HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/Shawwal/1437H
Daidai da 15/Yuli/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AUWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
NI'IMAR AMINCI DA ZAMAN LAFIYA
Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh
Al-Subaitiy –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 10/ Shauwal, 1437H, mai taken: NI'IMAR AMINCI DA ZAMAN
LAFIYA,
Wanda kuma a cikinta ya tattauna akan aminci da zaman lafiya, da yadda
ha'anonin rayuwa gabaxaya u ke rataye da shi, kuma cewa ba zai yiwu rayuwa ta
miqe ba, ai idan akwai zaman lafiya, sannan ya ambaci sabuban da su ke rushe
samun zaman lafiya, ko su ke girgiza gininsa, kamar yadda ya bayyana yadda ake
samar da aminci da zaman lafiya.
HUXUBAR FARKO
Yabo ya
tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya mana baiwa da ni'imar samun
aminci da zaman lafiya, Ina yin yabo a gare shi (سبحانه) kuma ina godiya a gare shi, kuma ina
roqonsa wa'aztuwa da xaukar izina.
Kuma ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da
abokin tarayya, wanda ya ke cewa: "Kuma kowani abu a wurinsa yana da gwargwado"
[Ra'ad: 8].
Kuma ina
shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
yayi kira (da'awah) zuwa ga Allah cikin hikima, da gwanancewa. Allah yayi qarin
salati a gare shi da iyalansa matukar dare da yini suna canjin aiki.
Bayan haka:
Ina yin
wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah.
Allah
(تعالى) yana cewa: "Allah ne ya sanya
qasa ta zama a gare ku TABBATATTA " [Gafir: 64].
Ma'ana: Ya sanya qasa ta zamto wurin da akansa
ku ke samun aminci da tabbatuwa, kuma ku ke rayuwa akanta, ku ke kuma sassarafa
qasa, domin ku aikata abinda ku ka ga dama, kuma ku ke tafiya a kan hanyoyi ko
vangarorinta.
Sha'anonin
rayuwa mabanbanta gabaxayansu sun ratayu ne, da SAMUN AMINCI
DA TABBATUWA, Kuma rayuwa ba za ta yiwu ba, matuqar aka rasa aminci da wurin
nitsuwa da tabbatuwa, saboda aminci abu ne da ake cikiyar samu da nema, kuma
buqata ce ta dole, kuma babu wani mutum da baya buqatar aminci da wurin nitsuwa
da tabbatuwa.
Ita
kuma rayuwa, bata yin daxi wa mutum, kuma mutum baya samun walwala, kuma ba zai
samu nashaxin raya qasa ba, face a qarqashin inuwar aminci da nitsuwa, ko samun
tabbatuwa, wanda shi ne mafi tsadan abin nema, kuma mafi daraja daga cikin
kyautukan abin bauta (wato: Allah); Allah (تعالى) yana
cewa: "Kuma mu ka ce: Ku sauka gabaxaya daga aljanna (zuwa duniya),
sashinku na maqiyi ga sashi, kuma, kuna da matabbata a cikin qasa, da jin daxi
zuwa ga wani lokaci" [Baqara: 36].
Kenan,
Abun da ya tattara ni'imar duniya da jin daxinta, ko samun walwala da sa'ada a
cikinta ya ratayu ne akan samun sabuban aminci da nitsuwa ko samun tabbatuwa,
Wannan ya sanya Manzon Allah (S.A.W) ya ke cewa: "Wanda ya
wayi-gari a cikinku da aminci ga ransa, ko a cikin jama'arsa da iyalansa da
dukiyarsa, ya wayi-gari da lafiya a cikin jikinsa, ya wayi-gari a wurinsa akwai
abincin yininsa, to kamar an haxa masa duniya ne kwacakam xinta".
Kuma
mumini an yi umurni a gare shi, da ya yawata a doron qasa, don neman inda zai
samu tabbatuwa ko aminci da nitsuwa, Allah (تعالى)
yana cewa: "Lallai ne waxanda Mala'iku su ka karvi rayukansu, suna masu zaluntar
kayukansu, Su kan ce: A kan me ku ka kasance? Sai su ce: Mun kasance waxanda
aka raunana, a bayan qasa, Sai su ce: Ashe qasar Allah bata kasance mayalwaciya
ko faxi ba; da za ku yi hijira zuwa gare
ta!" [Nisa'i: 97].
Lamarin
neman nitsuwa da tabbatuwa, ko samun aminci sha'aninsa yana da girma, wannan ya
sanya Allah (ta'alah) ya sanya shi a
matsayin sakamakon 'yan aljanna da ni'imarsu, a inda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Ma'abuta aljanna a
wannan yinin sune su ke da matabbata ta alkhairi, kuma su su ka fi kyan wurin kishingixa" [Furqan:
24].
Kuma Allah (سبحانه) ya
ce: "Suna masu dawwama a cikinta, ta yi kyau ga zama matabbata da mazauni"
[Furqan: 76 ].
Kuma
addinin musulunci ya tanadi narkon azaba mafi tsanani ga yin varna a doron qasa
bayan gyaruwanta, da amincinta da tabbatuwanta, Allah (تعالى) yana cewa: "Daga cikin mutane,
akwai wanda maganarsa tana baka sha'awa a kan rayuwar duniya, kuma ya ce Allah
yana shaide da abinda ke cikin zuciyarsa, amma shi mai tsananin husuma ne *
Idan kuma ya juya, sai ya yi gaggawa a cikin qasa domin ya yi varna a cikinta, kuma ya halaka shuka da 'ya'yan dabbobi, kuma
Allah baya son varna * Kuma idan aka ce masa: ka bi dokokin Allah da taqawa,
sai buwayar savo ta xauke shi, to jahannama ta ishe shi, kuma haqiqa shimfixa ta
munana" [Baqara: 204-205].
To, duk wanda ya yi varna a bayan qasa, ya
kuma rushe ma'anonin da su ke kawo aminci da tabbatuwa, da da'awa ko riyawar
cewa shi gyara wai ya ke yi, ko kuma zai kawo gyara, da kuma da'awar cewa: Shi,
yana daga ma'abuta gaskiya, to wannan mavarnaci ne, kamar yadda Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan aka ce masu: Kada ku yi varna a
doron qasa, Sai su ce: Lallai mu masu kawo gyara ne * Ku saurara! Lallai su,
mavarnata ne, saidai basu sani ba" [Baqara: 11-12].
Musulunci
da tsari ko manhajinsa na Ubangiji, shine: Mavuvvugar samun aminci da
tabbatuwa, kuma shine tushensa; wato: tabbatuwa ko amincin cikin zuci, da
tabbatuwa ta samun aminci da zaman lafiya, da tabbatuwa ko aminci a cikin
al'ummai.
Kuma yana gusar da sabuban da suke jawo
tsanani da wahala ko qunci da takura, Allah (تعالى)
yana cewa: "Wanda Allah ya nufi ya shiryar da shi, ya kan yalwata zuciyarsa da
son musulunci, Wanda kuma ya nufi ya vatar da shi, ya kan sanya qirjinsa ya
zama cikin qunci, kai ka ce, yana hauhawa sama" [An-aam:
125].
Kuma
musulunci ya sanya xaukacin abinda Allah ya ajiye a bayan qasa, na dukiyoyi
masu girma, da qofofin shigan kuxi masu yawa a qarqashin gudanarwan mutane,
domin su samar da aminci da tabbatuwa, Allah (تعالى)
yana cewa: "Shine wanda ya sanya muku qasa abar horewa mai sauqi, sai ku yi
tafiya cikin vangarorinta, kuma ku ci daga arziqinsa, kuma zuwa gare shi za a
tayar da ku" [Mulk: 15].
Kuma
dukkan umurni da hani (wato: تكاليف الشريعة),
da manufofin shari'a (مقاصد الشريعة),
da wajibabbunta na lalura (ضرورات الشريعة),
sun zo ne domin su tabbatar da ginshiqan kawo tabbaci ga rayuwar mutane, Wannan
kuma kasancewar umurni da hani na wannan shari'ar, suna komawa ne izuwa ga
kiyaye manufofin shari'ar a cikin halittu. Kuma waxannan manufofin babu makawa sai
an samar da su gabanin tsayuwar maslahohin addini dana duniya, ta yadda idan
aka rasa su, maslahohin duniya ba za su tsayu ba, Sai ma su gurvace, su lalace,
har a rasa rayuwa.
Manufofin kuma sune: (1) Kiyaye
addini, (2) da rayuka, (3) da tsatso, (4) da dukiyoyi, (5) da hankali.
Al'ummomin
da suke fatan samun bunqasa da ci-gaba suna farawa ne da kakkafa ginshiqan samun
aminci da tabbatuwa, kuma wannan shine farkon abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fara maganansa akai, a yayin da ya shiga
garin Madina, yana mai hijira, saboda ya faxi ma'anonin da za su jawo aminci da
tabbatuwa, cikin kalmomin soyayya da salamar aminci, a inda yake cewa: "Ya ku mutane!
Ku yaxa sallama, ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi sallah da dare
alhalin mutane suna barci, Sai ku shiga aljanna da salamar aminci".
A nan, Musulunci ya kafa tsari ko manhajin da
zai jawo aminci da tabbatuwa, wanda ginshiqinsa shine : kyakkaywar mu'amalar da
take ginuwa akan 'yan'uwantaka, da watsar da tsanani ko tsanantawa, da qarfafa
taimakakkeniya.
Sai garin Madina ya wayi-gari a matsayin babban
misali, wajen aminci da salama da haxewar kai, da tabbatuwa.
Mai yin tunani cikin halin al'ummomin
da suka rasa aminci da tabbatuwa a cikinsu, idanunsa ba za su kasa ganin
yaxuwar tashin hankali da firgici ba, sai mutane su riqa wayan-gari basu da
wani aminci akan dukiyoyinsu ko mutuncinsu (wato: iyalansu).
Wanda
kuma yafi kowa sanin qimar aminci da tabbatuwa sune: Waxannan da aka jarrabe su
da rashin aminci; har suka gudu suka bar qasarsu, ko suka yi nesa da iyalansu,
suka kuma xanxani xacin yunwa, ko kuma qasarsu ta faxa cikin duhun zaman kara-zube
da rashin tsari, har ake zubar da jinane akan turvayarta, Sai gawawwakin mutane,
ko vangarorin jikinsu suke ta zuba, a cikinta, ko yanayin kwace dukiyoyi da
wawashe su ya game ko-ina, a cikinta.
Kuma,
da haka ne za mu sani cewa: Lallai samun aminci da tabbatuwa, a cikin garurruka
da rayuka da dukiya da mutunci (ko iyalai) aljannar Allah ce, da baiwarsa ga
muminai tun a nan gidan duniya, kuma shine mafi girman abinda Allah yayi baiwa
da shi ga al'ummai da mutane, Allah (تعالى)
yana cewa: "Sai su bauta wa Ubangijin wannan xaki * Wanda ya ciyar da su daga
yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].
Kuma masu hankali basa shakkar cewa, lallai
aminci shine ginshiqin bunqasa, kuma shine kyakkyawan yanayin da zai kai ga
gina qasa, ko bunqasa ta, da kawo aikin rayar da qasa.
Yana
daga abinda ke rushe aminci, ko ya sanya ginshiqansa rawa, Yaxuwar
jita-jita, da bazuwar qare-rayi, da kuma karvarsu ba tare da tunani ko tsanaki
ba.
Yin haka kuma yana tayar da fitintinu, kuma
yana shuka rarrabuwar kai da savani.
Kamar
yadda, munana xaukar ababen da aka samu ta kafar sada zumunta na zamani (wato: facebook,,,);
kafar da take da matsayi na gaba-gaba wajen samun himmar mutane: ya haifar da
kwan-gaba, kwan-baya wajen tarbiyya, kuma ya sanya shakku kan wasu aqidun, kuma
ya rushe dayawa daga tabbatattun halayya, Sai waxannan hanyoyin -da irin wannan
fahimtar- su ka wayi-gari gatarin da ke rurrushe, aminci da zaman lafiya.
Sakaci wajen mu'amala da haram, da qoshi da
dukiyar riba, yana kwashe ginshiqan tabbaci ta vangaren dukiya, Allah (تعالى) yana cewa: "Allah yana kwashe
albarkar riba, kuma yana bunqasa sadakoki, Kuma Allah baya son dukkan mai
kafirci mai yawan savo" [Baqara: 276].
Qetare
iyaka da riqon sakainar kashi ga ni'imomi, da qaranta yin godiya, tare da
almubazzaranci, ko rowa, su kuma suna jawo rashin nitsuwa ko rashin aminci a
cikin al'ummai, Allah (تعالى)
yana cewa: "Sau dayawa mun halaka alqaryoyi waxanda suka yi sako-sako da lamarin
rayuwarsu, Kuma waxancan sune wuraren zamansu, ba a zauna a cikinsu, a bayansu ba,
sai xan kaxan, kuma mun kasance mune masu gajewa"
[Qasas: 58].
Lallai
ne fitintinun da suke kewaye da mu, sun nuna mana, kuma mun koya daga gare su,
cewa: Kiyaye aminci da tabbatuwa, wani lamari ne da ba za a iya wadatuwa ga barinsa
ba. Kuma yin aiki don tabbatar da ginshiqan aminci, da kakkafa vangarorinsa, da
yin duka da qarfe ga hannun mai rushe-rushe da mavarnaci wajibi ne na shari'a,
kuma abun nema ne ga qasashe.
Kuma
kiyaye samun aminci da tabbatuwa yana tabbata ta hanyar
samar da Imani, da kuma yin riqo da alqur'ani da Sunnah, da samar da haxin kai,
da guje wa sabuban da suke jawo rabuwar kai da savani, Allah (تعالى) yana cewa: "Duk wanda ya sava
wa Manzo bayan shiriya ta bayyana masa, kuma ya ke bin turbar da ba ta muminai
ba, za mu jivinta masa abinda ya jivinta, kuma mu shigar da shi jahannama, kuma
ta yi muni ga makoma" [Nisa'i: 115].
Aminci
yana tabbatuwa kuma yana dawwama: Ta hanyar yaxa ilimin da ke haskaka
duhu, ya kuma yaye baqin ciki, ya kawo bunqasa, sannan ya riqa bada kariya daga
aqidu da shubuhohi, ko aukawa cikin qari ko sakaci (ga addini). Kuma shi ilimi
shine ginshiqin samun rabo ga xaixaikun mutane, da kuma wadaci ga al'ummomi,
Allah (تعالى) yana cewa: "Ka ce: Shin waxanda
suke da sani, za su yi daidai da waxanda basu da sani" [Zumar:
9].
Kuma
aminci yana dawwama: Da ambaton falalar Allah (تعالى), da yin godiya a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa: "A lokacin da
Ubangijinka ya bada shela cewa: Idan kuka yi godiya, to zan yi qari a gare ku,
Idan kuma kuka butulce to lallai azabata mai tsanani ce"
[Ibrahim: 7].
Allah
yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu
da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman
gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
…
HUXUBA TA BIYU
Yabo
na Allah ne wanda ya yi halitta kuma ya daidaita, "Wanda ya qaddara,
kuma ya shiryar" [A'alah: 3], Ina yin yabo a gare shi, kuma ina gode
masa, akan ni'imarSa da ba a iya qididdige ta, kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukaki
Wanda yafi xaukaka,
Kuma
ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma
manzonSa, Wanda ya yi kira zuwa ga kowani alkhairi da shiriya,
Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa da
sahabbansa, da waxanda suka bi shiriya.
Aminci
yana tabbatuwa kuma yana dawwama: Ta hanyar kulawar al'umma da yin
Umurni da kyakkyawa, da hani kan aikata mummuna, tare da bunqasa lamarin
aiyukan alkhairi, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma a samu wata al'umma daga cikinku, suna yin kira zuwa ga
alkhairi, suna yin umurni da kyakkawa, kuma suna hani ga mummuna, kuma waxannan
sune masu samun rabo" [Ali-Imraan: 104].
Sai ya tabbatar da alkhairi, ga al'ummar wanda
shine, ginshiqin samun aminci, ta hanyar samar da taimakakkeniya da alaqa, da
danqon zumunta da soyayya. Kuma lallai yin aiyuka na alkhairi ko na
taimakakkeniya, ginshiqi ne na bunqasar al'umma, da samun wadaci, da aminci, a
lokacin da rayuwa zata tabbatu ga marayu da miskinai da matar da ta rabu da
mijinta, da marasa lafiya. Kuma aiyukan kyauta, su kan sanya ganuwa ga faxar
banbancin matsayi (da ke aukuwa tsakanin masu kuxi da marasa, shi), kuma ganuwa
ga hassada, Sai su fiskantar da kowa (talaka da mai kuxi) izuwa ga yin aiki, da
tunanin cigaba, da gina al'umma, ko qasa, Allah (تعالى) yana cewa: "Wanda ya yi aiki na
kwarai, namiji ne ko mace, alhalin yana mumini, lallai za mu rayar da shi,
rayuwa daddaxa, kuma za mu sakanta musu ladansu da mafi kyan abinda suka
kasance suke aikatawa" [Nahl: 97].
Sai
ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku
da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati
ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi
Muhammadu da da iyalan Muhammadu, kamar yadda ka yi salati wa wa Ibrahima, da
iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.
Kuma ka yi albarka ga
annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka wa
Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda
huxu shiryayyu; Abubakar da Umar da
Usmanu da Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da afuwarka
da karramawarka da kyautatawarka, Ya mafificin masu rahama.
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da
musulmai,
kuma ka qasqantar da
kafirci da kafirai,
kuma Ya Allah! Ka
ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta
zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya
Allah! Wanda ya nufe mu, ya nufi musulunci da musulmai da mummuna to ka shagaltar
da shi, da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsare-tsarensa, Ya Mai amsa
addu'a.
Ya
Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da
yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Mafificin rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka
aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi
gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga
cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa;
na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba
mu sani ba.
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda
ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna
roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu,
ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla musu
akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara
akan wanda ya zalunce mu,
Ya
Allah! Ka gafarta mana, da iyayenmu, da musulmai maza, da mata, Ya
Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka bada waraka ga marasa lafiyanmu, ka yaye ibtila'I ga wanda aka
jarrabe shi daga cikinmu,
Ya Allah! Ka yi rahama ga matattunmu,
Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda ka ke so,
kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya
aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da
littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya Mafificin masu rahama.
Ya
Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi),
Ya Allah! Ka kiyaye jami'an
tsaronmu a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye su gabaxaya da kiyayenka, ka
basu kulawa, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai tagaza musu,
Ya Ubangijin talikai, Ya Allah! Ka kiyaye su cikin iyalansu, da zurriyarsu da
'ya'yansu da dukiyarsu, lallai kai mai iko ne akan komai.
"Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi
mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da
imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya
Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 10].
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a
lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].
"Lallai ne Allah
yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin
hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama
masu tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment