MA'AIKATA GUDA
4,200 AKA AJIYE DOMIN SAUKAKE FICEWAN MAHAJJATA,
MINTUNA 40 KUMA,
SHINE LOKACIN DA ZA SU CI A KAFOFIN FICEWA DAGA KASAR
(4200
موظف وعامل يسهلون مغادرة الحجاج ...
و40 دقيقة مدة
بقائهم في المنافذ)
Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya
BADA KULAWAR JAGORORIN MASARAUTAR SAUDIA DA HIMMATUWARSU DA BAKIN
ALLAH; MAHAJJATA
|
MA'AIKATA
|
Labara
|
SASHEN SADARWA
|
Fdakar da Mahajjata
|
MAUDU'I
|
Cikin kasar Saudia da wajenta
|
YADAWA
|
25/ Zul-hijjah/1439h
|
RANA
|
>Shugaban majalisar gudanar da ofishin da
aka hade na Wukala'u
|
MASU MAGANA
|
KULAWA DA BAIWA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA MUHIMMANCI
|
SAKON AIKIN
|
Sakamakon
fadakarwar ministirin hajji da umrah … Shugaban majalisar gudanar da ofishin da
aka hade na Wukala'u:
MA'AIKATA GUDA 4,200 AKA AJIYE DOMIN SAUKAKE FICEWAN MAHAJJATA,
MINTUNA 40 KUMA, SHINE LOKACIN DA ZA SU CI A KAFOFIN FICEWA DAGA
KASAR
Mai girma Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na
Wukala'u; wato, Dr. Faruk bn Yahya Bukhariy ya tabbatar cewa, domin yin aiki da
fadakarwar ministirin hajji da umrah, dangane da hajjin shekarar 1439H, to
lallai an takaita lokacin jiran Mahajjata a dukkan kafofin ficewarsu daga kasar
Saudia na tudu da ruwa da sama, daga awa biyu zuwa minti arba'in (40), kuma
minti arba'in lokaci ne wanda hankali zai karba idan aka auna da tarin yawan
bakin Allah; Mahajjata.
Kuma Dr. Bukhariy ya ambata cewa lallai tsarin gudanar da hajjin
shekarar 1439H, wanda aka mika shi ga Mai girma ministan hajji da umrah, wato
Dr.Muhammadu bn Salih Dahir Bintin, ya kwadaitar da mu ma'aikata kan ninka
ayyuka, da bunkasa su, tare da gabatar da mafificin hidima ga Mahajjata dakin
Allah mai alfarma, domin aiki da umurnin Mai hidimar harami biyu madaukaka;
sarki Salman bn Abdul'aziz Alu-Sa'ud, da mai girma yarimansa amintacce –Allah
ya kiyaye su-, na cewa: a yi amfani da dukkan damammaki, kuma a hada karfi
domin hidmar bakin Allah, domin a basu damar su gabatar da ayyukansu na hajji
cikin sauki da walwala, yana mai tsanantawa ko nuna muhimmancin hukuma ta daga
darajar iya gabatar da ayyukanta, a karkashin kulawar ministirin hajji da
umrah, domin a gabatar da mafificin abinda za a iya na hidimomi ga Mahajjata.
Kuma tsarin aiki na ofishin da aka hade na Wukala'u ya
dauki yanayi mai kyau wanda ya banbanta da na shekarun da suka shude, domin
samun tabbacin gabatar da jeringiyar cikakkun hidimomi na a gani, a fada, ga
Bakin Mai rahama, kari akan bayar da tirenin da kosa-kosen koyar da aiki da
sanar da shi ga sababbin ma'aikata, da samun tabbaci iya gabatar da hidimomin
kammala hidimomin Mahajjata a lokuta guda biyu na shigowa da fita.
Kuma ya ce: "Kuma sakamakon kulawan hukumar hajji da umrah
ta wizara ga akan mu'assasosin mudawwifuna, wanda kuma daga cikinsu akwai: ofishin
da aka hade na Wukala'u, to wannan ofishin yana matukar kwadayin
tallafawa wannan hukumar, ya karfafe su, ya agaza musu, domin su cimma
manufofinsu, su kuma sauke abinda aka
dora musu, ta fiskar da zata yardar, kuma wacce ake nema".
Kuma Mai girma Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka
hade na Wukala'u; wato, Dr. Faruk bn Yahya Bukhariy ya yi nuni cewa, lallai
su a wannan ofishi, suna yin aiki kan tambari ko taken da hukumar hajji da
umrah ta wizara suka runguma "Hidimar Mahajjaci daukaka ne a gare mu",
kuma domin kasancewar wannan ofis na wukala'u shi ke sada Mahajjata da
Mu'assasosin Mudawwafai da Adilla'u, sai wannan ofishin ya sanya babban sakonsa
ya zamto shine, FARO AIKI, SADARWA, da YIN FICE A KODA-YAUSHE, wajen yin
hidima da amfanar da Bakin Mai rahama, da kuma sauran bangarori masu alaka, a
dukkan mashigan Saudia.
Kuma Ofishin da aka hade na Wukala'u; ya kwadaitu wajen
bunkasa aikinsa don samun gamsuwar Mahajjaci a lokacin komawansa kasarsa, ta
hanyar gabatar da hidindimu, wadanda suke cike da marabta da girmamawa, kuma
ofishin ya tsayu da yin ayyuka masu girma domin bunkasa ayyukansa, da kawo
kayan aiki da na'urori na lantarki da injinan dora kaya da jaka, domin saukake
wa Mahajjata, wannan kuma saboda aikin jigilar kayan Mahajjata a wuraren
shigowa da fitansu yana da muhimmanci na musamman.
Kuma wannan Ofishin (hadadde na Wukala'u) ya tafi da
cigaban zamani, ta hanyar amfani da amalanke mai na'ura domin daukar kayan
Mahajjata, musamma a lokacin karuwar adadin Mahajjatan da suke shigowa a lokaci
ko kwanakin cunkoso, kuma yana karo adadinsa da kimanin dari da ashirin bias
dari 120%.
Kamar yadda ofishin ya sanya tsare-tsare wadanda za su bayar da
daman fadada aikinsa, domin ya game daukacin matakan jigilar kayan Mahajjata a
lokacin zuwansu da komawansu.
Kuma Ofishin da aka hade na Wukala'u yana jibintar hidimar
Mahajjata masu komawa gida, ta dukkan hanyoyin ficewa na sararin sama da tudu
da teku, wanda adadinsu shine, mafita biyu na jiragen sama, wato airport na
sarki Abdul'aziz na kasa-da-kasa da ke garin Jiddah, da airport na Amir
Muhammadu bn Abdul'aziz a Madinatul munawwarah, da kuma mafita guda daya ta
cikin teku, mai suna Maina'u Jiddah al'islamiy, da hanyoyi tara na kasa
(ko mota) wadanda sune, Judaidah, Ar'ar, Ruk'iy, Halah, Ammar, Wadiy'ah,
Alab, Khadra'u, Hadiysah, Bad-ha, da Jisr Malik Fahad.
Kuma gwargwadon abinda Shugaban majalisar gudanar da ofishin da
aka hade na Wukala'u; ya bayyanar, lallai yawan Mutanen da suke aiki a
ofishin hidimar Mahajjata, a dukkan mafitan da muka ambata, sun kai kamar mutum
4,200, wadanda suke yin ayyuka mabanbanta domin saukake lamuran Mahajjata.
WASU DAGA AYYUKAN OFISHIN DA AKA HADE NA WUKALA'U, A
LOKUTAN HAJJI
-
Taryo Mahajjata a kafofin shigowa Saudia da marabtarsu da shiryatarsu izuwa ga
gurabensu da aka kebe.
-
Aikin kulawa kan walwalarsu da taimakonsu
wajen biyan bukatunsu, a tsawon kwanakin kasancewarsu a Saudia.
-
Jigilar kayan Mahajjata, da samar da
ma'aikatan da za su yi hakan, a dukkan mashigai (tashoshi).
-
Aiki tare da Hukumomin hajji na kasashe da
kuma mu'assasosin Mudawwafai da Adilla'u, domin shigar da Mahajjatansu ta
dukkan mashiga.
-
Tuntubar gamammiyar hukumar kulawa da motoci
domin kawo Bus-bus da suke jigilar Mahajjata.
-
Manna rasid da ke nuna an karbi kudin da
Mahajjaci ya bayar a jikin passport nasa, domin ya samu hidimar Mudawwifai da
masauki da motocin jigila.
-
Kammala dukkan tsare-tsaren ficewar Mahajjata
daga Saudia bayan sun gama ayyukansu.
-
Bibiyar halin da Mahajjata ke ciki, a
ko-da-yaushe, da taimaka musu wajen kammala mu'amalolinsu na hukuma.
-
Sanar da ofososhin da aka tanadar kan
Mahajjatan da suka bace, a kafofin shigowa Saudia da ficewa.
-
Isar da sako ga mafi kusa daga cikin
cibiyoyin lafiya, a lokacin da wani cikin Mahajjata ya kamu da wata cuta, a
kafofin shigowa ko ficewa.
-
Sanar
wa ressan hukumar hajji da umrah a Jidda, da mu'assar Mudawwafan da abin ya
shafa, sunayen wadanda suka mutu, daga Mahajjata.
Domin Karin bayani/ OFISHIN DA AKA HADE NA WUKALA'U,
HAJJIN SHEKARA TA 1439h
No comments:
Post a Comment