2018/09/13

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 4 Muharram 1440H حسين آل الشيخ









HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 04/MUHARRAM/1440H
daidai da 14/SATUMBA/ 2018M








LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI BN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH





TARJAMAR

ABUBAKAR HAMZA ZAKARIYYA

YANA DAGA SUNAYEN ALLAH; AR-RAKIBU
(من أسمائه تعالى الرقيب)
Shehin Malami wato: Husaini bn Abdul'aziz Al-as-sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DAGA SUNAYEN ALLAH AKWAI AR-RAKIBU, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda wani abu a cikin kasa da kuma cikin sama basu buya a gare shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya a Lahira da Duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, annabi zababbe.
Allah yay i Karin salati a gare shi da kuma iyalansa da sahabbansa ma'abuta cike alkawari da takawa.

Ya ku Bayin Allah!
Ina muku wasici da ni kaina da jin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, saboda takawar Allah Mabuwayi da daukaka, a cikinta akwai tsira daga sharrace-sharrace da kuma musibun Duniya da Lahira.

Yak u Bayin Allah!
Yana daga cikin SUNAYEN ALLAH Mabuwayi da daukaka, AR-RAKIBU (MAI TSARON HALITTU), Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne Allah ya kasance a kanku, Mai tsaro ne" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Kuma Allah ya kasance Mai tsaro ga dukkan komai" [Ahzab: 52].
Don haka, Shi Allah (S.W.T) shine Mai tsaro, wanda ke tsinkayar duk abinda kiraza suka boye, wanda yake tsaye akan kowace rai da abinda ta aikata, kuma Mai kiyayewa wanda babu wani abu da yake buya a gare shi, Wanda ke ganin dukkan halittu, yana ganin halayensu, kuma yana kididdige ayyukansu, Ibnul-kayyim ya ce:

Kuma shine Mai ganin ababen da suke darsuwa, da wadanda sai an lura
Ta, yaya ba zai iya ganin ayyukan da aka aikata da gabbai ba?

Kuma lallai tabbatuwan wannan ma'ana mai girma a cikin zuciyar Bawa zai bashi yakinin dawwamar ilimin Allah, da tsinkayarSa ga zahirin Mutum da badininSa, sai hakan ya haifar masa da tabbataccen ilimi cewa, Allah yana tsaronsa, yana ganinsa, yana jin maganarsa, yana ganin aikinsa, yana tsinkayar aikinsa a kowane lokaci da dakika, da kuma kowane kyaftawar ido;
Saboda Bawa ya san Allah Mai tsaro ne a gare shi, hakan yin bauta ne da sunan Allah AR-RAKIBU (Mai tsaro) ALHAFIZU (Mai kiyayewa) AL-ALIMU (Mai ilimi) ALMUHIDU (Mai kewayewa) ALKHABIRU (Masani Mai labartawa Mai kididdigewa) AL-LADIFU (Masanin abinda ya buya saboda kankantarsa) ALMUHAIMINU (Mai rinjaye) saboda tsinkayarsa ga lamuran da suka buya, da abubuwan da kiraza suka boye. ASH-SHAHIDU (Mai halartar kowane abu) AS-SAMI'U (Mai jin kowane sauti), boyayyunsu da wanda ke bayyane, ALBASIRU (Mai ganin dukkan samammun ababe; kananansu da manyansu, kankanansu da wulakantattunsu), ALKARIBU (Makusanci da ilimkinSa da kowace halitta, ta hanyar saninta da tsaronta da ganinta da gamewar iliminsa);
Don haka,
Duk wanda ya fahimci MA'ANONIN WADANNAN SUNAYEN NA ALLAH KYAWAWA, KUMA YAYI BAUTA A GARE SHI DA ABINDA SUKE HUKUNTAWA, to, ibadar sanin Allah yana tsaron bayi ta gaskiya zata samu a wurinsa, wanda zata kai izuwa/ Zuciyarsa ta rika kulawa da ganin Allah a gare ta, cikin dukkan abinda ke darsuwa a gare ta, da dukkan taku.

Lallai abinda ke wajaba ga Bawa a wannan rayuwar shine/ Zuciyarsa ta kasance cikin kulawa da Allah Mai tsaro madaukakin sha'ani, har ya zama zuciyar ba za ta waiga ba, sai izuwa gare shi, ba za ta ji tsoron kowa ba face shi, sai mutum ya zama mai madawwamin kiyaye umurninSa da haninSa, mai tafiyar da himmarsa ga abubuwan da za su yardar da shi, kuma suke kusantarwa zuwa gare shi سبحانه.
Kuma duk lokacin da Bawa ya san Allah yana tsaronsa (wato, ibadar murakabah) sai hakan ya hukunta masa jin kunyar MahaliccinSa, da girmama wanda ya kage shi, kuma ya hukunta masa tsoron Allah da son Allah, da mayar da lamari ga wanda ya samar da shi, da tawakkali, da kankan-da-kai a gare shi.
Domin gyaruwan gidajen nan biyu (Duniya da Lahira) da samun babban rabo a cikinsu, duka suna rataya ne ga yakinin Bawa, kan UbangijinSa yana tsaronsa, da kirdadon samun yardarSa, da lazimtar Bawa ga bautar Allah, akan sunnar Annabi, tare da lazimtar ikhlasi a gare shi (سبحانه), irin tsarkake niyyar wanda yake da yakinin cewa idan Mutane suna tsaron zahirinsa, to shi kuma Allah yana tsaron zahirinsa ne da badininsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne Allah, babu wani abin da yake boyuwa a gare shi a cikin kasa, ko a cikin sama" [Ali-imrana: 5].
Kuma Allah Mabuwayin sha'ani ya ce: "Kuma ku sani lallai Allah yana sanin abinda yake cikin zukatanku, saboda haka, ku ji tsoronsa" [Bakara: 235].

Kiyayar Allah (da sanin, Allah yana tsaronka) yana hukunta Bawa ya rika yi ma kansa hisabi, yana mai amsawa ga fadinSa (سبحانه): "Ya ku wadanda suka yi imani, ku bi Allah da takawa, kuma rai ta yi dubin abinda ta gabatar wa kanta domin gobe (kiyama), kuma ku yi takawar Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne ga abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].
Ibnul-kayyim ya ce: "Sai Bawa ya yi dubin abinda ya gabatar domin ranar karshe; shin yana cikin ayyuka ne kyawawa, wadanda za su tseratar da shi, ko kuma daga cikin munanan da za su halakar da shi … manufar dai ita ce, lallai gyaruwan zuciya tana kasancewa ta hanyar yi ma kai hisabi, lalacewanta kuma, idan aka kyale zuciya, aka yi ballagaza da ita".

   Ya ku taron Musulmai!
   Lallai kiyayar Allah na hakika (da sanin cewa, Allah yana tsaron bayinsa), yana sanya Bawa kokarin ayyukan da'a, da ficewa daga dukkan abinda ke cin karo da umurnin Ubangijin kasa da sammai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne, su, sun kasance suna yin gaggawan ayyukan alkhairi, kuma suna rokonmu akan kwadayi da fargaba, kuma sun kasance masu khushu'i ne a gare mu" [Anbiya'i: 90].

Don haka, Mumini wajibi ne ya kasance a cikin madawwamin kiyayar UbangijinSa, ta hanyar biyayyarsa da tsarkake niyya (ikhlasi) da bin umurni cikin kamala. Dagane da hane-hane kuma, ya tsawatu, ya kame, ya komo daga rakiyarsu, ya tuba; saboda ba a kiyaye dokokin Allah da haramiyarsa, kuma masu isa da wusuli ga Allah basu isa gare shi (سبحانه) face ta hanyar/ TsoronSa, da kiyayarSa, da fatanSa, da kaunarSa.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga Ubangijinsa yana da Aljannoni guda biyu" [Arrahman: 46].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga UbangijinSa, kuma ya kange kansa daga son rai * to lallai ne Aljannah itace makoma" [Nazi'at: 40].
Ibnul-jauziy ya ce: "Allah Mabuwayi da daukaka, yafi kusa da bawanSa, fiye da jijiyar wuya -har zuwa fadinsa-: Amma zukatan jahilai, su kan ji nisa, don haka suke aukawa cikin sabo, domin da kiyayarsu ga Wanda yake halarce kuma yake ganin bayi ta tabbatu, to da sun kame hannayensu daga fadawa cikin laifuka".
An ce wa wani daga cikin Magabata, cewa: "Menene abinda zai taimake ni wajen runtse idanu? Sai ya ce: Shine saninka cewa, lallai kallon mai kallonka (wato Allah) yana rigayar kallonka ga wanda ka ke kallonta".
Kuma a irin wannan ma'anar ne Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- yake tunatar da mu, Mutanen nan guda bakwai wadanda Allah zai sanya su a karkashin inuwarsa a ranar da babu wata inuwa sai tasa, a inda ya ce: "Jinsi bakwai, Allah zai sanya su karkashin inuwarsa ranar da babu wata inuwa face tasa, Shugaba adali, da saurayin da ya rayu cikin da'ar Allah, da Mutumin da zuciyarsa take rataye da Masallatai, da Mutane biyu da suka yi soyayya domin Allah; suka hadu akan haka, suka rabu akan haka, da Mutumin da wata mata ma'abuciya matsayi da kyawu ta kira shi (domin lalata) sai ya ce, lallai ni ina tsoron Allah, da Mutumin da ya yi wata sadaka sai ya boye ta, har hannunsa na hagu bai san me damansa ta bayar ba, da Mutumin da ya ambaci Allah a kebe, sai idanunsa biyu suka zubar da hawaye", Bukhariy da Muslim.

Sanin Allah yana tsaron bayi (wato, murakaba) yana tsarkake daidaikun Mutane daga fadawa cikin laifuka da ayyukan haramun, kuma yana tsaftace zukata daga abubuwan da suke sanya su cikin dauda, kuma suke lalata su, kuma da aikata hakan ne, za a samu al'umma ta gari, wanda Allah yake nufinta da fadinSa: "Kuma Muminai maza da muminai mata, sashensu majibinta sashe ne, suna umurni da kyakkyawa, suna hani daga abin ki, kuma suna tsayar da sallah, suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, kuma wadannan lallai Allah zai musu rahama", [Tauba: 71].
Don haka, kiyayar Allah (murakabarsa) tana samar da al'umma tsarkakakku daga dauda, masu wofinta daga aikata miyagun ayyuka, wanda al'ummarsu suke sifantuwa da dukkan abu mai falala, suke yin rayuwa yarjejjiya, masu taimakakkeniya akan ayyukan biyayya da takawa, suna masu riko da igiyar Allah, masu hade kansu akan kalmar Allah, suna watsar da dukkan rabuwar kai da kungiyanci, suna watsar da kowane manhaji ko salo na wuce iyaka da guluwwi, suna yin rayuwa akan ginshikan addininsu, da abinda ya kunsa na adalci da sauki da sassauci da akidar tsakaitawa da taushi da tausasawa da soyayya, Allah Ta'alah yana fada a inda yake sifanta Muminai: "Masu tawali'u ga Muminai, masu izza akan kafirai", [Ma'ida: 54]. 
Suna rayuwa karkashin tsaron Ubangijinsu, cikin istikama da kawo gyara, amintattu, masu samar da zaman lafiya, suna bautar Ubangijinsu, kuma suna gode wa Mahaliccinsu, kuma suna hada kansu cikin soyayyar imani, da kauna irin ta musulunci, tambarinsu shine: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10].
Kuma Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Kada ku yi hasada, kuma kada ku yi najsh (a cikin kasuwanci), kuma kada ku yi kiyayya, kuma kada sashenku ya yi ciniki akan cinikin sashe, kuma ku kasance –Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna, saboda Musulmi dan'uwan Musulmi ne, baya zaluntarsa, baya tabar da shi, baya raina shi. Takawa a nan take, sai ya yi nuni ga kirjinsa, har sau uku".
        Don haka, sai ku tsare Allah Mabuwayi da daukaka, wajen bayar da hakkokinSa (سبحانه), da kuma bayar da hakkokin bayinSa, domin ku rabauta ku samu babban rabo.

        Mu da muke magana akan: Tsare Allah Mabuwayi da daukaka, to babu makawa, dole ne sai mun mai da hankali kan wani lamari wanda dole sai mun fadakar akansa, wannan kuma shine:
Lallai wajibi na dole akan masu da'awa da maluma, shine su tsare Allah (سبحانه) cikin abinda suke fitarwa ga Mutane,
kuma dole su sani cewa lallai FATAWA lamarinta yana da hatsari, kuma wajibi ne a tsarkake Allah da ikhlasi a cikinta, da yin gaskiya ma Allah (سبحانه), da tsare shi a cikin sirri da kuma a bayyane.
        Kuma yana wajaba akan kowa, kiyayar yin fatawa ta daidaiku cikin lamuran da suke shafar dukkan al'umma, da sababbin ababen da suke da gamewa ga daukacin al'umma, wadanda baya halattan ayi gaggawa a cikinsu, ko sauri, A'a, babu makawa, sai anyi a taka-tsantsan, tare da komawar gaskiya zuwa ga Allah (سبحانه) kan ya kimsa mana ko ya mana ilhamar bin daidai.
        Kuma babu makawa, sai an lura da abubuwan da lamuran za su haifar, tare da kula da ka'idodin shari'a da manufofinta masu gamewa, da yin nazari mai zurfi akan ka'idar/ Janyo maslaha da kokarin yawaita ta, da tunkude barna, da bin hanyoyin karanta su, tare da yin bakin kokari, kai da fata, wajen hadin kan al'umma da haduwar kansu, da nisantar dukkan abinda zai yi mummunan tasiri akan hakan, koda ta bayan fage ne.
        Kuma babu makawa, a cikin wadannan fatawowin a rika komawa ga Maluma tabbatattu cikin ilimi, kari akan abinda suke da shi na sanin jiya da yau, da zurfin hangen nesa.
        Kuma babu makawa, sai an bada kulawa ga fatawowin da jama'a suke fitarwa; wato wadanda majami'an fikihu na Maluman al'umma suke fitarwa, masu zuwa bayan shawari irin na fikihu, da nazarin wurare, da ingantaccen fahimtar mas'alolin, da nazari mai zurfi ta bangarorin fikihu mai asali da dalili, a cikin sharuddan ijtihadi gaba daya.
        Kuma irin wadannan fatawowin, tabbas za su kai zuwa ra'ayin da yafi maslaha, wanda kuma da shi (da izinin Allah) halaye za su gyaru, lamura kuma su daidaitu.
        Kuma, matukar ba a kula da wadannan dokokin ba, al'umma zata auka cikin yawaitar kace-nace, wanda zai kai ga munanan akibar da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya tsawatar akansu, a cikin fadinSa: "Har idan be bar wani Malami (na hakika) ba, (duk sun mutu), sai Mutane su riki wasu jagorori jahilai, sai a tambaye su, sai su yi fatawa ba da ilimi ba, sai su bata, su batar".

Muna rokon Allah Mabuwayi da daukaka ya tseratar da mu daga hakan
Kuma muna rokon Allah Mabuwayi da daukaka, ya datar da mu zuwa ga abinda yak e sonsa kuma ya yarda da shi, lallai ne shi akan kowane abu Mai iko ne.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
   Godiya ta tabbata ga Allah, yabo mai yawa mai dadi mai albarka a cikinsa.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa.
Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da kuma sahabbansa.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai!
Ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, domin itace wasiyyar Allah ga na farko dana karshe.

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai ne, kuna cikin watan Allah ALMUHARRAM, wata mai tarin girma, sai ku nuna wa Allah alkhairan da suke cikin zukatanku, Muslim ya ruwaito daga Abu-hurairah, daga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-, ya ce: "Mafificin azumi bayan Ramadhana shine a cikin watan Allah Almuharram".

   Kuma mustahabbi ne yin azumin ranar Ashurah, wanda kuma shine yinin goma, daga watan Allah Almuharram, an ruwaito daga Abu-katadah, ya ce: "An tambayi Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- dangane da azumtar ranar Ashura, sai ya ce: Yana kankare zunubin shekarar da ta shude".
A wata riwaya kuma: "Azumtar yinin Ashura ina tsammanta wa Allah zai kankare zunuban shekarar da take gabaninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma sunna ne, ayi azumin ranar tara (Tasu'ah) tare da Ashurah, saboda fadin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- cewa: "Idan har na wanzu zuwa shekara ta gaba, to lallai zan yi azumin ranar tara", Muslim ya ruwaito.

Kuma babu abinda ya inganta daga cikin ayyuka na mustahabbi wadanda aka kebance su da ranar Ashura, banda abinda ya zo daga shari'a, wanda kuma shine muka ambata, kamar yadda Maluma ma'abuta tahkiki suka nassanta.

   Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...