ABUBUWAN DA HARAMA KE HANAWA
(محظورات الإحرام)
TANADAR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
ABUBUWAN DA HARAMA KE
HARAMTAWA
A cikin ibadar hajji
ma'anonin tauhidi da miqa-wuya ga Allah Mabuwayi da xaukaka suna fitowa a
sarari, wannan kuma shi ne a lokacin da Mahajjaci ke tovuwa daga al'adodinsa da
ya saba rayuwa a cikinsu, na sanya tufafin da ya saba, da shafa turare, da
makamancin haka daga cikin abin qawa na duniya,
Sai Allah ya shar'anta wa mahajjaci yin haramar shiga
aikin, domin shiga cikin ayyukan hajji, gadan-gadan, kuma domin ya zama alamar
miqa-wuya ga umarnin Allah,
Kuma sai ya kasance ihrami
yana da abubuwan da aka yi hani kan samar da su, ga wanda ya fara wannan aiki,
ko ya shiga cikin wannan xa'a (ta hajji da umrah);
KUMA YANA DAGA CIKINSU;
1- GUSAR
DA GASHIN KAI;
ta hanyar askewa, ko tuzgewa, ko waninsu, saboda faxinsa Maxaukakin sarki:
(Kuma kada ku aske gashin-kanku har sai hadaya ta kai
mahallinta) [Baqara: 196].
2- Kuma
haqiqa an yi qiyasin gusar da sauran gashin jiki, daga jiki, da yanke faratu.
3- KUMA
YANA DAGA CIKINSU;
Farautar dabbar sarari (tudu), da kuma ci daga gare ta, saboda
faxinsa Maxaukakin sarki:
(Ya ku waxanda su ka yi imani kada ku kashe abar farauta
alhalin kuna cikin harama) [Ma'ida: 95].
Kuma haqiqa an bada kyautar jakin dawa (jeji) ga Manzon Allah (sallal
lahu alaihi wa sallama) sai ya mayar da shi, yana mai cewa:
(Lallai ba mu mayar maka da shi, sai don kasancewarmu a
cikin harama) [Bukhariy da Muslim].
4- KUMA
YANA DAGA CIKINSU;
Yin amfani da turare, a jikin tufafi ko a jiki, ko
makamancinsu, saboda abinda ya tabbata cewa lallai Annabi (sallal lahu alaihi
wa sallama) ya hana mai harama, kan sanya tufafin da turaren za'afaran ko waras
su ka tava su.
5- KUMA
YANA DAGA CIKINSU;
YIN JIMA'I, Wannan kuma shi ne ya fi tsanani daga cikinsu, kuma
shi ya fi girman haramci, a haqqin mai harama.
6- Kuma haqiqa,
an riskar da ababen da su ke rigayar jima'i, na sumbanta (ko runguma), ko
waninsu, kuma haqiqa an tambayi A'ishatu (R.A) kan abinda ke halatta ga
mahajjaci daga matarsa, sai ta ce:
(Komai ya haramta a gare shi, in banda magana).
7- KUMA
YANA DAGA CIKINSU;
DAURA AURE GA MAI HARAMA, KO GA WANINSA, saboda faxin Manzon Allah
(sallal lahu alaihi wa sallama): (Mai harama, ba zai yi aure ba, kuma ba zai
aurar ba).
Kuma an haramta, wa mai harama IDAN YA KASANCE NAMIJI,
abubuwan da su ke tafe:
Sanya xainkakken tufafi,
kamar riga da wando, ko kuma lulleve kai da abinda ke tava kan, kamar tagiya da
rawani, ko riga mai hula da makamancinta, saboda Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama)
an tambaye shi akan abinda Mai harama zai sanya na tufafi, Sai ya ce: (Ba
zai sanya riguna ba, da kuma rawwuna, da wanduna, haka riguna masu hula, da
huffofi) [Bukhariy da Muslim].
Kuma haramun ne ga MACE mai harama, Ta sanya
niqabi, da safar hannu biyu, saboda faxin Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa
sallama): (Mace mai haram aba za ta sanya niqabi ba, kuma ba za ta sanya safar
hannu ba) [Bukhariy da Muslim].
Kuma an halatta wa mace, xinkakkun tufa, waxanda ba
wannan ba, kamar riga, da wando, da huffi biyu, da safunan qafofi.
Kamar yadda aka halatta mata, sake mayafin rufe fiskarta,
daga saman kanta, kuma idan ya tava fatar fiskarta ba zai cutar da ita ba.
Duk kuma wanda ya auka cikin abinda aka yi hani na
mahzuraat, alhalin yana cikin harama, to wajibi ne, ya yi ta tuba zuwa ga
Allah, kuma wajibi ne akansa ya yi fid-ya, sai dai kawai jima'i, saboda shi kam
hajjin yana vaci da shi, kuma dole ne akansa ya cika hajjin nasa, a vace,
sa'annan ya raman wannan hajjin a shekara mai zuwa.
No comments:
Post a Comment