HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/Ramadhana /1440H
daidai da 10/Mayu/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
NI'IMAR ALQUR'ANI DA IMANI
(نعمة
القرآن والإيمان)
Shehin Malami
wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: YI WA KAI HISABI A WATAN RAMADHANA,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo
na Allah ne; Ubangijin kasa da sammai, Ma'abucin ni'imomi da albarkoki,
Ayyukan
xa'a basu amfanar da shi, kuma munana basu cutar da shi, kawai suna amfanar ko
su cutar da wanda ya aikata su ne, saboda Allah Wadatacce ne; baya buqatar
halittu,
Ina
yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda muke sani,
da waxanda bamu sani ba, saboda yabo da godiya nasa ne a cikin dukkan halaye
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake, bashi da
abokin tarayya, Yana da sunaye mafiya kyau, da mafi girman sifofi.
Ina
kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa,
wanda aka qarfafe shi da hujjoji da kuma mu'ujizozi.
Ya
Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka
Muhammadu, da IyalanSa da SahabbanSa masu gaggawar aikata alkhairori.
Bayan
haka;
Ku
kiyaye dokokin Allah Mabuwayi da xaukaka ta hanyar ayyukan da suke yardar da
shi, da nisantar fushinSa da savonSa, saboda babu mai samun rabo sai masu taqawa.
Kuma babu mai yin hasara face mujirimai.
Ya
ku musulmai …
Yin
hisabi ga Rai, da qoqarin yin ayyukan xa'a, da neman qara kyawawan ayyuka, da
kiyaye abinda Allah ya taimaki bawanSa ya masa taufiqin dace; na daga ayyuka
nagari, da nisantar lamurran da suke vata ayyukan xa'oi = sune haqiqanin samun
rabo da tsira a cikin wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwa; Allah Ta'alah ya
ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwar gaban UbangijinSa,
sai ya kange ransa daga son Rai * to lallai Aljannah ita ce makoma"
[Nazi'at: 40-41].
Kuma
Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce dangane da ma'abuta Aljanna: "Sai
sashensu ya fiskanci sashe suna tambayar juna * suka ce: Lallai mu, mun kasance
a gabanin wannan (a Duniya), a cikin iyalanmu munan jin tsoro * Sai Allah ya yi
mana kyautar falala, kuma ya tsare mu daga azabar iskar zafi"
[Xur: 25-27].
Kuma
Allah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani ku yi xa'a ga
Allah, kuma ku yi xa'a ga ManzonSa, kuma kada ku vata ayyukanku"
[Muhammadu: 33].
Ibnu-kasir
–Allah ya yi masa rahama- yake faxa dangane da tafsirin faxin Allah Ta'alah:
"Kuma Rai ta yi dubi kan abinda ta aikata domin gobe"
[Hashr: 18], Ma'ana: Ku yi hisabi ga rayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku
yi dubi kan abinda kuka yi tanadi ga kayukanku na kyawawan ayyuka, domin ranar
da za a dawo da ku, kuma a bijiro da ku ga Ubangijinku. maganarsa ta kare.
Kuma
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mai
hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa, sannan ya yi aiki domin abinda zai
kasance a bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya biye wa son zuciyarsa;
sai yake ta kwallafa buri ga Allah". Hadisi ne
hasan.
Yi
ma kai hisabi, yana kasancewa cikin abinda ya gabata, da kuma cikin yininka, da lokacin da kake
fiskanta, ta hanyar tuba daga dukkan zunubai, da kiyaye kyawawan ayyuka daga
abubuwan da suke lalata su, da qoqarin qara ayyukan alkhairi.
Kamar
yadda TAVEWA DA HASARAR RAYUWA YAKE CIKIN BIN SOYE-SOYEN ZUCIYA, DA AIKATA
HARAMUN, DA BARIN AYYUKAN XA'A, KO AUKAWA CIKIN ABABEN DA SUKE RUGUZA KYAWAWAN
AYYUKA, kuma lallai, ya ishi Mutum sharri, ya riqa aikata abunda zai tauye masa
ladansa!
Ya
ku Musulmai…
Lallai
kuna ganin saurin tafiyar darare da yini, da yadda shekaru suke ta wucewa, Kuma
lallai duk yinin da ya shuxe, to lallai ya tafi da abinda aka yi a cikinsa; ba
zai dawo ba.
Kuma
rayuwa gaba xayanta ba komai ba ce, face wasu darare da yini, sai ajalin Bawa
ya sauka a gare shi, aikinsa ya yanke, sai kuma Mutum ya samu yaqini kan yadda
guri ya rude shi.
Bayan
haka
Kuma
lallai ku, a farko-farkon watanku (na Ramadhana) mai albarka, haqiqa Allah a
cikinsa ya buxe muku qofofin alheri, kuma ya sauqe muku sabubba, sai ku shiga
qofofin alkhairi, kuma ku kiyayi shiga qofofin halaka, Allah Ta'alah ya ce: "Ya
ku waxanda suka yi imani, ku shiga cikin Musulunci gaba xaya, kuma kada ku bi
hanyoyin Shexan, lallai shi a gare ku maqiyi ne mabayyani"
[Baqara: 208].
Ya
ku Musulmai!!!
Ku
girmama ni'imar imani da ni'imar Alkur'ani, saboda ba a tava baiwa wani kyauta
wanda tafi imani da Alqur'ani fala ba.
Kuma
Musulmi ba zai yi azumin ramadhana cikin imani da neman lada ba, face ya samu
wani abu na imani, kuma ya samu albarkar Alqur'ani.
Kuma
ahalin Alqur'ani sune masu aiki da shi, koda basu hardace shi ba. Wanda kuma
bai yi aiki da Alqur'ani ba, to baya cikin ahalin Alqur'ani, koda ya hardace
shi.
Kuma
farkon ni'ima ga wannan Al'ummar ta hanyar shiryar da ita, da rahama gamammiya
da kevantacciya, da samun rayuwa mai karamci ya kasance da saukar Alqur'ani ne,
a cikin watan Ramadhana; saboda saukar Alqur'ani a cikin watan azumi shine mafarin alkhairai,
da albarkoki, da gyaran rayuwa, da samun rabo a Lahira da maxaukakin darajoji,
kuma shine mafarin haske mai yaye duffai, mai xauke jahilci da vata, Allah
Ta'alah ya ce: "Kamar haka, muka yi maka
wahayin ruhi daga al'amarinmu, baka kasance ka san menene littafi da imani ba,
saidai mu mun sanya shi haske muna shiryar da wanda muke so daga cikin Bayinmu,
kuma lallai kai kana shiryarwa izuwa ga hanya madaidaiciya" [Shura:
].
Kuma Allah
ya ce: Allah Ta'alah ya ce: "Ya
ku Mutane, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma lallai mun sauqar
muku da haske mabayyani * Amma waxanda suka yi imani da Allah, kuma suka yi
riqo da shi, to lallai zai shigar da su cikin wata rahama daga gare shi da
falala, kuma ya shiryar da su zuwa gare shi, hanya madaidaiciya" [Nisa'i:].
Don
haka, Wanda ya yi imani da Alqur'ani mai karamci daga na farkon wannan
Al'ummar, ko kuma wanda ya yi imani da Alqur'ani, bayan haka, har zuwa qarshen
Duniya, to haqiqa ya yi godiyar ni'imar Alqur'ani gamammiya cikakkiya, kuma ya
gode wa ni'imar imani cikin abinda ya kevance shi.
wanda
kuma bai yi imani da Alqur'ani ba, to haqiqa ya kafirce wa ni'imomi gaba
xayansu, kuma lallai zai dawwama a cikin wuta, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
duk wanda ya kafirce da shi daga cikin qungiyoyi, to lallai wuta ce makomarsa" [].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya kafirta da
shi, to waxannan sune asararru" [].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai
waxanda suka qaryata ayoyina, kuma suka yi girman kai da barinsu, ba za a
bubbuxe musu qofofin sama ba, kuma ba su shiga Aljannah sai raqumi ya shiga ta
kafar allura, kuma kamar haka ne muke saka wa masu laifi * suna da wata
shumfuxa daga Jahannama, kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar
wancan ne muke saka wa azzalumai" [A'araf: 40-41].
Yana
daga cikin rahamar Allah a gare mu, da hikimarsa, da gamewar iliminsa, yadda ya
farlanta mana azumtar watan Ramadhana mai albarka, sai Manzon Allah kuma -صلى الله
عليه وسلم- ya sunnata
mana tsayuwar dare a cikinsa, kuma ya kevance shi da wasu falaloli, koma bayan
waninsa, Sai mafi girman ibadodi suka haxu a cikin watan, da nau'ukan ayyukan
biyayya, sai Allah ya ninninka ladan ayyuka a cikinsa, domin Musulmi ya tsayu
wajen godiya kan ni'imar Alqur'ani da ni'imar Imani, saboda ni'imomi wajibi ne
a yi godiya ga mai bayar da ni'imomin Mabuwayi da xaukaka, domin ya kiyaye su
daga gushewa, kuma domin ya qara wasu ni'imomin a nan, da kuma makoma.
Kuma
godiya wa Allah akan ni'imominsa yana kasancewa da nau'oin ibadodi, kuma mafi
girmansu shine Tauhidi (kaxaita Allah). Kuma yana kasancewa ta hanyar
kyautatawa ga halittunsa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai
ne mu, mun yi maka kyauta mai yawa * sai ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka
soke raqumi" [kausar: 1-2]. Kuma abinda ake
nufi da kalmar "kausar" shine alheri mai tarin yawa wanda ba mai
kewaye da iliminsa in ba Allah ba, yana kuma daga cikinsa, tafkin alkausara,
wanda yake cikin Aljannah.
Sai
Allah –a nan- ya shiryar da Annabinmu -صلى الله
عليه وسلم- zuwa godiya
ga ni'imominsa, da nau'ukan ibadodi, da kuma al'amarin kyautata wa halittunsa da
nau'ukan kyautatawa da amfani.
Kuma
haqiqa shugabanmu annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- ya baiwa waxannan matakan haqqinsu, kuma ya bi umurnin
Ubangijinsa cikakken bi, da fatan Allah ya yi sakayya wa Annabinmu Muhammadu -صلى الله
عليه وسلم- akanmu da mafi
alherin abinda ya sakayya ga wani annabi akan al'ummarsa, saboda ya isar da
manzanci, kuma ya sauke amanar Allah, ya yi nasiha ga al'umma.
Kuma
Allah Ta'alah yake faxa dangane da annabi Musa –عليه الصلاة والسلام-: "Ka yi riko da abinda na baka, kuma
ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Ku aikata godiya –Ya ku diyan
dawuda-, kuma kadan ne mai godiya daga cikin bayina"
[Saba'i: 13].
Wasu
daga cikin Maluman tafsiri suke cewa: Babu wata sa'a da ta shuxe cikin dare ko
yini, face wasu daga iyalan annabi Dawud suna cikin ruku'i ko sujjada.
Kuma
a lokacin da Allah ya ambaci ni'imominSa ga Maryama –عليها السلام-
sai ya umurce ta da yin godiya, a inda ya ce: "Ya
Maryamu! Ki Qanqan-da-kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujjada, kuma ki yi ruku'i
tare da masu ruku'i" [Ali-imrana: 43].
Kuma
Allah Ta'alah yake faxa dangane da sahabbai –Allah ya qara yarda a gare su-:
"Kana ganinsu suna masu ruku'i, masu sujjada, suna
neman falala daga Allah, da yardarSa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu na
guraben sujjada" [Fat-h: 29].
Don
haka, yin ibadodi a cikin watan Ramadhana da waninsa suna daga godiyar Allah
akan ni'imar imani da ni'imar sauqe Alkur'ani.
Kuma
Alqur'ani yana da qarfin tasiri ga ruhi, a cikin watan Ramadhana, saboda raunin
masu fizga zuwa ga sharri, da qarfin sifofin alkhairi, a sakamakon azumi, da
raunin qarfa-qarfar Shexan.
Sai
ku yawaita tilawarsa da nazari cikinsa.
Kuma
halin Musulmai ba zai gyaru ba, sai da Alqur'ani da sunnah.
Kuma
da masu hikimar Duniya za su haxu gaba xayansu, daga farkonsu har na karshensu,
da rayayyunsu da matattunsu, domin warware matsala xaya daga cikin matsalolin Duniya,
to lallai da ba za su shiryu zuwa ga hakan ba, Saidai Alkur'ani ya bayyana gaskiya cikin kowace mushkila.
Dubi
MAS'ALAR AQIDAR HALITTU KAN ALLAH TA'ALAH DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA DA
AYYUKANSA, DA HAQQINSA NA A MASA BAUTA, akidu nawa ne akan wannan mas'alar? Ba
za su iya kididdiguwa ko kirguwa ba?
Kuma
gaskiya a cikin mas'alar aqida shine abinda Alkur'ani ya faxa.
Kuma
matsalar TATTALIN ARZIKI a Duniya itama ta gagari masu hikima, kuma gaskiya a
cikinta shine abinda Al-qur'ani mai karamci ya faxa akanta.
Wasu
masu hikima daga cikin waxanda ba Musulmai ba, sun amfana da shari'ar Musulunci
a cikin wasu mas'alolin.
Kuma
ba zai yiwu Mutane gaba xayansu su kasance Musulmai ba. Saidai kuma wajibi ne
akan Musulmai su yi riqo da Alkur'ani da sunnah, har idan sauran Mutane suka ga
abin koyi mai kyau, daga kowane Musulmi, sai su amfana da su, koda kuwa cikin al'amuransu
na Duniya ne.
Kuma
Alqur'ani mai girma shine garkuwa ga Al'umma, da qarfinta, da dalilin
wanzuwarta da buwayarta, Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai
ne wannan Alkur'anin yana shiryarwa ga hanyar da tafi miqewa, kuma yana yin
albishir ga Muminai waxanda suke aikata ayyuka kwarai, cewa: Lallai suna da
lada mai girma" [Isra'i:9].
Allah
ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Mai qagar halitta, kuma ya mayar da ita (bayan mutuwa)Mai
aikata abinda yake nufi, Mulki na Ubangijina ne, kuma godiya tasa ce, yana
hukunta abinda yake so.
Ina
yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan falalarSa, kuma muna roqonsa
qari.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin
tarayya; Majivinci abin godiya.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai
shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.
Ya Allah
ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa shiryaryayyu.
Bayan
haka
Ku ji
tsoron Allah a cikin kowane hali; domin ku rabauta da samun kykkyawar aqiba a
cikin al'amurranku gaba xaya, a Duniya da Lahira.
Ya
ku Bayin Allah
Lallai
farillar azumi, a cikinta kuna da mafi girman lada, tare da abinda ke cikinta
na amfani a wannan rayuwar, ga wanda ya yi tunanin hakan, da tunani mai haske.
Saidai
kuma azumi ba zai bayar da fa'idarsa ba, kuma ma'abucinsa ba zai amfana da shi
ba, sai idan ya tsarkake shi da kyawawan ayyuka, kuma ya kiyaye shi daga
abubuwan da suke vata shi, da kuma abubuwan da suke tauye ladansa, na daga
zununbai da savo.
Don haka,
Idan ka yi azumi -Ya kai Musulmi- to jinka
ya yi azumi, da ganinka, da harshenka da sauran gavvai, daga dukkan haram;
domin ranka ta tsarkaka da aikata xa'oi, Allah Ta'alah ya ce: "Ya
waxanda suka yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi biyayya wa Manzo, kuma
kada ku vata ayyukanku" [Muhammadu: 33].
Kuma ya zo
cikin hadisi, cewa: "Idan ranar azumin xayanku ya kasance,
to kada ya yi kwarkwasa, kuma kada ya yi fasikci, Idan wani Mutum ya zage shi,
ko nemi faxa da shi, sai ya ce: Lallai ne, mai azumi ne".
Kuma Annabi
-SAW- ya ce: "Azumi garkuwa ne, matuqar bai keta ta ba", wato makuqar bai keta shi da zunubai kamar
giba da annamimanci ba.
Kuma ka yi
hisabi ga kanka -Ya kai Musulmi- a cikin
watan azumi, domin hisabin ya yi sauqi akanka a qiyama,
Kuma ka
tambayi kanka, shin ka tsayar da sallah kamar yadda umurce ka?
Shin ka
bada zakkarka tare da azumi?
Shin ka
tuba zuwa ga Allah daga zunubai?
Shin ka
tuba daga cin dukiyar haram, kamar riba, da saye-da-sayarwa na haram?
Shin ka
sadar da zumuncinka?
Shin ka yi
biyayya ga iyaye biyu?
Shin ka yi
umurni da kyakkyawa, kuma ka yi hani daga mummuna?
Shin ka yi
qoqari wajen riqo da shiriyar Annabi, domin ka kasance tare da shiryayyu?
Allah
Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani ku ji
tsoron Allah, kuma ku faxi magana madaidaiciya * Zai gyara muku ayyukanku, kuma
ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da Manzonsa, to
haqiqa ya rabauta da babban rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].
Ya ku
Bayin Allah!
"Lallai
ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi
imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment