HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12 /ZULQA'ADAH/1438H
daidai
da 04/OGOSXOS/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Ya ku musulmai …
Duniya kaxan ce, mai qarewa, ni'imar
lahira kuma tana da girma, tana wanzuwa,
Ya zo daga Almustaurid bn Shaddad (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wallahi! Duniya idan an yi kwatanci da lahira, ba komai ba ce, sai
kamar misalin xayanku, ya sanya hannunsa a cikin teku, sai xayanku ya yi dubi
da me hannunsa zai koma", Muslim ya
rawaito shi.
Don haka, Duniya kamar ruwan da ya
maqale ne a yatsar wanda ya nitsar da ita a cikin kogi mai yawan ruwa, Ita kuma
lahira ita ce kamar sauran kogin da ruwansa ke maqare, wanda kumfarsa ke
hauhawa, tashinsa kuma ke xaukaka,
Ta yaya Mai sakaci zai yi sakaci kan
ni'imar lahira, saboda wani abin duniya qasqantacce, wanda kuma an yi kusa a
barta, kuma rabuwa da ita ya qarato, kuma babu abinda ya saura daga duniya face
tavo mai sharri da wari, da dudduvin ruwa mai gauraye, da ababen firgici na
xaukar izina, da uqubobi masu wanzuwa, da fitintinu yanki- yanki, da jeruwan
musibu masu tsanani, da sakacin mutanen qarshe, da qarancin mataimaka, cikin
rayuwar da ta cakuxa da gauraye, wanda ke haxe da zogi da raxaxi.
Sai ku ji tsoron Allah da taqawa –Ya ku
bayin Allah- saboda mutuwa an qulla ta a goshinku, duniya kuma ana nannaxe ta,
ta bayanku, kuma sau-dayawa rauni ya kan yi kisa, kuma tuntuve na iya
halakarwa, kuma sau-dayawa kalma tana halakarwa.
Ya kai bawan Allah… !!!
Da za ka xauka duniya gaba xayanta, tana
hannunka,
Da kwatankwacinta, duka an haxa maka,
To me, ze wanzu na duniya, a wurinka, lokacin mutuwarka?
Cikin kowani yini akwai tarin ababen lura,
Kuma cikin yadda ake mutuwa, akwai abin hani, in ka kasance wanda
zai hanu
To, kuma har yaushe, zuwa yaushe
Ba za ka hanu daga aikata laifi ba, kuma ba za ka yi taqawa ba,
Har zuwa yaushe za ka cigaba da dogewa cikin ruxu, da gafala
Kuma har yaushe irin wannan barcin,
kuma a wani yinin za ka farka
Haqiqa rayuwa ta tozarta, mummunan tozarci,
Alhalin sa'a xaya daga cikinta za a saye ta, da gwargwadon cikin
sama, da qasa,
Mai qarewa, za ka canza da mai wanzuwa, saboda wautarka
Ko ka canji neman fushin Allah da yardarsa, ko shiga wuta da
aljanna
A hakan, Shin kai masoyin kansa ne, ko maqiyi?
Domin kana jifan ranka da dukkan musiba
Haqiqa ka sayar da ranka, Vacin ran da zanyi akanka mai araha ne
Alhalin ta kasance da haka, ba na haqiqa ba
Ya ku musulmai!!!
Lokutan rayuwa suna xauke da abin lura,
wanda qaddara ta ke gudana da su, mulki ne da ake tsige shi, da lafiyar da ake
xauke ta, da bala'in da ke aukuwa,
kuma kowani mahaluki an yi shi domin
qarewa, haka shima mulki na tafiya domin qarewa, kuma babu mai dawwama idan ba
mulkin Allah ba; tsarki ya tabbata a gare shi sarki Mai mulki Mai rinjaye,
wanda kuma ya kaxaitu da buwaya da wanzuwa. Duk wanda ba shi ba kuma, to mai
qarewa ne.
Me ya samu idanu ga su a bubbuxe, amma basu gani!
Me ya samu qaiqasassun zukata basu yin tunani!!
Me ya samu rayuka su ke mantuwa; basu tunawa!!!
Ko dai talalar da aka yi a gare su, shi ya ke ruxar su?
Ko kuma ayyukansu ne suka musu albishir da samun tsira?
Ko kuma basu da tabbaci ne, a batun qarewar duniya?
Ko ruxuwa ce ta mamaye su, sai rufi ya yi dabaibayi ga zukatansu?
Ya ke Rai; wanda ta ke ganin tana da yalwar lokaci,
Ya wanda ke ganin akwai wata saurar dama,
Ka taqaita buri, saboda lamarin ba a hannunka ya ke ba
Kuma alama, ko tutar mutuwa tana gaba gare ka
Shin ka manta, cewa mu mutane ne?
Wanda qaddara ke lulluve da mu,
Kuma muna cikin wata tafiya,
Wacce muke qarewa a cikin ramukan qabari?
Mutuwa za ta naxe mu,
Sa'annan za a tattara mu
To kuma har yaushe, ba za ka dena savo; ka hanu daga aikata su ba,
Kuma har yaushe jinka ba zai kiyaye maganar mai wa'azi ba
Zuciyarka kuma, ba zata yi taushi, ga maganar mai jan kunne ba
Shin lokacin qanqan-da kai, bai yi ba? Ina kuma sallar dare
Shin a cikin gyangyaxi mu ke, ko zuciyar ce, ta qaiqashe?
Ka farka –Ya kai xan'uwana- kuma ka kiyaye,
kuma ina horonka akan barcin gafala
Shin za ka yi barci –Ya ruxaxxe- alhalin wuta ana rura ta
Kuma zafinta ba a kashe shi, garwashinta kuma baya mutuwa
Madalla da mutumin da tunatarwa ta amfanar da
shi
Sai wa'azi ya faxakar da shi,
sai ya kama aiki haiqan, bai zama cikin gafala ba
Ya kuma zage damtse; bai ruxu ba
Ya yi gaggawa, bai riqa cewa: da-sannu ba
Ya yi taka-tsan-tsan, ya kuma qauracewa abokan banza
Ya mayar da lamari ga Allah, ya tuba
Hasara kuma ta tabbata ga mutumin da son
zuciyarsa ya lulluve masa gaskiya,
Shexaninsa kuma ya vatar da shi, ya dulmuyar da shi,
Bai qaru da komai ba face, gafala da qaiqashewar zuciya, da
ji-da-kai, da girman-kai
"Ka ce: (Allah
ya ce) Ya ku bayina, waxanda suka yi varna akan
rayukansu, kada ku xebe tsammani daga rahamar Allah, lallai ne Allah yana
gafarta zunubai gaba xaya, kuma lallai shi Mai gafara ne Mai jin-qai" [Zumar: 53].
HUXUBA TA BIYU
Yabo na Allah ne; wanda ya kai matuqa wajen cika, da qurewarsa.Yabon
da ke hukunta yardarSa, kuma ya ke qarin kusantarwa zuwa gare shi,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, shaidawar
da mu ke fatan samun afuwar Ubangijinmu da jin-qanSa,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa; kuma annabinSa
zavavvenSa, abin ganawarSa, majivincinSa, abin yardarSa, kuma abin zavinSa.
Allah
yayi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya
yi aiki da sunnarsa, kuma ya shiryatu da shiriyarsa.
Ya ku musulmai!!!
Ku
bi dokokinAllah da taqawa, saboda taqawar Allah ita ce babbar abin nema, kuma xa'a
a gare shi, shine mafi xaukakar nasaba, "Ya ku
waxanda su ka yi imani ku bi dokokin Allah, iyaka tsoronsa, kuma kada ku mutu
face kuna musulmai" [Ali-imrana: 102].
Ya ku Musulmai!!
Ya waxanda ku ke tsoron abu mai guba,
Ya waxanda ku ke guduwa daga zafin rana,
Ya wanda ku ke bayyanar da raki, akan tsananin zafi; na lokacin
bazara,
Ya waxanda ku ke maganin cutarwar zafi, da dangogin tufafin
auduga, da kittani da riguna,
Kuma ku ke yin garkuwa daga tartsatsin rana da gidajen cikin qasa,
da waxanda su ke maganin zafi, da bishiyoyi da gidaddaji, da runfuna da lemomi,
da kuma (uwa-uba) balaguro zuwa garurruka masu sanyi,
Ku nemi kariya daga wutar jahannama, da barin aikata savo, saboda wuta, ita tafi dacewan ku gudu daga
gare ta, da garwashinta da dafin gubanta,
Kana gudun zafin rana, kuma kana neman kariyarsa,
To me yasa ba za ka gudu daga aukawa wutar jannama ba?
Rayuwarka ta hanyar kariya, ka qarar da ita, kana mai tsoron abu
mai sanyi ko zafi
Sai dai abin da ya fi dacewa a gare ka, shi ne, ka kiyaye, yin
savo, domin kada ka auka cikin wuta,
Lallai, ku -a yau-
kuna cikin wani zamanin fitintinu ratata, da sharrace-sharracen da su ke a jejjere,
fitintinu irin na shubuhohi, da sha'awowi, waxanda sashensu ke sassauta sashe, qurar
fitinar ta taso, aukuwarta kuma ta sanya zogi, cikin rayuwa marashin tabbas, wanda
ta ke xaukar duk mutumin da ya miqa mata wuya, zuwa koma-baya, cikin aqidarsa
da xabi'unsa, ta mayar da shi kuran baya cikin tunaninsa da halayensa,
Sai ku farkar da
zukata, daga makwancin gafalarsu, kuma ku karkatar da rayuka daga magangarar
sha'awarsu, kuna masu fakewa a qarqashin inuwar littafin Allah, da kuma Sunnah,
Kuma, ku sani
lallai ku, kuna cikin kwanakin jinkirtawa, wanda kuma a bayansu sai zuwan ajali,
cikin gaggawa,
Kuma duk wanda
yau xinsa bai amfane shi ba, to nesansa shi ya fi wahala a gare shi, kuma
abinda ya vuya masa zai fi gazawa a cikinsa,
Kuma lallai babu
barcin da ya fi gafala nauyi,
kuma babu bautar da ta fi mallake mutum fiye da sha'awarsa,
kuma babu musibar da ta fi mutuwar zuciya,
kuma babu mai gargaxin da ya fi furfura (ko tsufa),
babu makomar da ta fi muni fiye da wuta,
saboda wuta "Ba komai ba ce,
face tunatarwa ga mutane * A aha, (Allah ya ce:) ina rantsuwa da wata, da dare a lokacin da ke juyar da baya * da safiya
a lokacin da ta waye * lallai (wutar) xayan manyan musifu ce * mai gargaxi ce ga
mutane * Wanda ya so daga cikinku ya gabata, ko ya jinkirta" [Mudassir: 31-37].
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad Mai shiryarwa, Mai ceton mutane gabaxaya;
saboda idan Mutum ya yi salati a gare shi guda xaya, sai Allah
ta'alah ya yi masa guda goma,
Ya Allah ka yi salati da sallama ga
bawanka kuma manzonka Muhammadu,
Kuma ya Allah ka
yarda da dukkan iyalan Annabi da sahabbai,
Ka haxa da mu, Ya Mai
karimci, Ya Mai yawan baiwa,
Ya Allah ka xaukaka musulunci da
musulmai,
Kuma ka qasqantar da shirka
da mushirkai,
Kuma ka halaka maqiya
wannan addinin,
Ka sanya wannan qasa ta
zama cikin aminci da zaman lafiya da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah ka datar da shugabanmu
kuma jagoranmu izuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda,
Ka kama qeyarsa izuwa
biyayyarka da aikin taqawa
Ya Allah ka datar da xaukacin masu
jagorantar lamuran musulmai izuwa ga yin hukunci da shari'arka,
da bin sunnar annabinka Muhammadu
(صلى الله عليه وسلم), Ya Ubangijin
halittu.
Ya Allah ka zama mai taimakon garin
Halab da Shaam,
Ya Allah ka tausaya wa rauninsu,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka saukar da azaba da
qasqanci da fushinka ga wanda ya rushe gidajensu akansu,
Ya Allah ka kashe su da makaminsu,
ka qona su da wutar da su
ka fura,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka tseratar da waxanda ake
ta raunana su daga cikin musulmai, a kowani wuri, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kawo aminci a
iyakokinmu,
ka kare rundunoninmu,
ka taimake su akan
maqiyanka kuma maqiyansu,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka karvi matattunsu cikin
shahidai,
ka warkar da wanda aka yi
masa rauni daga cikinsu,
Ya Mai amsa addu'a.
Ya Allah ka sanya addu'anmu ya zama
karvavve,
Sautinmu kuma abun xagawa,
Ya Mai karimci, Ya Mai
girma, Ya Mai jin qai.
No comments:
Post a Comment