Tsakurowa daga huɗubar Juma'a, ta
Masallacin Annabi SAW
1- Kuma lallai kala-kalan ibadodin da aka
shar'anta, a cikin jerin manufofin samar da su kaso na biyu, da hikimominsu
mabanbanta, suna xauke da abinda yake sanya Musulmi yin ado (qawa) da halaye
masu girma, da kuma sifantuwa da sifofi maxaukaka, domin al'umma gaba xayanta;
rayuwarsu ta tsayu a cikin tsari, qarqashin jeringiyar halayya managarta, da
xabi'u masu kyau, waxanda za su sanya
al'ummar ta kasance al'umma mai walwala da jin daxi, wanda falaloli da dukkan
nau'ukansu za su riqa yaxuwa a cikinta, haka xabi'un kirki masu yawa mabanbanta
da dukkan kalolinsu.
2- A cikin azumin watan Ramadhana, akwai
tarbiyyantar da Halittu akan nisantar munanan halaye masu yawa, da kautar da
rayuka daga nisantar xabi'un banza, Annabi -صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar zancen zur da aiki
da shi ba, ,,, to, lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin
shansa", Bukhariy ya
ruwaito shi.
3- A watan Ramadhana a cikinsa, akwai tarbiyyantar da Musulmi akan
xabi'ar tausayi (rahama), da dukkan kalolinsa da nau'ukansa. Kuma yana daga
abinda zai bayyanar da hakan, abinda ya zo, na falalar yin sadaka a cikin wannan
watan, da falalar shayar da mai azumi, da ciyar da mai jin yunwa, da toshe
matsalolin mabuqata. Kuma da aikata hakan, Musulmi zai tuna cewa, lallai sifar tausayi
(rahama), da ma'anoninta masu faxi da gamewa, masu kyau, sifa ce, da ya wajaba
Musulmi ya riqa sifantuwa da ita, a cikin dukkan zamaninsa (na azumi da gabaninsa
da bayansa), da gaba xayan mu'amalolinsa.
4- Lallai Ramadhana lokaci ne na haxuwar Mutane da cunkoso, a yayin
sallolin farillai da kuma tsayuwan dare, da kuma lokacin haxuwar Mutane domin
buxa-baki, da wajen ibadar i'itikafi, da yayin ibadar umrah, don haka, abinda
yake wajibi shine a irin waxannan wuraren ayi matsanancin kwaxayin riqo, kuma
ana bayyana mafi kyan sifofin tausayi, rahama, da natsuwa, tare da bayyanar da
sauran mu'amaloli masu kyau, da ayyuka kyawawa waxanda za su riqa nuna girman
wannan addinin namu (na Musulunci).
5- Ya ku Limamai: Ku
riqa tuna sifar tausayi, har a cikin sallolinku na dare, da tahajjudin da kuke
yi da Mutane, a lokacin qiyamu Ramadhana, tare da kwaxayin riqo ko aiki da
sunnah, gwargwadon ikonku, kuma ku nisanci tsawaitawa a cikin addu'ar alqunuti,
saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Idan
xayanku ya yi sallah tare da Mutane, to ya sassauta, saboda a cikin Mutane
akwai mai rauni da maras lafiya da mabuqaci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
6- Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
kasance yana qoqari a cikin goman qarshen Ramadhana, qoqarin da baya irinsa a
wasu kwanakin ba su ba, Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da sahihu Muslim, daga
hadisin A'isha -رضي الله عنها-
ta ce: Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- "Ya kasance -idan goman nan (na qarshe) suka shigo- ya kan
raya darensa, ya riqa tayar da iyalansa, kuma ya tamke kwarjallensa".
No comments:
Post a Comment