HUDUBAR MASALLACIN
ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 27/RAJAB/1439H
daidai da 13/AFIRILU/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
GABAR SHEDAN GA 'YAN ADAM
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin
bn Muhammadu Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: GABAR SHEDAN GA 'YAN ADAM, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai shugabanmu
kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi a sirrace da a
bayyane.
Ya ku musulmai …
Duniya
gidan ibtila'i ne da jarabawa, kuma mafi girman bala'I shine wanda ya yanke
alakar bawa da UbangijinSa da kuma addininSa.
Kuma a duniya babu abinda yafi tsananin fitina ga halittu
fiye da Iblis da rundunoninsa; saboda Iblisu shine abokin gaba na farko wanda
yafi girma, kuma shine kuma daga wurinsa ne mafarin kowane laifi da sabo.
Adawarsa gag a 'yan-Adam tana da tsanani kuma a bayyane take;
saboda a tarihi da gaba babu makiyan da suka fi shi bayyanar da adawa; Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne Shaidan ga Mutum, hakika makiyi ne
bayyananne"
[Yusuf: 5].
Shaidan makiyi ne wanda
baya yin rauni kuma baya yanke adawa, kuma rufa-rufa ko tausasawa baya amfani a
gare shi.
Ya yi rantsuwar yin kiyayya
ga dayawa daga 'ya'yan-Adam, Shaidan "Ya ce: to insa rantsuwa da
halakarwar da yi mini! Lallai ne zan zauna musu a tafarkinka madaidaici *
sa'annan kuma zan je musu daga gaba gare su, da kuma baya gare su, da kuma
jihohin damansu, da jihohin hagunsu, kuma ba za ka samu mafi yawansu masu
godiya ba"
[A'araf: 16-17].
Kuma tushen abinda ya dago
wannan kiyayyar, shine hassada, saboda Allah ya daukaka annabi Adamu, ya kuma
bashi falala, ta yadda ya halitta shi da hannayensa biyu, ya kuma shigar da shi
AljannarSa, ya ilmantar da shi dukkan sunaye, ya sanya Mala'iku suka yi masa
sujada, ya karrama zurriyarsa a bayansa, To sai Iblisu ya bayyanar da
kiyayyarsa a gare su, ya ce: "Shin ka ganka, wanga da ka fifita a kaina,
lallai ne idan ka jinkirta ni zuwa ga ranar Kiyama, zan karkatar da zurriyarsa,
face kadan"
[Isra'i: 62].
Sai zuciyar Iblisu ta kimsa
girman kai wanda shi ke jagoranci ga kowane cuta da sharri, sai yak i yin
sujada ga Adam, ya ce: "Ni na fi shi alkhairi; domin ka halitta ni
daga wuta, shi kuma halitta shi daga tabo", [A'araf: 12].
Kuma korarsa daga Aljanna
da nesatar da shi, shi ya dauke shi ga bayyanar da kiyayya kuma ya shelanta ta,
"Ya ce: ina rantsuwa da buwayarka, lallai zan batar da su gaba-daya" [Sad: 82].
Daga nan sai ya kulla
makida ga annabi Adamu da Hawwa, ya kawata musu sabon Allah, har aka fitar da
su daga Aljanna. Kuma Iblisu bai gushe ba, akan halinsa da kaidinsa yana cutar
da mutane a zahiri da ma'ana; cikin akidunsu da ibadodinsu, da jikinsu da
rayukansu, da dukiyoyinsu da 'ya'yansu, da abincinsu da abin shansu, da
barcinsu da tashinsu, da lafiyarsu da cutarsu, da sauran dukkan halayensu,
Annabi –صلى
الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Shaidan yana halartar dayanku cikin
kowane abu na sha'aninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Ta bangaren AKIDU Gayar Iblisu, shine lalata
wa mutane su, Allah (تعالى) ya ce: "Ashe ban yi alkawari da ku ba, Ya
'Diyan-Adamu, cewa kada ku bauta wa Shaidan, lallai shi makiyi ne a gare ku
bayyananne"
[Yasin: 60].
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan Iblisu ya wayi
gari, sai ya tura rundunoninsa, sai ya ce: Wanda ya batar da musulmi a yau, zan
sanya masa fular sarauta (kan sarki)", Ibnu-Hibbana
ya ruwaito shi.
Kuma Iblisu ba zai gushe
yana sanya shakku ga bawa har sai ya sa shi sakka ga Ubangijinsa, yak um afitar
da shi daga addininSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Shaidan zai zo wa
dayanku, sai y ace: Way a halitta kaza? Wa ya halitta kaza? Har y ace masa: Way
a halicci Ubangijinka, Idan bawa ya iso ga haka, to ya nemin tsarin Allah, ya
kuma hanu"
Bukhariy da Muslim.
Kuma Allah ya halitta bayi
akan fidirat Tauhidi, sai Shaidanu suka batar da su, Allah (تعالى) ya fada cikin
hadisin kudusiy: "Lallai ne Ni na halicci bayina dukkansu akan mikakken
addini, kuma lallai Shaidanu sun zo musu, sai suka kautar da su daga addininsu,
suka rika haramta musu abinda na halatta musu, suka rika umartarsu da yin shirka
a gare ni, da abinda ban saukar da hujja akansa ba", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma dukkan mai bautar
wanin Allah, to lallai yana rokon Shaidan ne yan bauta masa, Allah (تعالى) ya ce: "Ba
kowa suke roko, baicinsa ba face gumaka da sunan mata, kuma ba ga kowa suke
bauta ba face Shaidani mai tsaurin kai" [Nisa'i: 117].
Kuma rana tana fudowa tana
faduwa a tsakanin kafo biyu na Shaidan, a lokacin da masu bauta mata suke yin
sujjada a gare ta.
Kuma yana daga LALATA
AKIDA wanda Shaidan yake yi, koyar da sihiri, domin wanda ya aikata sihiri
ya kafirta, da mutumin da ya je wajen mai sihirin don a masa sihiri, Allah (تعالى) y ace: "Sai
suka bi abinda Shaidanu suke karantawa a lokacin mulkin annabi Sulaimanu, kuma
Sulaimanu bai kafirta ba, Saidai shaidanu sune suka kafirta; suna karantar da
mutane sihiri" [Bakara: 102].
Aikin "NUSHRAH" shine kokarin warware
sihiri, da wani sihirin kwatankwacinsa, kuma lallai yana daga ayyukan Shaidan.
Kuma bokaye sun sayar da
addininsu ne ga Shaidan; sai Shaidan ya rudar da su, da cewa zai taimake su,
Annabi –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Lallai Mala'iku suna sauka a cikin girgije, sais
u ambaci lamarin da aka hukunta a sama, Sai Shaidanu su yi satar ji; sais u ji
wannan lamarin, daga nan sais u yi wahayinsa zuwa ga bokaye, sai su kuma su yi
karya guda dari daga wurinsu su hada da ita", Bukhariy ya ruwaito shi.
A karshen zamani Dajjal
zai fito, "Sai Allah ya tayar da wasu Shaidanu tare da shi suna Magana da
mutane", Ahmad ya ruwaito shi.
Ba za a yi kiyama ba, sai
akan ashararn halittu; Sai Shaidan ya umarce su da yin bautar gumaka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sai
ashararun mutane su saura, da karanci hankali da wauta irin na dabbobi masu
farauta, basu sanin aiki mai kyau, kuma basu kyamar mummuna, Sai Shaidan ya zo
musu cikin wata sura, sai ya ce: Shin ba za ku amsa ba? Sai su ce: zuwa ga me
kake umartarmu? Sai ya umarce su da bautan gumaka", Muslim ya ruwaito
shi.
AMMA KAIDIN SHAIDAN CIKIN
IBADODI To
lallai ba zai gushe da ma'abucin ibada ba, face ya bata masa bautarsa;
Sai ya rika sanya bawa sakku
cikin tsarkinsa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan Shaidani ya zo wajen
dayanku, sai yace masa: Lallai ka karya alwalarka, to ya ce: ka yi karya",
Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma idan musulmi ya tashi
domin yin sallah, sai shaidan ya shiga tsakaninsa da sallarsa da waswasinsa, Annabi
(صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne dayanku, idan ya tashi domin yin
sallah, sai Shaidan ya zo masa, domin ya rikirkita masa ita, har ya zama bai
san raka'a nawa ya sallata ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan Shaidan ya samu gibi
a cikin sahu, to sai ya shiga cikinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku
tottoshe gibi; domin Shaidan yana shiga tsakaninku", Ahmad ya ruwaito
shi.
Kuma waigawa a cikin
sallah yana daga kaidinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Waigawa wafta ne wanda
Shaidan ke waftarsa daga sallar bawa", Bukhariy ya ruwaito shi
Kuma Shaidan yana da tsananin
kwadayin yaga ya yanke wa bawa sallah, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan
dayanku zai yi sallah, to ya yi sallah zuwa ga sutra, sai ya kusance ta, domin
kada Shaidan ya yanke masa sallarsa", Hakim ya ruwaito shi.
Kuma "Babu mutane
uku a wata alkarya ko kauye, wanda ba a tsayar da salla a cikinsu, face Shaidan
ya rinjaye su". Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kiyayyar Shaidan ga mutane,
lallai bata da iyaka;
Ta yadda ya ke tarayya da
mutane cikin abincinsu da abin shansu, da auratayyarsu, Allah Mabuwayi da
dauka ya ce: "Kuma ka yi tarayya da su. Cikin dukiya da 'ya'ya"
[Isra'i: 64]. Sai shaidan ya yi jayayya da 'Dan-Adam cikin abincinsa; ya ci
tare da shi, matukar bai ambaci sunan Allah ba, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai
Shaidan yana halatta abinci, matukar ba a ambaci sunan Allah akansa ba",
Muslim ya ruwaito shi.
Sai kuma Shaidan ya rika
cinye abinda ya fadi daga Mutum, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan loma ta fadi
dayanku, to ya gusar da abinda ya makale mata na dauda, sa'annan ya cinye ta,
amma kada ya barta ga Shaidan", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan dayanku ya zo
kwanciya da iyalinsa sai Shaidan ya ta aikin cutar da su, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Da
'dayanku idan ya zo saduwa da iyalinsa zai ce: Ya Allah, ka nesatar da Shaidan,
kuma ka nisantar da Shaidan daga abinda zaka azurta ni, Idan har 'da ya shiga
tsakaninsu, to Shaidan ba zai cutar da shi ba, kuma ba za a bashi iko akansa ba",
Bukhariy ya ruwaito shi.
Haka kuma Shaidan yana
jayayyar wurin zama da mutum, matukar bai ambaci sunan Allah a gidan ba;
Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Idan 'dayanku zai shiga gidansa, sai ya ambaci
Allah a lokacin shigansa, da lokacin cin abincinsa, Sai Shaidan ya ce: Bani da
wurin kwana a wurinku, kuma bani da abinci. Idan kuma ya shiga bai ambaci sunan
Allah ba a lokacin shigansa, sai Shaidan ya ce: Na samu wurin kwana. Kuma idan
bai ambaci sunan Allah a wurin cin abincinsa ba, sai ya ce: Na riski wurin
kwana, da abinci", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan farkon dare ya
zo, sai Shaidanu su yadu, domin cutar da bayi, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan
dare ya shigo, ko kuka yi yammaci, to ku rike yaranku kanana; domin Shaidanu
suna watsuwa a wannan lokacin", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan baya yanke
kiyayyarsa, kuma baya kosawa, saboda baya barin har mai barci, daga cutarwarsa,
Sai "Ya kulla kulli guda uku a karshen kayin dayanku, idan ya yi barci;
sai kuma ya dauri kowane kulli; da fadinsa: kana da dare mai tsawo; sai ka yi
barci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma idan bawa ya yi barci
bai yi salla ba, Sai Shaidan ya yi fitsari a kunnensa; don walakanta shi;
saboda an ambaci wani Mutum a wurin Annabi –صلى الله عليه وسلم- da cewa, ya yi barci har ya wayi gari,
sai ya ce: "Wannan mutum ne, wanda Shaidan yay i fitsari a cikin
kunnuwansa, ko kunnensa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana yin barci
a cikin karan hancin mai barci, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan dayanku ya tashi
daga barcinsa sai ya zo alwala, to ya fyace hanci sau uku, domin Shaidan yana
kwana a cikin karan-hancinsa",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma duk abinda ya karu na
wurin shumfudi, to na Shaidan ne, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shimfudi n farko na miji ne,
wani shimfidin kuma na matarsa, wani shimfudin na bako, shimfidi na hudu kuma
na Shaidan ne", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan ba zai bar dimautar
da mutum a cikin barcinsa ba, ko ya rika tsoratar da shi a cikin
mafarke-mafarkensa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mafarki daga Allah ne, kwashe-kwashen
mafarki kuma daga Shaidan ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana kokarin
kawo rarraba a tsakanin mutane, domin ya bata tsakaninsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai
Shaidan ya debe tsammanin masallata za su masa bauta a tsibirin larabawa,
saidai zai yi ta zuga a tsakaninsu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma farkon wannan kawo
rarrabar yak an kasance a tsakanin miji da matarsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "lallai
Iblisu yana sanya gadon al'arshin mulkinsa a saman teku, sa'annan sai ya aike
sojojinsa, wanda zai fi kusancin wurin zama da matsayi a cikinsu a wurinsa
shine wanda ya fi tsananin fitinarwa; dayansu zai zo sai y ace: Na aikata kaza
da kaza, sai Shaidan y ace: baka aikata komai ba. Ya ce: Sai dayansu ya zo
yace, Ban bar wane ba, sai da na rabe tsakaninsa da matarsa, Ya ce: Sai ya
kusantar da shi jikinsa, y ace da shi, Madalla da kai", Muslim ya
ruwaito shi.
Kuma shaidan baya jin-kan
yaro domin karancinsa; saboda farkon haihuwar mutum shaidan yana yin cakala a
kuibinsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu wani yaron da za a Haifa,
face Shaidan ya taba shi a lokacin haihuwarsa, sai ya kwaye baki da ihu;
sakamakon Shaidan ya bata shi, sai dai Maryam da 'danta", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana gudu a
jikin 'dan-Adam ta magudanar jinni, kuma babu wani daga cikinku, face an
wakilta masa abokin gaminsa daga Aljanu" Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Shaidan yana shiga
cikin jikin mutane, sai Aljanu su buge mutum, Allah (سبحانه) ya ce: "Wadannan
da suke cin riba, basu tashi sai kamar wanda bugun shedan ke buge su na shafa",
[Bakara: 275]. Shaikhul Islami –رحمه الله- ya ce: "Babu –a cikin jagororin
musulmai- wanda ke musanta cewa Aljani yana shiga jikin mai farfadiya da
waninsa. Kuma duk wanda ya yi inkarin hakan, ko ya yi da'awar cewa, wai shari'a
tana karyata hakan, to hakika ya yi karya ga shari'ar, saboda a cikin dalilai
na shari'a akwai abinda ke kore hakan".
Kuma Shaidan ba zai gushe
yana cutar da 'diyan-Adamu ba, har zuwa lokacin magagin mutuwa, saboda ya zo
cikin addu'oin Annabi –صلى الله عليه وسلم- cewa: "kuma lallai ina neman
tsarinka; kada Shaidan ya yi wasa da hankalina a lokacin mutuwa",
Nasa'iy ya ruwaito shi.
Shaidan a kaidin da yake
kulla wa ga dan-Adam yana da salo-salo, da hanyoyi daban-daban masu yawa; sai ya
kawata musu barna, yana mai kyautata a idonsu, yana sa musu wahamin cewa hakan
gaskiya ne; wannan ya sanya a ranar yakin badar Shaidan sai ya kawata wa
mushirkai aikinsu, Allah (تعالى) ya ce:
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ke rayar da zukata da littafin
Alkur'ani, yana karbar kyawawan ayyuka, kuma yana yin afuwa ga munanan ayyuka.
Ina yin yabo ga Ubangijina,
kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masanin
ababen da suka buya,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai kira zuwa ga
aikata alkhairori,
Ya Allah ka yi dadin salati
da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa;
jagororin shiriya, kuma fitilun haskaka dufu.
Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah,
iyakar takawa, saboda tsoron Allah shine mafi alherin tanadi a duniya da
lahira,
Ya ku Bayin Allah …
!!
Lallai rayayyar zuciya,
Itace, wanda kyakkayawan aiki ke faranta mata, mummunansa kuma ke bakanta mata.
Matacciyar zuciya kuma, itace wanda bata jin
radadin aikata zunubi, kuma bata damuwa kan haka, kuma bata yin farin ciki kan
aikata kyakkayawan aiki, ko biyayya; kuma bata damuwa da ukobobin da aka rataya
ga zunuban; Sai ni'imar lafiyar jiki, da yadda duniya take fiskanto shi, ta
rude shi. Har ya rika zaton ni'imar da aka bashi, wata karama ce a gare shi
daga Allah, Allah Ta'alah yana cewa: "Shin zato, suke yi, cewa lallai
abinda muke karfafarsu da ita na dukiya da 'ya'ya, * muna gaugawan basu alheri
ne? Kai dai basu sani ba" [Mu'uminuna: 55-56].
Kuma ya zo cikin hadisi
cewa, "Lallai ana bijirar da fitintinu ga zukata, kamar yadda ake bijiro da
tabarma; tsinke-tsinke. Kuma duk zuciyar da ta kyamaci fitina, sai a sanya mata
farar alama. Duk kuma zuciyar da ta kwankwadeta, sai a zana mata bakar alama;
har zukatan su wayi gari, kamar zuciya guda biyu; zuciya fara kal, kamar
falalen dutse; wanda wata fitina ba ta cutar da ita, tsawon dawwamar sammai da
kassai. Da zuciyar da tayi baki; launinta ya caccanza, kamar kofin da aka kife
shi, wato aka mayar da kansa kasa; wanda bata sanin aiki mai kyau, kuma bata
iya kyamatar mummuna, in banda wanda ta
kwankwada na bin son zuciyarta".
Kuma dukkan cutukan zukata,
suna sanya zuciyar jinya, ko kuma su kashe ta gabadaya, matukar har mutum bai
rika yin hisabi ga zuciyarsa ba.
Kuma yana daga azama da
alheri ga mutum, ya rika yin hisabi ga ransa a cikin yini da dare, da sati, da
wata, da shekara, domin ya rika gano ta ina shedan ya kutso masa, sai ya tuba,
kuma ya iya risko abinda yayi sakaci a cikinsa, da fatan a yaba wa ayyukansa, a
kuma datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe.
Shi mumini; zuciyarsa
rayayya ce, mai zurfin basira, Idan aka bashi; sai ya yi godiya, idan kuma ya
aikata zunubi, sai ya tuba, idan kuma aka jarrabe da wani ibtila'i, sai ya
dangana ya yi hakuri; saboda a cikin zuciyar mumini akwai mai masa wa'azi, da
ke farkar da shi daga gafala, mai tsoratar da shi daga aukawa halaka, saboda ya
zo cikin wani hadisi cewa:
"Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya zana mana mikakken zane,
sai ya zana wasu
zanen ta geffansa,
kuma akan wannan
zanen, akwai wani mai yin da'awa,
A samansa kuma
akwai mai wa'azi;
SHI WANNAN
MIKAKKEN ZANEN, SHINE: HANYAR ALLAH,
MAI YIN KIRA KUMA
AKAN WANNAN HANYAR SHINE LITTAFIN ALLAH,
WANDA KUMA YAKE
WA'AZA A SAMAN WANNAN HANYAR, SHINE MAI WA'AZI ZUWA GA ALLAH WANDA KE CIKIN
ZUCIYAR KOWANE MUMINI,
SU KUMA HANYOYIN
DA SUKE TA DAMA DA HAGUN DINSA, SUNE HANYOYIN BATA".
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama ta aminci"
[Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, ……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment