2018/04/12

ADAWAR SHAIDAN GA DIYAN-ADAMU 27 Rajab 1439 daidai da 13 Afrilu 2018 ta dr Abdulmuhsin












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 27/RAJAB/1439H
daidai da 13/AFIRILU/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
GABAR SHEDAN GA 'YAN ADAM
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: GABAR SHEDAN GA 'YAN ADAM, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi a sirrace da a bayyane.

        Ya ku musulmai …
        Duniya gidan ibtila'i ne da jarabawa, kuma mafi girman bala'I shine wanda ya yanke alakar bawa da UbangijinSa da kuma addininSa.
        Kuma a duniya babu abinda yafi tsananin fitina ga halittu fiye da Iblis da rundunoninsa; saboda Iblisu shine abokin gaba na farko wanda yafi girma, kuma shine kuma daga wurinsa ne mafarin kowane laifi da sabo.
        Adawarsa gag a 'yan-Adam tana da tsanani kuma a bayyane take; saboda a tarihi da gaba babu makiyan da suka fi shi bayyanar da adawa; Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne Shaidan ga Mutum, hakika makiyi ne bayyananne" [Yusuf: 5].
Shaidan makiyi ne wanda baya yin rauni kuma baya yanke adawa, kuma rufa-rufa ko tausasawa baya amfani a gare shi.
Ya yi rantsuwar yin kiyayya ga dayawa daga 'ya'yan-Adam, Shaidan "Ya ce: to insa rantsuwa da halakarwar da yi mini! Lallai ne zan zauna musu a tafarkinka madaidaici * sa'annan kuma zan je musu daga gaba gare su, da kuma baya gare su, da kuma jihohin damansu, da jihohin hagunsu, kuma ba za ka samu mafi yawansu masu godiya ba" [A'araf: 16-17].
Kuma tushen abinda ya dago wannan kiyayyar, shine hassada, saboda Allah ya daukaka annabi Adamu, ya kuma bashi falala, ta yadda ya halitta shi da hannayensa biyu, ya kuma shigar da shi AljannarSa, ya ilmantar da shi dukkan sunaye, ya sanya Mala'iku suka yi masa sujada, ya karrama zurriyarsa a bayansa, To sai Iblisu ya bayyanar da kiyayyarsa a gare su, ya ce: "Shin ka ganka, wanga da ka fifita a kaina, lallai ne idan ka jinkirta ni zuwa ga ranar Kiyama, zan karkatar da zurriyarsa, face kadan" [Isra'i: 62].

Sai zuciyar Iblisu ta kimsa girman kai wanda shi ke jagoranci ga kowane cuta da sharri, sai yak i yin sujada ga Adam, ya ce: "Ni na fi shi alkhairi; domin ka halitta ni daga wuta, shi kuma halitta shi daga tabo", [A'araf: 12].
Kuma korarsa daga Aljanna da nesatar da shi, shi ya dauke shi ga bayyanar da kiyayya kuma ya shelanta ta, "Ya ce: ina rantsuwa da buwayarka, lallai zan batar da su gaba-daya" [Sad: 82].
Daga nan sai ya kulla makida ga annabi Adamu da Hawwa, ya kawata musu sabon Allah, har aka fitar da su daga Aljanna. Kuma Iblisu bai gushe ba, akan halinsa da kaidinsa yana cutar da mutane a zahiri da ma'ana; cikin akidunsu da ibadodinsu, da jikinsu da rayukansu, da dukiyoyinsu da 'ya'yansu, da abincinsu da abin shansu, da barcinsu da tashinsu, da lafiyarsu da cutarsu, da sauran dukkan halayensu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Shaidan yana halartar dayanku cikin kowane abu na sha'aninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Ta bangaren AKIDU Gayar Iblisu, shine lalata wa mutane su, Allah (تعالى) ya ce: "Ashe ban yi alkawari da ku ba, Ya 'Diyan-Adamu, cewa kada ku bauta wa Shaidan, lallai shi makiyi ne a gare ku bayyananne" [Yasin: 60].
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan Iblisu ya wayi gari, sai ya tura rundunoninsa, sai ya ce: Wanda ya batar da musulmi a yau, zan sanya masa fular sarauta (kan sarki)",  Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi.
Kuma Iblisu ba zai gushe yana sanya shakku ga bawa har sai ya sa shi sakka ga Ubangijinsa, yak um afitar da shi daga addininSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Shaidan zai zo wa dayanku, sai y ace: Way a halitta kaza? Wa ya halitta kaza? Har y ace masa: Way a halicci Ubangijinka, Idan bawa ya iso ga haka, to ya nemin tsarin Allah, ya kuma hanu" Bukhariy da Muslim.

Kuma Allah ya halitta bayi akan fidirat Tauhidi, sai Shaidanu suka batar da su, Allah (تعالى) ya fada cikin hadisin kudusiy: "Lallai ne Ni na halicci bayina dukkansu akan mikakken addini, kuma lallai Shaidanu sun zo musu, sai suka kautar da su daga addininsu, suka rika haramta musu abinda na halatta musu, suka rika umartarsu da yin shirka a gare ni, da abinda ban saukar da hujja akansa ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma dukkan mai bautar wanin Allah, to lallai yana rokon Shaidan ne yan bauta masa, Allah (تعالى) ya ce: "Ba kowa suke roko, baicinsa ba face gumaka da sunan mata, kuma ba ga kowa suke bauta ba face Shaidani mai tsaurin kai" [Nisa'i: 117].
Kuma rana tana fudowa tana faduwa a tsakanin kafo biyu na Shaidan, a lokacin da masu bauta mata suke yin sujjada a gare ta.

Kuma yana daga LALATA AKIDA wanda Shaidan yake yi, koyar da sihiri, domin wanda ya aikata sihiri ya kafirta, da mutumin da ya je wajen mai sihirin don a masa sihiri, Allah (تعالى) y ace: "Sai suka bi abinda Shaidanu suke karantawa a lokacin mulkin annabi Sulaimanu, kuma Sulaimanu bai kafirta ba, Saidai shaidanu sune suka kafirta; suna karantar da mutane sihiri" [Bakara: 102].
Aikin "NUSHRAH" shine kokarin warware sihiri, da wani sihirin kwatankwacinsa, kuma lallai yana daga ayyukan Shaidan.
Kuma bokaye sun sayar da addininsu ne ga Shaidan; sai Shaidan ya rudar da su, da cewa zai taimake su, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Mala'iku suna sauka a cikin girgije, sais u ambaci lamarin da aka hukunta a sama, Sai Shaidanu su yi satar ji; sais u ji wannan lamarin, daga nan sais u yi wahayinsa zuwa ga bokaye, sai su kuma su yi karya guda dari daga wurinsu su hada da ita", Bukhariy ya ruwaito shi.
A karshen zamani Dajjal zai fito, "Sai Allah ya tayar da wasu Shaidanu tare da shi suna Magana da mutane", Ahmad ya ruwaito shi.
Ba za a yi kiyama ba, sai akan ashararn halittu; Sai Shaidan ya umarce su da yin bautar gumaka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sai ashararun mutane su saura, da karanci hankali da wauta irin na dabbobi masu farauta, basu sanin aiki mai kyau, kuma basu kyamar mummuna, Sai Shaidan ya zo musu cikin wata sura, sai ya ce: Shin ba za ku amsa ba? Sai su ce: zuwa ga me kake umartarmu? Sai ya umarce su da bautan gumaka", Muslim ya ruwaito shi.

AMMA KAIDIN SHAIDAN CIKIN IBADODI To lallai ba zai gushe da ma'abucin ibada ba, face ya bata masa bautarsa;
Sai ya rika sanya bawa sakku cikin tsarkinsa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan Shaidani ya zo wajen dayanku, sai yace masa: Lallai ka karya alwalarka, to ya ce: ka yi karya", Ahmad ya ruwaito shi.

Kuma idan musulmi ya tashi domin yin sallah, sai shaidan ya shiga tsakaninsa da sallarsa da waswasinsa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne dayanku, idan ya tashi domin yin sallah, sai Shaidan ya zo masa, domin ya rikirkita masa ita, har ya zama bai san raka'a nawa ya sallata ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan Shaidan ya samu gibi a cikin sahu, to sai ya shiga cikinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku tottoshe gibi; domin Shaidan yana shiga tsakaninku", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma waigawa a cikin sallah yana daga kaidinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Waigawa wafta ne wanda Shaidan ke waftarsa daga sallar bawa", Bukhariy ya ruwaito shi
Kuma Shaidan yana da tsananin kwadayin yaga ya yanke wa bawa sallah, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan dayanku zai yi sallah, to ya yi sallah zuwa ga sutra, sai ya kusance ta, domin kada Shaidan ya yanke masa sallarsa", Hakim ya ruwaito shi.
Kuma "Babu mutane uku a wata alkarya ko kauye, wanda ba a tsayar da salla a cikinsu, face Shaidan ya rinjaye su". Abu-dawud ya ruwaito shi.

Kiyayyar Shaidan ga mutane, lallai bata da iyaka;
Ta yadda ya ke tarayya da mutane cikin abincinsu da abin shansu, da auratayyarsu, Allah Mabuwayi da dauka ya ce: "Kuma ka yi tarayya da su. Cikin dukiya da 'ya'ya" [Isra'i: 64]. Sai shaidan ya yi jayayya da 'Dan-Adam cikin abincinsa; ya ci tare da shi, matukar bai ambaci sunan Allah ba, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Shaidan yana halatta abinci, matukar ba a ambaci sunan Allah akansa ba", Muslim ya ruwaito shi.
Sai kuma Shaidan ya rika cinye abinda ya fadi daga Mutum, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan loma ta fadi dayanku, to ya gusar da abinda ya makale mata na dauda, sa'annan ya cinye ta, amma kada ya barta ga Shaidan", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan dayanku ya zo kwanciya da iyalinsa sai Shaidan ya ta aikin cutar da su, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Da 'dayanku idan ya zo saduwa da iyalinsa zai ce: Ya Allah, ka nesatar da Shaidan, kuma ka nisantar da Shaidan daga abinda zaka azurta ni, Idan har 'da ya shiga tsakaninsu, to Shaidan ba zai cutar da shi ba, kuma ba za a bashi iko akansa ba", Bukhariy ya ruwaito shi.
Haka kuma Shaidan yana jayayyar wurin zama da mutum, matukar bai ambaci sunan Allah a gidan ba; Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan 'dayanku zai shiga gidansa, sai ya ambaci Allah a lokacin shigansa, da lokacin cin abincinsa, Sai Shaidan ya ce: Bani da wurin kwana a wurinku, kuma bani da abinci. Idan kuma ya shiga bai ambaci sunan Allah ba a lokacin shigansa, sai Shaidan ya ce: Na samu wurin kwana. Kuma idan bai ambaci sunan Allah a wurin cin abincinsa ba, sai ya ce: Na riski wurin kwana, da abinci", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan farkon dare ya zo, sai Shaidanu su yadu, domin cutar da bayi, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan dare ya shigo, ko kuka yi yammaci, to ku rike yaranku kanana; domin Shaidanu suna watsuwa a wannan lokacin", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma Shaidan baya yanke kiyayyarsa, kuma baya kosawa, saboda baya barin har mai barci, daga cutarwarsa, Sai "Ya kulla kulli guda uku a karshen kayin dayanku, idan ya yi barci; sai kuma ya dauri kowane kulli; da fadinsa: kana da dare mai tsawo; sai ka yi barci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma idan bawa ya yi barci bai yi salla ba, Sai Shaidan ya yi fitsari a kunnensa; don walakanta shi; saboda an ambaci wani Mutum a wurin Annabi –صلى الله عليه وسلم- da cewa, ya yi barci har ya wayi gari, sai ya ce: "Wannan mutum ne, wanda Shaidan yay i fitsari a cikin kunnuwansa, ko kunnensa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana yin barci a cikin karan hancin mai barci, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan dayanku ya tashi daga barcinsa sai ya zo alwala, to ya fyace hanci sau uku, domin Shaidan yana kwana  a cikin karan-hancinsa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma duk abinda ya karu na wurin shumfudi, to na Shaidan ne, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shimfudi n farko na miji ne, wani shimfidin kuma na matarsa, wani shimfudin na bako, shimfidi na hudu kuma na Shaidan ne", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan ba zai bar dimautar da mutum a cikin barcinsa ba, ko ya rika tsoratar da shi a cikin mafarke-mafarkensa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mafarki daga Allah ne, kwashe-kwashen mafarki kuma daga Shaidan ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Kuma Shaidan yana kokarin kawo rarraba a tsakanin mutane, domin ya bata tsakaninsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Shaidan ya debe tsammanin masallata za su masa bauta a tsibirin larabawa, saidai zai yi ta zuga a tsakaninsu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma farkon wannan kawo rarrabar yak an kasance a tsakanin miji da matarsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "lallai Iblisu yana sanya gadon al'arshin mulkinsa a saman teku, sa'annan sai ya aike sojojinsa, wanda zai fi kusancin wurin zama da matsayi a cikinsu a wurinsa shine wanda ya fi tsananin fitinarwa; dayansu zai zo sai y ace: Na aikata kaza da kaza, sai Shaidan y ace: baka aikata komai ba. Ya ce: Sai dayansu ya zo yace, Ban bar wane ba, sai da na rabe tsakaninsa da matarsa, Ya ce: Sai ya kusantar da shi jikinsa, y ace da shi, Madalla da kai", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma shaidan baya jin-kan yaro domin karancinsa; saboda farkon haihuwar mutum shaidan yana yin cakala a kuibinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu wani yaron da za a Haifa, face Shaidan ya taba shi a lokacin haihuwarsa, sai ya kwaye baki da ihu; sakamakon Shaidan ya bata shi, sai dai Maryam da 'danta", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana gudu a jikin 'dan-Adam ta magudanar jinni, kuma babu wani daga cikinku, face an wakilta masa abokin gaminsa daga Aljanu" Muslim ya ruwaito shi.

Kuma Shaidan yana shiga cikin jikin mutane, sai Aljanu su buge mutum, Allah (سبحانه) ya ce: "Wadannan da suke cin riba, basu tashi sai kamar wanda bugun shedan ke buge su na shafa", [Bakara: 275]. Shaikhul Islami –رحمه الله- ya ce: "Babu –a cikin jagororin musulmai- wanda ke musanta cewa Aljani yana shiga jikin mai farfadiya da waninsa. Kuma duk wanda ya yi inkarin hakan, ko ya yi da'awar cewa, wai shari'a tana karyata hakan, to hakika ya yi karya ga shari'ar, saboda a cikin dalilai na shari'a akwai abinda ke kore hakan".

Kuma Shaidan ba zai gushe yana cutar da 'diyan-Adamu ba, har zuwa lokacin magagin mutuwa, saboda ya zo cikin addu'oin Annabi –صلى الله عليه وسلم- cewa: "kuma lallai ina neman tsarinka; kada Shaidan ya yi wasa da hankalina a lokacin mutuwa", Nasa'iy ya ruwaito shi.

Shaidan a kaidin da yake kulla wa ga dan-Adam yana da salo-salo, da hanyoyi daban-daban masu yawa; sai ya kawace musu barna, yana mai kyautata a idonsu, yana sa musu wahamin cewa hakan gaskiya ne; wannan ya sanya a ranar yakin badar Shaidan ya kawace wa mushirkai aikinsu, Allah (تعالى) ya ce: "A lokacin da Shaidan ya kawace musu ayyukansu, kuma ya ce: babu mai rinjaye a gare ku a yau, daga mutane, kuma ni makwabci ne gare ku" [Anfal: 48].
Ibnul kayyim –رحمه الله- ya ce: "Yana daga makidar Iblis, lallai shi ya kan sihirce hankali koyaushe, domin ya masa makida, kuma babu mai kubuta daga sihirinsa a yau, sai wanda Allah ya nufa; sai Shaidan ya kawace masa aikin da zai cutar da shi, ta hanyar sanya masa tunanin cewa hakan yana daga ababe mafi amfani".

Kuma yana daga kawacewar Shaidan kiran ayyukan sabo bada sunayensu ba, kamar yadda ya ce wa Adam: "Shin in nuna maka bishiyar tabbata, da mulkin da baya tsufa? " [Daha: 120].

Kuma yana daga kaidinsa, lallai shi ya kan shiga wa rai ta kofar da take sonsa take karkata zuwa gare shi, sai y ace wa Adamu da Hawwa'u: "Ubangijinku bai hane wannan bishiyar ba, sai domin kad ku kasance mala'iku biyu, ko ku sance daga cikin masu dawwama" [A'araf: 20], Kuma sai ya yi ta rantsuwa akan haka, Allah (تعالى) ya ce: "Sai ya musu rantsuwa su biyun cewa lallai ni a gare ku ina cikin masu nasiha", [A'araf: 21].
Kuma sai ya yi ta alkawari, yana sanya buri, alhalin shi mai yaudara ne cikin haka, "Yana yi musu alkawari, kuma yana sanya musu guri, alhalin Shaidan baya musu wani wa'adin komai face rudi", [Nisa'i: 120].
Kuma yana rudin ne da gurace-guracensa na karya, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne alkawalin Allah gaskiya ne, kada rayuwar duniya ta rude ku, kuma kada marudin nan ya rude ku game da Allah", [Lukman: 33].
Kuma yana tsoratar da salihan mutane da rundunoninsa masu rauni, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai wancan Shaidan ne yake tsoratar da ku masoyansa", [Ali-imrana: 175].
Kuma yana hana su ciyarwa cikin yardarm Allah, kuma sanya musu waswasin cewa yana janyo talauci, Allah (تعالى) ya ce:  "Shedan yana alkawarta muku talauci, kuma yana umartarku da alfasha", [Bakara: 268].
Yana janyo bacin rai ga bayi, kuma yana bude musu nadama da ciza-dan yatsa akan abinda ya gabata, kamar fadin mutum: Da na aikata kaza, da ya zama kaza, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "saboda Kalmar danasani tana bude aikin Shaidan", Muslim ya ruwaito shi.

Akan gada ko tungar sha'awowi Shaidan ke kaiwa zuwa ga samun burinsa; saboda "Namiji ba zai kebe da mace ba, face Shaidan ya zama na ukunsu" Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana kiran mutane zuwa ga ficewa daga kunya, da yin watsi da lullubi da kamewar maza da mata, Allah (سبحانه) ya ce: "Sai Shaidan ya sanya musu waswasi su biyun; domin ya bayyanar da abinda aka rufe daga al'aurarsu" [A'araf: 20]. Ibnu-Kasir –رحمه الله- ya ce: "idan bayyanar da al'aura ya bayyanu, to ukuba za ta safka".
Sai kuma Shaidan ya sassafce hankulan bayi da jin sautuka na haramun; na kade-kade da makamantansu; Allah (تعالى) y ace: "Kuma ka rikitar da wanda ka sami iko akansa, daga gare su, da sautinka (na kade-kade da wasunsu)" [Isra'i: 64]. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Karaurarawa sharewa Shaidan", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma Shaidan yana son sifofin rauni ga bayi, kuma yana kiye musu sabuban samun karfi, Annabi –صلى الله عليه وسلم-: "Hamma daga Shaidan ne", Bukhariy da Muslim.
Kuma idan raunin bawa ya bayyana a gaban Shaidan, sai jiji-da-kansa da raininsa su karu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kada ka ce: Shaidan ya halaka, saboda ka fadi haka, sai yay i ta kumbura, har sai ya zama tudunsa kamar gida, sai kuma y ace: An fadi haka ne, saboda karfina. Saidai k ace: BISMILLAHI; saboda idan ka fadi haka, to sai shedan ya yi kankancewa, har sai ya zama kamar kuda", Abu-dawud ya ruwaito shi.

Hanyoyin Shedan sune:
Babban shirka; domin batar da halittu, da son ya rabauta da samun muradinsa, Allah (تعالى) ya ce: "kuma kada ku bi hanyoyin Shaidan; domin si a gare ku makiyi ne mabayyani" [Bakara: 168].
Kuma a cikin lamarin batar da halittu yana da runduna da mataimaka, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma lallai Shedanu suna yin wahayi zuwa ga majibintansu, domin su yi jayayya da ku, kuma idan kuka yi da'a a gare su, to lallai ku mushirkai ne" [An'am: 121].

Kuma Shedan cikin makirce-makircensa da kiyayyarsa, yana da munanan manufofin da yake son cin musu, Kuma babba daga shine katange halittu daga yin biyayya ga Allah, da batar da su, domin Shaidan yana cewa: "Ubangijina, saboda abinda ka yi na batar da ni, lallai zan kawata musu rayuwa a cikin kasa, kuma hakika zan batar da su gaba daya" [Hijr: 39].
Sai Shaidan ya sanya ayi ta rafkanuwa, ya kuma mantar da bayi ambaton Allah, Allah (تعالى) ya ce: "Shaidan yay i rinjaye akansu, sai ya mantar da su ambaton Allah" [Mujadilah: 19].

Kuma Shaidan na kiran halittu izuwa ga kowane laifi, yana kuma toshe kowace falala, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai shi yana umartarku ne da mugun aiki da alfasha, da kuma lamarin ku fadi abinda ba ku sani bag a Allah" [Bakara: 169].

Kuma yana cikin manufofin Shaidan Bata tsakanin halittu, da nisanta su ga Mahalicci,  Allah (سبحانه) ya ce: "Abin sani kawai, Shaidan yana nufin ya aukar da adawa da keta a tsakaninku, a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, da kuma sallah" [Ma'idah: 91].

Kuma karshen manufar Shaidan ita ce, nesata halittu daga rahamar Allah, da kuma shigansu wutar Jahannama, Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Abin sani kawai, Shaidan yana kiran kungiyarce domin su kasance 'yan wutar sa'ira", [Fadir: 6].

Kuma akiba ko sakamakon bin Shaidan shine shu'umci ne da azaba, kuma dukkan tabewa a duniya da wahala a lahira, yana daga sakamakon binsa, Allah (سبحانه): "Lallai wannan makiyi ne a gare ka, da kuma matarka; don haka kada ya fitar da ku daga Aljannah, sai ku wahala" [Daha: 117].

Wanda ya yi da'a ga Shaidan zai kasance cikin dimuwa da bata, Allah (سبحانه) ya ce: "Ka ce: Shin za mu kirayi baicin Allah, abinda baya amfaninmu kuma ba zai iya cutar da mu ba, kuma a mayar da mu akan dugaduganmu bayan Allah ya riga ya shiryar da mu, kamar wanda Shaidanu suka batar da shi a bayan kasa, yana mai dimuwa" [An'am: 71].

Yin hasara dukkanta, yana cikin yin soyayyar Shaidan, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma duk wanda ya riki Shaidan majibinci baicin Allah, hakika ya yi hasara mabayyaniya" [Nisa'i: 119].
Kuma idan kiyama ta tashi, za a tattaro su gaba daya: "To, muna rantsuwa da Ubangijinka, lallai za mu tayar da su, da kuma shaidanun, sa'annan mu halarto da su gyefen Jahannama suna gurfane" [Maryam: 68].

Kuma nadama tana kara girma, a lokacin da ke barranta daga wadanda suka bi shi, sai y ace musu: "Lallai ne Allah ya muku alkawarin gaskiya, ni kuma na muku alkawali sai na saba muku" [Ibrahim: 22].

Kuma karshen makomar mabiyin da wanda aka bi, it ace wutar Jahannama, tir da ita ga makoma, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya ce: ka fita daga gare ta (Aljanna) kana abin zargi korarre, lallai ne wanda ya bi ka daga gare su, hakika zan cika Jahannama da ku gaba daya", [A'araf: 18].

Bayan haka:
Ya ku musulmai
Lallai Shaidan, yafa batar da 'ya'yan wasu Annabawa ko iyayensu, kamar dan annabi Nuh, da Mahaifin annabi Ibrahim, kuma shine sababin halakar da wasu al'ummai gaba dayansu, Allah (سبحانه) ya ce: "Da adawa da Samudu, alhali alamun azaba sun bayyana a gare ku daga wuraren zamansu, kuma Shaidan ya kawata musu ayyukansu, sai ya kange daga hanyar Allah, kuma sun kasance masu basira" [Ankabut: 38].
Kuma babu mai tsira daga halakawar Shaidan face mumini mai tawakkali ga Allah, Allah ta'alah: "Lallai ne shi bashi da wani karfi akan wadanda suka yi Imani kuma ga Ubangijinsu suke tawakkali" [Nahli: 99].

Don haka; wajibi ne akanmu, mu tuba gaba daya zuwa ga Allah, mu kuma bi umarninsa, mu nisanci saba masa, saboda buwaya da daukaka suna cikin biyayya ne ga Allah, kuma mu bi umarnin Allah cikin fadinsa: "Sai ku gudu zuwa ga Allah, lallai ne ni mai gargadi ne a gare ku mai bayyanan gargadi" [Zariyat: 50].
Sai mu kiyaye aukawa cikin tarkon Shaidan



Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ke rayar da zukata da littafin Alkur'ani, yana karbar kyawawan ayyuka, kuma yana yin afuwa ga munanan ayyuka.
Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masanin ababen da suka buya,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai kira zuwa ga aikata alkhairori,

Ya Allah ka yi dadin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa; jagororin shiriya, kuma fitilun haskaka dufu.

Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah, iyakar takawa, saboda tsoron Allah shine mafi alherin tanadi a duniya da lahira,

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai rayayyar zuciya, Itace, wanda kyakkayawan aiki ke faranta mata, mummunansa kuma ke bakanta mata.
Matacciyar zuciya kuma, itace wanda bata jin radadin aikata zunubi, kuma bata damuwa kan haka, kuma bata yin farin ciki kan aikata kyakkayawan aiki, ko biyayya; kuma bata damuwa da ukobobin da aka rataya ga zunuban; Sai ni'imar lafiyar jiki, da yadda duniya take fiskanto shi, ta rude shi. Har ya rika zaton ni'imar da aka bashi, wata karama ce a gare shi daga Allah, Allah Ta'alah yana cewa: "Shin zato, suke yi, cewa lallai abinda muke karfafarsu da ita na dukiya da 'ya'ya, * muna gaugawan basu alheri ne? Kai dai basu sani ba" [Mu'uminuna: 55-56].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa, "Lallai ana bijirar da fitintinu ga zukata, kamar yadda ake bijiro da tabarma; tsinke-tsinke. Kuma duk zuciyar da ta kyamaci fitina, sai a sanya mata farar alama. Duk kuma zuciyar da ta kwankwadeta, sai a zana mata bakar alama; har zukatan su wayi gari, kamar zuciya guda biyu; zuciya fara kal, kamar falalen dutse; wanda wata fitina ba ta cutar da ita, tsawon dawwamar sammai da kassai. Da zuciyar da tayi baki; launinta ya caccanza, kamar kofin da aka kife shi, wato aka mayar da kansa kasa; wanda bata sanin aiki mai kyau, kuma bata iya kyamatar mummuna, in banda wanda ta  kwankwada na bin son zuciyarta".

Kuma dukkan cutukan zukata, suna sanya zuciyar jinya, ko kuma su kashe ta gabadaya, matukar har mutum bai rika yin hisabi ga zuciyarsa ba.
Kuma yana daga azama da alheri ga mutum, ya rika yin hisabi ga ransa a cikin yini da dare, da sati, da wata, da shekara, domin ya rika gano ta ina shedan ya kutso masa, sai ya tuba, kuma ya iya risko abinda yayi sakaci a cikinsa, da fatan a yaba wa ayyukansa, a kuma datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe.

Shi mumini; zuciyarsa rayayya ce, mai zurfin basira, Idan aka bashi; sai ya yi godiya, idan kuma ya aikata zunubi, sai ya tuba, idan kuma aka jarrabe da wani ibtila'i, sai ya dangana ya yi hakuri; saboda a cikin zuciyar mumini akwai mai masa wa'azi, da ke farkar da shi daga gafala, mai tsoratar da shi daga aukawa halaka, saboda ya zo cikin wani hadisi cewa:
"Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya zana mana mikakken zane,
sai ya zana wasu zanen ta geffansa,
kuma akan wannan zanen, akwai wani mai yin da'awa,
A samansa kuma akwai mai wa'azi;
SHI WANNAN MIKAKKEN ZANEN, SHINE: HANYAR ALLAH,
MAI YIN KIRA KUMA AKAN WANNAN HANYAR SHINE LITTAFIN ALLAH,
WANDA KUMA YAKE WA'AZA A SAMAN WANNAN HANYAR, SHINE MAI WA'AZI ZUWA GA ALLAH WANDA KE CIKIN ZUCIYAR KOWANE MUMINI,
SU KUMA HANYOYIN DA SUKE TA DAMA DA HAGUN DINSA, SUNE HANYOYIN BATA".

        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,





No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...