2019/05/23

19 Ramadhana 1440 Husain Alus Sheikh الرحمة بالناس في رمضان











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 19/RAMADAHANA/1440H
daidai da 24/MAYU/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUS-SHAIKH



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
RAMADHANA WATAN TAUSAYI DA RAHAMA NE
(رمضان شهر الرحمة)
Shehin Malami wato: Husain xan Abdul'aziz Alus-Sheikh–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TASIRIN AZUMI AKAN HALAYEN MUTANE,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Lallai jiga-jigan DABI'U DA HALAYE MASU KARAMCI, a Musulunci suna da matsayi masu girma da sha'ani cikakke, saboda nassoshin shari'a mutawatirai sun zo suna kwadaitarwa akan kyawawan halaye, da xabi'u na kwarai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai kai, haqiqa kana kan xabi'un kirki masu girma" [Qalam: 4].
Kuma lallai kala-kalan ibadodin da aka shar'anta, a cikin jerin manufofin samar da su kaso na biyu, da hikimominsu mabanbanta, suna xauke da abinda yake sanya Musulmi yin ado (qawa) da halaye masu girma, da kuma sifantuwa da sifofi maxaukaka, domin al'umma gaba xayanta; rayuwarsu ta tsayu a cikin tsari, qarqashin jeringiyar halayya managarta, da xabi'u masu kyau, waxanda za su  sanya al'ummar ta kasance al'umma mai walwala da jin daxi, wanda falaloli da dukkan nau'ukansu za su riqa yaxuwa a cikinta, haka xabi'un kirki masu yawa mabanbanta da dukkan kalolinsu.
'Yan uwa Musulmai
Watan Ramadhana, a cikinsa an shar'anta ibadodi da ayyukan kusancin da suke tsaftace zukata, kuma suke tsarkake su, sannan su tsaftace gavvai, su gyara su, ta yadda Musulmai gaba xayansu za su fa'idantu da samun tarbiyyar da zata jagorance su ga bin mafi alherin hanyoyi, suna masu aiki da mafi kyan halaye.
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas -رضي الله عنهما- ya ce: "Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya kasance, yafi dukkan Mutane kyauta, kuma ya kasance yafi yawaita kyautarsa a cikin watan Ramadhana, a lokacin da mala'ika Jibrilu yake haxuwa da shi, kuma ya kasance yana haxuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadhana, sai ya yi bitar Alqur'ani da shi. Kuma Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم - yafi iska sakakkiya yawan kyautar alheri", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kalmar "judu; kyauta" a cikin hadisin, ta qunshi dukkan kyawawan xabi'u da halayya masu falala.
'Yan'uwa Musulmai
A cikin azumin watan Ramadhana, akwai tarbiyyantar da Halittu akan nisantar munanan halaye masu yawa, da kautar da rayuka daga nisantar xabi'un banza, Annabi -صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar zancen zur da aiki da shi ba, ,,, to, lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Wannan ya sanya, Jabir xan Abdullahi -رضي الله عنه- yake cewa: "Idan kana azumi, to, lallai jinka, da ganinka, da harshenka, su yi azumi daga qarya da savo, kuma ka bar cutar da hadiminka. Sa'annan ka sifantu da shiru da natsuwa a ranar azuminka".
Muradin -a nan- shine, istiqama da tabbatuwa akan waxannan halayyen, da yin tafiya ko-yaushe akan waxannan xabi'un.
Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan ranar azumin xayanku ta kasance, to kada ya yi kwarkwasa a wannan ranar, kuma kada ya yi shewa, kuma idan wani ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi, to ya ce, lallai ni Mutum ne mai azumi".
A watan Ramadhana a cikinsa , akwai tarbiyyantar da Musulmi akan xabi'ar tausayi (rahama), da dukkan kalolinsa da nau'ukansa. Kuma yana daga abinda zai bayyanar da hakan, abinda ya zo, na falalar yin sadaka a cikin wannan watan, da falalar shayar da mai azumi, da ciyar da mai jin yunwa, da toshe matsalolin mabuqata. Kuma da aikata hakan, Musulmi zai tuna cewa, lallai sifar tausayi (rahama), da ma'anoninta masu faxi da gamewa, masu kyau, sifa ce, da ya wajaba Musulmi ya riqa sifantuwa da ita, a cikin dukkan zamaninsa (na azumi da gabaninsa da bayansa), da gaba xayan mu'amalolinsa, saboda faxin Allah Ta'alah: "Sa'annan ya kasance daga waxanda suka yi imani, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haquri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi" [Balad: 17].
Da kuma saboda faxin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Misalin Muminai cikin, tausayawarsu ga juna, da qaunarsu, da tausasawarsu, kamar jiki ne guda xaya, idan wata gaba a cikinsa ta yi ciyo, sai sauran jikin su taya ta kururuwa, da rashin barci da kuma jin raxaxi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma dangane da wannan sifar Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Masu tausayawa, Mai rahama (Allah) yana tausaya musu, ku ji tausayin halittun qasa, sai wanda yake sama ya ji tausayinku".
Don haka, Xabi'ar Tausayawa halittu, sifa ce mai daraja, kuma manufa ce mai girma daga cikin manufofin tarbiyya, a cikin dukkan ibadodi, saboda Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].
Kuma Allah Ta'alah yake faxa a inda yake sifanta Annabinsa -صلى الله عليه وسلم-: "Kuma ga muminai mai tausayi ne mai jin-qai" [Taubah: 128].
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah -رضي الله عنه- ya ce: "An ce, Ya Manzon Allah, ka yi addu'ar halaka ga mushirkai? Sai ya ce, lallai ba a turo ni domin la'anta ba, lallai an turo ni domin na zama rahama", Muslim ya ruwaito shi.

Ya ku taron Musulmai
Lallai Ramadhana lokaci ne na haxuwar Mutane da cunkoso, a yayin sallolin farillai da kuma tsayuwan dare, da kuma lokacin haxuwar Mutane domin buxa-baki, da wajen ibadar i'itikafi, da yayin ibadar umrah, don haka, abinda yake wajibi shine a irin waxannan wuraren ayi matsanancin kwaxayin riqo, kuma ana bayyana mafi kyan sifofin tausayi, rahama, da natsuwa, tare da bayyanar da sauran dangogin mu'amaloli masu kyau, da ayyuka kyawawa wanda za su riqa nuna girman wannan addini (na Musulunci).
Wannan ya sanya Annabi ya tsawatar ga Muminai; da cewar kada mu'amalolinsu su wofinta daga  wannan sifa mai kyau; da kuma xabi'a mai girma (ta rahama), a inda yake cewa:  "Allah baya tausaya ma wanda baya tausayin Mutane" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma duk lokacin da waxannan jeringiyar sifofi masu kyau suka vuya daga rayuwar Musulmi, (aka rasa su) a cikin mu'amalolinsa da alaqoqinsa, to sai ya faxa cikin tavewa da asara, Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba a cire xabi'ar tausayi sai daga shaqiyyi", Tirmiziy ya ruwaito, kuma ya ce: hadisi ne hasan, kuma Hafizan Maluma sun ce, hadisi ne hasan.
Sai a yi tausayin qaramin yaro, muna masu girmama babban Mutum, kuma mu taimaki mai rauni, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Baya cikinmu; wanda baya tausayin qaraminmu, kuma bai san girman babbanmu ba", Ahmad ya ruwaito shi da Tirmiziy, kuma ya ce, hadisi ne mai kyau ingantacce.

Ya ku Limamai: Ku riqa tuna sifar tausayi, har a cikin sallolinku na dare, da tahajjudin da kuke yi da Mutane, a lokacin qiyamu Ramadhana, tare da kwaxayin riqo ko aiki da sunnah, gwargwadon ikonku, kuma ku nisanci tsawaitawa a cikin addu'ar alqunuti, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan xayanku ya yi sallah tare da Mutane, to ya sassauta, saboda a cikin Mutane akwai mai rauni da maras lafiya da mabuqaci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
kuma lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai nakan tsayu a cikin sallah, ina son tsawaita ta, sai na ji kukan qaramin yaro, sai in taqaita sallata, tsoron kada in takura wa Mahaifiyarsa", Bukariy da Muslim suka ruwaito shi.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana qoqari a cikin goman qarshen Ramadhana, qoqarin da baya irinsa a wasu kwanakin ba su ba, Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da sahihu Muslim, daga hadisin A'isha -رضي الله عنها- ta ce: Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- "Ya kasance -idan goman nan (na qarshe) suka shigo- ya kan raya darensa, ya riqa tayar da iyalansa, kuma ya tamke kwarjallensa".
Sai ku raya dararen -Allah ya muku rahama- da ayyukan alkhairori, kuma ku yi gaggawa zuwa ga kyawawan ayyuka, domin ku samu yardar Ubangijin sammai da qasa.


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...