HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27/zulhijjah/1439H
daidai da 7/Satumba/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
NI'IMAR NAU'INTA IBADA
نعمة تنوع العبادات
Shehin Malami wato:
Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
NI'IMAR
NAU'INTA IBADA,
Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Ni'imomin Allah akan
bayinSa suna da yawa, Idan Bawa ya ce zai kidanya su, sai kididdige sun ya
gagare shi, sai kuma ya kasa sanin iyakansu.
Kuma Musulunci shine mafi
girman ni'imomin Allah; ana haifar abin haifuwa a kan fidira ko halittar
Musulunci, sai kuma ya taso cikin al'ummar da ake bautar Allah a cikinta, ake
daga sauti da kiran sallah, ake karatun Alkur'ani, don haka muna yin godiya ga
Allah wanda ya shiryar da mu zuwa ga wannan, bamu kasance zamu shiryatu ba, ba
don Allah ya shiryar da mu ba.
Kuma yana
daga manyan ababen da suke biye da ni'imar Musulunci, kuma daga cikin ressansa:
NI'IMAR NAU'INTA
IBADA, DA YAWAITARSU, kuma wannan ni'ima ce da ta kunshi hikimomin Ubangiji.
Hanya zuwa ga Allah guda
daya ce, kuma hanyar ta game dukkan abinda Allah yake so, su kuma abubuwan da
suke yardar da shi suna dayawa, kuma nau'i-nau'i ne, gwargwadon lokatai da
wurare da Mutane da halaye, saboda banbancin shirye-shiryen bayi da yadda za su
iya karbar abu, kuma domin a sassauta musu a saukaka musu, da abinda zai dace
da ikonsu a halin nashadi ko tilasci.
Cikin nau'antuwan farillai
da wajibai na ibadodi akwai jarabawa ga Mumini domin ya iya rinjayar son
zuciyarsa, da sanin gaskiyarsa wajen aiki domin neman yardar Allah, saboda Bawa
ya taso daga wata ibada zuwa wata, gwargwadon lokacin kowanne daga cikinsu,
dalili ne da yake nuna cewa shi Bawa ne ga Allah na hakika, wanda manufarsa –a
koyaushe- ita ce bibiyar yardar UbangijinSa Madaukaki.
IBADODI SUNA ZAMA
NAU'I-NAU'I LURA DA MANUFOFINSU: Sai kowace ibada daga cikinsu ta tabbatar da wata
hikima ta Ubangiji, da wata manufa ta tarbiya, saboda a lamarin SALLAH Allah
Ta'alah yana cewa: "Lallai ne sallah tana yin hani daga alfasha da abin kyama"
[Ankabut: 45].
A
dangane da ZAKKAH kuma, Allah Ta'alah ya ce: "Ka karbi sadaka daga
dukiyoyinsu, kana mai tsarkake su, kana mai tabbatar da kirkinsu da ita"
[Taubah: 103].
A
sha'anin AZUMI kuma Allah Ta'alah ya ce: "Tsammaninku za ku samu takawa",
[Bakara: 183].
A dangane da lamarin HAJJI
kuma sai Allah Ta'alah ya ce: "Domin su halarci abubuwan amfani a gare su, kuma
su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu"
[Hajj: 28].
IBADODI SUNA ZAMA NAU'I-NAU'I LURA DA YADDA
KO HANYOYIN DA AKE GUDANAR DA SU: Saboda haka, duk wanda saboda jinya ko bulaguro ko
rauni ya gaza aiwatar da wata ibada, to sai ya samu ladansa cikin rangwame, ko
wata ibadar ta daban, wannan kuma domin kulawa ne da yanayin Bayi, da kuma
dauke kunci a gare su, da saukaka musu, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma Allah yana nufin sauki
gare ku, baya nufin tsanani a gare ku" [Bakara: 185].
Musulunci ya bada kulawa
ga halin fakiran da suka yi zaton cewa Mawadata sun shige su, saboda abinda
suke da shi na rarar dukiyarsu da suke sadaka da ita, saboda Fakirai sun ce: "Ma'abuta dukiya sun tafi da
lada! Suna yin salla kamar yadda mu ke yi, suna yin azumi kamar yadda mu ke yi,
kuma suna sadaka da abinda ya zama rara daga dukiyoyinsu, Sai Manzon Allah
–sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Shin Allah bai sanya muku abinda za ku
yi sadaka da shi ba ne? Lallai kowane tasbihi sadaka ne, kowane kabbara sadaka
ne, kowane hamdala sadaka ne, kowane hailala sadaka ne, kuma umurni da
kyakkyawa sadaka ne, hani ga mummuna sadaka ne, kuma cikin saduwar dayanku
akwai lada", Muslim ya ruwaito shi.
Musulunci ya dasa mafarin
sassautawa ne, domin bada kulawa ga mabanbantan halayen Bayi, saboda wata Mata
daga kabilar Khas'am ta zo, sai ta ce: "Ya Ma'aikin Allah, lallai
farlantawar hajji da Allah ya yi ga bayinsa ya riski Mahaifina yana tsofo mai
yawan shekaru, ba zai iya zama akan abin hawa ba, Shin zan iya yin hajji a gare
shi? Sai ya ce: E,", Bukhariy ya ruwaito shi.
Cikin wannan kuma, akwai halaccin wani ya
na'ibci wani cikin ibadar hajji.
Kuma yana daga cikin
hadisai masu girma wadanda suke nuni kan fadi da yalwar rahamar Allah da
falalarSa, da yadda yake kulawa da halin da Bayinsa suke ciki, akwai fadinsa
(SAW): "Idan Bawa ya yi rashin lafiya, ko ya yi tafiya, sai a rubuta masa
ladan abinda ya saba aikatawa a lokacin yana mai lafiya wanda ba matafiyi ba".
Kuma Musulunci ya bada
kulawa ga bayin Allah Mata, a inda suke da gazawa kan tsayuwa da wasu daga
cikin ayyukan Maza, sai ya rataya lada mai yawa ga ayyukan Matan, domin girmama
matsayinsu, da nuna kimar ayyukansu, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa
sallama- yana cewa: "Idan Mace ta yi sallolinta biyar, kuma ta yi
azumin watanta, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, sai a ce mata: Ki
shiga Aljannah , ta kowace kofar Aljannah kika so".
IBADODI SUNA ZAMA NAU'I-NAU'I LURA DA
FALALOLINSU: Sai
kowace ibada ta kara samar da wani shafi na alkhairi a cikin littafin ayyukan
Musulmi, da wani tulin sakamako da lada mai girma, saboda a cikinsu akwai
ibadun da suke kaiwa ga/ shafe zunubai da kura-kurai, An ruwaito daga Usman
–Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-
ya ce: "Babu wani mutum Musulmi da sallar farilla zata halarce shi, sai ya
kyautata alwalarta, da khushu'inta, da ruku'inta, face ta zama kankarar abinda
ya gabace ta na zunubai, matukar bai aikata kaba'ira ba, wannan kuma tsawon rayuwa
ne gaba dayansa".
Daga cikinsu kuma akwai/
wanda take kasancewa sababin shiga Aljannah, saboda Annabi –sallal Lahu alaihi
wa sallama- ya ce: "Shi kuma hajji gangariya mabruri bashi da wani
sakamako face Aljannah".
Daga cikinsu kuma akwai/
wanda take tseratar da bawa Musulmi daga azabar Wuta: saboda Annabi –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ba zai shiga wuta ba, Mutumin da ya yi kuka domin
tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, har sai tatsattsen nono ya koma cikin hantsa.
Kuma kurar da aka same ta a yaki fisabililLahi ba za ta taba haduwa da hayakin
Jahannama ba".
Kuma daga cikin nau'ukan
falalan ayyuka akwai/ wanda Mutum Musulmi yake samun daukaka da shi zuwa ga
matsayi mai girma, wanda ba a cimma sa, Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-
yana cewa: "Lallai mafi soyuwanku a wurina, wanda kuma ya fi ku kusancin wurin
zama tare da ni a ranar Kiyama, shine wanda ya fi ku kyawun halaye".
Kuma BANBANCIN LOKUTAN
IBADA DA BANBANCIN FALALOLINSU yana ingiza Musulmi kan ya cike rayuwarsa
gaba dayanta wajen shigi da fici tsakanin gonakin ibada da lambunansu, saboda
lallai shi Allah SWT idan ya so Bawa sai ya aikatar da shi a cikin lokatai masu
falala, da ayyuka masu fifikon daraja, idan kuma ya ki wani Bawa, sai ya
aikatar da shi da munanan ayyuka, a lokuta na musamman masu falala.
Kuma babu wani lokacin
bauta na musamman mai falala, face Allah a cikinsa yana da wani aiki daga cikin
ayyukan biyayya a gare shi, wanda ake kusantarsa da shi. kuma a wannan lokacin
Allah yana da wata busa daga rahamarsa wanda ya ke shafan wanda ya nufa da ita,
da falalarSa da jinkanSa.
CIKIN NAU'INTUWAR IBADA akwai
tunkude dabi'ar yin rauni da kosawa, kuma hakan ya kan baiwa rai nashadi, kuma
yana sanya Musulmi ya rika jin dadi da zakin ibadar.
Akwai IBADODI NA
DAIDAIKU, WADANDA SUKE DA FALALA, KUMA A CIKINSU AKWAI HIKIMOMI, domin suna
karfafa alakar Bawa da Allah, kuma suna tarbiyyantar da Mutum akan tsarkake
niyya (ikhlasi) da nisantar riya, kuma suna kara tsaftace ruhi, suna kawo debe
kewan Bawa da Allah Ubangijinsa, Alhasan Albasariy yana cewa a lokacin da aka
tambaye shi: "Me yasa masu bauta a cikin
dare, haske yake kasancewa a fiskokinsu? Sai ya ce: saboda suna kebewa da
Ubangijinsu, sai ya tufatar da su daga haskensa S W T".
FISKANTAR ALLAH DA ADDU'A
CIKIN KAN-KAN-DA KAI DA TSORO, YANA DAGA CIKIN MAFI KYAN IBADODI NA DAIDAIKU, Allah
Ta'alah yana cewa: "Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin ranka da kankan-da
kai, da tsoro", [A'araf: 205].
YIN AZUMI DON ALLAH IBADA
NE NA DAIDAIKU, kuma dukkan ayyukan dan-adam nasa ne, in banda azumi, shi kam na
Allah ne, saboda ya zo cikin hadisin kudusiy, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi
wa sallama- ya ce: "Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Dukkan ayyukan
dan-adam nasa ne, mai kyau akan ninka masa da kwatankwacinsa goma, in banda
azumi shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa".
YIN SADAKA A BOYE IBADA
CE TA DAIDAIKU, Wanda hannun Musulmi na dama take bayar da ita ba tare da hagun
dinsa ya san abinda ya bayar ba, saboda ya zo cikin hadisi lallai Manzon Allah
–sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Jinsi bakwai, Allah zai
inuwantar da su ranar kiyama a karkashin inuwarsa ranar da babu wata inuwa sai
tasa", Sai ya ambata daga cikinsu: "Da Mutumin da ya yi sadaka,
sai ya boye ta, har hannunsa na hagun bai san abinda damansa ya aikata ba".
.
Allah ya yi mini albarka
NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina
neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani
zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai
rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Bayan haka:
Kuma kamar yadda ibadodin da Mutum yake yin su
shi kadai lamarinsu ya zama mai girma, to lallai ibadodin da Musulmai suke haduwa
su taru wajen yinsu kamar salla da hajji da wasunsu suna da manufa wadanda basu
boyuwa, Daga cikin hikimomin akwai: samun soyayya da kauna, da kuma Musulmai su
san halin da sashensu suke ciki, da bayyanar da buwayar Musulunci, ilmantar da
jahili, koyar da al'ummar Musulmai hadin kai da nisantar rabuwar kai, da
taimakakkeniya da samar da daidaito, da rushe banbance-banbance na zamantakewa.
Kuma cikin KASANTUWAR
IBADA NAU'I-NAU'I NE akwai fagen sukuwa mai girma na yin ayyukan kusanci,
saboda akwai daga Mutane wanda ake bude masa kofar yin wani aikin banda wani,
kuma kowane Mutum ana saukake masa abinda aka halicce shi domin shi, kuma
Mutane suna samun fifiko a wannan kofar,
saboda a cikinsu akwai wanda neman ilimi shine
abu mafi sauki a gare shi akan zuhudu da guje wa Duniya,
a cikinsu kuma akwai wanda zuhudun shine yafi
sauki a gare shi,
daga cikinsu akwai wanda ibada ce tafi sauki a
gare shi akan neman ilimi da zuhudu;
don haka, abinda aka shar'anta wa kowane Mutum
shine ya aikata abinda zai iya na alkhairi, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "Sai ku bi Allah da takawa gwargwadon abinda kuka
samu iko", [Tagabun: 16].
Kuma idan Musulmi ya san
ko ya riski girman ni'imar da take cikin NAU'INTUWAR IBADA, TO ya wajaba
akansa ya gode wa UbangijinSa akan hakan, kuma godiya ga kowace ni'ima shine
yin amfani da ita (ta fiskar da ta dace), saboda an ruwaito daga Anas bn Malik
–R.A- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- yana cewa: "Lallai Allah yana yarda ga
Bawa, ya ci abinci sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha, sai ya gode
masa akansa".
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka
yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu.
No comments:
Post a Comment