BULAGURO ZUWA HAJJI
(رحلة ملبي)
TANADAR
(زاد)
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Allah ya umarci annabi
Ibrahima (alaihis salam) da ya xaga ginin masallaci mai alfarma, sa'annan ya
kira mutane zuwa ga hajji, sai wannan wurin ya kasance mai albarka, kuma shiriya
ga talikai, kuma zuwa gare shi, rayukansu su ke shauqi, kuma zukatansu su ke
karkata.
Kuma a shekara ta tara (9) ta hijira ayar da ba a soke
hukuncinta ba, ta sauka ga Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama), wanda ta ke
wajabta wa mutane hajjin xakin Allah, ga wanda ya samu hanyar zuwa gare shi, domin
hajjin ya kasance farilla daga farillan musulunci, da rukuni daga cikin
rukunnan musulunci, (Kuma Allah ya wajabta wa mutane, hajjin wannan xakin,
ga wanda ya samuhanyar tafiya gare shi, kuma duk wanda ya kafirce to lallai
Allah mawadaci ne ga halittu) [Ali-imraana: 97].
Don haka,
Ya zama wajibi ga musulmi, ya yi gaggawan sauke farillar hajji,
duk lokacin da ya kasance yana da iko, saboda bai san mai zai kasance tare da
shi ba, idan ya jinkirta shi, saboda ya zo cikin hadisi daga Annabi (sallal
lahu alaihi wa sallama) lallai shi ya ce: (ku yi gaggawan yin hajji –yana
nufin na farilla- saboda xayanku be san abinda ka-iya bijiro masa ba) [Ahmad
ya ruwaito shi, 1/314, kuma Albaniy y ace hadisi ne hasan a cikin littafin
Irwa'ul galil, 990].
Kuma wajibi ne ga wanda ya yi azamar aiwatar da wannan
farillar mai girma
1-
SHIRI A GARE TA, ta hanyar gangariyar tuba
2-
DA IKHLASIN niyya ga Allah shi kaxai,
sai ya nemi ganin fiskar Allah, da hajjinsa, da kuma gidan lahira.
3-
Sai kuma YA YI QOQARIN
SAUKE HAQQOQI, DA BASUKA, DA KAYAN MUTANE DA SU KE HANNUNSA.
4-
Sai kuma ya yi WASIYYA GA
IYALANSA DA BIN DOKOKIN ALLAH da taqawa.
5-
Sai kuma ya rubuta
wasiyyarsa, idan akwai abinda zai yi wasiyyar da shi, na haqqoqi da wasunsu.
6-
Ya kuma TANADI GUZURI daga
dukiya ta halal.
7-
Ya kuma nemi abokan tafiya
nagari.
8-
Ya kuma KOYI FIQIHUN HAJJI
da SIFAR HAJJI.
9-
YANA MAI YIN GUZURI DA
LITTAFAN MA'ABUTA ILIMI da suke Magana akan haka.
Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa
sallama) ya ce:
(UMRAH ZUWA UMRAH SUNA
KANKARE ABINDA YA AUKU TSAKANINSU, SHI KUMA HAJJI GANGARIYA BASHI DA WANI
SAKAMAKO FACE ALJANNAH) [Bukhariy da Muslim].
No comments:
Post a Comment