HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26/Ramdhana/1440H
daidai da 1/Juniyo/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
Sheikh Dr. Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
BANKWANA DA WATAN AZUMI (RAMADHANA)
(رحيل رمضان)
Shehin Malami
wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya tsare shi- ya
yi hudubar juma'a mai taken: TAFIYAR WATAN AZUMI, wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode
maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah
daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar
da shi, Wanda kuma ya vatar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu
bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su qara tabbata a gare
shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya
ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da kuma a
bayyane (a lokacin ganawa).
Ya
ku Musulmai
Musulmai
sun rayu a cikin wannan wata (na Ramadhana) mai albarka, a ciki wani lokaci mai
falala, wanda yininsa azumi, darensa kuma salloli, an rayar da Masallatai a
cikinsa da ayyukan xa'a, da kuma karatun Alqur'ani, kuma Halittu a cikinsa sun
kusanci Allah Mai karamci Mai jin-qai, a lokacin da suke jujjuyawa a cikinsa a
tsakanin zikiri da addu'a da bayar kyauta da baiko. Zukata sun samu natsuwa,
gavvai kuma sun fiskanto Allah, sai Bayi a cikinsa suka xanxani wani abu na
halawar imani da zaqinsa, to amma ga kwanakinsa suna shelanta tafiya, kuma sun
yi kusa da qarewa. Don haka; Wanda aka masa dace, shine Mutumin da ya ribaci
sauran abinda ya rage daga cikinsa, saboda ayyuka suna zama abin lura ne da
abinda aka cike su da shi. Kuma abin dubawan shine kamalar qarshen ayyuka, ba
naqasar farko-farkonsu ba.
Kuma
duk wanda ya kasance cikin watansa yana mai mayar da al'amari ga Allah, kuma
cikin ayyukansa yana mai dace da sunnah, to sai ya qara kyautata gininsu, kuma
ya yi godiya wa Allah akan ni'imomi, kuma kada ya kasance kamar wanda ta
warware zaren saqarta filla-filla, a bayan ya yi qarfi.
Kuma
kiyaye aikin xa'a shine yafi wahalarwa akan aikata ta, kuma yana ciki addu'ar
salihai "Ya
Allah, muna roqonka aikata aiki na kwarai, da batun kiyaye shi (daga lalacewa)".
Wanda kuma
ya zama ta xaya vangaren, to sai ya yi gaggawan tuban gaskiya, saboda qofar
tana a buxe yake, Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Hancinsa ya bugi turvaya; Mutumin da watan Ramadhana ya
shiga, sa'annan ya fita, gabanin a gafarta masa" Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma ku
kasance dangane da al'amarin karvar aiki, kun fi tsananin himmatuwa fiye da
aiwatar da shi (aikin), saboda, kawai Allah yana karvar aiki ne daga masu
taqawa.
Kuma
Mumini yana haxa tsakanin kyautata aiki, da tsoron qin karva, saboda halinsa
kamar faxin Allah Ta'alah ne: "Kuma waxanda suke bayar da
abinda suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace, domin su masu komawa ne
ga Ubangijinsu" [Mu'uminuna: 60].
A'isha -رضي الله عنها- ta ce: "Ya Manzon Allah -صلى
الله عليه وسلم-
shin sune suke shan giya kuma suke sata? Sai ya ce: Ya 'yar gidan Siddiqu! A'a,
sune suke yin azumi, kuma suke yin sallah suke yin sadaka, amma suke tsoron
kada ya zamto ba a karva musu ba, (Waxannan
suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri, alhali kuwa suna masu rigaye a
cikinsu)" [Muminuna: 61]. Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma koda
watan azumi ya shuxe, to lallai aiki baya yankewa, sai idan an mutu, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta
zo maka" [Hijr: 99].
Kuma aiki dawwamamme
kaxan, shine yafi alheri akan mai yawa, mai yankewa, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Aikin da yafi soyuwa a wurin Allah, shine wanda aka fi
dawwama akansa, koda kaxan ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito
shi.
Kuma yana
daga alamar karvar aikin kwarai, yin wani aikin na kwarai a bayansa.
Kuma yana
da kyau a aikata kyakkyawa a bayan mummuna; domin ya kankare shi.
Abinda
kuma yafi kyau shine aikata mai kyau da biyar da shi bayan wani mai kyan!
Kuma yana
daga falalar Allah da karramawarSa: Yadda ayyukan watan azumi suka
kasance masu dawwama a tsawon kwanakin shekara, misalin tilawar Alqur'ani da sadaka
da azumi, da umrah da addu'a da sallolin dare, da wasun waxannan daga cikin
abinda Allah ya shar'anta aiwatar da su a tsawon rayuwa.
Kuma cikin
dawwamar aikin xa'a da tsawaitar zamaninsa akwai ni'ima mai girma ga salihan
Mutane, da sanyi ido ga Muminai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai
waxanda suka ce: Ubangijinmu shine Allah, sa'annan suka daidaitu, Mala'iku suna
sauka akansu (a lokacin mutuwa, suna ce musu:) Kada ku ji tsoro, kuma kada ku
yi baqin ciki, kuma ku yi bushara da Aljannah, wanda ta kasance ake muku
alqawali" [Fussilat: 30].
Kuma a
qarshen Ramadhana akwai albishir ga Ma'abuta azumi da sallah, "Wanda ya yi azumin Ramadhana cikin imani da neman lada,
an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa, Kuma wanda ya yi tsayuwar
lailatul qadari cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata
daga zunubansa" Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma "Wanda ya yi qiyamul laili na dararen Ramadhana an gafarta
masa abinda ya gabata daga zunubansa", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
"Kuma mai azumi yana da farin
ciki nau'i biyu da yake yinsu; na farko a lokacin buxa-bakinsa, da kuma wani
farin cikin a lokacin haxuwa da UbangijinSa" Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Bayan
haka:
Ya ku
Musulmai...
Rayuwa
numfashi ne kidayayyu, kuma ajali ne iyakantacce, kuma dukkan rayuwar da ake
qididdige ta da numfashi to mai saurin qarewa ce.
Kuma cikin
qarewar Ramadhana akwai darasi dangane da qarewar Duniya da abinda yake
cikinta, Kuma kamar ga ku, alhalin ayyuka sun qare, Duniya kuma ta shuxe, a
lokacin kowane Bawa jingine yake da abinda ya aikata, kuma wanda zai samu rabo
shine wanda ya amsa wa mai kiran Ubangijinsa, kuma ya kasance daga cikin masu
kyautatawa (muhsinai).
A UZU
BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM: "Wanda
ya aikata aiki na kwarai, daga namiji ko kuwa mace, alhali yana Mumini, to
haqiqa zamu rayar da shi rayuwa mai daxi, kuma haqiqa zamu saka musu ladansu da
mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahl: 97].
Allah
ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan
kyautatawarSa, kuma godiya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; ina mai girmama
sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi daxin salati a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai ninkuwa.
Bayan
haka
Allah ya
kevance wannan wata (na Ramadhana)da zakkar fid-da-kai, a lokacin qarewarsa,
domin ta zama tsarkaka ga masu azumi, kuma abinci ga miskinai.
Gwargwadonta shine: Sa'i
xaya, daga galibin abincin Mutanen wannan garin.
Kuma Mutum
zai fitar da ita wa kansa da iyalansa.
Kuma lokacin
fitar da ita na mustahabbi shine, daga gabanin sallar idi, amma ya halatta
a fitar da ita gabanin haka da yini xaya ko biyu.
Kuma a
qarshen Ramadhana, sunna ce mai qarfi a riqa kabbara, daga faxuwar ranar yinin
qarshe, har zuwa lokacin sallar idi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah akan yadda ya shiryar da ku,
kuma tsammaninku za ku gode" [Baqara : 185].
Kuma wanda
ya yi azumin Ramadhana, sai ya biyar da shida a bayansa daga watan Shawwal,
to kamar ya azumci kwanakin shekara ne gaba xayansu.
Sannan ku
sani, Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa, a inda
yake cewa: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin
salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi,
da sallamar aminci" [Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment