Huɗubar juma'a a taƙaice
RAMADHANA WATAN TAUSAYI
DA RAHAMA NE
1/ Lallai jiga-jigan DABI'U DA
HALAYE MASU KARAMCI, a addinin Musulunci suna da matsayi mai girma da sha'ani
cikakke, saboda nassoshin shari'a mutawatirai sun zo suna kwadaitarwa akan
kyawawan halaye, da xabi'u na kwarai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai kai, haqiqa kana kan xabi'un kirki masu
girma" [Qalam: 4].
2/ Watan Ramadhana, a cikinsa an shar'anta
ibadodi da ayyukan kusancin da suke tsaftace zukata, kuma suke tsarkake su,
sannan su tsaftace gavvai, sai su gyara su, ta yadda Musulmai gaba xayansu za su
fa'idantu da samun tarbiyyar da zata jagorance su ga bin mafi alherin hanyoyi,
suna masu aiki da mafi kyan halaye.
3/ Jabir xan Abdullahi -رضي الله عنه- ya ce: "Idan kana azumi, to, lallai jinka,
da ganinka, da harshenka, su yi azumi daga qarya da savo, kuma ka bar cutar da
hadiminka. Sa'annan ka sifantu da shiru da natsuwa a ranar azuminka".
4/ Xabi'ar Tausayawa halittu, sifa ce mai daraja, kuma manufa ce
mai girma daga cikin manufofin tarbiyya, a cikin dukkan ibadodi, saboda Allah
Ta'alah yana cewa: "Kuma bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].
5/ Kuma duk lokacin da waxannan jeringiyar sifofi masu kyau suka
vuya daga rayuwar Musulmi, (aka rasa su) a cikin mu'amalolinsa da alaqoqinsa,
to sai ya faxa cikin tavewa da asara, Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba a cire xabi'ar tausayi sai
daga shaqiyyi".
No comments:
Post a Comment