HADISAI
ARBA'IN (40)
KAN
HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA
أربعون حديثا تتعلق
بالحج والعمرة والزيارة
TATTARAWAR
DA TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم
الله الرحمن الرحيم
والصلاة
والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار
النبوية التي تتعلق بالعمرة والحج وزيارة المدينة، والله أسأل القبول والإخلاص،
فقد ورد عن عُمَرَ بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّمَا
الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ
هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ،
وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا
فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ». رواه
البخاريّ، ومسلم([1]).
An ruwaito
daga Umar xan Alkhaxxabi (r.a) ya ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"Dukkan aiyuka su kan inganta tare da niyya, kuma lallai kowane mutum
yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah
ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma
hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko saboda wata matar
da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da yayi hijira dominsa. Bukhariy
[lamba: 1], da Muslim [lamba: 1907] suka ruwaito shi.
بيان
أنّ حج بيت الله الحرام من الخمس التي بني عليها الإسلام
عَنِ عبد الله بْن عمر رضي الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ
الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ،
وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه البخاري ومسلم([2]).
AIKIN HAJJI NA CIKIN GINSHIQAI BIYAR DA AKA
GINA MUSULUNCI AKANSU
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace:
Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan abubuwa
guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu
manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da yin hajjin wannan xakin, da
azumin watan ramadana".
Bukhariyy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
بيان أنّ الحج مِن أسباب دخول الجنة
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قال: قلت يا رسول الله أَخْبِرْنِي
بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الْجَنَّةَ، وَيُبَاعِدُنِي مِنَ النَّارِ؟ قَالَ: "لَقَدْ سَأَلْتَ عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ
عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ اللهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللهَ وَلَا تُشْرِكُ بِهِ
شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ،
وَتَحُجُّ الْبَيْتَ".
الحديث رواه الترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
YIN HAJJI INGANTACCE SABABI NE
NA SHIGA ALJANNA
An
ruwaito daga Mu’azu xan Jabal (R.A) yace: Nace ya Manzon Allah bani labarin
wani aiki da zai shigar da ni aljanna, kuma ya nisantar da ni daga shiga wuta,
sai ya ce: Haqiqa ka yi tambaya game da abu mai girma, saidai abu ne mai sauqi
ga wanda Allah ya sauqaqe shi a gare shi; ka bauta wa Allah ba tare da ka haxa
shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka, kuma ka azumci
Ramadan, sannan ka ziyarci xakin Allah. Tirmiziy ya ruwaito shi [
2616] kuma yace: Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
قَالَ: «العُمْرَةُ
إِلَى العُمْرَةِ كَفَّارَةٌ لِمَا بَيْنَهُمَا، وَالحَجُّ المَبْرُورُ لَيْسَ
لَهُ جَزَاءٌ إِلَّا الجَنَّةُ»([3]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (Allah ya qara
yarda a gare shi), Lallai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ((Umrah zuwa wata
umarah na kankare zunuban da ke tsakaninsu, hajji kuma kuvutacce ba shi da
sakayya sai aljanna) Bukhariy da Muslim.
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ حَجَّ لِلَّهِ فَلَمْ يَرْفُثْ، وَلَمْ
يَفْسُقْ، رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ»([4]).
An ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya qara
yarda a gare shi-, Lallai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (Duk wanda ya yi
aikin hajji don Allah, bai yi batsa ko jima'i ba, da fasikanci: zai komo kamar
ranar da uwarsa ta haife shi), Bukhariy.
بيان فرض
الحج في العمر مرة
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ:
خَطَبَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ! قَدْ فَرَضَ اللهُ
عَلَيْكُمُ الْحَجَّ، فَحُجُّوا»، فَقَالَ رَجُلٌ: أَكُلَّ عَامٍ يَا رَسُولَ اللهِ؟ فَسَكَتَ حَتَّى
قَالَهَا ثَلَاثًا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"لَوْ قُلْتُ: نَعَمْ لَوَجَبَتْ، وَلَمَا
اسْتَطَعْتُمْ"،
ثُمَّ قَالَ: «ذَرُونِي مَا
تَرَكْتُكُمْ، فَإِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِكَثْرَةِ سُؤَالِهِمْ
وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِشَيْءٍ فَأْتُوا
مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ، وَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَدَعُوهُ»، رواه مسلم.
BAYANI KAN FARLANTA HAJJI SAU XAYA A RAYUWA
An ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya qara
yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya yi mana huxuba Sai ya ce:
(Ya
ku Mutane! Lallai ne Allah ya farlanta hajji akanku; sai ku yi hajji. Sai wani
mutum ya ce: Shin a kowace shekara ne ya ma'aikin Allah? Sai yace: Da na ce: E! da
hakan ya wajaba, da kuma kun gagara iyawa). Sannan ya
ce: Ku bar ni a yadda na qyale ku, lallai ne abinda ya halakar da waxanada
su ka zo gabaninku shi ne yawan tambayoyinsu, da savawarsu ga Annabawansu; Don haka, idan na
umurce ku da wani abu to ku zo da shi gwrgwadon iko, idan kuma na hane ku kan
wani abu to ku qyale shi” Muslim (1337).
بيان أن الحج على الفور
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم: "تَعَجَّلُوا إِلَى الْحَجِّ؛ فَإِنَّ أَحَدَكُمْ
لا يَدْرِي مَا يَعْرِضُ لَه"([5]).
GAGGAUTA YIN HAJJI
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas –Allah ya
qara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya
ce: "Ku yi gaggawar zuwa hajji; saboda xayanku bai san abinda ka
iya bijiro masa ba".
بيان مَن
استطاع الحج فمات ولم يحج
عن أبي أمامة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "مَنْ اسْتَطَاعَ الْحَجّ
فَلَمْ يَحُجَّ؛ فَلْيَمُتْ إنْ شَاءَ يَهُودِيًّا وَإِنْ شَاءَ نَصْرَانِيًّا"([6]).
WANDA YA SAMU IKON YIN HAJJI, HAR YA MUTU BAI YI BA
An ruwaito
daga Abiy-Umamah -Allah ya qara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah –Sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Wanda ya samu damar ya yi hajji, sai kuma
bai yi hajjin ba, to ya mutu in ya ga dama a bayahude, ko in ya so ya mutu akan
addinin nasara".
وعن قتادة قال: ذُكِر لنا أنَّ عمرَ بن الخطاب رضي
الله عنه قال: «لَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ
أَبْعَثَ إِلَى الْأَمْصَارِ فَينظروا كل من كان لَهُ جدَّةٌ ولَمْ يَحُجَّ
ليضربوا عَلَيْهِم الْجِزْيَةَ،
مَا هم بمُسْلِمِينَ، مَا هم بمُسْلِمِينَ» [سنن سعيد بن منصور].
Kuma Sa'idu xan Mansur ya ruwaito -a cikin littafinsa "sunan"-
daga Qatada ya ce: An ambata mana cewa Umar xan Al-khaxxab -Allah ya qara yarda a gare
shi- ya ce: "Haqiqa na niyyaci na tura zaratan mazaje zuwa waxannan biranen; don
su duba duk waxanda
suke da yalwar dukiya amma basu yi aikin hajji ba, sai su buga jiziya akansu, su
ba musulmai ba ne, su ba musulmai ba ne".
وعن علي بن أبي طالب رضي الله عنه، قال: «مَنْ قَدَرَ عَلَى الحَجِّ فَتَرَكَه
فَلاَ عَلَيْهِ أَنْ يَمُوتَ يَهُودِيًّا، أَوْ نَصْرَانِيًّا».
An
ruwaito daga Aliyu -Allah ya qara yarda
a gare shi- lallai ya ce: "Duk wanda ya samu ikon hajji sai ya qi ya je, babu wata
damuwa akansa in yaga dama ya mutu bayahude, ko banasare". A
wani lafazin kuma:
عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ مَلَكَ زَادًا وَرَاحِلَةً
تُبَلِّغُهُ إِلَى بَيْتِ اللَّهِ وَلَمْ يَحُجَّ فَلَا عَلَيْهِ أَنْ يَمُوتَ
يَهُودِيًّا، أَوْ نَصْرَانِيًّا، وَذَلِكَ أَنَّ اللَّهَ يَقُولُ فِي كِتَابِهِ:
{وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ البَيْتِ مَنْ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلًا،
وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عن العالمين} [آل عمران: 97]"، رواه الترمذي([7]).
An ruwaito daga Aliyu
xan Abiy-xalib –Allahya
qara yarda a gare shi-, daga Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa
sallama- –cikin
hadisi marfu'u-, ya ce: "Duk mutumin da ya mallaki guzuri da
abin hawa, da zai iya kai shi xakin Allah, sai ya qi ya yi hajji, babu wata damuwa akansa in yaga dama ya mutu
bayahude, ko banasare; Saboda Allah a cikin littafinSa yana acewa: ((Allah ya wajabta
wa mutane ziyartar wannan xakin; ga wanda ya samu hanya izuwa gare shi. Kuma
wanda ya kafirce to lallai ne Allah Mawadaci ne ga barin halittu)) [Ali-Imraan: 97]".
وجوب الحج على المكلف (البالغ العاقل) المستطيع
عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "رُفِعَ
الْقَلَمُ عَنْ ثَلاثَةٍ: عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ، وَعَنِ
الْمَجْنُونِ حَتَّى يفيق، وعَنِ الصَّغِيرِ حَتَّى يَبْلُغَ"([8]).
HAJJI NA WAJABA NE AKAN BALIGI
MAI HANKALI, MAI IKO
An ruwaito daga Aliyu (r.a), daga Annabi
(s.a.w) lallai shi ya ce: "An xauke alqalami akan mutane guda uku;
Ga mai barci har sai ya tashi, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake, da
qaramin yaro har sai ya balaga".
وعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ
رضي الله عنهما، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَقِيَ رَكْبًا
بِالرَّوْحَاءِ، فَقَالَ: «مَنِ
الْقَوْمُ؟» قَالُوا: الْمُسْلِمُونَ، فَقَالُوا: مَنْ أَنْتَ؟
قَالَ: «رَسُولُ
اللهِ»، فَرَفَعَتْ إِلَيْهِ امْرَأَةٌ صَبِيًّا،
فَقَالَتْ: أَلِهَذَا حَجٌّ؟ قَالَ: «نَعَمْ، وَلَكِ
أَجْرٌ»([9]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas –Allah ya
qara yarda a gare shi-, ya ce: daga Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa
sallama- lallai ne shi ya haxu da wasu mahaya a Rauha'u, Sai ya ce: "Su wanene? Sai su ka
ce: Musulmai ne. Sannan suka ce: Kai kuma wanene? Sai ya ce: "Manzon Allah ne), Sai wata mata ta xaga
wani yaro, ta ce: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai hajji akan wannan? Sai
ya ce: E, ke kuma kina da lada", Muslim.
وعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "أَيُّمَا صَبِيٍّ حَجَّ ثُمَّ
أَدْرَكَ فَعَلَيْهِ حَجَّة أُخْرَى، وَأَيُّمَا عَبْدٌ حَجَّ ثُمَّ عتِقَ فَعَلَيْهِ
حَجَّة أُخْرَى"([10]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas –Allah ya
qara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon
Allah –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Duk wani yaron da
ya yi hajji, sannan ya balaga, to wajibi ne akansa ya yi wani hajjin na daban,
Duk kuma bawan da ya yi hajji sa'annan aka 'yanta shi, to wajibi ne akansa ya
yi wani hajjin na daban".
عَنِ السَّائِبِ بْنِ
يَزِيدَ رضي الله عنه، قَالَ: «حُجَّ بِي مَعَ رَسُولِ
اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا ابْنُ سَبْعِ سِنِينَ» رواه البخاري.
An
ruwaito daga Al-Sa'ib xan Yazid
–Allah ya qara yarda a gare shi- ya ce: "An yi hajji da ni, tare da Manzon
Allah alhalin ina xan
shekaru bakwai" Bukhariy ya ruwaito shi([11]).
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لا يَحِلُّ لامْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ
الآخِرِ، أَنْ تُسَافِرَ سَفَرًا يَكُونُ ثَلاثَةَ أَيَّامٍ فَصَاعِدًا، إِلا وَمَعَهَا
أَبُوهَا، أَوِ ابْنُهَا، أَوْ زَوْجُهَا، أَوْ أَخُوهَا، أَوْ ذُو مَحْرَمٍ مِنْهَا"، رواه مسلم([12]).
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy –Allah ya
qara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon
Allah –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Baya halatta ga
wata mace; da ta yi imani da Allah da kuma ranar qarshe; ta yi tafiya ta
kwanaki uku, ko fiye, face a tare da ita akwai ubanta, ko xanta, ko mijinta, ko
dan'uwanta, ko kuma wani muharraminta" Muslim ya ruwaito shi.
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَال: «لاَ يَخْلُوَنَّ رَجُلٌ بِامْرَأَةٍ إِلَّا مَعَ ذِي مَحْرَمٍ، وَلَا تُسَافِرِ الْمَرْأَةُ إِلَّا
مَعَ ذِي مَحْرَمٍ» فَقَامَ رَجُلٌ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إنَّ امْرَأَتِي خَرَجَت حَاجَةً، وإِنِّي اكْتُتِبْتُ فِي غَزْوَةِ كَذَا،
قَالَ: (انْطَلِقْ فَحُجَّ مَعَها)"([13]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas –Allah ya
qara yarda a gare shi-, ya ce: daga
Annabi –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Kada wani ya keve
da wata mace face a tare da su akwai muharrami, kuma kada mace ta yi tafiya
face a tare da ita akwai muharrami" Sai wani
mutum ya tashi; ya ce: Ya ma'aikin Allah! Lallai ne matata ta fita izuwa ga
hajji, lallai ni kuma an rubuta ni don zuwa yaqi wuri kaza: Sai ya ce: "Ka tafi kayi hajji
tare da ita".
وعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنِينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، أَنَّهَا
قَالَتْ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، نَرَى الجِهَادَ أَفْضَلَ العَمَلِ، أَفَلاَ
نُجَاهِدُ؟ قَالَ: «لاَ،
لَكُنَّ أَفْضَل الجِهَادِ حَجٌّ مَبْرُورٌ» رواه البخاري"([14]).
An ruwaito daga A'ishah - Allah ya qara yarda
a gare ta- lallai ne ta ce: Ya ma'aikin Allah! Muna ganin jihadi shine
mafificin aiki; Shin ba za mu yi jihadi ba? Sai ya ce: "A'a! Ku mata kuna
da mafificin jihadi; wanda shi ne: Hajji kuvutacce"
Bukhariy ya ruwaito shi.
وعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ
عَلَى النِّسَاءِ جِهَادٌ؟ قَالَ: "نَعَمْ، عَلَيْهِنَّ جِهَادٌ لا قِتَالَ فِيهِ:
الْحَجُّ وَالْعُمْرَة"([15])، أحمد وابن ماجه.
An ruwaito daga A'ishah - Allah ya qara yarda
a gare ta- ta ce: Na ce: Ya ma'aikin Allah, Shin akan mata akwai wajabcin
jihadi? Sai ya ce: "E, akwai jihadi akansu wanda babu zubar da jini a
cikinsa; aikin hajji da umrah".
وروى الطبراني بسنده إلى أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا
خَرَجَ الرَّجُلُ حَاجًّا بِنَفَقَةٍ طَيِّبَةٍ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ فِي الْغَرْزِ،
فَنَادَى: لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ، نَادَاهُ مُنَادٍ مِنَ السَّمَاءِ:
لَبَّيْكَ وَسَعْدَيْكَ، زَادُكَ حَلَالٌ، وَرَاحِلَتُكَ حَلَالٌ، وَحَجُّكُ
مَبْرُورٌ غَيْرُ مَأْزُورٍ. وَإِذَا خَرَجَ بِالنَّفَقَةِ الْخَبِيثَةِ، فَوَضَعَ
رِجْلَهُ فِي الْغَرْزِ، فَنَادَى: لَبَّيْكَ، نَادَاهُ مُنَادٍ مِنَ السَّمَاءِ:
لَا لَبَّيْكَ وَلَا سَعْدَيْكَ، زَادُكَ حَرَامٌ وَنَفَقَتُكَ حَرَامٌ، وَحَجُّكَ
غَيْرُ مَبْرُورٍ» [الطبراني في الأوسط].
Imam Ax-xabaraniy ya ruwaito da isnadinsa
zuwa ga Abu-hurairah –Allah ya qara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah –Sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Idan mutum ya fita aikin hajji da dukiya
mai tsarki (ta halal) ya kuma sanya qafarsa akan abun hawansa, ya xaga sautinsa ya ce: LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA,
To sai mai kira ya kira shi daga sama cewa: An amsa maka, kuma ka rabauta,
kasancewar guzurinka na halal ne, abun hawanka na halal, kuma hajjinka ya zama
lafiyayye; ba irin wanda za a baka zunubi ba. Idan kuma ya fita da dukiya maras
tsarki (wacce ba ta halal ba) ya kuma sanya qafarsa akan abun hawansa, ya xaga sautinsa ya ce:
LABBAIKA, To sai mai kira ya kira shi daga sama cewa: Ba a amsa maka ba, kuma
ba ka rabauta ba, saboda guzurinka haram ne, abun cinka haram, kuma hajjinka
bai zama lafiyayye (kuvutacce) ba" Xabaraniy([16]).
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَجَّ هَذَا الْبَيْتَ فَلَمْ
يَرْفُثْ، وَلَمْ يَفْسُقْ رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ» متفق عليه.
An ruwaito daga Abu-hurairah –Allah ya qara
yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Wanda ya ziyarci
wannan xakin bai yi
jima'i ba, bai kuma yi fasiqanci
ba, zai koma daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi"
Bukhariy da Muslim([17]).
عَنْ أَبِي رَزِينٍ الْعُقَيْلِيِّ رضي الله عنه، أَنَّهُ قَالَ: يَا
رَسُولَ اللَّهِ إِنَّ أَبِي شَيْخٌ كَبِيرٌ، لَا يَسْتَطِيعُ الْحَجَّ، وَلَا
الْعُمْرَةَ، وَالظَّعْنَ قَالَ: "حُجَّ عَنْ أَبِيكَ واعْتَمِرْ"([18]).
An ruwaito daga Abu-razin -Allah ya qara yarda a gare shi-, lallai
ne shi ya ce: ya Manzon Allah, Lallai mahaifina tsoho ne mai girman shekaru;
wanda ba zai iya aikin hajji ko umra ko tafiya akan abin hawa ba, Sai ya ce: "Ka yi hajji ga
babanka, ka yi masa umrah", Abu-Dawud da Tirmiziy da Nasa'iy da
Ibnu-Majah.
بيان المواقيت المكانية لمريد الحج
والعمرة، والإهلال منها
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا،
قَالَ: «وَقَّتَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِأَهْلِ
المَدِينَةِ ذَا الحُلَيْفَةِ، وَلأَهْلِ الشَّأْمِ الجُحْفَةَ، وَلأَهْلِ
نَجْدٍ قَرْنَ المَنَازِلِ، وَلأَهْلِ اليَمَنِ يَلَمْلَمَ، هُنَّ لَهُنَّ، وَلِمَنْ
أَتَى عَلَيْهِنَّ مِنْ غَيْرِ أهلهِنَّ؛ مِمَّنْ أَرَادَ الحَجَّ وَالعُمْرَةَ، وَمَنْ
كَانَ دُونَ ذَلِكَ، فَمِنْ حَيْثُ أَنْشَأَ، حَتَّى أَهْلُ مَكَّةَ مِنْ مَكَّةَ"([19]).
BAYANIN MIQATAI GA WANDA YA NUFI HAJJI KO UMRA
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas -Allah ya
qara yarda a gare su-, ya ce: "Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa
sallama- ya sanya "ZULHULAIFAH" ga mutanen Madina a matsayin wurin
xaura niyya, mutanen Shaam kuma ya sanya musu "AL-JUHFAH", ga mutanen
Najdu kuma "KARNUL MANAZIL", mutanen Yamen kuma ya sanya musu
"YALAMLAM". Waxannan miqaatan na waxannan mutanen ne, da kuma duk wanda
ya zo musu ba daga cikin ahlin wajen ba; na waxanda suka nufi yin hajji da
umrah. Wanda kuma yake gaba (ta ciki) da waxannan miqatai to zai yi niyya ne
daga wurin da ya fari hakan, Su kuma mutanen Makka daga garin Makka"
Bukhariy da Muslim.
خ:
1542 –
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بن عمر ،
أَنَّهُ سَمِعَ أَبَاهُ، يَقُولُ: «مَا أَهَلَّ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَّا مِنْ
عِنْدِ المَسْجِدِ»
يَعْنِي مَسْجِدَ ذِي الحُلَيْفَةِ
م:
(1186) حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى، قَالَ: قَرَأْتُ عَلَى مَالِكٍ،
عَنْ مُوسَى بْنِ عُقْبَةَ، عَنْ سَالِمِ بْنِ عَبْدِ اللهِ، أَنَّهُ سَمِعَ
أَبَاهُ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، يَقُولُ: بَيْدَاؤُكُمْ هَذِهِ الَّتِي تَكْذِبُونَ
عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيهَا «مَا أَهَلَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ،
إِلَّا مِنْ عِنْدِ الْمَسْجِدِ» يَعْنِي ذَا الْحُلَيْفَةِ
صحيح خ:
1534 - حَدَّثَنَا الحُمَيْدِيُّ، حَدَّثَنَا الوَلِيدُ، وَبِشْرُ بْنُ بَكْرٍ
التِّنِّيسِيُّ، قَالاَ: حَدَّثَنَا الأَوْزَاعِيُّ، قَالَ: حَدَّثَنِي يَحْيَى،
قَالَ: حَدَّثَنِي عِكْرِمَةُ، أَنَّهُ سَمِعَ ابْنَ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُمَا، يَقُولُ: إِنَّهُ سَمِعَ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، يَقُولُ:
سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِوَادِي العَقِيقِ يَقُولُ: " أَتَانِي اللَّيْلَةَ آتٍ مِنْ
رَبِّي، فَقَالَ: صَلِّ
فِي هَذَا الوَادِي المُبَارَكِ [ص:136]، وَقُلْ: عُمْرَةً فِي حَجَّةٍ "
2337 - حَدَّثَنَا إِسْحَاقُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ، أَخْبَرَنَا شُعَيْبُ بْنُ
إِسْحَاقَ، عَنِ الأَوْزَاعِيِّ، قَالَ: حَدَّثَنِي يَحْيَى، عَنْ عِكْرِمَةَ،
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ، عَنْ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: " اللَّيْلَةَ أَتَانِي آتٍ مِنْ رَبِّي، وَهُوَ بِالعَقِيقِ، أَنْ صَلِّ فِي هَذَا الوَادِي المُبَارَكِ، وَقُلْ: عُمْرَةٌ فِي حَجَّةٍ "
7343 - حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ الرَّبِيعِ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ المُبَارَكِ،
عَنْ يَحْيَى بْنِ أَبِي كَثِيرٍ، حَدَّثَنِي عِكْرِمَةُ، قَالَ: حَدَّثَنِي ابْنُ
عَبَّاسٍ، أَنَّ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، حَدَّثَهُ قَالَ: حَدَّثَنِي
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: " أَتَانِي اللَّيْلَةَ آتٍ مِنْ
رَبِّي، وَهُوَ بِالعَقِيقِ، أَنْ صَلِّ فِي هَذَا الوَادِي المُبَارَكِ، وَقُلْ: عُمْرَةٌ
وَحَجَّةٌ " وَقَالَ
هَارُونُ بْنُ إِسْمَاعِيلَ، حَدَّثَنَا عَلِيٌّ: «عُمْرَةٌ فِي حَجَّةٍ»
ابن ماجة وصححه الألباني
2923 - حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ مُحَمَّدٍ قَالَ: حَدَّثَنَا وَكِيعٌ قَالَ:
حَدَّثَنَا سُفْيَانُ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي لَبِيدٍ، عَنِ الْمُطَّلِبِ
بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ حَنْطَبٍ، عَنْ خَلَّادِ بْنِ السَّائِبِ، عَنْ زَيْدِ
بْنِ خَالِدٍ الْجُهَنِيِّ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: "
جَاءَنِي جِبْرِيلُ، فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، مُرْ أَصْحَابَكَ فَلْيَرْفَعُوا أَصْوَاتَهُمْ بِالتَّلْبِيَةِ، فَإِنَّهَا مِنْ شِعَارِ الْحَجِّ "
ابن ماجة وصححه الألباني
2890
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: حَجَّ النَّبِيُّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى رَحْلٍ، رَثٍّ، وَقَطِيفَةٍ تُسَاوِي أَرْبَعَةَ
دَرَاهِمَ، أَوْ لَا تُسَاوِي، ثُمَّ قَالَ: «اللَّهُمَّ حَجَّةٌ لَا رِيَاءَ فِيهَا، وَلَا سُمْعَةَ»
بيان جواز التطيب عند الإحرام وبعد التحلل الأول
1536 في صحيح البخاري أَنَّ يَعْلَى قَالَ لِعُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَرِنِي
النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حِينَ يُوحَى إِلَيْهِ، قَالَ: "
فَبَيْنَمَا النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِالْجِعْرَانَةِ،
وَمَعَهُ نَفَرٌ مِنْ أَصْحَابِهِ، جَاءَهُ رَجُلٌ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ،
كَيْفَ تَرَى فِي رَجُلٍ أَحْرَمَ بِعُمْرَةٍ، وَهُوَ مُتَضَمِّخٌ بِطِيبٍ، فَسَكَتَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَاعَةً،
فَجَاءَهُ الوَحْيُ، فَأَشَارَ عُمَرُ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ إِلَى يَعْلَى،
فَجَاءَ يَعْلَى وَعَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ثَوْبٌ
قَدْ أُظِلَّ بِهِ، فَأَدْخَلَ رَأْسَهُ، فَإِذَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُحْمَرُّ الوَجْهِ، وَهُوَ يَغِطُّ، ثُمَّ سُرِّيَ عَنْهُ،
فَقَالَ: «أَيْنَ
الَّذِي سَأَلَ عَنِ العُمْرَةِ؟»
فَأُتِيَ بِرَجُلٍ، فَقَالَ: «اغْسِلِ الطِّيبَ الَّذِي بِكَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ، وَانْزِعْ عَنْكَ
الجُبَّةَ، وَاصْنَعْ فِي عُمْرَتِكَ كَمَا تَصْنَعُ فِي حَجَّتِكَ».
مسلم
7 - (1180) وحَدَّثَنَا ابْنُ أَبِي عُمَرَ، قَالَ: حَدَّثَنَا سُفْيَانُ، عَنْ
عَمْرٍو، عَنْ عَطَاءٍ، عَنْ صَفْوَانَ بْنِ يَعْلَى، عَنْ أَبِيهِ، قَالَ: أَتَى
النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ وَهُوَ بِالْجِعْرَانَةِ،
وَأَنَا عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَعَلَيْهِ
مُقَطَّعَاتٌ - يَعْنِي جُبَّةً - وَهُوَ مُتَضَمِّخٌ بِالْخَلُوقِ، فَقَالَ: إِنِّي أَحْرَمْتُ بِالْعُمْرَةِ وَعَلَيَّ
هَذَا، وَأَنَا مُتَضَمِّخٌ بِالْخَلُوقِ فَقَالَ لَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا كُنْتَ صَانِعًا فِي حَجِّكَ؟» قَالَ: أَنْزِعُ عَنِّي
هَذِهِ الثِّيَابَ، وَأَغْسِلُ عَنِّي هَذَا الْخَلُوقَ، فَقَالَ لَهُ النَّبِيُّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا كُنْتَ صَانِعًا فِي حَجِّكَ، فَاصْنَعْهُ فِي
عُمْرَتِكَ»
وعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَتْ: "كُنْتُ أُطَيِّبُ
رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم لِإِحْرَامِهِ قَبْلَ أَنْ يُحْرِمَ.
وَلِحِلِّهِ قَبْلَ أَنْ يَطُوفَ بِالْبَيْتِ" متفق عليه.
HALACCIN SHAFA TURARE GABANIN
HARAMA, DA BAYAN TAHALLUL NA FARKO
An ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها); matar Manzon Allah -Sallal lahu alaihi
wa sallama- tace: "Lallai na sanya wa
Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- turare lokacin haramarsa gabanin
ya yi haramar, da lokacin warware haramar gabanin ya je ya yi xawafin xakin Allah (na ifadha"
Bukhari da Muslim.
بيان ما يلبس المحرم وما لا يلبس
عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما، عَنِ النَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّ رَجُلًا سَأَلَهُ: مَا يَلْبَسُ
المُحْرِمُ؟ فَقَالَ: «لاَ يَلْبَسُ القَمِيصَ، وَلاَ
العِمَامَةَ، وَلاَ السَّرَاوِيلَ، وَلاَ البُرْنُسَ، وَلاَ ثَوْبًا مَسَّهُ
الوَرْسُ أَوِ الزَّعْفَرَانُ، فَإِنْ لَمْ يَجِدِ النَّعْلَيْنِ فَلْيَلْبَسِ
الخُفَّيْنِ، وَلْيَقْطَعْهُمَا حَتَّى يَكُونَا تَحْتَ الكَعْبَيْنِ، وَلاَ
تَنْتَقِبِ المَرْأَةُ المُحْرِمَةُ، وَلاَ تَلْبَسِ القُفَّازَيْنِ»([20]).
BAYANI AKAN MENENE MUTUMIN DA YA YI
HARAMA ZAI SANYA, MENENE KUMA BA ZAI SANYA BA (NA TUFAFI)
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar –Allah ya
qara yarda a gare su-, daga Annabi –Sallal lahu alaihi wa sallama-, Lallai wani
mutum ya tambaye shi cewa: Menene kayan da mutumin da ya yi harama zai sanya?
Sai ya ce: "Ba zai sanya riga ba, ba zai sanya rawani ba, haka ba zai sanya wanduna
ba, kuma ba zai sanya riga mai fula ba (burnus), ko kuma tufar da turaren waras
ko za'afaran su ka tava su. Idan kuma bai samu takalman silifas ba to sai ya
sanya huffi guda biyu, amma sai ya yanke su har su zama qasa da idanun sawu. Kuma
kada mai harama ta sanya niqaabi,
kuma kada ta sanya safar hannu biyu".
وفي لفظ عند الإمام أحمد: «وَلْيُحْرِمْ أَحَدُكُمْ فِي إِزَارٍ وَرِدَاءٍ، وَنَعْلَيْنِ، فَإِنْ لَمْ
يَجِدْ نَعْلَيْنِ فَلْيَلْبَسْ خُفَّيْنِ، وَلْيَقْطَعْهُمَا حَتَّى يَكُونَا
أَسْفَلَ مِنَ الْعَقِبَيْنِ»([21]).
A wani lafazin kuma na Imam Ahmad: "Xayanku ya yi harama cikin kwarjalle da mayafi, da
takalma silifas guda biyu, Idan kuma bai samu silifas biyu ba, to sai ya sanya
huffi guda biyu, sai kuma ya yanke su har su zama qasa da idanun sawu ". Ahmad
ya fitar da hadisin.
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: خَطَبَنَا
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِعَرَفَاتٍ، فَقَالَ: «مَنْ لَمْ يَجِدِ الإِزَارَ فَلْيَلْبَسِ
السَّرَاوِيلَ، وَمَنْ لَمْ يَجِدِ النَّعْلَيْنِ فَلْيَلْبَسِ الخُفَّيْنِ»([22]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas –Allah ya
qara yarda a gare su-, ya ce: Annabi –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya mana
khuxuba a arafaat, sai ya ce: "Duk wanda bai samu kwarjallen da zai xaura ba, to ya sanya
wando, wanda kuma bai samu takalma silifas guda biyu ba, to ya sanya huffi biyu".
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: «كَانَ
الرُّكْبَانُ يَمُرُّونَ بِنَا وَنَحْنُ مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُحْرِمَاتٌ، فَإِذَا حَاذَوْا بِنَا أَسْدَلَتْ إِحْدَانَا جِلْبَابَهَا
مِنْ رَأْسِهَا عَلَى وَجْهِهَا، فَإِذَا جَاوَزَنَا كَشَفْنَاهُ»([23]).
An ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها), lallai ta ce: "Mahaya sun kasance
suna shige mu alhalin muna tare da Manzon Allah (r) cikin haramar
aiki hajji, idan su ka zo daura da mu sai xayarmu ta saki hijabinta daga kanta zuwa
fiskarta, idan kuma su ka wuce sai mu yaye shi".
وعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا، أَنَّ رَجُلًا أَوْقَصَتْهُ
رَاحِلَتُهُ وَهُوَ مُحْرِمٌ فَمَاتَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اغْسِلُوهُ
بِمَاءٍ وَسِدْرٍ وَكَفِّنُوهُ فِي ثَوْبَيْهِ، وَلَا تُخَمِّرُوا رَأْسَهُ وَلَا
وَجْهَهُ، فَإِنَّهُ يُبْعَثُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مُلَبِّيًا»([24]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas -Allah ya
qara yarda a gare su- Lallai wani mutum abin hawansa (raquma) ya take wuyansa,
alhalin yana cikin harama, sai ya mutu, Sai Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: "Ku yi masa wanka da ruwa da gabaruwa, kuma ku sanya shi cikin
tufansa guda biyu ku yi masa likkafani da su, kuma kada ku lulluve masa kansa, ko
fiskarsa; saboda za a tayar da shi a ranar kiyamah yana yin talbiyyah
(LABBAIKAL LAHUMMA…)". Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
عن عُثْمَانَ بْن عَفَّانَ رضي الله عنه، قال: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَنْكِحُ
الْمُحْرِمُ، وَلَا يُنْكحُ، وَلَا يَخْطُبُ»([25]).
An ruwaito daga Usman -Allah ya qara yarda a
gare shi- ya ce: Manzon Allah –Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Mai harama baya yin
aure, kuma baya bada aure, kuma baya neman aure".
Muslim ya ruwaito shi.
بيان اشتراط التحلل بعذر
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: دَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى ضُبَاعَةَ بِنْتِ الزُّبَيْرِ بْنِ عَبْدِ
الْمُطَّلِبِ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا، فَقَالَ لَهَا: «لَعَلَّكِ أَرَدْتِ الحَجَّ؟» قَالَتْ: وَاللَّهِ لاَ أَجِدُنِي إِلَّا وَجِعَةً،
فَقَالَ لَهَا: «حُجِّي
وَاشْتَرِطِي، وَقُولِي: اللَّهُمَّ مَحِلِّي حَيْثُ حَبَسْتَنِي»([26]).
An ruwaito
daga A'isha -Allah ya qara yarda a gare ta-, Ta ce: Manzon Allah –Sallal lahu
alaihi wa sallama- ya shiga wa Duba'ah bint Az-zubair bn Abdilmuxxalib -Allah
ya qara yarda a gare ta-, Sai ya ce mata: "La'allakin nufin
zuwa hajji? Sai ta ce: Bana samun kaina face maras lafiya, Sai ya ce
mata: "Ki yi hajji, sai ki sanya sharaxi; Ki ce: Ya Allah! Wurin warware hajjina shi ne
wurin da ka kawo uzurin da ya riqe ni". Bukhariy da Muslim su ka ruwaito.
«إِنَّ
هَذَا الْبَلَدَ - يعني مكة - حَرَامٌ
بِحُرْمَةِ اللهِ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ، لَا يُعْضَدُ شَجَرُها، وَلَا
يُنَفَّرُ صَيْدُها، وَلاَ يُخْتَلَى خَلَاهَا، وَلاَ تَحِلُّ سَاقِطَتُهَا إِلاَّ
لِمُنْشِدٍ».
Ma'ana: "Lallai wannan garin –yana
nufin: Makkah- harami ne, da haramtawar da Allah ta'alah ya yi masa, har zuwa
tashin alqiyamah, ba
a cire bishiyoyinsa, ba a korar abun farautar cikinsa, haka ba a cirar ciyawar
da ta tsira a cikinsa, sannan kuma abun tsuntuwar cikinsa baya halatta a xauke
shi sai ga mai cikiyarsa"([27]).
Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
"اللَّهُمَّ
إِيمَانًا بِكَ، وَتَصْدِيقًا بِكِتَابِكَ، وَوَفَاءً بِعَهْدِك، واتِّبَاعًا
لسَنَة نَبِيِّكَ مُحَمَّد صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ".
"ALLAHUMMA IYMANAN BIKA, WA TASDIYQAN
BI KITABIKA, WA WAFA'AN BI AHDIKA, WAT TIBA'AN BI SUNNATI NABIYYIKA MUHAMMADIN
(r)". To hakan ya yi Kyau;
saboda faxin hakan
an ruwaito shi daga Annabi (r).
Ma'anar wannan kuma shi ne: "Ya Allah
(zan yi aikin xawafi
alhalin ) ina mai imani da kai, da gaskata littafinka, ina kuma cika alkawari
da nayi maka, tare da bin sunnar annabinka Muhammadu (r)".
(لاَ
إِلَهَ إِلاَّاللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ،
وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَحْدَهُ، أَنْجَزَ
وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ وَحْدَهُ).
"LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA
LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR, LA ILAHA
ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAHU, WA HAZAMAL AHZABA
WAHDAHU".
«افْعَلِي
مَا يَفْعَلُ الْحَاجُّ، غَيْرَ أَنْ لاَ تَطُوفِي بِالْبَيْتِ حَتَّى تَطْهُرِي».
Ma'ana: "Ki aikata duk abinda mai
hajji yake aikatawa, saidai ba za ki aikata xawafin xakin Allah ba, har sai kin yi
tsarki"([28]).
Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
(Aikin hajji shine tsayuwar arafah).
«خَيْرُ
الدُّعَاءِ دُعَاءُ يَوْمِ عَرَفَةَ، وَخَيْرُ مَا قُلْتُ أَنَا وَالنَّبِيُّونَ
مِنْ قَبْلِي: لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ
الْمُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».
Ma'ana: "Mafi alherin addu'a shine
addu'an yinin arafah, kuma mafi alherin abinda na faxa ni da annabawa a gabanina shine:
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA
ALA KULLI SHAI'IN QADIIR"([30]),
Muslim,
daga A'ishah (رضي الله عنها)
lallai Annabi (r) ya ce:
«مَا
مِنْ يَوْمٍ أَكْثَرَ مِنْ أَنْ يُعْتِقَ اللَّهُ فِيهِ عَبْدًا مِنَ النَّارِ
مِنْ يَوْمِ عَرَفَةَ، وَإِنَّهُ لَيَدْنُو ثُمَّ يُبَاهِى بِهِمُ الْمَلاَئِكَةَ
فَيَقُولُ: مَا أَرَادَ هَؤُلاَءِ؟».
Ma'ana: "Babu wani yini wanda Allah ya
fi 'yanta bayi a cikinsa daga wuta fiye da yinin arafah, kuma lallai Allah yana
kusantowa, sannan sai ya yi alfahari da su ga Mala'ikunsa, sai ya ce: Me waxannan su ka nufa?" ([31]).
«وَقَفْتُ
هَاهُنَا _ يعني: على المشعر
_، وَجَمْعٌ كُلُّهَا مَوْقِفٌ».
Ma'ana: "Ni na yi tsayuwata a nan
–yana nufin: akan mash'arul haraam- ita kuma muzdalifah dukkanta wurin tsayawa
ce" ([32]).
Muslim ya ruwaito shi
«كُنْتُ
أُطَيِّبُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِإِحْرَامِهِ قَبْلَ
أَنْ يُحْرِمَ، وَلِحِلِّهِ قَبْلَ أَنْ يَطُوفَ بِالْبَيْتِ».
Ma'ana: "Na sanya turare wa Manzon
Allah (r) saboda
yin haramarsa, gabanin ya yi haramar, da kuma lokacin da ya warware aikinsa
gabanin ya yi xawafin xakin ka'abah"([33]),
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
«مَنْ
كَانَ مَعَهُ هَدْيٌ فَلْيُهْلِلْ بِالْحَجِّ مَعَ الْعُمْرَةِ، ثُمَّ لاَ يَحِلُّ
حَتَّى يَحِلَّ مِنْهُمَا جَمِيعًا».
Ma'ana: "Wanda ya ke da hadaya a tare
da shi to ya yi haramar aikin hajji tare da umrah, sannan ba zai warware a
matsayin ya gama aikinsa ba sai a tare; su biyun", har zuwa faxinta:
«فَطَافَ
الَّذِينَ أَهَلُّوا بِالْعُمْرَةِ، بِالْبَيْتِ وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ،
ثُمَّ حَلُّوا، ثُمَّ طَافُوا طَوَافًا آخَرَ، بَعْدَ أَنْ رَجَعُوا مِنْ مِنًى
لِحَجِّهِمْ».
Ma'ana: "Sai waxanda suke aikin umrah suka yi xawafin xakin Allah, da kuma sa'ayi
tsakanin safah da marwah, sa'annan suka warware, daga bisani sai suka sake yin
wani xawafin na
daban bayan sun dawo daga minah; na hajjinsu"([34]).
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
A'ishah - رضي الله عنها-
ta ce:
"مَا أَتَمَّ اللَّهُ حَجَّ
امْرِئٍ، وَلاَ عُمْرَتَهُ لَمْ يَطُفْ بَيْنَ الصَّفَا وَالمَرْوَة" ([35]).
(Allah baya cika hajjin mutum ko umrarsa matuqar
bai yi xawafi tsakanin safah da marwah ba), da kuma saboda faxinsa
(r):
Ma'ana:
(Ku yi sa'ayi saboda Allah ta'alah ya wajabta muku yin sa'ayi).
«أَهَلَّ
الْمُهَاجِرُونَ وَالأَنْصَارُ وَأَزْوَاجُ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم فِي
حَجَّةِ الْوَدَاعِ وَأَهْلَلْنَا، فَلَمَّا قَدِمْنَا مَكَّةَ قَالَ رَسُولُ
اللهِ صلى الله عليه وسلم: اجْعَلُوا إِهْلاَلَكُمْ بِالْحَجِّ عُمْرَةً إِلاَّ
مَنْ قَلَّدَ الْهَدْيَ، فَطُفْنَا بِالْبَيْتِ، وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ،
وَأَتَيْنَا النِّسَاءَ، وَلَبِسْنَا الثِّيَابَ، وَقَالَ: مَنْ قَلَّدَ الْهَدْيَ
فَإِنَّهُ لاَ يَحِلُّ لَهُ حَتَّى يَبْلُغَ الْهَدْيُ مَحِلَّهُ. ثُمَّ أَمَرَنَا
عَشِيَّةَ التَّرْوِيَةِ أَنْ نُهِلَّ بِالْحَجِّ، فَإِذَا فَرَغْنَا مِنَ
الْمَنَاسِكِ جِئْنَا فَطُفْنَا بِالْبَيْتِ، وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ».
Ma'ana: "Waxanda suka yi hijira (daga garin
Makkah) da mataimaka (ga waxanda suka
yi hijira) tare da matan Annabi (r);
dukkansu sun yi niyyar aikin hajji, a shekarar hajjin bankwana, muma duk muka
yi niyyah, A yayin da muka iso garin Makkah, Sai Annabi (r) ya ce:
Ku mayar da niyyarku na hajji ta zamto ta umrah, sai ga wanda kawai ya koro
dabbar hadayarsa, Sai mu ka yi xawafin xakin Allah, da kuma na safah da
marwah, muka kuma sadu da mata, muka sanya tufafi, Sai Annabi ya sake cewa: Duk
mutumin da ya jawo dabbar hadayarsa to lallai ba zai warware haramarsa ba, har
sai hadayar ta riga ta kai ga wurin yanka ta (10/12). Sannan sai ya umurce mu a
yinin da ake ce da shi: ranar tarwiyah (08/12) cewa mu qulla niyyar aikin hajji, idan kuma
muka kammala aiyukanmu sai mu zo; don yin xawafin xakin
ka'abah, da kuma a tsakanin safah da marwah"([37]).
«فَمَا سُئِلَ يَوْمَئِذٍ عَنْ شَيْءٍ قُدِّمَ، أو
أُخِّرَ، إِلاَّ قَالَ: افْعَلْ،
وَلاَ حَرَجَ».
Ma'ana: "Ba a yi wa Annabi tambaya ba
a cikin wannan yinin; kan wani abin da aka gabatar ko aka jinkirta face ya ce:
Ka aikata, babu wani laifi"([38]).
"خُذُوا عَنِّي مَنَاسِكَكُم".
Ma'ana:
(Ku kwaikwayi aikin hajjinku daga gare ni).
Bukhariy daga A'ishah da Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما) sun ce:
«لَمْ
يُرَخَّصْ فِي أَيَّامِ التَّشْرِيقِ أَنْ يُصَمْنَ إِلاَّ لِمَنْ لَمْ يَجِدِ
الْهَدْي».
Ma'ana: "Ba a yi
rangwamen ayi azumin kwanakin AT-TASHRIQ ba sai ga mutumin da bai samu dabbar hadaya da zai yanka ba".
«حَجَجْنَا
مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَمَعَنَا النِّسَاءُ
وَالصِّبْيَانُ، فَلَبَّيْنَا عَنِ الصِّبْيَانِ، وَرَمَيْنَا عَنْهُمْ».
Ma'ana: "Mun yi aikin hajji tare da
Manzon Allah (r), a tare
da mu kuma akwai mata da yara, sai mu ka yi talbiyyah a madadin yara, muka kuma
yi musu jifa"([39]).
Ibnu-maajah ya ruwaito shi.
Abdullahi xan
Abbas -t-:
"أُمِرَ النَّاسُ أَنْ يَكُونَ
آخِرُ عَهْدِهِمْ بِالْبَيْتِ، إِلا أَنَّهُ خُفِّفَ عَنِ الْمَرْأَةِ الْحَائِضِ"([40]).
(An umurci mutane da cewa aikinsu na qarshe
ya zama xawafin xakin Allah ne, Sai dai kuma an yi
rangwame ga macen da take haila).
«أُمِرَ
النَّاسُ أَنْ يَكُونَ آخِرُ عَهْدِهِمْ بِالْبَيْتِ، إِلَّا أَنَّهُ خُفِّفَ عَنِ
الْمَرْأَةِ الْحَائِضِ».
Ma'ana:
"An umurci mutane da ya kasance aikinsu na karshe –a garin Makkah- ya
zamto jaddada alkawari ne da xakin ka'abah, sai dai kuma an yi rangwame ga mace mai haila"([41]), Bukhariy da Muslim suka yi tarayya kan
inganta shi.
Abdullahi xan
Abbas -t- cewa:
(Duk mutumin da ya manta wani abu daga
cikin aikinsa, ko kuma ya barshi to sai ya zubar da jini).
(Lallai Allah ta'alah ya yi rangwame wa
al'ummata kan kuskure da mantuwa, da kuma abinda aka tilasta su akansa).
Ka'ab xan
Ujrah -t- a lokacin da kwarkwatan
kansa suka cutar da shi:
"احْلِقْ رَأْسَكَ، وَصُمْ
ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ، أَوْ أَطْعِمْ سِتَّةَ مَسَاكِينَ، أَوْ انْسُكْ بِشَاةٍ"([44]).
(Ka aske kanka; sai ka yi azumin yini uku,
ko ka ciyar da miskinai guda shida, ko kuma ka kusanci Ubangijinka da yanka
akuya).
Abdullahi xan
Abbas -t- cewa:
(Duk mutumin da ya manta wani abu daga
cikin aikinsa, ko kuma ya barshi to sai ya zubar da jini).
(لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ
لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ،
لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَحْدَهُ، أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ
وَحْدَهُ).
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHUW, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA HAZAMAL AHZABA
WAHDAH.
"لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ،
وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ".
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
BABI NA BIYAR: WURAREN DA
AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSU A GARIN MADINAH:
"لاَ تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلا إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: المَسْجِدِ
الحَرَامِ، وَمَسْجِدِ الرَّسُولِ r، وَمَسْجِدِ الأَقْصَى"([46]).
(Ba
a xaura sirdi -a kimtsa
tafiya da nufin lada- Sai in zuwa ga masallatai ne guda uku:
1) Masallaci mai alfarma -da ke garin Makkah-.
2) Da masallacin wannan Manzo -r-.
3) da kuma
masallaci mai nisa -da ke Qudus-).
"صَلاَةٌ فِي مَسْجِدِي
هذَا خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ صَلاَةٍ فِيمَا سِوَاهُ، إِلاَّ الْمَشْجِدَ الْحَرَام"([47]).
(Sallah a masallacina wannan yafi alkhairi
fiye da sallah dubu a waninsa; sai dai
masallaci mai alfarma).
Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما) lallai Annabi (r) yace:
«صَلاَةٌ
فِي مَسْجِدِي هذَا أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ صَلاَةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلاَّ
الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ».
Ma'ana: "Yin sallah a masallacina wannan yafi sallah
dubu a waninsa falala; saidai masallaci
mai alfarma"([48]), Muslim ya ruwaito shi. Har ila yau, ya zo
daga Abdullahi xan Az-zubair (t) ya ce: Manzon Allah (r) yace:
«صَلَاةٌ
فِي مَسْجِدِي هَذَا أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلَّا
الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ، وَصَلَاةٌ فِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ أَفْضَلُ مِنْ
مِائَةِ صَلَاةٍ فِي مَسْجِدِي هَذَا».
Ma'ana: "Yin Sallah a masallacina wannan yafi sallah
dubu a waninsa falala; saidai masallaci
mai alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah xari
a masallacina wannan"([49]), Ahmad ne da Ibnu-Khuzaimah da Ibnu-Hibban
su ka fitar da shi. Wani hadisin kuma ya zo daga Jabir (t) lallai Manzon Allah (r) ya ce:
«صَلَاةٌ
فِي مَسْجِدِي هَذَا أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلَّا
الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ، وَصَلَاةٌ فِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ أَفْضَلُ مِنْ
مِائَةِ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ».
Ma'ana: ''Yin sallah a masallacina wannan yafi sallah dubu
a waninsa falala; sai dai masallaci mai
alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah dubu xari
a cikin wanda ba shi ba"([50]), Ahmad ne da Ibnu-Maajah suka fitar da
shi. Kuma hadisai da suke xauke da wannan ma'anar suna dayawa.
Idan mai ziyara ya isa wannan masallacin to mustahabbi ne ya
fara gabatar da qafarsa ta hagu lokacin shigarsa; ya kuma ce:
«بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله،
أَعُوذُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ، وَبِوَجْهِهِ الْكَرِيمِ، وَسُلْطَانِهِ
الْقَدِيمِ، مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ». «اللَّهُمَّ
افْتَـحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ».
BISMILLAH, WASSALATU WASSALAMU ALA RASULIL LAHI, A'UZU
BILLAHIL AZIMI, WABI WAJHIHIL KARIMI, WA SULXANIHIL QADIIMI, MINASH SHAIXANIR
RAJIIMI. ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIKA.
Ma'ana: "(Ina shiga) da sunan Allah, qarin
yabo da sallama su tabbata ga Manzon Allah, Ina neman tsarin Allah mai girma,
da fiskarsa mai karimci, da kuma qarfin mulkinsa daxaxxe
= daga Shexan jefaffe([51]).
(بسم الله، والصلاة والسلام
على رسول الله، اللهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِك).
"BISMILLAH, WAS SALATU WAS SALAMU ALA
RASULIL LAH, ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIK".
(Tsakanin gidana da minbarina dausayi ne
daga dausayin aljanna).
"مَا مِنْ أَحَدٍ يُسَلِّمُ عَلَيَّ إِلا رَدَّ اللَّهُ عَلَيَّ رُوحِي حَتَّى
أَرُدَّ عَلَيْهِ السَّلام"([54]).
Ma'ana: (Babu
wani mutum guda da zai yi min sallama face Allah ya dawo min da raina don na
amsa masa sallama).
(السلام عليك يا
رسول الله، السلام عليك يا أبا بكرٍ، السلام عليك يا أبتاه).
(aminci ya qara tabbata akanka ya ma'aikin Allah, aminci
ya tabbata akanka ya Aba-bakrin, aminci ya tabbata akanka ya babana!)
«لَا
تَتَّخِذُوا قَبْرِي عِيدًا، وَلَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قُبُورًا، وَصَلُّوا
عَلَيَّ فَإِنَّ تَسْلِيمَكُمْ يَبْلُغُنِي أَيْنَمَا كُنْتُمْ».
Ma'ana:
"Kada ku riqi qabarina wajen kai-komo, haka kuma (kada ku riqi)
gidajenku a matsayin qaburbura (ya zama ba kwa yin sallah a cikinsu); kuma ku rinqa
yin salati a gare ni; saboda sallamarku za ta iso ni a duk inda ku ke"([55])
«كَانَ
النَّبِي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَزُور مَسْجِدَ قُبَاءٍ رَاكِبًا
وَمَاشِيًا، فَيُصَلِّي فِيهِ رَكْعَتَيْنِ».
Ma'ana:
"Annabi (r) ya kasance
ya kan ziyarci masallacin quba'a akan
abin hawa (a wani lokaci, a wani lokacin kuma) da qafa; sa'annan ya sallaci raka'oi
guda biyu a cikinsa"([56]).
Ya zo kuma
daga Sahal xan Hunaif
(t) lallai
ya ce; Manzon Allah (r) yace:
«مَنْ
تَطَهَّرَ فِي بَيْتِهِ، ثُمَّ أَتَى مَسْجِدَ قُبَاءٍ فَصَلَّى فِيهِ صَلَاةً،
كَانَ لَهُ كأَجْر عُمْرَةٍ».
Ma'ana:
"Duk wanda ya yi tsarki (alwala) a gidansa sa'annan ya zo masallacin quba'a; sai ya sallaci wata sallah
a cikinsa to yana da kamar ladan umrah"([57]).
Kuma an
sunnanta masa ziyartar qaburburan
Baqi'i, da maqabartar waxanda suka yi shahada (a yaqin Uhud) da qabarin Hamza (t); saboda Annabi (r) ya
kasance ya kan
ziyarce su ya kuma yi musu addu'a, kuma saboda faxinsa (r):
«زُورُوا القبورَ؛ فإنها تذكِّرُكُمُ الآخرةَ».
Ma'ana: "Ku ziyarci qaburbura;
domin suna tuna mu ku Lahira"([58]), Muslim ne ya ruwaito shi. Har ila yau,
Annabi (r) ya kasance yana ilmantar da sahabbansa idan suka ziyarci qaburbura
da suce:
«السَّلَامُ
عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنْ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وإِنَّا إِنْ
شَاءَ اللَّهُ بِكُمْ لَاحِقُونَ، أَسْأَلُ اللَّهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ».
Ma'ana: "Aminci ya tabbata a kanku ya ku ma'abotan waxannan
gidaje na mu'uminai da musulmai, Kuma muma –In sha' Allahu– Ma su haxuwa
ne da ku, muna roqon Allah lafiya; a mu da ku"([59]), Muslim ne ya ruwaito shi daga hadisin
Sulaiman xan Buraidah daga Babansa.
Haka
kuma tirmiziy ya fitar daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) ya ce: Annabi (r) ya wuce qaburburan garin Madina; sai ya fiskance su da fiskarsa
sa'annan yace:
«السَّلَامُ
عَلَيْكُمْ يَا أَهْلَ القُبُورِ، يَغْفِرُ اللَّهُ لَنَا وَلَكُمْ، أَنْتُمْ
سَلَفُنَا، وَنَحْنُ بِالأَثَرِ».
Ma'ana: "Aminci ya tabbata gare ku ya
ku ma'abuta qaburbura!
Allah ya yi mana gafara mu da ku, ku marigaya ne a gare mu, mu kuma muna tafe"([60]).
kamar hadisin:
(مَنْ حَجَّ ولم يَزُرْني
فقد جَفانِي).
(Duk wanda ya yi aikin hajji, bai ziyarce
ni ba; To ya gajarta wajen bani haqqina
–ma'ana: yayi mini jafa'i-). Da hadisin:
(مَنْ زارَ قبري وَجَبَتْ
له شفاعَتِي).
Ma'ana: (Wanda ya ziyarci kabarina cetona ya tabbata masa).
"مَنْ تَطَهَّرَ فِي بَيْتِهِ ثُمَّ أَتَى مَسْجِدَ قُبَاءَ، فَصَلَّى
فِيهِ صَلاةً، كَانَ لَهُ كَأَجْرِ عُمْرَةٍ"([61]).
Ma'ana: (Duk wanda ya tsarkaka –yayi alwala-
a gidansa sa'annan ya zo masallacin Quba'a; kana ya sallaci wata sallah a
cikinsa to yana da kamar ladan umrah".
Ma'ana: (Ku ziyarci qaburbura; domin ziyartarsu yana tuna mutuwa).
"السَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ،
وَإِنَّا، إِنْ شَاءَ اللهُ لَلاحِقُونَ، أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمُ الْعَافِيَةَ"([63]).
Ma'ana: (Amincin Allah ya tabbata a gare ku
ya ku ma'abota waxannan
gidajen; muminai da musulmai, kuma lallai muma –insha Allahu- muna nan tafe,
Ina roqon Allah lafiya ga mu da ku).
Ma'ana:
(Duk wanda ya aikata wani aikin da babu umurninmu akansa to an mayar masa).
BABI NA SHIDA: MAGANA KAN LAYYAH:
"أنَّ النَّبِيّ r ضَحَّى بِكَبْشَيْنِ
أَمْلَحَيْنِ أَقْـرَنَيْنِ، ذَبَـحَـهُمَا بِـيَدِهِ، وَسَـمَّى وَكَـبَّـرَ، وَوَضَعَ
رِجْلَهُ
Anas
-t-: (Lallai Annabi –r- ya yi
layyah da raguna guda biyu masu roxin
fari da baqi, madaidaita qaho guda biyu, ya
yanka su da hannayensa, yana mai anbaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma xora
qafarsa
a gefen wuyansu).
Abu-ayyub -t- cewa:
"كَانَ الرَّجُلُ فِي عَهْدِ رسول الله r يُضَحِّي بِالشَّاةِ عَنْهُ، وَعَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ،
فَيَأْكُلُونَ وَيُطْعِمُون"([66]).
Ma'ana:
(Mutum ya kasance a zamanin manzon Allah –r-
ya kan yi layyah da akuya -ko tinkiya-, wa kansa, da kuma iyalan gidansa, sai
su ci, su kuma ciyar).
"نَحَرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ r عَامَ الْحُدَيْبِيَةِ الْبَدَنَةَ عَنْ سَبْعَةٍ،
وَالْبَقَرَةَ عَنْ سَبْعَة"([67]).
Ma'ana:
(Mun yi layyah tare da manzon Allah –r- a
shekarar sulhun hudaibiyyah, mutane bakwai ga raqumi xaya,
itama saniya xaya mutane bakwai).
"لا تَذْبَحُوا إِلا مُسِنَّةً إِلا أَنْ يُعْسِرَ عَلَيْكُمْ، فَتَذْبَحُوا
جَذَعَةً مِنَ الضَّأْن"([68]).
Ma'ana:
(Kada ku yi yankar layyah sai dabbar da ake mata laqabi
da "musinnah", sai dai in kun rasa wannan, sai ku yanka
"jaza'ah" daga cikin tumaki).
"Musinnah"
daga cikin raquma itace: wanda ta cika shekaru biyar. Daga cikin
"shanu" kuma itace: wanda ta cika shekaru biyu. Daga cikin
"awaki" kuma: wacce ta cika shekara xaya.
Kuma ana kiranta "Saniyyah".
Ma'ana:
(Ni na samu "jaza'ah –tinkiya 'yar wata shida" ne, Sai Annabi –r- yace: To
sai ka yi layyah da ita).
Uqbah xan
Aamir -t-:
Ma'ana:
(Mun yi layyah tare da manzon Allah –r-
da "jaza'ah daga cikin tumaki –wato: 'yar watanni shida-).
1-
2-
3-
Annabi
(r)
ya ce:
"أَرْبَعٌ لا تُجْزِئُ فِي الأَضَاحِيِّ: الْعَوْرَاءُ الْبَيِّنُ عَوَرُهَا،
وَالْمَرِيضَةُ، الْبَيِّنُ مَرَضُهَا، وَالْعَرْجَاءُ الْبَيِّنُ عَرَجُهَا، وَالْعَجْفَاء
الَّتِي لا تُنْقِي"([71]).
Ma'ana:
(Dabbobi guda huxu basa isarwa a "layyah": Dabba mai harari-garke
wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da
gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse).
Al-bara'u xan Aazib -t-, yace: Manzon
Allah (r)
ya ce:
"مَنْ صَلَّى صَلاَتَنَا، وَنَسَكَ نُسْكَنَا فَقَدْ أَصَابَ النُّسُكَ، وَمَنْ
ذَبَح قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ فَلْيُعِدْ مَكَانَهَا أُخْرَى"([72]).
Ma'ana:
(Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace
da yankan layyah akan tafarki, Amma mutumin da ya yi yanka kuma gabanin ya yi
sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta).
Jubair
xan
Muxim -t- daga Annabi (r) yace:
Ma'ana:
(Dukkanin ranakun "tashriq" lokacin yanka ne).
A
Al-bara'u xan Aazib -t-, lallai Annabi (r) yace:
"أَوَّل مَا نَبْدَأُ بِهِ يَوْمنَا هَذَا نُصَلِّي، ثُمَّ نَرْجِعُ فَنَنْحَرُ،
فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ فَقَدْ أَصَابَ سُنَّتَنَا، وَمَنْ ذَبَحَ قَبْلَ ذَلِك فَإِنَّمَا
هُوَ لَحْمٌ قَدَّمَهُ لأَهْلِهِ؛ لَيْسَ مِنَ النُّسُكِ فِي شَيْءٍ"([74]).
Ma'ana:
(Abun da zamu fara yininmu wannan da shi, shine mu yi sallar idi, sa'annan sai
mu dawo don mu soke abun layyarmu. Duk wanda ya aikata haka to ya dace da
sunnarmu, Duk kuma mutumin da ya yanka abun layyansa gabanin haka to ya sani
cewa: nama ne ya gabatar da shi ga iyalansa, ba layyah ba).
Abdullahi xan Abbas -t- yana siffanta
layyar Annabi (r),
ya ce:
"ويُطْعِمُ أَهْلَ بَيْتِهِ الثُّلُثَ، وَيُطْعِمُ فُقَرَاءَ
جِيرَانِهِ الثُّلُثَ، وَيَـتَصَدَّقُ عَلَى السُّؤَّالِ بِالثُّلُثِ"([75]).
Ma'ana: (Zai ciyar da iyalan gidansa xaya-bisa-uku
1/3, ya ciyar da faqirai
makwabtansa xaya-bisa-uku 1/3, kuma ya yi sadaka wa
masu roqo da xaya-bisa-uku 1/3).
Buraidah -t-, Lallai Annabi (r) yace:
"كُنْت نَهَيْتُكُمْ عَنْ ادخار لُحُومِ الأَضْاحَى بَعْدَ ثَلاَثٍ فَكُلُوا،
فَأَمْـسِكُوا مَا بَـدَا لَكُم"([76]).
Ma'ana: (Na kasance na hana ku ijiye naman layyah fiye da
kwanaki uku, to ku ijiye na tsawon yadda ya yi muku).
"إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ وَعِنْدَهُ أُضْحِيَّةٌ يُرِيدُ أَنْ يُضَحِّيَ فَلا
يَأْخُذَنَّ شَعْرًا، وَلا يَقْلِمَنَّ ظُفُرًا"([77]).
Ummu-salamah
–رضي الله عنها-, daga Annabi (r) (Idan kwanaki goma
suka shiga, a wajen xayanku ya zama akwai abun layyah da zai yi layya da shi to
kada ya cire wani gashi, ko ya yanke wani farce).
(kada ya tava wani abu daga gashinsa da fatarsa).
A
wani lafazin kuma:
"وَمُهَلُّ أَهْلِ الْعِرَاقِ مِنْ ذَاتِ عِرْقٍ".
Ma'ana: (Wurin da mutane Iraaq
zasu xaga sautinsu da niyya shine: ZAATU-IRQIN).
([42]) Ad-daraquxniy ya ruwaito shi
(2/191, lamba: 2512), da Albaihaqiy (5/152),
da wassunsu. Wannan maganar ta tabbata i zuwa ga Abdullahi xan Abbas
cewa shine ya faxe ta, ba
Annabi (r) ba,
kamar yadda Ibnu-abdilbarri ya faxa
(Duba: Al'istizkaar, 12/184), da kuma Albaniy a cikin littafin (Irwa'u algalil,
4/299).
([55]) Alhafiz Abdulganiyyul maqdisiy ne ya ruwaito
shi, a cikin littafinsa mai suna: AL-AHADISUL MUKHTARAH, (lamba: 428, shafi:
244), da Abu-ya'alah a cikin Musnad xinsa, (lamba: 469, 1/361). Alhaisamiy a
cikin littafin "MAJMA'UZ ZAWA'ID" (lamba: 5847, 4/6): Abu-ya'alah ya
ruwaito shi, amma a cikin isnadinsa akwai: Hafs xan Ibrahima al-ja'afariy,
wannan mutumin Shehin malami Ibnu-hibban ya ambace shi a cikin littafinsa, amma
bai ambaci wata suka akansa ba, su kuma sauran maruwaita hadisin su kuma mutane
ne amintattu Haka kuma Imam Ahmad shima ya ruwaito shi, amma a
"musnad" xin Abu-hurairah (t), (2/367), da Abu-dawud (lamba: 2042), amma ba da lafazin da ya gabata ba.
Lafazin nasa yana tafe.
No comments:
Post a Comment