2018/03/29

حسين آل الشيخHUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم JUMA'A, 13RAJAB1439H








HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
 JUMA'A, 13/RAJAB/1439H
Daidai da 30/MARIS/2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ AL-AS-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA





بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; yabo mai yawa mai dadi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu ke so, kuma kamar yadda ya yarda.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya saI Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; a Lahira da Duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa; Annabi zababbe, kuma Manzo wanda Allah ya zabo.
Ya Allah ka yi karin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta falala da takawa.
Bayan haka;

Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah, kuma ku masa da'a; domin idan mutum ya yi da'a a gare shi, Sai ya jiyar da shi dadi, ya kuma Allah ya yardar da shi.

Ya ku musulmai
Kyawawan halaye alamar sa'idar bawa ne da samun nasararsa da rabautarsa, kuma ba a iya janyo alkhairi, da abinda yafi dabi'u kyawawa, ko ayyuka managarta.

Lallai nassoshin wahayin Kur'ani da hadisai, sun zo ta hanyoyi masu yawa (na tawaturi), kan kiran halittu zuwa ga bin hanyar daidai, da riko da kyawawan dabi'u.
Yana daga sifofi masu girma, da kyawawan halayen fiyayyen halittuصلى الله عليه وسلم  Abinda UbangijinSa Mabuwayi da daukaka ya siffatanta shi da su cikin fadinSa: "Kuma lallai hakika, kai kana kan halayen kirki masu girma" [Kalam: 4].
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai ya takaice sakon da'awarsa a cikin ka'idodinta, a inda yake cewa: "Lallai an turo ni ne, domin na cike kyawawan halaye", Ahmad da Malik suka ruwaito, kuma hadisi ne ingantacce a wurin ma'abuta ilimi.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya fada a inda yake kira domin riko da kyawawan halaye: "Ka ji tsoron Allah a duk inda ka kasance, kuma ka biyar da mai kyau a bayan mummuna, domin ya goge shi, kuma ka yi mu'amalla da mutane da kyakkyawan halaye". Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne, mai kyau ingantacce.

        Kyawawan dabi'u halayya ne da suke kusantar da bawa ga MajibincinSa, suke daukaka darajojinsa, suke girmama ladansa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka tunkude cutarwa da abin da ya fi kyau, sai wanda akwai kiyayya a tsakaninka da tsakaninsa ya zama kamar Majibinci Masoyi * Kuma babu wanda zai samu hakan sai wadanda suka yi hakuri, kuma babu mai samun hakan face ma'abucin rabo mai girma", [Fussilat: 34-35].
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mumini wanda yafi cikar imani, shine wanda ya fi kyan hali, Kuma zababbu a cikinku sune wadanda suka fi alkhairi ga matansu", Ahmad da Tirmiziy ya ruwaito, kuma yace: hadisi ne hasan sahih.
        Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai mumini da kyan halinsa yana riskar darajar mai azumi da tsayuwar dare", Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Ibnu-Hibbana ya inganta shi.

        Ya ku Muminai!
Ma'abucin tsarkin hali, zai samu martaba madaukakiya, da matsayi mai girma, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce:  "Lallai wanda -a cikinku- yafi soyuwa a wurina, kuma yafi ku kusancin wurin zama daga gare ni a ranar kiyama, shine wanda yafi ku kyan hali", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace hadisi ne hasan.
Kuma an tambayi Annabi –صلى الله عليه وسلم- akan abinda yafi yawaita shigar da mutane Aljannah, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyakkyawan halayya", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce, hadisi ne ingantacce garibi.

Kyakkayawan halaye suna daga sabbuban samun yardar Allah Mai rahama, da nauyaya mizani ko ma'auni, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu abinda yafi nauyi ga ma'aunin bawa mumini a ranar kiyama, fiye da kyawawan halaye...".
Kuma Muslim ya ruwaito, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Biyayya, itace kyakkyawar halayya".

Ya ku, 'yan'uwana Musulmai:-
Idan kun fahimci abinda ya gabata, to lallai, kyakkyawan hali, ya game dukkan zantukan harshe masu kyau, da kuma ayyuka managarta; don haka; kyawawan halaye hanya ce yardadda ga shari'a, da dabi'a, a cikin ayyuka gaba daya, da mu'amaloli dukkansu.
Kyakkyawan hali shine yin aiki da ladduban shari'a, wadanda suka zo cikin nassoshin ayoyi da hadisai; na zantuka masu dadi, da ayyuka masu kyau, da sifofi ababen yabo, da halayya madaukaka.
Kyakkayawan hali, shine dukkan aikin da mutum zai aikata, sai masu jituwa da shi su yawaita, masu adawa da shi su karanta, sai kuma lamura masu wahala su saukaka, kuma da kyakkyawan hali zukatan da suka cike da bakin ciki suke yin taushi; domin matakan ma'abuta kyakkayawan halaye, a cikin mu'amaloli gaba daya masu kyau ne, da taushi, da kyautatawa, tare da sifantuwa da ababe masu falala da sauran halayya na girma. Annabi –صلى الله عليه وسلم- yace: "Kada ka raina wani abu daga kyawawan aiki, koda kuma ka hadu da 'dan'uwanka da sakakkar fiska ne", Muslim ya ruwaito.

Kuma yana daga cikin misalan kyawawan halaye, ba da nufin kididdige su ba; Shumfuda fiska, da sake ta, da sanya ta cikin walwala, da yin kyauta, da kamewa daga cutarwa, da juriyar abinda ka iya kasancewa daga mutane; na munanawa da kura-kurai.

Kuma yana daga cikin kyawun hali, Kame fushi, da nisantar duk abinda bashi da amfani, da nisantar aibantawa, da husuma, da jayayya.
Kyakkyawan hali yana nufin mutum ya kasance mai biyayya, mai jin-kai, mai karamci da kyauta, mai sauki, mai bayarwa daga zuci da hannu; ba marowaci ko mai mammako ba, mai hakuri da godiya, mai yarda da juriya, mai taushi da tawali'u, mai kamewa, da rashin boyo, mai tausayi, mai saukin hali, mai taushi cikin dabi'arsa, mai yafiya cikin mu'amalolinsa, Allah Ta'alah ya ce: "Kada ka karkatar da kumatunka ga mutane,kuma kada ka yi tafiya a cikin kasa kana mai nuna fadin rai", [Lukman: 18].
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin wanda wuta ta haramta a gare shi, ko ya haramta ga wutar ba, Tana haramta ne, ga dukkan mutum mai kusanci da sauki ko taushin mu'amala", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace, hadisi ne hasan garib.
       
        Yana daga Kyan hali: Tace ko tsaftace laffuza, da kyautata zamantakewa, da taushin mu'amala, da nisantar wauta, da abinda bai dace ba, ko abinda bashi da kyau. Kuma ma'abucin kyan hali, a majalisosin zama ba a kiyaye lokacin da zai aikata ko ya fadi abin aibi, ko ya yi tuntube, ko kuskure. Abdullahi bn Abbas –رضي الله عنه- ya ce: "Tsakaitawa da natsuwa da kyawawan dabi'u, bangare ne daga bangarori ashirin da biyar na annabta".

        Ma'abucin madaukakan halayya, (a kullum) zaka same shi natsattse, mai hakuri, ma'abucin tsanaki da bin abu a sannu-sannu, kamamme, madaukaki, ba mai kaushi ko tsinuwa ba, ba mai shewa ko ihu ba, ba mai gaggawa, ko alfasha ba.
Koyaushe yana maida mu'amalar da mutane suka masa da abinda yafi kyau, yafi falala, kuma yafi kara kusanci da biyayya ga Allah da takawa, wanda shine abinda yafi kamantaccewa da ababen da ake yabo, kuma suke kaiwa ga daukakar mutane.

        Yana daga mafi girman nau'ukan kyawawan halaye halin kunya, kamar yadda Ibnul-kayyim yake fada: "Kunya itace mafificinsu, wanda kuma ta fi su girman matsayi". Uwar muminai; A'ishah –رضي الله عنه- ta ce: "Shugaban kyawawan halaye shine, Kunya".

        Kuma yana daga mafifitan halayya, wadanda suka fi kyau: Halin fifita mutane, da suturce ko boye aibinsu, da bayar da kyauta, da yin murmushi a lokacin saduwa da mutane, da maida hankalinka ga mutumin da ke maka zance, da bubbuda wa mutane domin su samu wurin zama, da yada sallama da yawaita yinta, da yin musabahar hannu da mutane a lokacin ganawa, da yin sakayya akan kyautatawar mutane da fiye da abinda suka maka, da kokarin kubutar da rantsuwar musulmi, da kawar da kai ga abinda ba damuwarka ba, da wautar masu wauta; cikin hakuri da hikima.

        Haka suma sauran ayyukansa, za su zama masu kyau, ta yadda zai sanya babba daga cikin musulmai ya zama kamar uba a gare shi, karaminsu kuma kamar 'da, matsakaicinsu kuma kamar 'dan'uwa. Kamar yadda wannan mawakin ke cewa:
Yana ganin musulmai suna da hakkoki akansa
Kamar aikin uba, mai tausayi da jin-kai

        Ya tattara daukacin ma'anar ka'idar halayya, wannan zance wanda ke da kankanin lafazi, yake da girman ma'ana, daga fadinsa –صلى الله عليه وسلم-: "'Dayanku ba zai yi imani ba, face ya so wa 'dan'uwansa abinda ke so ga kansa".

        Allah ya amfanar da mu da abinda muka sani, kuma ina fadan wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da kuma sauran musulmai, daga dukkan zunubai, sai ku nemi gafararSa; lallai shi Mai yawan gafara ne Mai jin-kai.


HUDUBA TA BIYU
        Ina yin yabo ga Ubangijina kuma gode masa, ina tuba zuwa gare shi kuma ina neman gafararSa,
        Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai yake bashi da abokin tarayya
        Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa
        Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa

        Bayan haka:
Ya kai musulmi, Ka kasance daga cikin ma'abuta kyawawan halayya, wanda yake yin sabo da mutane, suma suke sabawa da shi, domin ya zo cikin hadisin da Ahmad ya ruwaito shi daga Annabi –صلى الله عليه وسلم-, ya ce: "Mumini akan yi sabunta da shi, kuma babu alheri ga wanda baya sabo, ko ayi sabunta da shi".

        Ya ku bayin Allah
Wajibin da ya zama dole, shine kada muyi bautar Allah, face da abinda dalilin Kur'ani da sunnah suka zo akansa, don haka; Duk wanda ke riya cewa watan Rajab (wanda muke ciki) ya kebantu da wasu falaloli, ga ibadodi, to lallai babu wani abu daga shari'a da ta zo da hakan, kamar yadda maluma muhakkikai (na-yankan shakku) suka tabbatar, kamar Ibnu-Hajar, da Ibnu-Rajab, da Nawawiy, da Ibnu-Taimiyyah, da 'Dar'dushiy, da wasunsu dayawa.

        Sai ku yi salati da sallama, ga Muhammadu




No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...