2016/07/08

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI ta, 3/SHAWWAL/1437H daga SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
 JUMA'A, 03/SHAWWAL/1437H
Daidai 08/07/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI?
     Shehin Malami wato: Husaini xan Abdul'aziz Alu Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan watan ramadana da tunatarwa kan shuxewar yinin ramadana da dadarensa, da abinda suka qunsa a cikinsu na aiyukanmu; na alkhairinsu da sharrinsu, Sannan ya ambaci lamarin tayar da boma-bomai da ya zama sababin zubar da jinane da kashe rayuka a qasar Harami guda biyu, Yana mai faxakar da iyaye da Maluma da wayayyu da kafafen sadarwa cewa su riqa karantar da samari suna faxakar da su kan shari'ar Allah (تعالى).

بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da ba a qididdige su. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da abokin tarayya, a lahira da duniya, kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, annabi zavavve, kuma bawa zavavve. Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta gaskiya da bin dokoki da taqawa.
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

'Yan'uwan Musulunci
Ka yi mamakin saurin shuxewar kwanaki, da wucewar watanni! Shi mai hankali wanda aka yi masa dacen taufiqi shine yake riqan kwanaki da watanni a matsayin lokatai na kusantar Allah majivinci –جل وعلا-, Sai ya kiyaye yin biyayya a gare shi, a sirrance da a bayyane.

Kuma lallai abinda ya wajaba akan musulmi a cikin wannan rayuwar shine ya yi qoqarin tabbatar da manufar samar da shi, a tsawon rayuwarsa gabaxayanta; ta hanyar tsayuwa akan tauhidi da bin dokoki , da biyayya wa Allah.
Saboda rayuwa gabaxayanta; Manufarta mafi girma itace, yin aiki da umurnin Allah, da qoqarin tabbatar da yin bauta a gare shi (سبحانه), Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka ce: Lallai sallata da yanke-yankena, da rayuwata, da mutuwata ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya, kuma da aikata haka aka umurce ni, kuma nine farkon musulmai" [An'aam: 162-163].
Kuma Allah (تعالى) yace: "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana ambaton Allah a dukkan lokutansa.

            Ya ku taron Musulmai!!
            Idan har Musulmi ya tsayu a cikin watan ramadana don ya amfana da lokutansa, ta hanyar gaggawa cikin aikata aiyukan alkhairori, da kuma kusantar Ubangiji da sauran mustahabbai, To wajibi ne akansa yayi godiya wa Allah ([g (جل وعلا) akan haka, Sai kuma yayi iya qoqarinsa a cikin shekaransa gabaxayanta, wajen aikata dangogin xa'a, gwargwadon iko, saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Mafi soyuwan aiyuka a wurin Allah shine wanda aka dawwama akansa, koda ya yi kaxan", Bukhariy da Muslim.

            Ka yi hanyoyin samun lada, da kwasan garavasar kyawawan aiyuka, a cikin shari'ar rangwame da sauqi da rahama da falala (shari'ar musulunci), suna da matuqar yawa, kuma nau'i-nau'i ne, a cikin zantuka da aiyuka.

            'Yan'uwan Musulunci!!
            Sha'anin da yafi girma, Shine musulmi ya tsayu wajen aikata aiyuka na wajibi, da nisantar munana; ababen kyama da shari'a ta yi hani akansu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka tsayu, kamar yadda aka umurce ka, da waxanda suka tuba a tare da kai, kuma kada ka qetare iyaka" [Hud: 112].     
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ka ce: Na yi Imani da Allah, sa'annan ka tsayu", Muslim ya ruwaito shi.

            Ya ku bayin Allah!
            Ku kiyaye aiyunku kyawawa da kuka aikata, kuma ku nisanci gurvata abinda Allah yayi muku ni'ima da shi, saboda fallasasshen Mutum a madubi na shari'a, kamar yadda nassoshi suka nuna shine: Wanda zai gina aiyuka kyawawa manya-manya, sa'annan sai ya rushe su, ta hanyar sakar wa gavvansa linzami cikin zaluntar halittun Allah, da yin ta'addanci a gare su, cikin magana ko aiki.

            Ya ku taron Musulmai!
            A qarshe-qarshen watan azumi, a lokacin da musulmai suke farin cikin qarisa azumi da salloli ko tsayuwar dare, bayan kuma Allah ya yi wa Musulmai dacen kammala tilawar maganar Allah Mai hikima, Masani: Sai kwatsam musulmai suka tashi da jin labarin aika-aikan kaiwar harin boma-boman da suka zubar da jini suka kuma kashe rayuka suka tsoratar, har guda uku, a qasar harami guda biyu, wanda a cikinsu suka qunshi mafi girman ababen qi, Daga cikin laifuka kuma mafi muninsu, Daga cikin kaba'irai kuma mafi girmansu, daga wata qungiya, wanda ta karkace daga karantarwar wahayin alqur'ani da sunnar Manzo, sannan qungiyar ta gudu daga jama'ar musulmai, kuma ta haifar da ababen da suka jawo varna mai girma a qasashen musulmai, da kuma sharri mai yaxuwa, Wanda babu mai farin ciki da aukuwar haka sai maqiyan addini.
            Shin waxannan, ba za su ji tsoron damqar Mai girma Allah ba, Shin ba za su yi taqawar Mabuwayi Mai rinjaye ba. Ina suke lokacin da Ubangijinsu zai tambaye su, kan kashe rayukan mutanen da basu jib a, basu gani ba?! Menene kuma matsayansu dangane da mahaliccinsu, alhalin suna yawo da varna mai faxi, ta hanyar razanar da amintattu, masu bauta, da sallah, ta hanyar kashe marasa laifi, masu azumi, musamman a kusa da masallacin ManzonSa amintacce, a cikin wata mai girma, alhalin sauran mutane su kuma suna cikin salloli, da qanqan da kai ga Ubangijin talikai!
            Ku saurara!
            Ya ku samari Musulmai!
            Ku tsaya, tsayawa ta hankalta, da tunani, kuma ku xauki darasi daga munanan qarshe, wacce aqidun waxanda suka karkace daga jama'ar musulmai, su ke kai su, mutanen da suka halatta jinin masu bauta, masu azumi, da salloli, da i'itikafi (don yin bauta) ga Ubanjinsu, suna masu ruku'i da qanqan-da kai (a gare shi).
            Ya wanda aqida da tunani suka sanya shi zamewa daga (turbar) daidai, har ya kauce wa hanya ya bar turbar gaskiya… Ka tuba izuwa ga Ubangijinka gabanin ka sadu da shi, Ka dawo zuwa ga hanyar muminai kamar yadda Ubangijinka ya umrce ka da aikata haka, kuma Manzonsa (صلى الله عليه وسلم) ya umurce ka da aikata haka, Ka komo izuwa ga kewayen jama'ar musulmai, saboda nassoshin shari'a sun tsawatar maka, daga fanxare wa jama'a, kuma sun hane ka, kan raba kai, da nisantar jama'a.
Kuma mafi girman hanyar da Shexanun aljanu ko na mutane suke bi don vata kwakwale, kuma domin fitar da su daga shiriya miqaqqa, ita ce: Nisantar jama'ar (musulmai) masallata, da shiriyar masu bauta, da turbar muminai, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kada ku bi hanyoyin da shexan ya tsattsara, lallai shi a gare ku, maqiyi ne mabayyani" [Baqara: 168, da 208, da An'aam: 146].
Kuma Alqur'ani da sunna basu nusar da mu ba, sai izuwa ga ababen da zasu gyara halayenmu, Kuma a duk lokacin da muka yi nisa da haka, sai varna mai faxi ta auku.

            Ya ku samari musulmai!
            Lallai mafi girman takobi ko makamin masu qiyayya da musulunci, kuma maqiya annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) suke bi; domin kekketa alfarmar addini, ko kuma domin su yaqar garurrukan musulmai: Mafi girman makaminsu shi ne Ta hanyar qosar da sabbuban  jawo rabuwar kai (a cikin al'ummah), da fitar da samari daga jama'ar musulmai, da hujjojin da zahirinsu rahama ne, baxininsu kuma azaba, wato: hujjar taimakon addini, da yin hidima wa lamuransa. Hakan kuma baya kasancewa daga gare su sai bayan sun nesanta samari daga Maluma na Allah, da jiga-jigan faqihai masu tantancewa, da shugabanni masu neman kawo gyara.
Kuma duk wanda ya karanta tarihi to hakan zai bayyana masa qarara; Saboda (a tarihance) babu abinda ya sha gaban al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) wajen hidima ga addininta, da yaxa saqon Annabinta, fiye da fitinar (khawarijawa) ta fanxarewa jama'ar musulmai, wanda dukkan ma'abuta musulunci gabaxaya suke tare da ita. Saboda idan akwai irin waxannan fitintinun to ba za a iya hidima wa addini ba, kuma ba zai yiwu a yi masa hidima ba, kuma ba za a iya tsayar da wata rayuwa managarciya ba. Hasali ma fanxarewa jama'ar musulmai bai jawo komai ga musulunci da musulmai ba, sai varna mai girma, ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da kuma sharri mai yaxuwa, wanda harshen mai fasaha bai isa ya qididdige irin varnar ba, a wuri irin wannan.

            Ya ku Mutanen wannan qasa !
       Lallai qasarku ana nufinta da sharri, cikin hidimarta ga harami guda biyu, da kuma cikin abinda Allah yayi mata na ni'imomi masu yawa, sai ku haxakanku akan alkhairi, ku nisanci rabuwa da dukkan nau'ukansa, ku kiyaye tarkon maqiya, da masu jiran ganin sharri, waxanda suke yin fata a gare ku, da al'ummarku, da 'ya'yanku da jikokinku masu zuwa suke muku fatan qarewa da halaka da rugujewa.

Lallai kafafen sadarwa wajibi ne akansu su gyara tafiyarsu, kuma su zama an fiskantar da su don kawo amincin al'ummai, da kiyaye yara da jikoki.
Kuma wajibi ne akan dukkan musulmai su nisanci makami mai illa, wanda raunin da yake yi yana zubar da jini, Shine: Jita-jita masu mugun manufa, da qarerayi da ake watsawa.
Wajibi ne ga ma'abuta garin harami biyu, su zama jinni da tsoka tare da jagororinsu, suna xauka daga malumansu na Allah, waxanda aka yi musu shaida da zurfin ilimi da addini da tsantseni da hikima da sanin jiya-da-yau.
Kuma wajibi ne akan kowa, ya rinjayar da maslahohi na gabaxaya, akan na xaixaiku. Kuma suyi ta faxi-tashi wajen hidima wa qasarsu, da gaskiya da ikhlasi, suna masu neman lada da sakayya (a wurin Allah), saboda su qasar harami ne guda biyu da suke yin hidima wa addini, kuma suke yin hidima wa musulmai gabaxaya, wajibi ne su yi qoqari wajen haka, suna xaukar haka daga faxakarwar addininsu da manufofin shari'arsu.
Wajibi ne akan iyalai su riqa kula da 'ya'yansu samari, suna bibiyar halayensu, suna dubi cikin yanayinsu, kuma su riqa sanya musu ido cikin ababen da suke fiskanta, tare da komawa zuwa ga Allah (جل وعلا) da yin addu'ar cewa ya kiyaye 'ya'yansu daga kowace fitina da jarabawa da aqida vatacciya, saboda addu'a daga iyaye guda biyu sababi ne mai girma na samu gyaruwa.

Ya malaman wannan al'ummar!
Himmatuwa da lamuran wannan al'ummar ya kasance kuna sanya hikima a cikinsa da kaifin hankali, da kyautata duban mai zai kai ya komo, kuma mu kiyayi kowani Magana ko fatawar da samari za su iya fahimtarta ba a gurbinta ba, ko su su xora ta ba a ingantaccen wajen xaukar ta ba. Wannan kuma ba zai yiwu ba, sai idan ana lura da manufofin shari'a, waxanda maluman musulunci suka yi bayaninsu, tare da kyautata karatun fahimtar addini ta hanya miqaqqa, wanda zai xauki samari izuwa ga aiki da hikima da bi sannu-sannu, da tausasawa, da nisantar gaggawa.

Daga qarshe:
Kalmar godiya ce, ga jami'an tsaro a qasarmu, da kuma mutum na farko mai kula da tsaro (shugaba), saboda suna kan tozo na azama, da hasama, da kula da hidima wa musulmai, da kiyaye musu amincinsu, da zaman lafiya, bayan Allah (جل وعلا); da fatan Allah ya saka musu da mafi alkhairin sakamako, kuma Allah ya kiyaye su daga kowani mummuna. Kuma ya karvi wanda yam utu daga cikinsu cikin shahidai, kuma Allah ya warkar da kowani maras lafiya mai rauni.

Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran musulmai daga kowani zunubi, sai ku nemi gafararsa, lallai shi mai gafara ne mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
            Ina godiya wa Ubangijina kuma ina yin yabo a gare shi.

            Ya ku Musulmai:
            Yana daga falalar Allah (سبحانه) ga al'umma: Abinda ya shar'anta a gare su, na aiyukan biyayya da xa'a; waxannan da za su basu lada mai yawa, Saboda (ai) ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) faxinsa:
"Wanda yayi azumin ramadana, sannan ya biyar da guda shida a watan shawwal, to kamar ya azumci shekara ne".

            Kuma baya halatta –a xayan zancen maluma guda biyu da yafi fitowa fili-, ga wanda akwai ramukon azumi na wajibi akansa ya gabatar da azumi na mustahabbi; saboda yin hakan ya saba wa qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi ingantattu.

            Sai ku kasance –Ya ku bayin Allah- kuna masu xaukar darasi daga watan azumi, wanda zai kai ku izuwa ga falaloli masu girma, da halayya kyawawa. Kuna masu siffantuwa da sifar kyauta a rayuwarku gabaxaya, da kuma kyautatawa da jin qai a asirce da a bayyane.
Kuna rayuwa a matsayin al'ummar annabi Muhammadu wacce take rayuwa a duniya da halayya maxaukaka, da kyawawan ababe masu girma. Kuma yin hakan, yana cikin MANUFOFIN ADDININ UBANGIJINKU na farlanta farillai, da wajabta wajibabbu.

            Sannan yana daga cikin aiyuka mafi girma: Yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
            Ya Allah! Kayi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu, masoyinmu annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
            Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye su da kiyayewarka, da kulawarka da kariyarka, Ya Allah! Ka yayebaqin cikinsu, ka kawar da vacin ransu.
            Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulunci, Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulmai, Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya Ma'abucin girma da karramawa, Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya  Mabuwayi Ya Mai hikima.
            Ya Allah! Ka gafarta wa muminai maza da muminai mata, da musulmai maza da musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu.
            Ya Allah! Ka datar da majivincin lamarinmu zuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda, Ya Ma'abucin girma da karramawa.  
            Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
            Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Allah! Ka qarfafe su, ka datar da su, ka tagaza musu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
            Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Ma'abucin girma da karramawa. Kuma ka mayar da su zuwa qasashensu cikin lafiya da riba, Ya Rayayye, Ya Tsayayye.
            Ya Allah ka bamu mai kyau a duniya, A lahira shima mai kyau, Ka kare mu daga azabar wuta.
            Ya Allah! Ka sanya mu cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu, kuma ka gafarta musu zunubansu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
            Ya Allah! Ka samar wa musulmi wani lamari na shiriya, Ya Allah! Ka samar wa musulmi gabaxaya wani lamari na shiriya, wanda zaka gyara halinsu da shi, Ya rayayye Ya tsayayye.
Qarshen addu'armu shine: ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...