2018/03/02

HUDUBAR YAU A TAKAICE

Hudubar Masallacin Annabi (S.A.W), A Takaice
14/Jumadal Akhirah/1439H
Limamin Masallacin Annabi, kuma Mai huduba; wato As-Sheikh *Salah bn Muhammadu Albudair* ya yi hudubarsa, akan maudu'in *TSAKAITAWA DA SASSAUTAWA, DA BAYANIN KA'IDODIN FATAWA*
 Lallai shari'ar Allah, ta zo da akidar tsakaitawa, da saukakawa, da sassautawa, da bada sauki, da fadadawa, da rangwame, da dauke kunci ga Mutane da Aljanu.
 An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-, ya ce: *Lallai addini yana da sauki, kuma babu mai tsanantawa a lamarin addini face ya gallabe shi, sai ku kwatanta daidai; ku kokarta, kuma albishir, sannan ku nemi taimako da ibadar safiya, da ta maraice, da wata a cikin duhun dare*, Bukhariy da Muslim.
 Ba manufar saukakawa a cikin addini itace, nemo ko bibiyar saukakawar mazhabobin fikihu, da na zantukan malamai, domin a zabo maganar da tafi sauki daga cikinsu ba, A'a! Manufar ita ce, yin aiki da sauki irin na shari'a, a cikin lamuran da dalilai na shari'a su ka zo da saukakawa a cikinsu, kamar ga ma'abuta uzurori.
 Yana daga *Ibtila'i*, Yadda wasu ke gaggawar kakkafa kayukansu a matsayin masu fatawa, alhalin dayansu a tsakanin maluma bako ne wanda bashi da makami a fagen ilimin fatawa, hasali ma bashi da wani kaso na ilimi. Abinda ke kara rudar da irin wadannan shine, tambayoyin da jahilai ke gabatar musu, da kuma yadda wadanda suka fi su jahilci, suke gaggawan zuwa daukar fatawowinsu.
 Irin wadannan mutanen su rika tuna ranar tunzuri da faduwa, wanda gabbai da bangarorin jiki a cikinsa ke bada shaida, ake kuma bayyanar da abinda ke cikin kiraza, a kuma tone abinda ke cikin kaburbura, to a wannan yinin ne, mayaudara za su san cewa, lallai su suna yaudarar kayukansu ne, kuma sun yi wasa ne da addininsu.
 Suhnun bn Sa'id -Allah ya masa rahama- ya yi gaskiya a inda yake cewa: *Wanda yafi mutane gaba-gadin bada fatawa, shine ya fi su karancin ilimi, saboda mutum kan iya babi daya na ilimi, sai ya yi zaton gaskiya gaba dayanta, tana cikin wannan babin* .
 Addinin Allah tsakaitawa ne tsakanin wanda ke ketare iyaka a cikinsa, da mai gajartawa. Kuma da guluwwi da jafa'i, da sakaci da wuce iyaka, cutuka ne guda biyu munana, kuma turbobi karkatattu, kuma binsu ficewa ne daga mikakken addini, da shiriya mai girma, da tafarki mikakke.
*Sako* / Daga Ofishin Fassara Na Masallacin Annabi (S.A.W).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...