HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
IDUL FIXR, 1/Shawwal/1440H
daidai da /Yuniyo/2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TABBATAR DA XABI'U
(تمكين للقيم)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TABBATAR DA
XABI'U, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR KABIRAN, WALHAMDU LILLAHI
KASIRAN, WA SUBHANAL LAHI BUKRATAN WA ASILAN
Godiya ta
tabbata ga Allah wanda ya saukar da mu ga bazarar falalarSa mai tarin yabanya, kuma
ya ajiye mu a tsaunin karamcinSa mai faxi, kuma ya karrama mu da samun rayuwa
mai yalwa mai ni'ima mai taushi, kuma ya sanya zuwan idi abu mai riba ga Bawa
mai yawan tuba, mai mayar da al'amari gare shi, mai komawa gare shi,
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yake bashi da abokin
tarayya, zuwa gare shi nake da'awa, kuma a gare shi na wakkala,
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ma'abucin
usuli a dangantaka da nasaba, da babban matsayi
Ya Allah
ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa salatin da zamu samu lada mai
gwavi da ita, da mafi girman rabo.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku
ji tsoron Allah, lallai jiya abin misali ne, yau kuma lokacin aiki, gobe kuma
buri ne, "Kuma abinda kuka gabatar domin kanku na alheri,
za ku same shi a wurin Allah, yana mafifici (daga wanda kuka ajiye), kuma yana
mafi girma ga sakamako" [Muzammil: 20].
Ya ku Musulmai
Haqiqa
idi mai walwala ya sauka a cikinku, wanda haskensa ya walqa a samanku, ga nan
idin alhalin ya yaryaxa qamshinsa mai tashi a cikinku, kuma ya watsa haskensa
mai qarfi, sai sanyin safiya ya cakuxa da haskensa, To lale da wannan idin, mai
qawa da furanni, mai xauke da jin daxi da farin ciki, kuma ya haskaka da
iskokin natsuwa da kwanciyar hankali. Idin da zamaninsa ya sauqa, matsayinsa da
mahallin aiwatar da shi suka xaukaka, kuma sunansa da takensa suka yi zaqi.
Jin
daxi ya tabbata a gare ku a ranar idinku mai walwalwa, Jin daxi ya qara tabbata
a gare ku a ranar idil fixr mai girma.
JIN
DAXI YA TABBATA A GARE KA A IDIN DA KAI NE IDINSA
KUMA
LALLAI KAI ZAKA QARA MASA KYAU DA HASKE
CIKIN
XA'A KA YI AZUMI, KUMA KA KWANA TSAWON WATA GUDA KANA AZUMI
KUMA
DA SUNNAR ALLAH ABAR YARDA ZAKA YI BUXA BAKI
KA
NI'IMTU DA IDIL FIXR, A MATSAYIN IDI, LALLAI SHI
YINI
NE MAI HASKE A CIKIN ZAMANI, KUMA SHAHARRE
YA
MAI AZUMIN DA YA BAR CIN ABINCI, YANA MAI KAMEWA** WANDA YA YI YININSA YANA
ABOTAR YUNWA DA WAHALA
ALBISHIRINKA,
DA SAMUN FARIN CIKI (IDI) A QIYAMA, DA ** KUMA RAHAMAR DA AKA KEWAYE TA DA
KYAUTA, DA KAYAN GARA
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI
Madalla
abin farin cikinku, a lokacin da kuka kammala qidayan watanku (na azumi), kuma
kuka fitar da zakkar fid-da-kanku, kuma kuka xaga sauti da girmama Ubangijinku,
saboda faxin Allahu akbar shine lafazin da ya kai maqura wajen girmama Allah.
Kuma
duk wanda ya san UbangijinSa sai zuciyarsa ta cika da kwarjininsa da girmama
shi; sai ku girmama Mahaliccinku yadda ya kamata a girmama shi, kuma ku ji
tsoron kamunsa da azabarsa, kuma kada ku gafala daga godiyar falalarSa da
ni'imarSa, kuma ku riqa bin umurninSa da hanuwa da haninSa. Kuma kada ku yi karan-tsaye
ga umurninsa da hani, saboda sakacin 'yan sakaci, ko wuce-iyakar mai guluwwi,
ko dalilin wani sababin da zai raunata gaskiyar binsa. Kuma kada ku ji tsoron wani sai shi, kuma
kada ku yi kwaxayi sai daga wurinsa, domin babu mai kusantar da bayi gare shi
face shi, kuma ba a samun yardarSa face ta hanyarSa, kuma ku girmama shi, kuna
masu tsarkake shi daga abinda Masu bautar gumaka da mushirkai suke faxa kuma
suke aikatawa.
Kuma
kada ku sanya wa takardun ayyukanku da bidi'oi da qirqirarrun lamura.
Kuma
kada ku lalata addininku ta hanyar tafiya ga masu sihiri da bokaye da maqaryata
(dujjal) da 'yan rufa-ido da canfi,
waxanda suke riya sanin abinda yake fake na gaibu, da yaye abinda aka
voye.
Kuma
kada ku yi miki ga imaninku, da rataya igiyoyi da daga, da layoyi da guru, da
sauran ababen ratayawa, waxanda basu janyo dukiya, kuma basu tunkuxe fitina,
basu bada kariya ga iyalai.
Kuma
kada ku ruguza ayyukanku da bautar qasusuwa rududdugaggu, kuma kada ku yi
xawafin qabari, kada ku yi yanka a wurin qabari, kada ku nemi agaji daga
qabari, kamar yadda masu bautar qabari da gumaka suke yi. Kuma duk wanda ya
kiyaye aqidarsa da tauhidin UbangijinSa, to lallai ya ji girman ma'anar
kabbara, kuma ya tsayu da wajibin girmamawa ga Ubangiji Mai girma.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Idan
ranar yinin idi ta fudo, sai fiskokin Mutane suyi ta farin ciki, suna haske
suna bushara, suna annashuwa da annuri.
Kuma
farin cikin idi sunna ne na Musulmai, kuma alama ce daga cikin alamomin addini.
A
lokacin idi an shar'anta bayyanar da jin daxi da farin ciki, ba wai bayyana
baqin ciki da kururuwa da kuka ba, ko tuna cutuka da fama raunuka ba.
BA
BAQIN CIKI DA VACIN RAI WANDA ZAI
RINJAYI FARIN CIKIN DA AKA SHAR'ANTA ** A RANAR IDI, DOMIN RANAR IDI NA
FARIN CIKI NE
Sai
ku bayyanar da farin ciki, ku yaxa su,
kuma ku yaxa sa'ida ku game Mutane da ita, kuma ku wargaza gajimaren baqin ciki, kuma ku futar da jiki,
ku shigar da farin ciki ga iyalai da makusanta da makwabta, ku warwatsa kuxi
watsawa, ku shumfuxa hannayenku biyu da kyauta, kuma ku yalwata wa iyalai, ku sanya
qananan yara sa'ida, ku yi kyautar murmushi da shumfuxa fiska.
An
ruwaito daga Umar xan Alkhaxxab -رضي الله
عنه- ya ce: An
tambayi Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- "Wane aiki yafi
falala? Sai ya ce: Shigar da farin ciki ga Mumini; ka qosar da yunwarsa, ko ka
tufatar da tsiraicinsa, ko ka biya masa buqatarsa",
Xabaraniy ya ruwaito shi a cikin littafin Al'ausax.
Farin
ciki ya tabbata ga dukkan mai baiwa mai yaxa alheri, da dukkan mai tausayi mai
jin-qai, wanda yake tallafawa faqirai da miskinai, kuma yake shigar da farin
ciki a zukatan marayu da marasa, da waxanda musiba ta ritsa da su, kuma yake
tausayin zawarawa da waxanda mazansu suka mutu, da waxanda dukiyarsu ta yanke,
kuma yake tausayin masu rauni da waxanda musiba ta shafa, kuma ya tallafa wa mutanen
da aka raunata da 'yan gudun hijira.
Kuma
shigar da farin ciki ga iyaye biyu, da yin biyayya a gare su, da tunkuxe dukkan
abinda zai baqanta musu, shine yafi zama lazimi kuma wajibi.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Idi
ya sake komowa domin tafkunan soyayya da gulabensu su dawo, kuma magudanan
qauna da qoramunsu su cigaba da gudana, sai a tsarkake zukata daga dauxar kyashi
da qiyayya, kuma su wanke zukatan daga cutukan qiyayya da gaba.
Idin
ya sake komowa domin farin cikinsa ya tsamar da kowane mai baqin ciki, kuma
farin cikinsa ya xebe kewar kowane mai matsala, walwalarsa ta faranta wa kowane
mai baqin ciki da vacin rai.
Idin
yana zuwa ne domin ya wanke wasu fiskoki wanda baqin ciki ya zanu a jikin
fatotinsu, har zuka zama sun xebe tsammanin nasara, tare da cewa, alhini baya
dawo da abinda aka rasa, kamar yadda nuna an yi asara baya dawo da matacce.
BAN KASANCE ZAN RISKI
ABINDA NA RASA BA, ** DA XANKWARA RAI, KO DA YIN DA-NASANI, KO DA FAXIN: DA DAI
NI...
Sai ku yi amfani da
wannan idin ta mafi kyan amfani, domin bayar da magani ga zukatan da suke
karye, da bada magani ga rayukan da suke cikin hasara, kuma ku ziyarci marasa
lafiya da waxanda matsaloli suka zaunar da su, kuma ku dawo da murmushi ga
wanda ya rasata, haka farin ciki, shima ga wanda ya salwantar da shi.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Yin gaisuwar idi tana
qara soyayya, kuma tana gwavava qauna. Shi kuma musabahar haxa hannaye tana
buxe gadar sanayya da haxin kai, sai ku sanya haxa hannaye ya zama mabuxi ga
tsarkin zukata, kuma ku yi rangwame ga wanda ya yi laifi, ya yi kuskure, kuma
ku yi afuwa ga wanda ya yi zalunci ya munana, kuma ku yi kyautar raba qauna, ku
furta kalmar soyayya, kuma a cikin idinku ku yaryaxa qamshin afuwa mai daxi, ku
shelanta afuwa, har qamshinsa ya yi ta tashi, cikin wani yanayi mai daxi,
Kuma "Baya halatta,
Musulmi ya qaurace wa xan'uwansa fiye da kwanaki uku, sai su haxu; wannan ya
kau da kai, wannan ya kau da kai, kuma mafi alherin biyun shine wanda yake fara
yin sallama".
Kuma
wane idi ne, ga zukatan da suka qaurace wa juna, kuma ina walwala ga rayukan da
suke faxa, kuma ina farin ciki yake, ga qarfi biyu masu husuma.
Idi,
wani fage ne na aminci da xinke varaka. Idi ne da ake samun haxin kai a
cikinsa, kuma ake haxe kalma a cikinsa, ake toshe varaka a cikinsa, ake kunyata
Shexan a cikinsa, a cikin wata al'umma mai qaunar juna, da tsarkin hali mai
jagora, a cikin wani taron da yake maimaituwa yake sake komowa.
Kuma
babu wani idi ko farin ciki ga zukatan da girman kai, da ruxi, da zalunci suke
jagorantsarsu.
Haka
babu farin ciki (idi) ga jikin da suka yi wanka irin na idi, saidai basu wanku
daga dauxar gaba da qiyayya da adawowi. Haka babu shi ga suka sanya tufafin
idi, a jikin dauxar qiyayya.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Iyali
sune suke bayar da tarbiyya ga zuciya, kuma suke magance raunuka, Shi kuma idi
lokaci ne na haxuwan iyalai da iyayensu da kakanni, sai vangarorin iyalai na
nesa su tattaru, sai 'ya'ya da jikoki a cikinsa su haxu, sai samarinsu su haxu
da dattawansu; A nan, sai ku tsayu da wajibin sadar da zumunci da kyautatawa,
kuma ku yi dashe a cikin zukatan 'ya'yanku maza da mata, aqidar so ko jivintar
addini da aqida da tauhidi. Da kuma aqidar jivintar wannan qasa mai girma, da
kulawa da amincinta da zaman lafiyarta da haxin kanta, da kulawa da 'yan qasan,
da wajabcin lazimta jama'a, da watsi da rarrabuwar kai da savani. Kuma ku xora
'ya'yanku akan manhajin tsakaitawa, ku kare su daga faxawa hanyoyin ketare
iyaka da guluwwi da irhabi. Kuma ku riqa qarfafarsu domin su kasance masu
taimakon jami'an tsaro, wajen kiyaye amincin qasar da tsare-tsarenta. Kuma ku
kwashe su zuwa ga wuraren samun ilimi, da sani, da cin nasara da gogewa. Kuma
ku tarbiyantar da su akan kyawawan halaye da xabi'u, da qoqarin samun tsarkin
hali masu falala, da kamewa a cikin zance, da abinci, da cakuxa. Kuma ku
tarbiyantar da su akan haquri da adalci da tawali'u, da sadar da zumunci, da
girmama qarami da babba, da mutunta ma'abuta falala da ilimi
FALALA ITACE, LADABI YA KASANCE
A CIKIN IYAYE DA KAKANNI ** TABBATACCE, HAKKA KUMA YA DASU A CIKIN 'YA'YA DA
JIKA
SUN QAWATA TSHOHONSU, DA KYAWUN
NA YANZUNSU ** DA KUMA KYAWAWAN
HALAYE, DA MANAGARTAN SIFOFI
MADALLA DA MUTANEN DA KAI RESHEN
ASALIMSU NE? ** KUMA MADALLA DA KAI, TUNDA KAI DAGA TUSHENSU KA ZAMA RESHE
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Shari'a
ta yi umurnin a riqa cika alqawalin da Mutane suke qullawa a tsakaninsu na saye
da sayarwa, da haya, da auratayya da shika, da muzara'a da sulhu da mallakawa,
da wanin waxannan daga cikin abinda Mutane suke qullawa, sai a samu jayayya da
inkari da makirci a tsakanin masu qullawan, ko a samu ha'inci da gisshu da
bugun hanci, da yin qarya a tsakanin wakilai da masu haya da ma'aikata da wanda
ake mu su aikin. Kuma wasu ma'aikatan su kan qulla ciniki kan wasu sana'oin da
basu iya su ba, da ayyukan da basu kware a cikinsu, koma basun iya su ba.
Saboda kowa yana son tara kuxi ne, wa lau ta hanyar haram, kuma waxannan
burinsu shine su yi makirci ga 'yan'uwansu, sai dai wanda Allah ya kare shi da
taqawa. Kuma Allah zai yi hukunci a tsakanin Bayi a ranar hukunci da rarrabewa.
An ruwaito daga A'isha -رضي الله عنها- lallai wani Mutum ya zauna a gaban Annabi -صلى الله
عليه وسلم-sai ya ce:
Ya
Manzon Allah! Lallai ina da Bayi guda biyu, suna sharara mini qarya, kuma suna
ha'intata, kuma suna sava umurnina, Ni kuma zaginsu, ina dukansu, To yaya
lamarina yake dangane da su? Ya ce: "Za a qididdige
abinda suka yi na ha'intarka da sava maka da qaryar da suka yi maka, da uqubar
da ka musu; idan har uqubar da ka musu ya zama daidai da zunubinsu to shi
kenan; baka da zunubi kuma baka da wani abu akansu. Idan kuma uqubar da ka musu
bata kai zunubansu ba to wannan falalarka ce. Idan kuma uqubar da ka musu ta
wuce gwargwadon zunubansu, to sai a kwato musu abinda ya xoru. Ya ce: Sai Mutumin
ya koma gefe yana kuka yana kururuwa, Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: Shin baka iya karatun littafin
Allah ba ne, faxinsa: (Kuma za mu sanya ma'aunan adalci, ga ranar Qiyama,
saboda haka, ba a zaluntar rai da komai, kuma da zai kasance daidai da kwaya
daga komayya za mu zo da shi. Kuma mun isa mu zamo masu hisabi" [Anbiya'i:
47] Sai Mutumin ya ce: Wallahi! Ya rasulul lahi! Babu wani abu da
naga yafi alheri ga ni da su fiye da na rabu da su, Ina shaida maka cewa, allai
su 'yantattu ne gaba xayansu. Ahmad ya ruwaito shi da Tirmiziy.
Sai ku
ji tsoron Allah -Ya ku Musulmai- kuma ku yi adalci da gaskiya a cikin mu'amala.
Kuma duk wanda ya kasance wajen bayar da abinda yake wuyansa, kamar yadda yake
kiyaye abinda nasa ne, to lallai ya yi adalci cikin hukunci, kuma ya yi daidai
a hukunci.
Musulunci
yana umurni da cika alqawulan da aka qulla, da yin gaskiya cikin mu'amala. Kuma
yana hani akan cinye amana da ha'inci da zalunci.
Kuma
duk wanda ya shiga daga cikinmu; -Musulmai- yqasar waxanda ba Musulmai ba, da
alqawali da amana daga wurinsu -wato, bizar izinin shiga da suka bashi, domin
ya iya shiga qasarsu, to haramun ne ya ha'ince su, ko ya musu sata, ko ya yi
ta'addanci ga amincinsu da rayukansu da mutuncinsu da abubuwan da suka mallaka.
Kuma duk wanda ya sace musu wani abu, to wajibi ne ya mayar da shi ga ma'abutansa,
saboda dukiya ce, tsararriya.
ALLAHU AKBAR, ALLAHU
AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Kwanaki
suna juyawa, mutuwa kuma tana halartowa, Mutane kuma ko dai matafiyi ko wanda
ake bankwana da shi, da wanda ake wawashewa ake masa gaggawa, ko wanda ake masa
jinkiri. Kuma dukkan halittu zasu tafi ga qarewa, kuma dukkan mulki to zai
qare, kuma babu abinda zai dawwama sai mulkin Allah, tsarki ya tabbata a gare
shi; Mi mulki Mai rinjaye, wanda ya kaxaitu da buwaya da wanzuwa, duk kuma
abinda ba shi ba, to zai qare;
Domin DUKKANMU
MUTANE NE ** QADDARA TANA NAXE MU
KUMA MU
MUNA CIKIN TAFIYA NE **MUNA TAFIYA ZUWA QABARI
MUTUWA
ZATA NAXE MU ** SANNAN ZA A MANA MATATTARA
Kuma
don me kake jinkirta tuba, alhali baka da wani uzuri, kuma har yaushe ba za ka
dena laifi ka hanu ba
HAR
YAUSHE JINKA BAYA KARKATA GA MAI TUNATARWA ** KUMA KWARYAR ZUCIYARKA BATA YIN
TAUSHI GA MAI NUSARWA
INA
GANIN KANA RUXUWA DA RAYUWA ** KUMA BAKA YIN GAGGAWAR KOMAWA GA ALLAH
KUMA
KANA KWAXAYIN WANZUWA, AMMA TA YAYA ZAKA TABBATA? ** ALHALIN DUNIYA BA WURIN
ZAMA BA CE, GA MAZAUNINTA
Sai ku
nisanci aikata savo, da tasowa a cikinsa, da rungumarsa, da sakaci wajen keta
ladduba, da ta'addanci ga iyakokin shari'a da addini.
Kuma ku
nisanci aikata haramun, ku kiyayi kusantarsu da aikata su, kuma kada ku cakuxa
da sabubbansu da abinda suke kai mutane ga aikata su, kuna masu godiya ga
Allah, akan kyautatawansa masu gamewa, da baiwanmasu girma.
Kuma ku
kyautata makwabtakar ni'imomi, sai ku kiyaye ni'imomin da suke hannu, kuma ku
janyo ni'imomin da babu su, kuma sai kyautar Allah ta tabbata akanku da
karamcinsa da kyautarsa. Saboda ni'ima bata juyawa bayan ta fiskanto, kuma ba a
xauke baiwa bayan ta sauka, kuma ba a cire wata karama bayan an bayar da ita,
sai saboda wasu kyautan da ba ayi godiya akansu ba, ko saboda kura-kuran da
suka bayyana a cikin Mutane suka shahara. Kuma ni'imomi idan aka yi godiya
akansu sai su tabbatu, idan kuma aka kafirce aka butulce musu sai su gudu.
Kuma ku
kusanci qofar tuba da mayar da al'amari ga Allah, kuma ku yanke igiyar (tuba)
sai gaba, ,,, sai gaba, ,,, kuma ku goge abinda ya gabata na savo, da abinda
zai riske shi na kyautatawa. Kuma ku kiyaye salloli biyar na farilla, a lokacin
da ake kiransu, kuma kada ku qi halartar jam'i sai idan da uzuri. Kuma ku bayar
da zakkar dukiyoyinku. Ku yi gaggawan hajji matuqar kuna da iko. Kuma ku sada
zumuncin wanda ya yanke muku. Ku baiwa Mutumin da ya hana muku. Ku yi afuwa ga
wanda ya zalunce ku. Kuma mai sada zumunci bashi ne mai ramuko ba, a'a cikakken
mai sada zumunci shine idan aka yanke zumuncinsa sai ya sadar da ita. Kuma kada
ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da varna. Kuma kada ku yi mu'amala da kasuwancin
riba mai hasara, da qarin da yake cikinsa na zalunci, da ninke-ninkensa mai
muni. Kuma ku nisanci musa haqqoqi, da yin wasa da farashin kayan sayarwa, da
gisshu, da najashu, da zaftare sikeli da ma'aunai. Kuma ku nisanci dukiyar
marayu, da awaqafai da wasiyoyi; kada ku cinye su da zalunci da ta'addanci.
Kuma ku kyautata wa matanku da 'ya'yanku maza da mata, kuma ku tsayu wajen
ciyarwa ta shari'a ta dole, kuma ku mu'amalance su da tausasawa da tausasawa da
soyayya da jin-qai da rahama.
Kuma ku
kiyaye harsunanku, kuma ku kiyaye farjojinku, kuma ku tsarkake zukatanku daga
qyashi da qulli da hassada da qiyayya da gaba, kuma ahir xinku kan zama a
majalisar fasiqci da fajirci.
Kuma ku
nisanci husumomi da faxace-faxace, kuma ku riqa karvar uzuri, kuna yafiyar
tuntuve. Kuma kada ku yanke zumunci, kada ku juya baya, kada ku yi qiyayya,
kada ku yi hassadar juna, ku kasance -Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna.
YA KU
MUSULMAI,,,
Wannan
yini ne na yafiya, da gaisuwa, da sulhu, sai ku yi rahama ga juna, ku haxa
kanku, ku yi rangwame, ku gaggaisa, ku yi sulhu, domin farin cikinku xaya ya
ninninku, idinku ya yawaita.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Ina faxan
abinda kuke ji, kuma ina gafarar Allah ga ni da ku da sauran Musulmai daga
dukkan zunubai da kura-kurai, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance Mai
yawan gafara Mai jin-qai.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU
Godiya ta
tabbata ga akan ni'imominSa waxanda suka shuxe suka gabata, Ina gode masa godiyar da ta kai maqura, tafi
cika da kamala, da gamewa,
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yake bashi da abokin
tarayya,
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa zavavve
daga cikin halittunsa da ya qaga,
Ya Allah
ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa salati mai ninkuwa mai
dawwama, har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku
ji tsoron Allah wanda babu abinda yake vuya a gare shi na manufofi da niyyoyi,
kuma babu wani abu da aka voye a cikin zukata da yake vuya masa, saboda
voyayyun abubuwa na sirri a wurinsa a bayyane suke, kuma sirri a wurinsa a fili
yake, kuma yana tare da ku a duk inda kuke, kuma Allah dangane da abinda kuke
aikatawa Mai gani ne.
Ya ku Musulmai
Zaman lafiya yana da farashinsa,
Qasa kuma tana da rundunoninta, Hukunci kuma yana da mazajensa.
Kalmar godiya da yabo da jinjina
muke gabatarwa ga jami'an tsaronmu masu zaman dako, a wuraren xaukaka, waxanda
basu xauki rayukansu a bakin komai ba, kuma suka xauki makamai, suka fiskanci
mutuwa domin su kare alfarma da tsarkaka wurare.
Ya ku zaratan mazaje, dakarun
sojoji, Ya waxanda kuka shayar da turvayar wannan qasar da jinanenku, kuma kuka
bayar da rayukanku domin ku kare ta, Ya waxanda kuka tsaya, kuka toshe
ta'addanci mai muni, Ya masu bada kariya ga harami guda biyu, Ya tanadin gida,
kuma buwaya ga qasa, kuma garkuwansa, kuma sulken kare shi: Babu kalmar da zata
iya biyanku, kuma babu yabon da zai saka muku, kuma babu godiyar da zata saka
muku. Ku ne idin; wato masu tsaronsa kuma garkuwansa, kuma sulken kare shi.
Masu yin bauta sun yi bauta, masu
ruku'i sun yi ruku'i, masu azumi sun yi azumi, a cikin zaman lafiya da aminci,
wanda jihadinku ya samar da shi, kuma fansar da kuka bayar ya kiyaye shi.
Idinku mai albarka ne, (wannan)
kalma ce da zata kewaya kafafen aikinku da benayenku. Kuma kowace shekara ku
kasance cikin alheri, jihadinku abin taimako, maqiyanku qasqantattu, qasarku
abar kiyayewa, nasararku ta zo a kusa.
Godiya a gare ku, Ya masu gadin qasa, masu kiyaye
aqida da addini, godiyar da bata kai ga matsayinku ba!
KA BANI ARON HARSHE -YA KAI WAQA-
DOMIN NAYI GODIYA ** IDAN KA GAGARI GODIYA, TO BAKA KASANCE WAQA BA
ZAN RIQA AMBATONKU IRIN AMBATON
MASOYI GA MASOYANSA ** KUMA ZAN GODE MUKU IRIN GODIYA MAI FARI GA RUWAN SAMA
Addu'armu ta gaskiya a wannan
yini na idi, daga saman minbarin Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- mai
daraja, itace: Allah ya rubuta muku nasara cikin gaggawa, kuma ya mayar da
maqiyanmu cikin tavewa, da hasara.
AMIN, AMIN, BA ZAN YARDA DA FAXIN
GUDA XAYA BA ** SAI NA KAI SU ZUWA GA AMIN DUBU BIYU
Kuma za mu ce ga dukkan maqiyinmu
ga amincin qasarmu da zaman lafiyarmu da bunqasarta:
SAMUN NASARA A QASARMU YA MAKA
NISA ** ABUN NEMANMU SHINE KA TAFI QASARKA KA YI WALKIYA A CAN DA TSAWA
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU TARON MATA,,
Lallai ne Allah ya xaukaka ku, ya
darajanta ku, kuma ya xaukaka matsayinku, ya kiyaye haqqoqinku, sai ku yi
godiyar ni'ima, ku riqa tuna wannan baiwar, ku runtse sashe na ganinku, ku
kiyaye farjojinku, kuna yin sadaka, kuma ku yawaita neman gafara, kuma kada ku
yawaita tsinuwa, kuma kada ku butulce wa abokin zama, kada ku yi tabarruji,
kada ku yi fita na tsiraici.
Kuma mace maxaukakiya kamammiya,
ba za ta yarda ta zama tushen tayar da sha'awa ko fitina ga idanu mafarauta, da
gani na ha'inci na banza, da rayukan qasqantattu, da maganansu na wulaqantattu,
yasassu.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
YA
KU MUSULMAI,,
Lallai baqonku ya qaura, Ramadhan
ya tafi, saidai kyawawan ayyuka basu qarewa; don haka kada ku rufe Alqur'ani,
kada ku hana sadakar biredi, kuma kada ku hana mabuqaci, kada ku yanke ayyukan
kyautatawa, kada ku qauracewa yin azumi, kada ku bar sallolin dare; domin
kyautatawa ya kan yi kyau idan kyautatawa ya biyo bayansa, kamar yadda munanawa
yake da matuqar muni idan ya zo a bayan kyautatawa.
Kuma wanda ya azumci Ramadhana,
sannan ya biyar da guda shidda a watan shawwal, to kamar ya yi azumin shekara
ne.
Kuma wanda bai fitar da zakkar
fidda-kai ba, to ya yi gaggawan fitar da ita.
Wanda ya zo ta wata hanya, to ya
koma ta wata hanyar ta daban, idan ya samu damar aikata hakan, yana mai koyi da
Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Albishirinku:
Ya
waxanda kuka yi sallolin dare, kuka yi azumi ... Albishirinku, Ya waxanda kuka
yi sadaka, kuka yi qoqari, haqiqa wahalar ta tafi, kuma gajiyar ta gushe, ladan
kuma ya tabbata da izinin Allah Ta'alah.
Allah
ya karvi azuminku da sallolinku, kuma ya maimaita muku waxannan ranaku (na
Ramadhana) masu albarka na shekaru dayawa, da zamani masu tsawo, alhalin muna
cikin lafiya da rayuwa mai daxi.
Ya
Allah ka karvi ayyukanmu, kuma ka tsarkake su, kuma ka
xaukaka darajarmu.
Ya
Allah ka bamu daga cikin gurace-gurace na qololuwansu,
alherori kuma qarshensu.
Ya
Allah ka karvi azuminmu da sallolinmu, da addu'oinmu ya Mafi
jin-qan masu jin qai.
Ya
Allah ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da
shirka da mushirkai, ka ruguza maqiya wannan addinin, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah ka dawwamar wa qasar harami biyu maxaukaka, amincinta
da wadacinta da buwayarta, da zaman lafiyanta, da sauran qasashen Musulmai.
Ya
Allah ka datar da shugabanmu majivincin lamuranmu; mai
hidimar harami biyu maxaukaka; Bawanka Salman xan Abdul'aziz zuwa ga abinda kake
so, ka yarda da shi, kuma ka riqi makyamkyamarsazuwa ga aikin xa'a da taqawa,
kuma ka gyara masa abokan shawarinsa, ka azurata shi da lafiya, kuma ka kiyaye
shi daga dukkan sharri da abin qi.
Ya
Allah ka datar da na'ibinsa da 'yan'uwamsa da 'ya'yansa
da ministotinsa da masu taimakonsa, zuwa ga abinda xaukakar Musulunci da
gyaruwan Musulmai yake cikinsa, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah ka taimaki addininka da su, ka xaukaka kalmarka da su,
kuma ka sanya mu da su mu zama shiryayyu masu shiryarwa, da rahamarka ya mafi jin
qan masu jin qai.
Ya
Allah ka datar da xaukacin shugabannin Musulmai, su yi
hukunci da shari'arka, su bi sunnar annabinka Muhammadu -صلى الله
عليه وسلم-.
Ya
Allah ka yaye baqin cikin masu baqin ciki,kuma ka
kwaranye musibar masu musiba, kuma ka biya bashin masu bashi, kuma ka warkar da
marasa lafiyanmu da marasa lafiyan Musulmai, kuma ka yi rahama ga mamatanmu da
mamatan Musulmai.
Ka
gafarta wa iyayenmu maza da mata, da matanmu da zuriyyarmu da 'yan'uwanmu da
makusantanmu da malumanmu, da jagoran lamuranmu, Ya mafi jin qan masu jin-qai.
SUBHANA
RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUNA, WA SALAMUN ALAL MURSALINA WAL HAMDU
LILLAHI RABBIL ALAMINA.
ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD.
No comments:
Post a Comment