HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26/ZULKI'IDAH/1438H
daidai da 18/OGASDAS/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Nm,,
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: mn,,, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
wanda ya tsarkake rayuka, da farillai da wajibai, ya kiyaye su daga dauxa da shexanu,
ta hanyar haramta ababen haram da barin munana, kuma ya qarfafi zukata da
rayuwa da imani, da kuma abinda ya sassaukar na ayoyi bayyanannu, da abinda
Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) ya sunnanta na
shiriya da kalmomi masu cike da fasaha,
Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa akan
ni'imominSa waxanda babu mai qididdige su, face Shi,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Ubangijin
qasa da sammai.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda ya baiwa kowanne
matsaya haqqinsa na bautuka,
Ya Allah! ka yi salati, da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da
sahabbansa, masu gaggawan aikata alkhairori.
Bayan haka:
Ku bi Allah ta'alah
da taqawa ta hanyar tsayuwa da abinda Allah Mabuwayi da xaukaka ya farlanta na
umarninSa, da nisantar abinda Allah ya tsawatar na haninSa, saboda taqawar
Allah ita ce mafi alherin abinda aka yi guzuri domin ranar sakayya, kuma ita ce
mafi alherin abinda ke gyara lamuran
bayi, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma duk wanda ya yi taqawar Allah zai sanya masa sauqi a lamarinsa" [Xalaq: 4].
Ya ku, Musulmai…
!!!
Hajjin xakin Allah mai
alfarma, an wajabta shi ne akan musulmi mai hankali balagagge, a tsawon rayuwa,
sau xaya, duk kuma abinda ya qaru akan haka, to nafilar taxawwu'i ce.
Kuma duk wanda Allah ya
qaddara masa hajji, ya kuma datar da shi wajen aiwatar da shi, na farilla ne ko
na nafila, har ya tsayu wajen aikata ayyukansa a cike, to lallai Allah ya masa
babbar ni'imah, ya kuma bashi matsayi maxaukaki, da gafara mai yalwar faxi, da
ladaddaki nau'i-nau'i.
Kuma ya dace, ga mutumin da Allah ya bashi
damar yin hajji ya yi matsanancin farin-ciki da hakan, Allah ta'alah yana cewa:
"Ka ce: Da falalar Allah da rahamarSa, sai su yi farin ciki da
wannan, Shi ne mafi alheri daga abinda su ke tarawa" [Yunus: 58].
(zai yi farin ciki) Saboda
ya samu falalolin hajji wanda Qur'ani mai karamci ya zo da bayaninsu, da kuma
hadisan Annabi (SAW), Allah ta'alah ya ce, a inda ya yi bayanin ayyuka da
alamomin hajji: "Kuma ka yi bushara ga kyautata aiki" [Hajji: 37].
Kuma Allah subhanahu ya ce,
dangane da kyakkyawan aiki a lokacin hajji: "Kuma duk abinda ku
ka aikata na alkhairi Allah yana saninsa" [Baqara: 197], ma'ana: Sai ya sakanta muku
da shi.
Kuma Allah ta'alah ya faxa
dangane da wanda Allah ya karvi aiki daga gare su: "Kuma daga cikinsu
akwai wanda ke cewa, Ya Ubangijinmu! Ka ba mu mai kyau a cikin duniya, da mai
kyau a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta * Waxannan suna da rabo daga
abinda su ka sana'anta, kuma Allah Mai saurin yin hisabi ne" [Baqara: 201-202].
√Ya zo kuma cikin hadisi: "Umrah zuwa umrah ya
kan kankare abinda ya kasance tsakaninsu, Shi kuma hajji karvavve (mabruri) bashi
da wani sakamako, face Aljannah", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga
hadisin Abu-hurairah (رضي
الله عنه).
√Kuma Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Wanda ya yi hajji
don Allah, bai yi kwarkwasa ba, bai yi fasiqanci ba, zai koma kamar ranar da
mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin
Abu-hurairah (رضي الله عنه).
√Kuma an ruwaito daga A'isha
(رضي الله عنها) ta ce: "Ya Ma'aikin Allah!
Muna ganin jihadi shi ne mafificin ayyuka, shin (mu mata) ba za mu yi jihadin
ba? Sai ya ce: (Mata) Kuna da mafificin jihadi, kuma wanda ya fi kyau, wato,
hajji karvavve (mabruri)" Bukhariy da Nasa'iy suka ruwaito shi.
Kuma mahajjata da masu
umrah, fatake ne zuwa ga Allah, Shi kuma Ubangiji Mabuwayi da xaukaka shi ne ya
fi dukkan masu kyauta yin kyauta, √An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mahajjata da masu
umrah fatake ne zuwa ga Allah, idan su ka roqe Shi sai ya amsa musu, idan kuma
suka nemi gafararSa, sai ya gafarta musu", Nasa'iy ya ruwaito shi.
√Kuma an ruwaito daga
Abu-hurairah (رضي
الله عنه) , daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ana gafarta wa mahajjaci, da kuma wanda
mahajjacin ya nema masa gafara", Xabaraniy da Albazzar suka ruwaito shi.
√Kuma an ruwaito daga A'isha
(رضي الله عنها), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu wani yini
wanda Allah ya fi yawaita 'yanta bayi a cikinsa daga wuta, fiye da yinin arfah,
kuma lallai Shi yana kusantowa, yana bayyana, sa'annan ya yi alfahari da su ga
Mala'ikunsa, sai ya ce: me waxannan suka nufa", Muslim ya ruwaito shi.
Shi kuma LADAN HAJJI DA AMFANIN DA KE CIKINSA, Babu wanda zai iya
qididdige shi, sai Allah Mabuwayi da xaukaka, kuma mutane basu san komai daga
cikin haka ba, sai xan kaxan;
Saboda duk wanda Allah ya karva masa, to lallai ya samu
lada dayawa, kuma ya halarci amfanoni iri-iri, na duniya da na addini, koda
kuwa bai iya qididdige waxannan amfanin ba, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ka yi yekuwar
hajji ga mutane, za su zo maka suna masu tafiya da qafafu, da kuma akan
maxankwarin dawaki, suna zuwa daga kowani saqo mai zurfi * domin su halarci
abubuwan amfani a gare su" [Hajji: 27-28].
Kuma yana daga ALBARKOKIN HAJJI lallai musulmi kan koma, da samun gafarar
zunubai, idan aka karva masa,
Kuma za a kiyaye shi -saboda hajjin da ya yi- daga Shexan;
sai kaidin Shexan saboda hajjin da ya aiwatar ya yi rauni akansa, domin faxin Allah
ta'alah a qissar Iblisa: "Ya ce: Ina rantsuwa da buwayarka, wallahi
zan vatar da su gaba xaya * Sai dai bayinka, tsarkakku daga cikinsu" [Saad: 82-83], Don
haka; duk wanda ya yi ikhlasi cikin hajjinsa, ya kuma yi aiki da Sunnah,
to zai samu tsira daga vatarwar Shexan. Kuma duk wanda hajjinsa ya kuvuta masa,
to rayuwarsa ce gaba xaya ta tsira.
Kuma ya cancanta musulmi ya yi godiya ga UbangijinSa akan bashi damar hajji da
ya yi, da kuma sauqaqe masa sabbuban hajji, da samuwar muhimman vangarorin
wannan aikin, da hidimominsa, da ababen da aikin ke nema, da sauqaqe hanyoyin
hajji; na tudu, da teku, da jiragen sama, da kuma samuwar sabbuban da su ke janyo
hutu a cikin aikin, da sauqin hanyoyin kai-komo, da sauqin samun abinci, da samun
tabbatuwar aminci da zaman lafiya, a qasar haramin Makka da Madina maxaukaka, a
wannan zamanin da fitintinu ke hauhawa, kamar kumfa a cikin tuken da ke maqare,
wanda kuma yaqe-yaqe suke tasowa kamar wutar daji mai halakarwa, Allah ta'alah
yana cewa: "Shin ba mu tabbatar musu da mallakar harami mai alfarma, amintacce,
ana jawo 'ya'yan itacen kowani iri zuwa gare shi, bisa ga arzurtawa daga gare
mu, Amma kuma mafi yawansu basu sani ba" [Qasas: 57],
Kuma Allah ta'alah ya ce:
"Sai su bauta wa Ubangijin wannan xakin * Wanda ya ciyar da su daga
yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].
Kuma ya cancanta ga musulmi ya yi yabo wa Allah, ya gode masa, akan ni'imar wannan xakin
daxaxxe mai albarka, wanda babanmu annabi Ibrahima da Isma'ila (عليهما الصلاة والسلام) suka gina shi, da umarnin
Allah ta'alah, domin ya zama rahama ga mutane, kuma Allah ya sanya shi ya zama
sababin maslahohin addini da na duniya, Allah ta'alah yana cewa: "Allah ya sanya
Ka'aba xaki tsararre,ma'aunin addini ga mutane" [Ma'idah: 97].
Bagawiy (رحمه الله) ya ce: ka'aba ma'auni ce a gare su, domin
tsayuwar addininsu, da duniyarsu. Maganarsa ta qare.
Kuma Allah ya canacanci bayinSa su yi yabo a gare shi, suna masu gode masa,
saboda yadda ya musu zavin wuraren bauta masu tsarki, domin su yi ayyukan hajji
a cikinsu, kuma ya sanar da musulmai su, domin ibadodinsu su yi girma, ladansu
kuma su ninninku, a waxannan wuraren, saboda falalar wuraren, An ruwaito daga
Amru bn Al-ass (رضي
الله عنه) ya ce: "Mala'ika Jibrilu ya gangaro Minah da annabi Ibrahima (عليهما الصلاة والسلام) sai ya yi sallar azahar
da la'asar da magriba, da isha, da asubahi a Minah tare da shi, sa'annan ya yi
sammako da shi daga Minah zuwa Arfah, sai ya yi salloli biyu
da shi, sa'annan sai ya tsayu, har rana ta faxi, sa'annan sai ya zo da shi Muzdalifah, sai ya sauka a cikinta, ya kwana a cikinta, sa'annan ya yi
sallar asubahi a cikinta, kamar mafi gaggawan yadda musulmi zai yi sallah,
sa'annan sai ya tafi da shi zuwa Minah, sai ya
yi jifa, sa'annan ya yi aski, ya yanka dabba, sa'annan sai Allah Mabuwayi da
xaukaka ya yi wahayi zuwa ga Muhammadu (صلى الله عليه وسلم): ((Cewa, Ka bi aqidar Ibrahima
mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirki ba))" [Nahli: 123]. Xabaraniy ya ruwaito shi cikin [Mu'ujam
Kabir].
Allah ta'alah ya ce, dangane
da addu'ar annabi Ibrahima da Isma'ila (عليهما الصلاة والسلام): "Kuma ka nuna mana wuraren ibadar hajjinmu, kuma
ka karvi tubanmu"
[Baqarah: 128].
Bagawiy (رحمه الله) ya ce: Sai Allah ta'alah ya amsa
addu'arsu su biyu, sai ya turo Jibrilu ya nuna musu yadda ake aikin hajji.
Maganarsa ta qare.
Don haka, Duk mutumin da aka datar da shi, aka kuma
qaddara masa aikin hajji, to sai ya koyi hukunce-hukuncensa, da ayyukansa, sai
kuma ya yi aiki da su, domin hajjinsa ya zama karvavve (mabruri).
Kuma mafi girman AYYUKAN HAJJI shi ne RUKUNNANSA, wanda su ne: Niyyar shiga cikin ibadar da yin
harama, da kuma tsayuwa a arfah, da xawaful ifadha bayan daren Muzdalifah, da sa'ayi (tsakanin Safah da Marwa),
Kuma duk wanda ya bar
tsayuwa a arfah to lallai, hajji ya wuce masa.
Wanda kuma ya bar wani
rukuni, to hajjinsa ba zai cika ba, face ya kawo shi.
Su kuma WAJIBAN HAJJI, Sune: Yin harama daga
miqati, da kuma tsayuwa a arfah har zuwa faxuwar rana, da kuma kwana a Minah,
da kwanan Muzdalifah har zuwa rabin dare, da yin jifa, da aski, da xawafin
bankwana.
Kuma maniyyaci ya yi
kwaxayin aiki da SUNNONI.
Su kuma ayyukan hajji na
ranar layya, babu laifi wajen gabatar da sashensu akan sashe.
Busharar mutumin da ya yi tsarkake
niyyah ga Allah, cikin hajjinsa, ya kuma yi qoqarinsa wajen aiki da nau'ukan
xa'oi domin kusantar Allah, kamar yawaita zikiri, da tilawa, da kyautatawa, da
yin alheri, da tunkuxe sharri.
Kuma wajibi ne musulmi ya
nisanci MAHZUURAAT da harama ke hanawa, kuma
kada ya bijirar da hajjinsa ga ababen da suke vata shi.
Amma wanda ya zo hajji da niyyar
cutar da musulmai,
ko don ya shigar da wahala akansu, ko ya musu makirci, ko quqqula kaidi a gare
su, ko kuma yin kwace, ko don kawo ababe masu bugar da hankula (dangin koken),
ko don aikata laifuka masu halakarwa, na haramun, to lallai Allah yana nan ga
wannan mavarnacin a madakata. Kuma Allah ya iyar ma musulmai sharrinsa, kuma
aikinsa zai halaka shi, saboda irin wannan yana yaqar Allah mabuwayi da xaukaka
ne, da kuma ManzonSa (صلى
الله عليه وسلم), kuma duk wanda ya ce zai yaqi Allah, to tavavve ne,
wulaqantacce halakakke. Kuma dalilai na tarihi sun bayyanar da hakan, Allah
ta'alah yana cewa: "Lallai waxanda su ke sava wa Allah da ManzonSa, lallai
waxannan suna cikin waxanda suka fi qasqanci * Allah ya rubuta, cewa: Lallai
zan yi rinjaye Ni da Manzannina, Lallai Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [20-21].
Kuma wanda ke xauke da irin
wannan niyyar mummuna, za a haramta masa samun ladan hajji, da amfanin da ke
cikinsa, kuma zai koma da zunubai masu nauyi, waxanda manyan duwatsu ba za su
iya jure xaukansu ba.
Kuma Allah Masanin abinda
ke cikin zukata ne, yana yin uquba, akan niyyatar aikata savo, a gari mai
alfarma (Makka), to yaya kuma idan aka aikata savon, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma duk wanda ya
yi nufin karkata a cikinsa, da zalunci, za mu xanxana masa daga azaba mai
raxaxi"
[Hajji: 25].
Kuma Allah ya ce: "Allah ya san
yaudarar idanu, da abinda qiraza ke voyewa" [Gafir: 19].
Mutanen jahiliyya tare da kasancewarsu akan shirkinsu, saidai
suna girmama gari mai alfarma (Makkah), har xaya daga cikinsu kan haxu da wanda
ya kashe masa Uba, a Makkah, amma ba zai tayar masa da maganar ba. Don haka,
Musulmi na gaskiya shi ne wanda ke girmama ababen da Allah Mabuwayi da xaukaka
ya basu girma, kuma ya ke kula da haqqoqin 'yan'uwantakar musulunci, ya kuma
basu wata kulawa, Allah ta'alah yana cewa: "Duk wanda ya
girmama wuraren ibadar Allah, lallai hakan yana daga ayyukan taqawar zukata" [Hajji: 32].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai
matsanancin qarfi, Ina yin yabo ga Ubangijna, kuma ina gode masa, akam
ni'imominSa, waxanda waninsa ba zai iya qididdige su ba,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai mulki,
Na gaskiya, Mabayyani,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah ka qara salati da
sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa gaba
xaya.
Bayan haka … !!
Ku yi taqawar Allah, iyakar
taqawa, kuma ku yi riqo a cikin addininku da igiya mai qarfi.
Ya ku Musulmai … !!
Lallai Allah ta'alah cikin
jin-qansa, ya shar'anta mana hanyoyin samun alkhairi masu yawa, da qofofin
ayyuka nagari.
Don haka, mutumin da ba a
qaddara masa yin hajji, a wani lokacin ba, to haqiqa Allah ya yi masa baiwar, iya
kusantar Allah da dukkan sauran hanyoyin alkhairi, da falaloli waxanda ake
samun kwatankwacin ladan wanda ya yi hajji da umrah idan aka aikata su, Allah
ta'alah yana cewa: "Sai ku yi tsere ga ayyukan alkhairi, zuwa ga Allah ne
makomarku ta ke, sai ya ba ku labarin abinda kuka kasance a cikinsa ku ke
savani"
[Ma'idah: 48].
Kuma Allah ta'alah ya ce:
"Kuma duk wanda ya aikata kyawawa, alhalin yana mumini, to babu musu
ga aikinsa, kuma lallai mu masu rubutawa ne a gare shi" [Anbiya'i: 94].
Kuma an ruwaito a cikin
hadisi cewa: "Ka ji tsoron Allah a duk inda
ka kasance, kuma ka biyar da kyakkyawa bayan mummuna, sai ya goge shi, kuma ka
yi mu'amala da mutane da xabi'a mai kyau", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi
ne hasan.
A wassu bugun litttafin
kuma, hadisi ne mai kyau sahihi, daga hadisin Mu'azu bn Jabal.
Ya ku Bayin Allah…
!!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama ta aminci"
[Ahzab: 56].
……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment