya kai mita 98500, a lissafin murabba'i, wato: qarin kawai, ya kai ninkin tsofon Masallacin Annabi (gabanin qarin) har sau biyar.
A, haka, sai wuraren da za a iya yin sallah ya zama kusan gurbin masu sallah mutum miliyan xaya (1000000), a watan ramadana mai albarka, da kuma lokacin hajji.
Qarin hadimin masallatan harami guda biyu (Sarki Fahad), wanda ya aiwatar a masallacin Annabi, Ya haxa da RUMFUNA; waxanda suka qunshi fiye da FILOLI guda 2100, waxanda su kuma a samansu, akwai wasu baka; waxanda a lokacin sana'anta su, da tsatsara su an kula da tsarin da zai kawo daidaito ko ya sanya su, su zama abu xaya tare da qarin da ake masa laqabin: Qarin daular Saudia na farko.  
Shi kuma rufin wannan qarin ya kasu har zuwa yanki 95, waxanda aka lulluve su gabaxayansu. In banda yanki guda 27 waxanda su kuma aka keve su da QUBBOBI masu motsi.
Qarin da mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) ya yi, ya samar da sabin HASUMIYA guda shida akan hasumoyoyin da ake da su a masallacin Annabi maxaukaki; waxanda tsayin kowannensu shine:  mita 104.
Kuma guda huxu daga cikinsu, suna nan ne a kusurwan wannan qarin guda huxu, su kuma sauran guda biyun suna jikin mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, ta vangaren arewa.
Kuma a saman hasumiyoyin akwai hoton jinjirin wata, wanda aka leleye shi da ruwan zinari, nauyin kowani xaya daga cikinsu shine ton huxu.
Sai yawan hasumiyoyin gabaxaya su ka zama guda goma (10), suna haskaka sararin samaniyar Madina da alamar Imani, wacce ta cika da kevantacciyar alama ta kyau.   
Qarin ginin da mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka yayi wa masallacin annabi, ya qunshi MASHIGA GUDA BAKWAI manya-manya, ta vangaren gabas, da arewa da yamma, kuma kowani mashiga yana da qofofi guda biyar a kusa, da kusa, tare kuma da wassu qofofin guda biyu a ta gefensu.
Sannan kuma akwai manya-manyan mashiga guda biyu ta vangaren arewa na wannan qarin, kowanne daga cikinsu yana da qofofi guda uku a wuri xaya, a ta gefensu kuma akwai qofofi guda huxu.
Kamar yadda wannan qarin ya qunshi qofofi guda goma (10), a matsayin mashiga da mafitan matakalai masu motsi na lantarki; domin yin hidima ga hawa na sama na wannan qarin. Qari akan matakalai guda goma sha takwas (18 ba masu motsi ba) ta cikin masallaci.
Kuma a qarshen arewacin masallacin akwai qubbobi guda bakwai (7) da hasumiya guda biyu a saman mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, domin wannan mashigan ya banbanta da sauran, kuma domin ya yi nuni kan zanen kalmomin musulunci masu kyau.
Kuma a saman ginin da mai hidimar masallatan harami guda biyu (sarki Fahad) ya yi, akwai qubbobi guda 27 masu motsi, Nauyin kowanne xaya daga cikinsu ton 80 ne, tsayinsa ta sama kuma mita uku ne da rabi (3 1/2) daga tudun rufin, kuma fiye da mita 16 daga kan qasa. Kuma faxin qubba xaya shine mita 14 da uku bisa huxun mita (3/4), kuma an yi amfani da ton 40 ne wajen sana'anta kowace qubba. Kuma ana bubbuxe qobbobin ko a rufe su ne ta hanyar na'ura; domin a amfana da iska ta xabi'a a wassu yanayin da suka dace.
Mai hidiman masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- shi da kansa, da kuma tunaninsa ya ke bibiyar matakan zanen aikin da qirqiransa, da zartar da shi, a inda ya riqa miqa dukkanin abinda zai sauqaqe aikin, musamman idan wani abu ya gitta ko ya so ya tsaya a gaban wannan aiki mai xan karen girma na wahalhalu ko abinda zai hana ruwa gudu.
Kamar  yadda ya bada muhimmanci mai girma –Allah ya qara kiyaye shi- wajen yin hidima da kawo kwanciyar hankali ga masu ziyartar masallacin annabi maxaukaki; Sai aka qirqiri lemomi guda 12 don kare masallata daga zafin rana, a wurin da ake ce masa, HASWATU BIYU, daga cikin wuraren da aka qara, a lokacin qarin ginin da daular Saudia ta farko ta gabatar. A matsayin misalin da bashi da makamanci.
Kuma ana bubbuxe waxannan lemomin, ana kuma rurrufe su da na'ura, duk da girman kowanne daga cikinsu. Kamar yadda a lokacin sana'anta su an lura da abinda zai kawo haske, da kyautata iska, da kawo sanyi a jikinsu. Kuma girman kowace lema ya kai mita 306. Sannan ana sana'anta lemar daga sejintiplon wanda gobara ko wuta bata qona shi, haka kuma, da wassu layukan na haske qanana; waxanda da ido kawai ba za a iya ganinsu ba.

Su kuma gine-gine da hadimin masallatan harami biyu maxaukaka ya yi don hidimomi mabanbanta ya haxa da; Gini guda 15, wanda kowannensu ya qunshi: hawa huxu (a cikin qasa); Kuma a cikin waxannan gine-ginen akwai: wuraren alwala guda 6214, da kuma banxakai guda 2432, da mataka guda 116 na latarano wanda aka yi su, a wurare talatin mabanbanta (30), qari akan matakalolin da basa motsawa suma guda talatin (30).
Kuma wannan qarin ya qunshi gini guda 27 don wassu kevantattun hidimomi; kamar cibiyoyin lafiya, da cibiyoyin kunne-kunne, da kashe-kashe (control), da cibiyoyin gyaran na'urori,  da cibiyan kashe gobara, da xakin kula da aiyukan tsaro.
Qarin da mai hidiman masallatan harami maxaukaka ya yi, ya qunshi: Kevantacciyar tashan wutan lantarki, domin samar da wutan wucin gadi ko kar ta kwana , wanda mashuna ko injuna guda biyar suke yin aiki a cikin wannan tashar; don su iya wadatar da vangarorin da aka qara na masallacin, da kuma wani injin guda xaya na daban don ya bada wuta a wuraren fakin xin motoci. Sannan sai aka qaro wassu injunan guda biyu; domin wutan da ake samu idan aka haxa shi, ya iya kaiwa wanda zai haskaka birni guda cikakke.
Shi kuma aikin kawo sanyi (A C) a masallacin Annabi maxaukaki yana dogara ne, akan cibiyoyin kawo sanyi guda shida (6), wanda suke aiki da injunan wuta; qarfin xaya daga cikinsu qisan dubu bakwai (7000) ne, Kuma a cikinsu akwai babban abin sanyaya ruwa, a duniya. Kuma tashar sanyayawar ta qunshi galan 17000 na ruwan da ake sanyaya shi a kowani minti xaya. Kuma tafiyan ruwan da aka sanyaya shin yana farawa ne daga tashar sanyaya shi; wanda nisanta –zuwa da komawa- shine: kilomita bakwai daga masallacin Annabi, kuma ruwan ya kan kasance ne, cikin wani hanyar tiyo na musamman, wanda ya ke bi ta cikin hanyar da aka yi a cikin qasa; wacce aka mata suna da NAFAQUL KHADAMAAT.
Kuma a nan za mu ga cewa, hanyar wannan aiki da aka bunqasa, wajen kawo sanyi, wanda bashi da makamanci a duk duniya, Ta yadda a cikinsa ake: Tace iskar da za a riqa shaqarta, tare da sanyaya ta, sai watso ta, ta wassu kafofi ko vuli-vulin da aka samar da su a jikin qasan filolin masallaci; wannan kuma ba don komai ba; sai domin yanayi mai sanyi (da daxi) ya game xaukacin masallacin Annabi maxaukaki.

(Ruwan zamzam): Shi kuma ruwan zamzam ana xauko shi ne, daga cibiyar tashar da ake cika gorunan zamzam; wacce take Makkatul mukarramah, zuwa cibiyar tashar sanyayawa ta garin Madinatul munawwarah. Kuma aikin dako, ko xauko ruwan zamzam yana ci-gaba a cikin wassu tankunan da aka tabbatar da su akan motoci, a tsawon duka kwanakin shekara.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...