2016/08/04

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم TA Alhuzaifiy 02 Zul'ka'adah 1437H daidai 05 Ogasdos 2016M






HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 02/ZUL-QA'ADAH/1437h




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah Ma'abucin girma da karramawa, da matsayi da xaukaka, kuma ma'abucin bada ni'imomi, Wanda ya cancanci yabo, a halin farin ciki, da cuta. Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina yin godiya a gare shi, Ina kuma tuba zuwa gare shi; ina neman gafararSa,
Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Ubangijin qasa da sama,   
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonsa;  wanda ya aiko da miqaqqen addini mai sauqi,
Ya Allah! Ka yi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu biyayya da bin dokoki da taqawa.

Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, ta hanyar yin biyayya a gare shi, saboda taqawar Allah ita ce: Mafi alherin guzuri. Kuma babu wanda zai yi riqo da taqawa face ya rabauta da samun alherorin duniya, kuma ya tsira a yinin komawa ga Allah, (سبحانه) Allah yana cewa: "Wanda ya bi dokokin Allah zai kankare masa munanan aiyukansa, kuma ya girmama lada a gare shi" [Xalaq: 5].

            Ya ku Mutane!
            Ku tuna abinda Allah ya kwararo akanku, da abinda ya muku baiwarsa na ni'imomi, da waxanda ya tunkuxe muku na bala'o'i, Ku yi mamakin kyautar Allah! Kuma ka yi mamakin girman baiwarSa, tare da faxi ko yalwar rahamarSa, da kyan shari'arSa,
            Yana daga cikin RAHAMARSA: Kasancewar Allah ya shar'anta wa Bayi abinda zai amfanar da su, ya sanya su cikin walwala, kuma ya rayar da su rayuwa daddaxa, amintacciya;
            Sai Allah ya shar'anta wa bayi SABUBAN da aminci yake samuwa da su, da zaman lafiya da nitsuwa, da samun rayuwa mai karimci, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya waxanda suka yi imani, ku amsa wa Allah, da kuma Manzo, idan ya kira ku zuwa ga abinda zai raya ku" [Anfal:  24]. 

            Shi AMINCI ganuwa ne da ya tsare Musulunci. Su kuma ma'abuta musulunci sune suke zaune a cikin wannan ganuwar, Ita ganuwar ta kan kare su daga cutarwar maqiya musulunci, Su kuma musulmai su suke kula da wannan ganuwar; saboda kada mavarnata su rushe ta (ganuwa). Don haka shi aminci; shine katangar musulunci wanda musulmai suke samun kariya daga gare ta, kuma ita katangar ita take toshe musu ta'addancin mavarnata, da zaluncin azzalumai. Sai su kuma musulmai su riqa gadin wannan katangar daga gaturan rushewa, suna kuma kiyaye ta daga tsagewa, ko faxuwa, Saboda abinda Allah ya sanya a cikin wanzuwar aminci da zaman lafiya na/ KIYAYE ADDINI, da JINANE da MUTUNCI, da DUKIYOYI, da DAMAR CANJIN KAYAN AMFANI, da 'YANCIN MOTSAWA A CIKIN RAYUWA, a cikin dukkan aiyukanta, da KIYAYE HANYOYI, waxanda ta cikinsu mutane suke kaiwa izuwa ga dukkan garurruka, domin biyan buqatunsu da maslahohinsu da jawo arziqinsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Shin bamu basu harami amintacce ba ne, wanda ake kawo masa 'ya'yan itatuwan kowani abu, arziqi daga wurinmu!? Saidai kuma mafi yawansu basa sani" [Qasas: 57].
An ruwaito daga Ubaidullahi xan Muhsin (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda ya wayi-gari a cikinku da aminci ga ransa, ko a cikin jama'arsa da iyalansa da dukiyarsa, ya wayi-gari da lafiya a cikin jikinsa, ya wayi-gari a wurinsa akwai abincin yininsa, to kamar an haxa masa duniya ne gabaxayanta", Tirmiziy ya ruwaito, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau.
            Shi "AMINCI" ana gwama ambatonsa da "IMANI", kuma "aminci" yana daidai da "musulunci", An ruwaito daga Xalhah xan Ubaidullahi (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan ya ga jinjirin wata sai ya ce:
«اللَّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلَيْنَا بِالْأَمْنِ وَالْإِيمَانِ، وَالسَّلَامَةِ وَالْإِسْلَامِ، رَبِّي وَرَبُّكَ اللَّهُ، هِلَالُ خَيْرٍ وَرُشْد».
Ma'ana: "Ya Allah! Ka bayyanar da jinjirin wata akanmu da aminci da imani, da kuma salama da musulunci, Ubangijina kuma Ubangijinka shine Allah, Jinjirin watan alheri, da shiriya", Tirmiziy ya ruwaito, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau.

            AMINCI fa Shine samun nitsuwa ga ADDINI.
            Kuma shine samun nitsuwa ga MUTUNCI.
            Kuma shine samun nitsuwa ga DUKIYOYI da abubuwan da aka mallaka, kuma masu alfarma.
            Da samun nitsuwa ga HANYOYI, ta hanyar kada mutum ya riqa jin tsoro akan haka, gabaxaya.
            Da kuma samun nitsuwa ga HAQQOQI na ma'ana, da waxanda mutane suka xora wa kansu, wanda kuma musulunci ya basu lura da kulawa; Ta hanyar rashin tozartar da haqqoqin; ko lalata su da tauye su.

            Aminci na daga musulunci, Ita kuma shari'ar musulunci ta zo ne domin baiwa musulmi tabbacin samun aminci, a cikin RAYUWARSA, da kuma bayan MUTUWARSA, kuma domin ya rayu rayuwa daddaxa amintacciya, kamar yadda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Wanda ya yi aiki na kwarai, namiji ne ko mace, alhalin yana mumini, lallai za mu rayar da shi, rayuwa daddaxa, kuma za mu sakanta musu ladansu da mafi kyan abinda suka kasance suke aikatawa" [Nahl: 97].

            Kuma shi TAUHIDIN Ubangijin halittu shine wajibi na farko, kuma duk wanda ya tabbatar da tauhidi, To sai Allah yayi masa sakayya da samun aminci da shiriya, kuma sai ya kiyaye shi da uqubobin shirka a nan duniya, Ya kuma kiyaye shi daga tavewa da tsoro; a lahira, Allah (تعالى) a qissar babanmu; Annabi Ibrahima (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ya ce: Shin za ku yi jayayya da ni a lamarin Allah, alhalin ya shiryar da ni, kuma ba zan ji tsoron abinda kuke masa shirka da shi ba, Saidai wani abinda Ubangijina ya nufa, Ubangijina ya game komai da ilimi, Shin ba za ku wa'aztu ba * Kuma ta yaya zan tsoraci abinda ku ka yi shirka, ku kuma ba kwa jin tsoron kun yi shirka wa Allah, abinda babu wata hujja, Wane vangare ne cikin biyun; yafi cancantar aminci idan kun kasance kuna sani * Waxanda suka yi imani, kuma ba su cuxanya imaninsu da wani zalunci ba -shirka- Waxannan suna da wani irin aminci, kuma su shiryayyu ne" [An'am: 80-82].
Imam ibnu-Taimiyya (رحمه الله) ya ce: ((Duk wanda ya kuvuta daga jinsin zalunci guda uku; waxanda sune: Shirka, da zaluntar bayi, da zaluntar mutum ga kansa, da abinda bai kai shirka ba, To wannan cikakken aminci zai kasance a gare shi, da samun shiriya cikakkiya. Wanda kuma bai kuvuta daga zaluntar kansa ba, to zai samu muxlaqin aminci ne, da muxlaqin shiriya)) Maganarsa ta qare  –Wato ibnu-taimiyyah na nufin cewa: Irin wannan, za su samu aminci da shiriya ne: gwargwadon yadda suka kuvuta daga laifukan da suke qasa da babbar shirka-.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Firgici mafi girma ba zai baqanta musu rai ba, kuma mala'iku suna ganawa da su, Wannan shine yininku da kuka kasance ake muku alkawari" [Anbiya'i: 103].

            Samun aminci, yana daga cikin SABUBANSA: Musulmi ya yi aiki da shari'ar musulunci, saboda ita shari'ar musulunci tana lamunce bada haqqoqin Allah (تعالى), da haqqoqin bayi, kuma shari'ar tana yin hani kan aikata savo, da zalunci, da qetare iyaka, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka tsayar da sallah, Lallai sallah tana hana alfasha da munkari, kuma ambaton Allah shine mafi girma" [Ankabut: 45] har qarshen ayar.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Kuma an ruwaito daga Abu-Hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kada ku yi hassada yi wa juna, kada ku yi kore (cikin kasuwanci), kada kuyi qiyayya da juna, kada ku juya wa juna baya, kuma kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin xan'uwansa. Ku kasance bayin Allah ‘yan'uwan juna. Musulmi xan'uwan musulmi ne, baya zaluntarsa, baya qin taimakonsa, baya yi masa qarya, baya wulaqantar da shi. Taqawar Allah tana nan, (har sau uku) -Yana nuna qirjinsa, Ya ishi mutum sharri, ya riqa raina xan'uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi. Muslim ne ya ruwaito shi [2564]".
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Kada ku zalunci kafiran amana".

            Kuma haqiqa Allah ya sanya AMINCI ya zama abin lura, kuma sharaxi ga wasu daga cikin ibadodi, da hukunce-hukunce, Allah (تعالى) yana cewa dangane da yin sallah a cikin sifarta, ba a hali na tsoro ba: "Kuma idan za ku yi sallah, sai ku ambaci Allah a tsaye, da a zaune, da kuma akan kuivinku, kuma idan kuka samu nitsuwa sai ku tsayar da sallah, lallai ne sallah ta kasance akan muminai wajiba ce mai lokaci" [Nisa'i: 103].

            Itama ZAKKA ba a iya karvota daga dukiya ta zahiri (tumaki, shanu…) da 'ya'yan itatuwa da kwaya, Sai idan akwai cikakken aminci.

            Kuma Allah (تعالى) a dangane da HAJJI yana cewa: "Idan kuka samu aminci, to wanda ya yi tamattu'in umrah zuwa hajji, ya gabatar da abinda ya sauqaqa na hadaya" [Baqara: 196].

            Kuma lallai ibadodi suna samun xaukaka idan aka yi su cikin aminci, akan ibadodin da aka yi su cikin yanayi na tsoro, Allah (تعالى) yana cewa: "Allah ya yi alkawari ga waxanda suka yi imani, daga cikinku, kuma suka aikata aiyuka kyawawa, lallai zai shugabantar da su a cikin qasa kamar yadda ya shugabantar da waxanda suke, daga gabaninsu, kuma lallai ne zai tabbatar musu da addininsu wanda ya yarda musu, kuma lallai ne, zai musanya musu, daga bayan tsoro, da wani aminci, suna bauta mini basa haxa ni da komai. Kuma wanda ya kafirta a bayan wannan, lallai waxancan, sune fasiqai" [Nur: 55].

            Kuma yana daga cikin SABUBAN samun aminci: Al'umma ta kula da zaman lafiya, ta kiyaye shi daga mavarnata, da masu rushe-rushe, da masu laifuka, da masu qetare iyaka, ta hanyar yin umurni da kyakkyawa, da hani kan mummuna, da faxakarwa da shiryarwa da karantarwa, da tsawatarwa kan bidi'oi da aikata haramun, da tsawatarwa kan aqidar fito-na-fito da jama'ar musulmai da jagoransu, da daga ko bada sunayen karkatattun mutane, mavarnata, da ma'abuta laifuka, ga shugaba, matuqar sun doge kan aikata laifi abin qi, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma wata al'umma ta kasance daga cikinku, suna yin da'awa zuwa ga alkhairi, kuma suna yin umurni da kyakkyawa, suna yin hani ga mummuna, kuma waxannan sune masu samun rabo" [Ali-imrana: 104]. 
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy (رضي الله عنه) Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ga mummuna daga cikinku to, ya canza shi da hannunsa, Wanda kuma ba zai iya ba to, ya canza da harshensa, Wanda kuma ba zai iya ba to, da zuciyarsa, Wannan kuma shine mafi raunin imani", Muslim ya ruwaito shi.

            Yana daga cikin Manyan SABUBAN samuwar aminci da zaman lafiya: Qarfin shugaba, da yadda yake kame hannun masu aikata laifuka, da tsawatar musu kan aikata varna a doron qasa, da abinda shari'a mai sauqi (ta musulunci) ta tabbatar, Saboda azzalumi mai ta'addanci akan toshe qofar sharrinsa da abinda zai hana ko toshe zaluncinsa da ta'addancinsa, koda kuwa musulmi ne.
Shi kuma kafirin amana daga cikin ahlul kitabi (yahudu da nasara) akan tabbatabar da shi akan addininsa, saboda sharrinsa da kafircinsa yana taqaituwa ne akansa, matuqar dai bai yi ta'addanci ga wani ba.   

            Shi kuma SHUGABA abun tambaya akan abinda aka bashi kiyo, Usman (رضي الله عنه) ya ce:
"Lallai Allah yana hana aukuwar varna –a bayan qasa- ta hanyar samun tsayayyen shugaba, fiye da hanin alqur'ani ga aukuwar savo –ga masu raunin imani-".

            Kuma mafi kyan halin al'umma shine: Addininsu ya kasance mai qarfi, sannan shugabansu shima ya kasance mai qarfi, A irin wannan halin lamuran al'umma za su kasance akan mafi kyan hali, cikin addininsu da duniyarsu.

            Hali na biyun kuma da yake biye da wancan Shine: Idan shugaba ya kasance mai qarfi, sai kuma aka samu raunin addini a wurin sashin al'umma, to a nan shugaba zai gyara su, ta hanyar kame hannayen mavarnata da masu laifuka, don haka, al'umma a cikin irin wannan halin zata hau tudun mun tsira.

            Kuma lallai ne, ta hanyar bibiyar hukunce-hukunce musulunci, da yadda mutane suka sanya su cikin aiki: Za mu samu, ko mu san cewa/ Mutane dayawa daga cikin musulmai, bayan sun yi shekaru masu yawa, Wani mutum bai tava neman wani abu da suka zalunce shi, a cikin jini (ko rayuka), ko tava mutunci, ko dukiya, ko wani haqqin (na daban) ba; wannan kuma bai kasance ba sai saboda yadda suka yi aiki da hukunce-hukuncen shari'ar musulunci, kuma suka sauke haqqoqin da suka rataya a wuyansu.
Kuma lallai waxannan sun mori ni'imar aminci da imani.
Kuma duk wanda ya yi aiki da shari'ar musulunci a rayuwarsa to babu wata hanyar kama shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi gaskiya cikin faxinsa:
"Cikakken musulmi shine wanda musulmai suka kuvuta daga sharrin harshensa da hannunsa".

            Kuma lallai lamarin aminci, Shari'a ta kewaye shi da katanga ta kiyayewa don ba shi kariya mai qarfi, saboda a jikin aminci Allah (تعالى) ya rataya amfanin mutane na addini dana duniya, Don haka; Idan wani ya yi ta'addanci, ta hanyar yin zina, ko irin aikin mutanen annabi Lux, to sai shugaba ya tsayar masa da haddi, domin kiyaye mutunci da karama da kuma dangantaka, idan har an samu tsayuwar shaidu da hujjoji. Haka idan wani ya gurgunta aminci, da yin sata, sai a tsayar masa da haddi domin kiyaye dukiyoyi. Idan kuma wani ya sha abu mai bugarwa, ko yayi amfani da kayan sanya maye, ko ya tallata su, to lallai ya qetara ko yayi ta'addaci ga katangar aminci, sai kuma ayi masa haddi, domin kiyaye kwakwale.
Idan kuma ya zubar da jini da-gangan, sai shugaba ya tsayar masa da haddin qisasi, domin bada kariya ga jinane da rayuka.
Idan wata jama'a ta taso, ta zubar da jinane ko ta kashe rayuka na haram, ko suka kwace dukiya, ko tuntsurar da ababen da aka mallaka, to sai shugaba ya tsayar da hukuncin Allah (تعالى) wanda y azo cikin faxinsa:
"Kawai sakamakon waxanda suke yaqar Allah da ManzonSa, kuma suke yawo a bayan qasa da varna, shine a kakkashe su, ko a tsire su, ko a gugguntule hannayensu da qafafunsu da savani, ko a kore su daga qasa, Wannan kuma wulaqanci ne a gare su a duniya, kuma a lahira suna da azaba mai girma * Saidai waxanda suka tuba gabanin ku samu iko akansu, to ku sani lallai ne Allah Mai gafara ne Mai rahama" [], Kuma duk wanda Allah da ManzonSa suka yaqe shi to lallai ne ya tave.

            Kuma babu wata uquba da aka tanada face don ta kare al'umma daga sharrin masu ta'addanci ga amincin al'umma ko qetare iyaka. Kuma domin su zama kaffara da kankarar zunubai. Kuma duk wanda ya tuba, sai Allah ya karvi tubarsa.
Kuma duk wanda Allah ya rufa masa asiri cikin zunubinsa, kuma ya zama bai cutar da wani ba, to hisabinsa yana ga UbangijinSa.

            Kuma idan Allah ya yi baiwar aminci ga al'umma to sai arziqinsu samunsa ya musu sauqi, rayuwarsu ta bunqasa, dukiya ta kwarara, al'amura su ci-gaba, rayuwarsu ta yi daxi, kuma sai a kiyaye rayuka da dukiyoyi da mutunci.
Amma idan aminci ya yi rauni, sai rayuwa ta kasance –a lokacin gurvacewar- ma'abuciyar xaci, da ba za a iya jure mata ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Allah ya buga misalin wata alqarya, wacce ta kasance amintacciya natsattsiya; arziqinta yana zuwa mata a wadace daga kowani wuri, Sai ta kafirta da ni'imomin Allah; Sai Allah ya xanxana mata tufafin yunwa da tsoro saboda abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahli: 112].

            Shi yana daga cikar addini, kuma yana cikin manufofin shari'a masu girma, An ruwaito daga Khabbab bn Al'arat (رضي الله عنه) y ace:
"Mun kai kukanmu zuwa ga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) alhalin yayi matashi da alkebba, a qarqashin inuwar ka'aba, Sai muka ce: Shin ba z aka nema mana nasara ba, shin ba z aka yi addu'a a gare mu ba? Sai ya ce: Waxanda suka zo a gabaninku haqiqa sun kasance ana xaukar mutum daga cikinsu, sai a tona masa rami a cikin qasa, a sanya shi a cikinsa, Sa'annan sai a zo da zarto, sai a sanya shi a kansa; a raba shi kashi biyu. Kuma ana ttaje musu kai da abin tajewa na qarfe, tsakanin namansa da qashinsa, amma hakan baya hana shi yin addininsa. Na rantse da Allah! Akan cewa Allah zai cika wannan lamarin (addini), har sai mahayi ya yi tafiya daga garin San'a'a har zuwa HadaraMaut, bay a tsoron komai sai Allah, da kuma kerekeci ga dabbobinsa, Saidai ku, kuna yi gaggawa ne ", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Allah (تعالى) yana cewa:
"Ku ambace ni zan ambace ku, kuma ku yi godiya a gare ni, kada ku kafirce mini" [Baqara: ].

            Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima,      kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban manzanni, da kuma maganganunsa miqaqqu,    Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma wa Ni da Ku, da kuma sauran musulmai,     Ku nemi gafararSa; lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.


HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,   Mai matsanancin qarfi. 
Kuma ina shaidawa lallai shigabanmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa ne Amintacce.
            Ya Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.

Bayan haka;;;
            Ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma ku yi riqo a musulunci da igiya mai qarfi.

            Bayin Allah…
            Lallai ni'imar aminci da zaman lafiya ni'ima ce mai girma.
Kuma  daga cikin mutane akwai masu godiya ga ni'imomi, sai ayi masa sakayya daga Allah, kuma sai Allah ya yi masa qari.
Akwai kuma daga cikin mutane waxanda basa ganin girman ni'imomi, kuma basa haquri akansu, to sai ayi musu uquba, kuma a haramta musu ita, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan muka xanxana wa Mutum wata rahama daga gare mu, sa'annan muka kwace ta daga gare shi, lallai ne shi mai xebe tsammani ne, mai yawan kafirci * Amma da za mu xanxana masa wata ni'ima, bayan cuta da ta shafe shi, sai ya ce: Munana sun kauce mini, lallai ne shi mai farin ciki ne mai alfahari * Saidai waxanda suka yi haquri, kuma suka aikata kyawawa, to waxannan kam suna da wata gafara da kuma lada mai girma" [Hud].

            Shari'ar Allah ita ce: Jin qai da adalci da musulunci, da alkhairi da aminci da Imani, Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Allah yafi girman rahama ga bayinsa, fiye da Uwa ga 'ya'yanta".

Bayin Allah,,,

"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin,   Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Manzon Allah kuma (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda yayi mini salati guda xaya to Allah zai yi masa salati guda goma ".
Sai ku yi salati da sallama ga shugaban mutanen farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni;
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Kuma ka yi musu sallama; tsiratarwa mai yawa.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya, da waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai,
Ya Allah ! ka kashe bidi'oi har zuwa ranar tashi qiyama;  
Ya Allah! Ka dusar da wutar bidi'a; wacce ta ke cin karo da addininka, kuma take cin karo da shari'arka,
Ya Allah! Ka kashe bidi'oi, har zuwa tashin qiyama, lallai kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ya Allah!
Ya Allah! 
       Addu'oi;;;;;;;;;;;;;;;;
            ;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;
            ;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;
"Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90]


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...