SHAR'ANTA
YIN SALLAMA DA AMSATA, DA YIN ADDU'A GA MAI ATISHAWA IDAN
YACE: "ALHAMDU LILLAH", DA ZIYARAR GAIDA MARAS LAFIYA([1])
An karvo
hadisi daga Abdullahi xan
Amru bn Al-aas (y),
lallai wani mutum ya tambayi Annabi (r):
أَيُّ الْإِسْلَامِ خَيْرٌ؟
قَالَ: «تُطْعِمُ
الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلَامَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ، وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
Ma'ana: "Wanne
musuluncin ne ya fi alheri? Sai ya ce: Ka ciyar da abinci, ka kuma yi sallama
ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba"([2]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An karvo
hadisi daga Abu-hurairah (t),
ya ce: Manzon Allah (r)
yace:
«لَا تَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ
حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا، أَوَلَا أَدُلُّكُمْ
عَلَى شَيْءٍ إِذَا فَعَلْتُــمُوهُ تَحَابَبْتُمْ؟ أَفْشُوا السَّلَامَ
بَيْنَكُمْ».
Ma'ana: "Ba za ku
shiga aljanna ba har sai kun yi imani, ba za ku yi imani ba har sai kun so
junanku, Shin ba zan nuna muku wani abinda idan kun aikata shi za ku so junanku
ba? Ku watsa sallama a tsakaninku"([3]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai Annabi
(r)
ya ce:
«خَمْسٌ تَجِبُ لِلْمُسْلِمِ عَلَى
أَخِيهِ: رَدُّ السَّلَامِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ،
وَعِيَادَةُ الْمَـــرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ».
Ma'ana: "Abubuwa
guda biyar suna wajaba ga musulmi akan xan'uwansa, amsa sallama, da addu'a ga
mai atishawa, da amsa gayyata, da ziyarar gaida maras lafiya, da rakiyar gawa"([4]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An sake samowa daga gare shi
(t)
daga Annabi (r)
lallai ya ce:
«حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى
الْمُسْلِمِ سِتٌّ» قِيلَ: مَا هُنَّ يَا رَسُولَ
اللهِ؟، قَالَ: «إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ، وَإِذَا دَعَــــاكَ
فَأَجِبْهُ، وَإِذَا اسْتَنْصَحَكَ فَانْصَحْ لَهُ، وَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللهَ
فَسَمِّتْهُ، وَإِذَا مَرِضَ فَعُدْهُ وَإِذَا مَاتَ فَاتَّبِعْهُ».
Ma'ana: "Haqqin musulmi akan musulmi guda
shida ne, Sai aka ce: Menene su ya ma'aikin Allah? Sai ya ce: Idan ka
gana da shi ka yi masa sallama, idan kuma ya gayyace ka to ka amsa masa, idan
ya nemi nasiharka ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya ce: alhamdu
lillah to sai ka yi masa addu'a, idan ya yi jinya ka ziyarce shi, in kuma ya
mutu ka raka gawarsa"([5]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai Annabi
(r)
ya ce:
«إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ
الْعُطَاسَ وَيَكْرَهُ التَّثَاؤُبَ فَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللَّهَ فَحَقٌّ
عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ سَمِعَهُ أَنْ يُشَمِّتَهُ، وَأَمَّا التَّثَاوُبُ
فَإِنَّمَا هُوَ مِنَ الشَّيْطَانِ فَلْيَرُدَّهُ مَا اسْتَطَاعَ، فَإِذَا قَالَ:
هَا ضَحِكَ مِنْهُ الشَّيْطَان».
Ma'ana: "Lallai
Allah ta'alah yana son atishawa, yana kuma qin hamma, don haka; idan xayanku ya yi atishawa sai kuma
ya ce: alhamdu lillah, to haqqi ne ga kowani musulmin da ya ji shi ya masa addu'ar nema
masa rahama (ya ce: Yarhamukal lahu), Amma shi kuma hamma to daga Shexan ne,
don haka; mutum ya mayar da shi gwargwadon iko, Idan ya ce: Ha,a,a Sai shexan ya yi ta yi masa dariya"([6]). Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
An sake karvowa
daga gare shi, daga Annabi (r)
yace:
«التَّثَاؤُبُ مِنَ
الشَّيْطَانِ، فَإِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ فَلْيَكْظِمْ مَا اسْتَطَاعَ».
Ma'ana: "Yin
hamma daga shexan ne,
idan xayanku
ya yi hamma to ya kame gwargwadon iko"([7]). Muslim ya ruwaito shi.
An karvo
daga Abu-sa'id alkhudriy (t),
ya ce: Manzon Allah (r)
yace:
«إِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ، فَلْيُمْسِكْ
بِيَدِهِ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ».
Ma'ana: "Idan xayanku zai yi hamma to ya kame
bakinsa da hannunsa, saboda shexan yana shiga"([8]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai
shi ya ce:
«إِذَا عَطَسَ أَحَدُكُمْ،
فَلْيَقُلِ: الْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلْـيَـقُلْ لَهُ أَخُوهُ أَوْ صَاحِبُهُ:
يَرْحَمُك اللهُ، وإذا قال له: يَرْحَمُك اللهُ فَلْيَقُلْ: يَهْدِيكُمُ اللهُ
وَيُصْلِحُ بَالَكُمْ».
Ma'ana: "Idan xayanku ya yi atishawa yace:
ALHAMDU LILLAH, Sai xan'uwansa
ko abokinsa ya ce: YARHAMUKAL LAHU, Idan ya ce masa: Yarhamukal lahu, to sai
yace: YAHDIYKUMUL LAHU WA YUSLIHU BAALAKUM"([9]). Bukhariy ya ruwaito shi.
Abu-musa al-ash'ariy (t) yace:
«إِذَا عَطَسَ أَحَدُكُمْ
فَحَمِدَ اللَّهَ فَشَمِّتُوهُ، وَإِذَا لَمْ يَحْمَدِ اللَّهَ فَلَا تُشَمِّتُوهُ».
Ma'ana: "Idan xayanku ya yi atishawa sai ya ce:
alhamdu lillah, to ku yi addu'ar neman rahama a gare shi, idan kuma bai ce:
alhamdu lillahi ba kada ku yi masa wannan addu'ar"([10]). Muslim ya ruwaito shi.
$&$
$&$
No comments:
Post a Comment