HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 16/ZUL-KA'ADAH/1437H
Daidai da 19/Agusxus/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALU- AL SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
GIRMAMA
WURAREN BAUTAR ALLAH DA ABUBUWAN DA YA BASU ALFARMA, A CIKIN HAJJI
Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Alu
As-sheikh –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a, 16 zulqi'idah, 1437H, mai taken: GIRMAMA WURAREN BAUTAR
ALLAH DA ABUBUWAN DA YA BASU ALFARMA, A CIKIN HAJJI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna kan farlanta hajji, da manufofin shari'a wajen shar'antata, kuma
lallai maxaukakin manufa na shar'anta hajji shi ne kaxaita Allah mabuwayi da xaukaka,
kuma lokacin hajji, dam ace na jaddada lamarin haxin kan al'ummah, kuma wajibi
ne akan kowa, Yin taimakakkeniya wajen aiki da dokokin da su ke kawo tsari a
cikin hajji, da lokacin umrah, Sannan ya tsawatar kan voye sharri ga mahajjata
da masu umrah.
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya
tabbata ga Allah, a farko, da qarshe.
Ina shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya
a lahira da duniya.
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawan Allah ne, kuma manzonSa zavavve.
Ya Allah ka
yi qarin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa
masu cika alqawari.
Bayan haka:
Ya ku
musulmai!
Ina yin
wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah da taqawarsa (جل وعلا), da yin za'a a gare shi, a sirrance da a
bayyane, domin ita ce: Nasara mai girma, da tsira mafi xaukaka.
Ya ku taron Musulmai!
Su ibadodi
a cikin musulunci, suna da FA'IDODI manya da suke cimma wa, da MANUFOFI masu
girma.
Kuma
lallai AIKIN HAJJI ta fiskar manufofi ya tattara waxanda suka fi xaukaka ne daga
cikinsu, da hadafi masu girma.
Kuma
lallai manufar hajjin xakin Allah da ta fi hasken xaukaka, ita ce: TABBATAR DA TAUHIDIN ALLAH, DA
KUMA BARRANTA DAGA SHIRKA: Saboda a
cikin jerin ayoyin da suke magana kan hajji Allah yana cewa: "Suna masu karkata
zuwa ga Allah; ba waxanda suke yin shirka a gare shi ba"
[Hajj: 31].
Ma'ana: Suna karkacewa; su bar kowani addini
karkatacce, izuwa ga addinin gaskiya, suna masu ikhlasin addini ga Allah, da
kuma yin bara'a daga bautar duk wanda ba Allah ba.
'Yan'uwa
Musulmai!
Aiyukan
da ake yi a cikin hajji, suna koyar da Musulmi cewa ya kasance abin fiskanta
cikin zantukansa da aiyukansa da dukkan motsawarsa da hanyoyinsa na rayuwa,
yana mai cikakken fiskantar Allah (سبحانه); a
zahiri da baxini "Kuma kowace al'umma mun sanya mata yanayin bauta, da
wurin yinsa domin su yi zikiri –wato su ambaci sunan Allah- akan abinda ya
azurta su, na dabbobin ni'ima; Kuma abin bautarku abun bauta ne guda xaya, kuma
a gare shi ne kawai za ku miqa wuya" [hajj: 34].
Babban
tambari ko bajin da ya zama alama ga hajji, wanda kuma hajjin ya banbanta da shi,
shine: Amsawa Allah da kalmomin talbiyya (wato: LABBAIKA ALLAHUMMA LABBAIKA); Wanda
ma'anoninsa suka qunshi: Tabbatarwar da Musulmi ke yi a cikin zuciya da rayuwa,
da zance da aiki, cewa: Zai yi kammalallen girmama Allah, da cikakken qasqantar
da kai, da kuma so wanda ya kai maqura, ga Allah (سبحانه), kuma zai yanke komai don yin biyayya a
gare Shi, da yin aiki da umurninSa, da cikakken sallamawa ga shari'ar Allah.
Umar (رضي الله
عنه) ya ce, a lokacin da ya sunbanci hajaru Al-aswad: "Wallahi! Lallai
ne ni, na san kai dutse ne baka cutarwa kuma baka amfanarwa, kuma ba don naga
Manzon Allah yana sumbantarka ba, to da ban sunbace ka ba".
A
lokacin yin xawafi kuma, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yana shiryar da mu cewa idan mun zo yin
raka'oi guda biyu na xawafi/ mu karanta (Qul ya ayyuhal kafiruna) a
raka'ar farko, domin tabbatar da raba hanya tsakanin turbar tauhidi da hanyoyin
shirka, da nau'ukansa da sabubansa da hanyoyinsa. A raka'a ta biyu kuma, sai mu
karanta (Qul huwal lahu ahad) wanda ta ke tabbatar da tauhidi
da nau'ukansa guda uku.
Kuma
kamar haka ne, tafiyar hajji a dukkanin matakanta, kuma cikin dukkanin
aiyukanta ta ke yin dashen ikhlasi ga Allah (سبحانه)
cikin zukata, da yin biyayya a gare Shi, da sonSa, da jin tsoronSa, da fatan
samun ladanSa.
Ibnu-Rajab yana cewa: ((Yana daga
abinda wajibi ne nisantarsa ga mahajjaci, kuma sai da shi hajjinsa ke zama
MABRUR: Kada ya nufi riya ko sum'ah da hajjinSa –wato yin ibada don a ji,
ko a gani-, ko kuma alfahari ko jiji-da-kai, da girman kai, kuma kada ya nufi
komai da shi sai fiskar Allah, da neman yardarSa, kuma ya yi tawali'u cikin
hajjinsa, ya kuma nitsu, ya yi kushu'i ko qanqan-da-kai ga UbangijinSa; saboda
an ruwaito daga Anas cewa: Lallai ne Annabi –صلى الله عليه
وسلم- ya yi hajji akan dabbar hawa, mai tsofaffin kaya, da katifar
da bata wuce dirhami huxu ba, kuma ya ce: Ya Allah! Ka sanya shi ya zama
hajjin da babu riya, babu sum'a a ciki!!!)).
Don
haka; Abinda yake madogara ga hajji shine, Samun faraga ko lokacin yin ambaton
Allah (wato: zikiri), da girmama shi, da yin yabo a gare shi, da nuna karaya a
gaba gare shi, da halartowar qanqan-da-kai a gare shi (سبحانه) a wajen aikata kowani aiki, daga cikin
aiyukan hajji, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma kowace al'umma mun sanya mata yanayin bauta, da wurin yinsa
domin su yi zikiri –wato su ambaci sunan Allah- akan abinda ya azurta su na
dabbobin ni'ima" [Hajj: 34].
Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya ce: "Mafificin
hajji shine, ajju da sajju". "Ajju"
kuma shine: Xaga sauti lokacin yin kabbarori da talbiyyah.
Kuma Ahmad da Tirmiziy da Abu-dawud sun fitar,
cewa lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
ce: "Lallai ne an shar'anta yin xawafin Xakin ka'abah, da kuma
tsakanin Safah da Marwah, da jifan duwatsu domin tsayar da zikiri (wato:
ambaton Allah)".
Kuma Allah (تعالى) ya
ce: "Kuma idan kuka gangaro daga arafaat, sai ku ambaci Allah (zikiri) a mash'arul haram -Muzdalifa-, kuma ku ambace
shi saboda shiryar da ku da ya yi" [Baqara: 198].
"Sa'annan sai ku gangaro ta wurin da sauran
mutane ke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, Lallai ne Allah Mai gafara ne
Mai rahama" [Baqara: 199 ]. A nan kuma abinda ake nufi da
"gangarowa" shine: ifada ko gangarowa daga Muzdalifa, a xayan zantuka
biyu da yafi inganci.
Dangane da aiyukan hajji kuma Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma idan kuka
kammala aiyukanku na hajji, sai ku ambaci Allah -zikiri- kamar yadda ku ke
ambaton iyayenku, ko kuma ambaton da ya fi haka yawa"
[Baqara: 200].
Ya
ku taron Muminai!
Lallai
hajji kamar baji ne mai girma, da ke tunatar da al'umma gabaxayanta, kan:
Girmama ababen da Allah ya basu wata alfarma, da kuma tsayuwa a kan shari'arSa;
da bin tsari ko dokokin Allah, "Duk kuma wanda ya girmama wuraren bauta wa
Allah, to lallai su suna daga taqawar zukata" [Hajj: 32].
Kuma babu tsira ga al'ummarmu a yau, daga
abinda ta samu kanta a cikinsu na fitintinu da musibobi, sai lokacin da
waxannan manufofin suka samu tabbatuwa a cikin rayuwarta, kuma suka yi aiki da
su a cikin sha'anoninsu, aqidarsu ta zama garau, haryar tafiyarsu ko manhaji ya
zama akan sawaba (ta dadai), da kyakkyawar hanya cikin halayya, Sai al'umma ta
rayu cikin izza, mai kwar-jini, maxaukakiyar geffa, da matsayi, wacce halinta zai
rabauta.
Kuma
daga ibadar hajji, Al'umma ya da ce ta fahimci cewa: lallai yana daga cikin
manya-manyan manufofi na shari'oin addini: Samar da kaxaitaka ta imani
da 'yan'uwantaka ta musulunci, wanda bata san qabilanci ko
vangaranci ba, Kawai 'yan'uwantaka ce da ta ke tsayuwa akan maslahohin addini
da duniya, akan mafi kyan hali, "Tabbas Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujuraat: 10].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "'Xayanku
baya zama mai imani sai ya so wa xan'uwansa abinda yake so wa kansa".
Kuma da haka ne, Al'umma za ta san cewa lallai
yadda ta samu kanta a wasu wurare ko wajen wasu 'ya'yanta bai yi daidai da
addini ba, kuma baya dacewa da manufofinsa, saboda ta yaya Musulmi zai kafirta
xan'uwansa, kuma ta yaya zai zubar da jininsa? Ko ya keta alfarmar mutuncinsa,
ko ya xauke dukiyarsa?
Hajji makaranta ce, wacce daga abinda aka koya
a cikinta Tsare-tsaren maqiyan musulunci
da suke tsattsarawa domin kekketa wannan al'ummar, ko su raunata sha'aninta, ko
su yi gunduwa-gunduwa da vangarorinta, ko don rarrabe al'amarinta, da kuma
watsa kashinta, domin bala'i ya auku, a kuma faxa cikin wahala = Hajji
makaranta ce da idan an bi darrusanta za su rurrushe tsare-tsaren maqiyan
musulmai.
Ya ku taron
Musulmai!
Lallai
wannan daula mai albarka (Masarautar larabawa ta Saudia) tana samun qarin
xaukaka, da yin hidima ga mahajjata, tana ganin hakan a
matsayin wajibi da ya doru a wuyanta ta fiskar addini, kuma qara samun xaukaka,
a duniyance. Kuma wannan qasar don ganin tabbatuwan haka tana bayar da duk wani
abu mai tsada, ga duk abinda zai tabbatar da hutu ko amfani ga baqin Allah (Mai
rahama), waxanda suka nufo masallacinsa (mai alfarma).
Kuma
wajibin kowani musulmi ne ya girmama waxannan wurare masu tsarki, kuma ya kula
da alfarmar su da suka tabbatu a cikin littafin Allah da Sunnah, da ijma'i.
kuma ya yi kwaxayin samar da aminci da zaman lafiya ga musulmai, da hutu a gare
su, saboda yana daga manya-manyan laifin alkaba'ira: Cutar da baqin Mai rahama
(wato: mahajjata), da qunsa nufin sharri a gare su, "Wanda a cikin
harami ya yi nufin karkata da zalunci, za mu xanxana masa daga azaba mai raxaxi"
[Hajj: 25].
KUMA YANA DAGA CIKIN WAJIBIN MUSULMAI:
Su yi aiki da dukkan tsarin da zai tabbatar da
maslahar musulmai cikin hajjinsu, ya kuma tunkuxe musu dukkan abinda zai cutar
da su; YANA KUMA DAGA CIKIN HAKA: Yin aiki da takardun izinin
isa wuraren aiwatar da aikin hajji, saboda aikata hakan an gina shi ne akan
qa'idar WAJABCIN TAIMAKAKKENIYA CIKIN BIYAYYAR ALLAH DA TAQAWA, Kuma duk
abinda musulmai suka haxu wajen ganin kyansa, to mai kyau ne.
Sai musulmi ya kiyayi yin wayo ga hakan, ko
kuma sakaci wajen tabbatuwansa; saboda maslahar al'umma gabaxayanta, ana
rinjayar da ita akan maslahar xaixaiku, wannan kuma har a cikin ibadodi na
nafilfili, kamar yadda ILIMIN SANIN MANUFOFIN SHARI'A ya yi nuni akan haka.
'Yan'uwan
Musulunci!
A
cikin hajji, akwai gyaran xabi'u, da kuma tsarkake rai daga dukkan sifofi
munana, da hanyoyi ababen kyama, waxanda suke iya cutar da musulmi a addinance
ko a duniyance, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma duk wanda ya niyyaci hajji a cikin watannin, to babu kwarkwasa,
kuma babu fasikanci, kuma babu jidalin jayayya a cikin hajji"
[Baqara: 197].
Kuma Manzo (صلى الله
عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda
ya ziyarci wannan xakin –aikin hajji-, bai yi batsa ko jima'i ba, da fasikanci:
to zai fita daga zunubansa kamar ranar da uwarsa ta haife shi".
Wajibi
ne akan kowani musulmi, ya fahimto –daga wannan ibada ta aikin hajji- ya
fahimto manufofinta, sannan ya yi miqaqqiyar rayuwa a cikin wannan rayuwar akan
darrusan da ya koya daga gare ta (ibadar hajji).
Allah
(سبحانه) ya datar da mu izuwa ga shiriyarSa, kuma
ya nuna mana abinda a cikinsa ake samun yardarSa.
Allah ya sanya mana albarka cikin wahayi guda
biyu, ya kuma amfanar da mu da shiriyar da take cikinsu.
Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman
gafarar Allah a ni da ku, da kuma sauran Musulmai, Ku nemi gafararSa; lallai
shi, Mai gafara ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU:
Ina
yin yabo ga Ubangijina, kuma gode masa, Kuma ina shaidawa babu abin bautawa
lallai annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Ya Allah ka yi salati da sallama
da albarka, akansa, da iyalansa da sahabbansa.
Al'ummar musulmai!
Lallai ne
al'ummar musulmai ba za ta samu rabauta da buwaya ba, kuma ba za su tava samun
wata bunqasa, ko wadaci, ko walwala, ko aminci ba, matuqar ba su tsayar da
rayuwarsu akan shari'ar Allah ba (سبحانه).
Kuma sai har littafin Allah, da sunnar zavavven Manzo (صلى الله عليه وسلم) sun kasance fitila, kuma tsari da salon
da suke gudanar da sha'aninsu na rayuwa akansu.
Kuma
wajibi ne ga al'umma ta xauka, daga irin hudubar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a hajjin bankwana, su xauki tabbatacciyar
manufar da za su riqa tafiya a kansa, a cikin siyasosinta, da alaqoqinta, da
cikin tattalin arziqi, da sauran sha'anoninsu.
Kuma
da aikata haka ne kawai, za su rabauta, kuma al'umma sai ta yi ta hauhawa izuwa
ga matakan kamala, da bunqasa, da wayewa. Idan kuma suka qi aiki da hakan, to
lallai al'umma tana cikin asara da wahala, kuma tana cikin tsanani da bala'i.
Sannan
ku sani, lallai mafi tsarkin abinda rayuwarmu take tsayuwa da shi, shine:
Shagaltuwa da yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
Ya Allah! Ka yi
salati da sallama da albarka da ni'ima ga bawanka kuma manzonka annabi
Muhammadu.
Ya Allah! Ka yarda
da khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa, Abubakar da Umar da
Usmanu da Aliyu. Da iyalan annabi da sahabbai gabaxaya, da wanda ya bi su, da
kyautatawa zuwa ranar sakamako.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai, Ya Allah ka datar da musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke ciki, Ya
Allah ka datar da musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke, Ya Allah ka datar da
musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke.
Ya Allah ka kiyaye mahajjata da masu umrah,
kuma ka mayar da su zuwa garinsu, cikin salama da riba, Ya ma'abucin girma da
karramawa.
Ya Allah ka datar da majivincin lamarinmu ga
abinda ka ke so, kuma ka yarda.
Ya Allah! Ka kiyaye qasar harami biyu, da
sauran qasashen musulmai.
gyara halinmu da halin Musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, ka
kore ababen vacin rai.
Ya Allah! Ka tseratar da bayinka
Musulmai daga kowani ibtila'i da fitina.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiyan
Musulmai; Lallai su, basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu
Musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance mai taimako a gare su; Ya
Mabuwayi ya Mai matsanancin qarfi.
Ya Allah! Ka datar da Mai hidiman
Masallatan harami biyu izuwa ga abinda kake sonsa, kuma ka yarda da shi, Ya
Allah ka taimaki addini da shi, kuma ka xaukaka kalmar Musulmai da shi.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza
da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bamu mai kyau a Duniya,
a Lahira itama mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar Wuta.
Bayin Allah!
Ku ambaci Allah ambato mai yawa,
Ku yi masa tasbihi safiya da maraice;
Qarshen addu'armu itace:
الحمد لله
رب العالمين