Bismillahir
Rahmanir Rahim
|
Lallai yabo na
Allah ne, muna gode masa, muna neman taimakonSa, kuma neman gafararSa, muna
neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah
ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar babu mai
shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah;
shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai annabi
Muhammadu bawanSa ne ManzonSa. Bayan haka:
|
Matashiya a
gabanin sharhi
|
LITTAFIN ALKAWA'IDUL ARBA'I shine
littafi na biyu, da ake karanta su a cikin
jerin littatafan da aka jeranta su ga dalibin ilimi (MUTUN DALIBIL ILMI). Yin sharhin wannan littafin ya ginu ne, akan sabbuba dayawa, daga
cikinsu:
:
|
Saboda
koyi da Magabata na kwarai
|
Saboda
littafin Kawa'idul arba'i kamar takaicewan littafin KashfusShubuhat ne
|
Saboda
nasihar da Malumanmu suka yi a gare mu (kan bashi muhimmanci).
.
La facilidad
|
Saboda a
cikin littafin akwai yaye shubuhohin Mushirkan zamaninmu namu.
|
Za mu fara
sharhin Kawa'idul
Arba'i
ne gabanin fara sharshin KashfusShubuhat; domin kada wata shubuha ta makale
a zuciyar Dalibin
ilimi.
|
ABUBUWAN DA SUKE CIKIN
LITTAFIN KAWA'IDUL ARBA'I
Ana kasa wannan littafin zuwa kashi uku, kamar haka:
|
2.Muhimmancin karanta ilimin Tauhidi
|
3.Sai ka'idodi guda hudu (4)
|
1.Gabatarwa (sabuban jin
dadi da walwala).
|
Na daya: Gabatarwa (sabuban jin dadi da walwala)
|
Domin koyi da Maluman da suka gabace shi, da
magabatan kwarai;
wadanda cikin al'adarsu akwai bude littatafansu da
sunan Allah. (Bismillah).
|
(1)SABABIN DA YA SANYA MAWALLAFIN YA FARI LITTAFINSA DA
"BISMILLAH"
|
Domin koyi da
littafin Allah, da Annabawa عليهم السلام.
|
Domin neman albarkar
farawa da sunan Allah Mai-karamci.
|
Bismillahir Rahmanir
Rahim
(1) Ina rokon Allah Mai
karamci, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya jibinci lamuranka, a nan duniya,
da lahira (2).
Kuma ya sanya ka zamo mai albarka
a duk inda ka kasance (3).
|
(2) Bayan
bismillah, sai Shehin –Allah ya yi masa gafara- ya fara littafinsa, da yin
addu'a ga dalibin ilimi, kamar yadda ya saba. Wannan kuma dalili ne kauna
da son da yake yi ga daliban ilimi, ta hanyar roka musu ya basu kowane
alheri.
(3) Waliyyan Allah sune suka hada tsakanin imani da
takawa, Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah yay i rahama
a gare shi- ya ce: "Wanda ya kasance mumini mai takawa, to shi
waliyyin Allah ne". dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: {LALLAI NE MASOYAN ALLAH,
BABU WANI TSORO AKANSU, KUMA BA ZA SU KASANCE CIKIN BAKIN CIKI BA}. [Yunus: 62-63].
|
ALBARKA: Ita ce, bunkasar abu, da
karuwarsa.
NEMAN ALBARKA: Yana nufin, neman bunkasarsa,
da karuwarsa.
MAI ALBARKA: Shine, wanda ake amfana da shi a duk inda ya safka.
|
Kuma ya sanya ka daga wadanda idan aka basu, sai su
yi godiya (1).
|
Neman albarka, wanda aka shar'anta.
|
Neman albarka, wanda aka hana, Wannan kuma shine neman albarkar da
shari'a bata tabbatar da shi ba, kuma irin wannan yana cikin nau'ukan
karamar shirka.
|
NEMAN
ALBARKA YANA KASUWA KASHI BIYU:
|
ALBARKAR DA
AKA RISKO (DA HISSI), Misalin ilimi da addu'a, da
makamantansu, saboda mutum ana iya samun albarkar iliminsa da da'awarsa
zuwa ga alkhairi, sai a kira hakan da: albarka, saboda yadda muka samu
alheri mai yawa daga wurinsa, kamar littafan Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah
da waninsa, daga cikin Maluman da Allah ya sanya albarka da alheri a
cikinsu, kuma al'umma ta amfana da su.
|
ALBARKA TA SHARI'A: Misalin sallah a Masallaci Mai alfarma, ko
Masallacin Annabi (SAW).
|
(1) Ni'ima jarabawa
ce, saboda dalilai dayawa, daga cikinsu akwai fadinSa: "KUMA MUNA MUKU
IBTILA'IN SHARRI DA ALHERI, A MATSAYIN JARRABAWA", Da fadinSa
"YAYIN DA YA GANSHI A TABBACE A WURINSA, SAI YA CE: WANNAN YANA DAGA
FALALAR UBANGIJINA, DOMIN YA JARRABE NI; SHIN ZAN BUTULCE NE, KO ZAN YI
GODIYA, KUMA WANDA YA YI GODIYA TO HAKIKA YANA YIN GODIYAR NE AKANSA, WANDA
KUMA YA BUTULCE, TO LALLAI UBANGIJINA MAWADACI NE MAI KARAMCI", Da
fadinSa: "AMMA MUTUM, IDAN UBANGIJINSA YA JARRABE SHI, SAI YA KARRAMA SHI,
YA MASA NI'IMA, TO SAI YA CE: UBANGIJINA YA KARRAMA NI".
Ya
zo cikin hadisi: "Lallai wasu Mutane uku daga Banu-isra'ila, Allah ya
yi nufin ya jarrabe su".
|
Rataya
zuciya ga Allah, gabanin samuwar ni'imah
|
Godiya wa Allah, bayan aukuwar
ni'ima, Kuma wannan yana kasancewa, da dayan:
|
ZUCIYA
|
HARSHE
|
GABBAI
|
NI'IMA TANA RATAYA DA TAUHIDIN RUBUBIYYA (AIKIN
ALLAH) DA KUMA TAUHIDIN ULUHIYYAH (AIKIN HALITTU)
KUMA GODIYA A GARE TA, YANA KASUWA KASHI BIYU:
:
|
Wannan
nau'in kuma, yana neman bawa ya samar da kuduri da imani na yakini
cewa lallai Mai bada ni'ima shine Allah SWT, don haka, ba zai rataya
zuciyarsa ga wanin Allah ba, kuma ba zai nemi wani alheri ba, face daga
Allah.
Kuma, kamar
yadda Aljannah ana nemanta ne daga Allah SWT, saboda shine ya mallake ta,
to haka arziki, ba zai yiwu a nemi shi ba, face daga Allah SWT.
"KUMA
KAYI TAWAKKALI GA RAYAYYEN DA BAYA MUTUWA".
"LALLAI
WADANDA KUKE BAUTA MUSU KOMA BAYAN ALLAH, BASU MALLAKA MUKU ARZIKI, SAI KU
NEMI ARZIKI DAGA ALLAH" (Wato, ku nema daga Allah, ba daga
waninsa zaku nemi arziki ba) "KUMA KU BAUTA MASA, KU YI GODIYA A
GARE SHI".
|
Wannan kuma ta hanyar salwantar da ni'imar ta fiskar da zata yardar da
Ubangijinmu Mabuwayi da daukaka akanmu. Tare da kara
ayyukan da'a da nufin kusantarSa Mai tsarki da daukaka, da kuma nisantar
ayyukan sabo, da nufin bin umarninSa.
|
Wannan kuma, ta hanyar yin zance kan ni'imar Allah, da yin
godiya a gare shi, da yabonSa, da yin jinjina a gare shi SWT, saboda
fadinSa Madaukaki: "KUMA AKAN NI'IMAR UBANGIJINKA, SAI KA BADA
LABARI (da nufin godiya)".
|
Wannan yana
kasancewa, ta hanyar gaskiyar imani da akida, da cikakken sallamawa, cewa
Mai azurtawa Mai bada ni'ima shine Allah Subhanahu Wa Sa'alah, kuma
lallai dukkan abinda ke tare da bawa na ni'ima, to daga wurin Allah ne
SWT.
|
(1) Wannan kuma
saboda hakuri wajibi ne, da ijma'in maluma.
|
Mutane a lokacin da musibun duniya suka sauka akansu suna kasuwa kashi hudu:
|
Kuma idan aka masa ibtila'i sai ya
yi hakuri (1)
|
Mai yin godiya
|
Mai yarda
|
Mai nuna bacin Rai
|
Mai hakuri
|
1. NUNA
BACIN RAI: a lokacin musiba haramun ne, kuma zunubi ne babba
daga cikin manyan zunubai, kuma hakan ya kan
kasance ko dai da:
|
Gabbai
|
Harshe
|
Zuciya
|
-
BACIN RAN ZUCIYA: Imam Ibnu-Kayyimil
Jauziyyah, ya fadi maganar da ma'anarta shine, Lallai wasu mutane
harshensu ba zai yi azarbabiyar fadin maganar bacin rai, Sai dai kuma
zuciyarsu da take cikin kirjinsu, tana shaidar da hakan, ta yadda yake
mummunan zato ga UbangijinSa, har yake fada a cikin zuciyarsa cewa,
Ubangijina ya zalunce ni, Ubangijina ya haramta mini, Ubangijina ya hana
ni, ... da makamancin haka, kuma a cikinsu akwai mai yin hakan a cikin
zuciyarsa dayawa, wani kuma kadan. Sai ka bincika Ranka, shin ka kubuta
daga wannan; domin idan ka zama ka kubuta, to lallai ka kubuta daga musiba
mai girma.
-
NUNA BACIN RAI DA HARSHE: Wannan ya kan kasance
ta hanyar ihu, shewan mutuwa, da kiran bone da bala'i da halaka, da
tsinuwa da la'anta, da zage-zage.
-
NUNA BACIN RAI DA GABBAI: Wannan kuma ya kan
kasance ta hanyar marin fiska, da yaga wuyar riga, da tuzge gashi.
2. HAKURI: Hukuncinsa wajibi ne, da ijma'in Maluma. Kuma
wajibi ne mutum ya yi hakurin musibar da ta auku masa da zuciyarsa, da
harshensa, da kuma gabbansa.
Imam Ahmad yana cewa:
"Hakuri ambatonsa ya zo a cikin Alkur'ani, a kusan wurare casa'in,
kuma shi wajibi ne, da ijma'in Maluman al'ummah. Kuma hakuri rabin imani
ne, saboda imani ya rabu gida biyu, rabinsa hakuri, rabinsa godiya"
[littafin MadarjisSalihina na Ibnul-Kayyim].
3. MATSAYIN YARDA: Hukuncin kaiwa matsayin
yarda da musiba mustahabbi ne, kuma wannan martaba ce da tafi girma akan
matsayin hakurtar da kai.
4. GODIYA: Hukuncin kaiwa
matakin gode wa Allah ga musibu mustahabbi ne, kuma shine matakin da yafi
sauran girma da cikar kamala.
,
|
Na biyu: Ka'idodi guda hudu
|
Bismillahir Rahmanir
Rahim
Ka sani –Allah ya shiryar
da kai ga aikin biyayya a gare shi-: Lallai Mikakken addini irin na annabi
Ibrahima shine, ka bauta wa Allah, kana mai tsantsanta nufin addini a gare shi,
kamar yadda Allah Ta'alah ya fada: "KUMA BAMU
HALITTA MUTUM DA ALJAN BA SAI DON SU KADAICE NI DA BAUTA"(1).
Kuma idan ka san cewa, Allah ya halitta ka ne,
domin bauta, to ka sani:
Lallai bauta bata zama bauta, sai an kadaita
Allah da ita (Tauhidi), kamar yadda salla bata cin sunan sallah sai idan an yi
ta da tsarki. Kuma idan shirka (nufin wani da ibada tare da Allah) ta shiga
cikin bauta, sai ibadar ta lalace, kamar yadda hadasi idan ya shigar ma tsarki.
Kuma idan ka san cewa, lallai shirka idan ya
cakuda da ibada, yak an lalata ta, ya rushe dukkan aiki, sai ma'abucinsa ya
kasance daga masu dawwama a cikin wuta, a nan za ka san cewa lallai abinda yafi
muhimmanci a gare ka, shine: Sanin hakan, da fatan Allah ya tsamar da kai daga
wannan tarko, wanda shine shirka ga Allah, wanda yake magana akansa: "LALLAI ALLAH BAYA GAFARAR AYI MASA SHIRKA, AMMA YANA
GAFARTA ABINDA BAI KAI HAKA BA, GA WANDA YA YI NUFI", [Nisa'i: 116].
Wannan kuma zai kasance ta hanyar sanin
ka'idodi guda hudu, wadanda Allah Ta'alah ya ambace a cikin littafinSa:
KA'IDAR
FARKO: Ka
sani, lallai kafiran da Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya yake
su, suna masu tabbatar da cewa lallai Allah Ta'alah shine Mahalicci Mai jujjuya
lamura, amma hakan bai shigar da su cikin musulunci ba, Dalili kuma akan wannan
shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: WANENE KE
AZURTA KU DAGA SAMA DA KASA, KUMA WANENE YA MALLAKI JI DA GANI, KUMA WANENE KE
FITAR DA RAYAYYE DAGA MATACCE, KUMA YAKE FITAR DA MATACCE DAGA RAYAYYE, KUMA
YAKE JUJJUYA LAMARI, LALLAI ZA SU CE, ALLAH NE, KA CE: SHIN BA ZA KU YI TAKAWA
BA"(2).
(1) Mawallafin –Allah
ya yi masa rahama- ya gaya mana, dalilin da ya sanya muke karanta Tauhidi.
(2) Kafiran da aka turo
Annabi –S.A.W- a cikinsu, sun kasance basu jayayya, ko in ce, suna tabbatar da
Tauhidin Rububiyya (wato, kadaitakar Allah cikin ayyukansa), tare da haka, Sai
Manzon Allah –S.A.W- ya yake su; wannan kuma saboda husumar da take tsakaninsu
da tsakanin Annabi –S.A.W- ta kasance ne, cikin Tauhidin Uluhiyyah (Kadaita
Allah da ayyukan bayi); Don haka, duk wanda ya yi wani abu na ibada ga wanin
Allah, to mushirki ne kafiri.
KA'IDA
TA BIYU: Lallai ne kafiran da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya
yake su suna cewa: Bamu roki ababen bautarmu muka fiskance su ba, sai domin
neman kusanci, da kuma ceto. Shi kuma dalilin neman kusanci shine fadinSa
Madaukaki: "WADANDA KUKA RIKA BAICINSA A
MATSAYIN MAJIBINTA; SUNA CEWA: BA MU BAUTA MUSU, SAI DON SU KUSANTAR DA MU
ZUWA GA ALLAH, KUSANCIN DARAJA, LALLAI ALLAH ZAI YI HUKUNCI A TSAKANINSU GA
ABINDA SUKA KASANCE SUNA SABAWA A CIKINSA, LALLAI ALLAH BAYA SHIRYAR DA WANDA
YAKE ME KARYA, MAI KAFIRCI" (1).
Dalilin neman ceton
ababen bautarsu kuma shine, FadinSa Madaukaki: "KUMA SUNA
BAUTA WA BAICIN ALLAH, ABINDA BAYA CUTAR SU, KUMA BAYA AMFANINSU, KUMA SUNA
CEWA: WADANNAN MACETANMU NE A WURIN ALLAH" [Yunus: 18].
Kuma ceto, nau'i biyu ne, ceton da aka kore,
da ceton da aka tabbatar(2).
|
(1)
Ma'abuta shirki da kafirci
suna kafa hujja, da cewar su basu roki ababen bautarsu na banza ba, koma bayan
Allah, kuma basu fiskance su ba, sai don su kusantar da su, ga Allah, su cece
su. Kuma da aikata hakan sun cancanci
Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kafirta su, sa'annan ya yake su.
(2)
Kalmar shafa'a: A harshen larabci, ta samu ne daga
Tarawa, ko sanya abu daya ya zama biyu
(shafa'i).
A shari'a kuma: Shafa'ah, tana nufin zamowa
tsani ga wani, wajen janyo masa amfani, ko tunkude masa wata cuta.
CETON DA AKA KORE: Shine ceton da ake
nemansa daga wanin Allah, cikin abinda babu wanda ke iya yinsa sai Allah,
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, KU CIYAR DAGA ABINDA MUKA
AZURTA KU, GABANI WANI YINI YA ZO WANDA BABU CINIKI A CIKINSA, KUMA BABU ABUTA,
KUMA BABU CETO, KUMA KAFIRAI SUNE AZZALUMAI" [Bakara: 254].
Shi
kuma CETON DA AKA TABBATAR: Shine ake nemansa daga Allah, Shi kuma wanda
aka karbi cetonsa an karfafa shi da karbar cetonsa, Wanda kuma za a karbi ceto akansa
shine wanda Allah ya yarda da zancensa da ayyukansa –bayan ya bada izini-,
kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "BABU
WANDA ZAI YI CETO A WURINSA, FACE DA IZININSA" [Bakara: 255].
KA'IDA
TA UKU (1): Lallai Annabi –sallal lahu alaihi wa
sallama- ya bayyana ne, ga mutanen da suke a rarrabe cikin ibadodinsu; daga
cikinsu akwai wanda ke bautar Mala'iku, daga cikinsu akwai wanda ke bautawa
Annabawa da Salihai, daga cikinsu akwai ke bautawa bishiyoyi da duwatsu, daga
cikinsu akwai wanda ke bautawa rana da wata, sai Manzon Allah –sallal lahu
alaihi wa sallama- ya yake su, bai rabe wani daga cikinsu ba.
Dalili kuma
shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU YAKE SU HAR
WATA SHIRKA BAZA TA KASANCE BA, KUMA ADDINI DUKANSA YA KASANCE NA ALLAH" [Anfal: 39].
Kuma dalilin
suna bautar rana shine fadinSa Madaukaki: "KUMA
YANA DAGA AYOYINSA; DARE DA YINI, DA RANA DA WATA, KADA KU YI SUJADA GA RANA,
KADA KU YI GA WATA, SAI KU YI SUJADA GA ALLAHN DA YA HALITTA SU, IDAN KUN
KASANCE A GARE SHI KAWAI KUKE YIN BAUTA" [Fussilat: 37].
Kuma dalilin suna bautar Mala'iku shine fadinSa
Madaukaki: "KUMA BAYA UMARTARKU, DA KU RIKI
MALA'IKU DA ANNABAWA ABABEN BAUTAWA ..." har zuwa karshen
ayar [Ali-imrana: 80].
|
(1)
Wannan ka'idar dalili ne, karara,
a fili, wanda ke raddi ga wanda ke cewa: Lallai shirka, kawai tana kasancewa
ne, cikin bautar sassaken gumaka. saboda, Dalilan shari'a sun zo akan gumakan,
da sauran lalatattun ababen da ake bauta musu koma bayan Allah, a wancan
zamanin, saboda Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- bai rabe tsakaninsu
ba, hasalima ya kirga su gaba dayansu a matsayin Dagutun da ake bauta musu koma
bayan Allah, sai ya yake su ba tare da ya toge wasu ba; wannan kuma domin
addini gaba dayansa ya kasance ya kebantu da Allah.
Kuma dalilin suna bautar Annabawa shine fadinSa
Madaukaki: "KUMA A LOKACIN DA ALLAH YA CE:
YA ISA 'DAN MARYAM! SHIN KAI NE KA CE WA MUTANE, KU RIKE NI, NI DA UWATA,
ABUBUWAN BAUTAWA BIYU, BAICIN ALLAH? ISA YA CE: TSARKINKA YA TABBATA, BA YA
KASANCEWA A GARE NI IN FADI ABINDA BANI DA WANI HAKKI A CIKINSA, IDAN NA
KASANCE NA FADE SHI, TO LALLAI KA SAN SHI, DOMIN KA SAN ABINDA KE CIKIN RAINA,
KUMA BANI SANIN ABINDA KE CIKIN RANKA, LALLAI NE KAI MASANIN ABUBUWAN DA SUKE
FAKE NE" [Ma'ida: 116].
Kuma dalilin suna bautar Salihai shine fadinSa
Madaukaki: "SUNE WADANCAN DA SUKE ROKO,
SUKE NEMAN KUSANCI, WANENE A CIKINSU YAFI KUSANCI, KUMA SUNA FATAN RAHAMARSA,
KUMA SUNA TSORON AZABARSA"
[Isra'i: 57].
Kuma dalilin suna bautar bishiyoyi da duwatsu
shine fadinSa Madaukak: "SHIN BAKU GANIN
GUNKIN LATA DA UZZAH *DA WANI GUNKIN WAI SHI MANATA NA UKUNSU"
[Najm: 19-20].
Da hadisin
Abu-Wakid Allaisiy –Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Mun fita tare da
Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- zuwa Hunain, alhalin muna sabin ficewa
daga kafirci. Alhalin mushirkai suna da bishiyar magarya wanda suke
lazimtatrta, kuma suke rataya makamansu, suna kiran bishiyar da suna,
ma'abuciya takkuban da ake ratayawa, sai muka shige ta jikin wannan bishiyar,
sai muka ce: Ya Ma'aikin Allah! Muma ka sanya mana bishiyar ratayawa, kamar
yadda mushirkai suke da bishiyar rataye tokobai... har karshen hadisin.
KA'IDA TA HUDU: Lallai mushirkan zamaninmu sun fi
munin shirka, akan mushirkan farko, saboda na farkon sukan yi shirki ne a
halin walwala, sai su yi ikhlasi ga Allah a lokacin tsanani. Su kuma
mushirkan zamaninmu shirkarsu a dawwame take; a halin wadaci da tsanani,
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA IDAN SUKA SHIGA JIRGIN
RUWA, SAI SU KIRAYI ALLAH, SUNA MASU TSARKAKE ADDINI A GARE SHI, TO A LOKACIN
DA YA TSIRATAR DA SU ZUWA GA TUDUN KASA, SAI GASU SUNA SHIRKI"
[Ankabut: 65],(1).
Allah shine Mafi sani.
Salatin Allah su kara tabbata ga annabi Muhammadu, da iyalanSa, da
sahabbanSa, tare da sallama.
|
(1) Mawallafin –Allah ya
yi masa rahama- a cikin wannan ka'idar, ya bayyana girman hatsarin mushirkan wannan zamani; saboda sun fi tsananin shirki, akan
mushirkan farko; saboda mushirkan zamaninmu suna yin shirka ne ga Allah a cikin
tsanani da yanayin walwala, yayin da su kuma mushirkan farko su ke yin shirka a
lokutan walwala, suke tuna Allah da kadaitakarSa, a lokacin tsanani.
Don haka;
Idan har kafiran da aka turo Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- sun
fi karancin shirka, sai kuma Allah ya kafirta su, To yaya lamarin zai kasance,
kan wadannan da shirkansu dawwamamme ne; a cikin halin lafiya da cuta; kenan,
sune suka fi cancantar zamowa kafirai.
LITTAFIN KAWA'IDUL ARBA'I; Wanda kamar
takaicewa ne ga littafin KASHFUS-SHUBUHAT
|
|||||
MATASHIYA; a cikinta an
kawo sabuban samun walwala
|
|||||
SABUBAN SAMUN WALWALA
|
|||||
Idan aka bashi sai ya yi godiya
|
Idan aka masa ibtila'i sai ya yi hakuri
|
||||
NI'IMA IBTILA'I CE, Dalili kuma shine fadinSa
Madaukaki: "KUMA MUNA JARABTARKU DA SHARRI DA
KUMA ALHERI A MATSAYIN JARABAWA".
|
YANAYIN MUTANE LOKACIN SAUKAR MUSIBA
|
||||
GODIYAR NI'IMAH
|
|||||
GODIYAR DA TA RATAYA DA TAUHIDIN RUBUBIYYA
|
WANDA TA RATAYA DA TAUHIDIN ULUHIYYAH
|
||||
Neman Aljannah baya kasancewa sai daga Allah, saboda
shine SWT ya mallake ta, to haka arziki shima, ba a nemansa, face daga Allah;
don haka Babu makawa kan rataya zuciya ga Allah, ba ga waninsa ba.
|
YA YI GODIYA DA
ZUCIYARSA:
Ta hanyar tabbatarwa cewa duk wani abinda ke
tattare da shi na ni'ima, to daga Allah
ne; ba daga waninsa ba.
|
YA YI GODIYA DA
HARSHENSA:
Ya ce: "WANNAN
DAGA FALALAR UBANGIJINA NE, DOMIN YA
JARRABE NI; ZAN YI GODIYA NE, KO ZAN BUTULCE".
|
YA YI GODIYA DA
GABBANSA:
Ta hanyar sarrafa wannan ni'imomin cikin godiya wa
mai bada ni'imomi. Kuma kowace ni'ima da yanayin yadda ake mata godiya; don
haka godiyar ni'imar dukiya ita ce, shine ya ciyar da ita cikin biyayya ga
Allah, godiyar ni'imar ilimi kuma ya rika bayar da shi, ga wanda ya yi
tambaya da harshensa, ko kuma yake bukata.
|
MAI NUNA BACIN RAI: Hukuncinsa
haramun ne, kuma daya daga manyan zunubai, har ma zai iya kaiwa zuwa ga
karamar shirka, kuma lallai nuna bacin rai kan kasance, ko dai da; zuciya, ko
da harshe, ko da gabbai.
|
MAI HAKURI: Hukuncin hakuri
a yanayin musiba wajibi ne, da ijma'in Maluman al'ummah. Kuma zai yi hakurin
ne da zuciyarsa, da harshensa, da kuma gabbansa. Kuma hakuri ya ci
sunansa; domin dandana shi akwai daci, sai dai abinda ke haifarwa zakinsa
yafi na zuma.
|
|
|
||||||
|
KA'IDODI GUDA HUDU (القواعد الأربع)
|
||||||
|
|
Idan kuma ya yi zunubi sai ya tuba
|
Don me, muke
karanta ilimin Tauhidi?
Da bayanin hatsarin shirka
|
KA'IDAR
FARKO: Lallai kafiran da Manzon Allah –sallal
lahu alaihi wa sallama- ya yake su, sun kasance suna tabbatar da Tauhidin
Rububiyyah, sai dai basu kasance suna tabbatar da Tauhidin Uluhiyyah ba, sai
ya zama hakan bai shigar da su cikin Musulunci ba.
|
KA'IDA TA BIYU: Lallai kafirai sun
kasance suna bautar gumaka ne, domin su kusantar da su ga Allah, su cece su.
|
KA'IDA TA UKU: Lallai Annabi –sallal
lahu alaihi wa sallama- ya bayyana ne ga mutanen da suke a rarrabe cikin
yanayin bautarsu, sai bai ware wani shirkan akan wani ba (duka ya yi fatali
da su).
|
KA'IDA TA HUDU: Lallai Mushirkan
zamaninmu sun fi girman shirka akan mushirkan farko.
|
MAI YARDA: Hukuncin
samun yarda ga musiba mustahabbi ne, kuma idan yardar bawa ga UbangijinSa ta
cika, zai san cewa, Dukkan abinda ya same shi, to daga Allah ne, Duk kuma
abinda Allah ya kaddara shi ga bawa to alheri ne.
|
MAI GODIYA: Gode wa
Allah ga musibu shine matakin da yafi sauran girmar martaba, kuma shine
abinda yafi soyuwa. Mai yinsa kuma yana kasancewa ne daga cikin bayin Allah
masu godiya.
|
MIKAKKEN ADDINI (Haniyfiyyah): Addinin Annabi Ibrahim, Lallai Allah ya
halitta ka, domin yin bauta a gare shi, ita kuma bauta ba a kiranta da suna
ibada, sai tare da tauhidi, saboda shirka idan ta cakudu da ibada, sai ta
lalata ta, ta kuma rushe dukkan ayyuka, sai ma'abucinta ya wayi gari daga
masu dawwama a cikin wuta; don haka shirka ita ce mafi muhimmancin abinda ya
wajaba ka sanshi.
|
JARABAWAR
LITTAFIN KA'IDODI HUDU (KAWA'IDUL ARBA'I)
SUNANKA
..................................................................
YAWAN ABINDA KA HARDACE
DAGA LITTAFIN "kitabut Tauhid".....................................
SHIN KA HADDACE LITTAFIN: KA'IDODI HUDU (القواعد الأربع) .............................................
AIKI
|
DALILINSA DAGA ALKUR'ANI KO HADISI
|
Ni'ima ibtila'i ne
|
|
Kafirai sun tabbatar wa Allah Rububiyya
|
|
Bautar alloli
don neman su kusantar da mai yinsu ga Allah
|
|
Nau'in ceton da aka kore
|
|
Dalilin cewa kafirai suna bautar Rana da Wata
|
|
Dalilin suna yin bautar Mala'iku
|
|
Dalilin suna yin bautar Annabawa
|
|
Dalilin suna yin bautar Salihan Bayi
|
|
Dalilin suna bautar duwatsu da
bishiyoyi
|
|
Mushirkan farko suna
tsarkake tauhidi a lokacin tsanani, sai kuma su yi shirka a lokacin wadaci
|
|
Dalilin da ke kaiwa ga shirka
|
|
RUBUTA ABINDA KA SANI KAN
ABUBUWAN DA SUKE TAFE:
Me ya sa muke karanta ilimin
Tauhidi?
|
1. 2.
3. 4.
|
5.
6. 7.
8. 9.
|
|
Me ya sa muke karanta littafin ka'idodi hudu (القواعد الأربع)?
|
1.
2.
|
LITTAFIN KA'IDODI HUDU ANA KASA SHI ZUWA
KASHI
|
1. 2. 3.
|
Littafin Ka'idodi hudu, kamar takaicewa ne ga littafin
|
|
Me ya sa ba za
mu fara da karatun littafin Kashfus Shubuhat ba?
|
|
Alamomin samun walwala da jin dadi
|
1. 2. 3.
|
Mikakken addini (Hnaiyfiyyah) shine:
|
|
Fa'idan karanta littafin ka'idodi hudu
|
|
Waliyyan Allah, sune
|
Sheikhul Islam
Ibnu-Taimiyyah ya ce:
|
Dalili akan haka
|
Don me:
|
Godiya akan ni'ima tana kasancewa, da, tare da misali
|
1.
|
2.
|
|
3.
|
|
Ta yaya bawa zai rataya ga Ubangiji wajen neman ni'ima?
|
|
Halayen Mutane a
lokacin saukar musiba, da hukuncinsu:
|
1. .................,,, hukuncinsa, kuma yana kasancewa ta ..... da
da
2. .................,,, hukuncinsa, kuma yana kasancewa ta ..... da
da
|
3.
|
4.
|
Ceto (shafa'ah) a harshen larabci:
|
|
Shafa'a a shari'ah:
|
|
Ceto yana kasuwa zuwa kashi:
|
1.
2.
|
Sharuddan ceto tabbatacce:
|
1.
2.
3.
|
Kuma tana kasuwa zuwa:
|
1.
2.
|
1- Shi
kuma ya kasu zuwa: da da
|
1. Shi kuma ya kasu
zuwa: da da
2. Shi kuma ya kasu zuwa: da da
|
KA'IDAR FARKO:
|
|
|
|
KA'IDA TA BIYU:
|
|
|
|
KA'IDA TA UKU:
|
|
|
|
KA'IDA TA HUDU:
|
|
|
|
Hukuncin aikin da shirka ta shiga cikinsa
|
Dalili:
|
|
|
1
|
Matashiya kan sabubban samun walwala
|
56
|
2
|
Ka'idar Farko
|
60-61
|
3
|
Ka'ida ta
Biyu
|
62-64
|
4
|
Ka'ida ta
Uku
|
64-65
|
5
|
Ka'ida ta
Hudu
|
66
|
6
|
Sharhin littafin a takaice a cikin jadwala
|
67-68
|
7
|
Jarabawa kan littafin ALKAWA'IDUL ARBA'I
|
69-72
|
8
|
Fihirisa (abinda ke cikin littafin).
|
73
|
Allah yasaka da alheri Dr
ReplyDelete