FALALAR GOMAN FARKO NA WATAN HAJJI
(وليال عشر)
TANADAR
(زاد)
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Yana daga falalar Allah
ta'alah akan bayinsa, yadda ya sanya musu lokaitai na musamman, na qara yin ayyukan xa'a, waxanda a cikinsu ake
ninnika lada, dan mutane su yi ta gasa a cikin ayyukan da za su kusantar da su, zuwa ga Ubangijinsu a
cikin waxannan lokutai,
Daga cikin waxannan lokutan
MASU FALALA:
KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN WATAN
HAJJI, Wannan
kuma ya kasance ne, saboda abinda Allah ya ajiye a cikinsu, na falalarSa, da
kuma yadda ya ke karrama bayinSa,
Saboda a cikinsu ne;
Ake samun YININ DA AKE KIRA
RANAR TARWIYAH (wato, takwas ga wata), da RANAR ARFAH, da RANAR LAYYAH,
Kuma domin girman sha'anin
kwanakin nan guda goma ne, Allah ya yi rantsuwa da su, a cikin faxinsa:
"INA RANTSUWA DA ALFIJIR * DA
KUMA DARARE GUDA GOMA"
[Fajr: 1-2].
Kuma Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa sallama) ya bada
labarin cewa, su ne mafifitan yinin da ake da su a duniya, a cikin faxinsa:
"Mafi girman kwanakin duniya
su ne, kwanakin nan guda goma", wato: goman farkon watan hajji.
[Ibnu-Hibban ya rawaito shi, kuma Albaniy ya inganta
shi].
Abu-Usman An-Nahdiy yana cewa:
"Magabatan kwarai sun kasance
suna girmama, kwanaki goma daga watanni uku, GOMAN QARSHE NA WATAN RAMADHANA,
da GOMAN FARKO NA WATAN HAJJI, da GOMAN FARKON WATAN MUHARRAM".
YAYA YA KAMATA MUSULMI YA TARBI WAXANNAN KWANAKIN?
An rawaito daga Abdullah ibn Abbas yana cewa:
Manzon Allah –sallal lahu
alaihi wa sallama- ya ce:
"Babu wasu kwanaki da aiki
nagari ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah Mabuwayi da xaukaka, fiye da
waxannan kwanakin",
wato, goman farko na watan hajji.
Sai sahabbai su ka ce: Ya
Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne, fi sabilillah?
Sai ya ce: "Koda jihadi ne, fi
sabilillah, sai ga mutumin da ya fita da kansa, da kuma dukiyarsa baki xaya, amma
shi da dukiyar tasa babu wanda ya koma". [Bukhariy ya ruwaito shi, 969].
Shi kuma, AIKI NA GARI Ya qunshi dukkan nau'uka na ibada, kamar azumi, da sallah, da hajji, da zikiri, da yin kabbara;
domin girmama Allah ta'alah, da tilawar Alqur'ani, da ciyarwa ta fiskokin
biyayya, da makamantan haka,
Daga cikin ibadodin da shari’a ta qarfafa YINSU A
WAXANNAN KWANAKI
YIN AZUMI: In banda rana ta goma (wato,
ranar sallah), saboda hadisin da aka ruwaito daga daya daga cikin Matan Manzon
Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ta ce:
"Manzon Allah –sallal lahu
alaihi wa sallama- ya kasance yana azumtar kwanaki tara na watan hajji".
[Abu-dawud da An-Nasa'iy ne
suka ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi].
Musamman yin azumi a ranar
arfah ga wanda ba mahajjaci ba, wanda azumtarsa, ke kankare zunaban shekaru
biyu.
ABU NA BIYU: Daga cikin ibadun da
shari’a ta qarfafi YINSU A WAXANNAN KWANAKI
YAWAN AMBATON ALLAH DA
KABBARORI,
Allah ta'alah yana cewa:
"KUMA SU AMBACI SUNAN ALLAH,
CIKIN KWANAKI SANANNU, AKAN ABINDA YA AZURTA SU DA SHI, NA DABBOBIN NI’IMA
(wato, raquma, da shanu, da tumaki)" [Hajj, 28].
KWANAKI SANANNU a cikin ayar sune KWANAKIN
GOMAN FARKO NA WATAN HAJJI.
ABU NA UKU: Daga cikin ibadun da
shari’a ta qarfafi YINSU A WAXANNAN KWANAKI
YIN AIKIN HAJJI,
Kuma shine mafificin ayyukan
da ake yi a cikin waxan nan kwanaki guda goma,
Manzon Allah –sallal lahu
alaihi wa sallama- yana cewa:
"Hajji mabruri (wato, hajji
karvavve), bashi da sakamako, face Aljannah" [Bukhariy da Muslim].
ABU NA HUXU: Daga cikin ibadun da
shari’a ta qarfafi YINSU A WAXANNAN KWANAKI
YIN LAYYAH,
Duk wanda ya yi nufin yin
Layyah, to sai ya kame, daga yanke gashinsa da faratunsa (akaifa),tun daga
shigar watan hajji, har zuwa lokacin da zai yanka, abin layyansa.
JAZAKALLAHU KHAIRAN.
ReplyDeleteAllah yasaka da alkairi
ReplyDelete