HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله
عليه وسلم)
JUMA'A, 23/JUMADAL
AKHIRAH/1437h
Daidai da 01 /AFIRILU/2016m
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI, HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUSH SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta
tabbata ga Allah; Mai tunkuxe bala'oi, Mai yaye cutuka, Mai jin addu'a.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Shi kaxai yake ba shi da
abokin tarayya; a lahira da duniya.
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa; Annabi zavavve,
kuma bawa abun zavi.
Ya Allah ka yi salati a gare shi da sallama,
da albarka, Shi; da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta cika alkawari.
Bayan
haka:
Ya ku
Musulmai!!
Ina yin
wasiyayya a gare ku da Ni kaina, da kiyaye dokokin Allah (taqawa), da yin biyayya
a gare shi a asirce da bayyane, domin da aikata haka ne kawai alheri da rabauta
da cin nasara suke kasancewa, a gidan lahira, da nan duniya.
Ya ku
Musulmai!!
GINSHIQI
WANDA DA SHINE KAWAI bawa Musulmi zai samu sa'ida, da kuma tabbatar da
shi ne zai tsira, kuma ta hanyar samar da shi ne zai rabauta, wannan ginshiqin Shine:
TABBATAR DA CIKAKKIYAR BAUTA GA ALLAH; Ubangijin talikai; Kuma don haka
ne aka halicce shi (Musulmi), kuma don shi aka samar da shi; "Kuma ban halitta
jinsin aljani da na Mutane ba sai don su bauta mini" [Zariyaat:
56]. Ma'ana: Su kaxaita Allah da ibada (bauta). Kamar yadda Abdullahi xan Abbas
–رضيى الله عنهما ya faxi hakan.
Tauhidin
Allah Mahalicci shine hanyar kowace nasara, kuma girmama Allah da
kaxaice shi da bauta shine musabbabin kowani rabo. Kasancewar sababi
mafi girma na samun rabo a gidan duniya da lahira, kuma ginshiqin da yafi girma
na samun aminci da zaman lafiya shine: Tabbatar da tauhidi ga Allah Makaxaici,
Wanda ake nufinSa da buqatu, Ta hanyar Bawa ya kasance mai ikhlasi wa Allah a
cikin Nufin zuciyarsa, Mai ikhlasi a gare shi (سبحانه)
cikin sonSa da girmama Shi Mabuwayi cikin sha'aninSa, Mai ikhlasi ga Allah a cikin tsoronSa da fatan
samun alherinSa, da cikin addu'oinSa, Mai ikhlasi ga Allah, a zahirinsa da
baxininsa; wato: cikin ababen da ya fiskanta da nufe-nufensa, Allah (سبحانه) yana faxa wa AnnabinSa Muhammadu (صلى الله عليه وسلم):
"Ka ce: Lallai sallata da yankana da
rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya,
kuma da aikata haka aka umurce ni, Kuma nine farkon Musulmai" [An'am:
162-163].
Kuma kamar yadda Allah yace:
"Abin bautanku abin bauta ne guda xaya, kuma,
A shi kaxai ne za ku miqa wuya" [Hajj: 34].
Kuma kamar yadda Allah yake cewa:
"Kuma ku yi ta komawa zuwa ga Ubangijinku,
kuma ku miqa wuya a gare shi" [Zumar: 54].
Xan'uwana Musulmi!
Haqiqa
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
yi kwaxayin dasa wannan ginshiqin mai girma, a cikin faxakarwar da yake yi, da
da'awarsa, da rayuwarsa, saboda kwaxayin alheri da yake yi wa al'ummarsa, da
yadda yake son tsira ga mabiyansa, Wannan ya sanya ya toshe dukkan hanyoyi, ya
kuma hana duk wani salo da zai kai zuwa ga suka ko samun tasgaro cikin tauhidi, ko yayi tasiri ga kamalar
tauhidi da cikarsa,
Kuma yana daga cikin faxakarwarSa (umurninsa)
don tabbatar da waxannan manufofin maxaukaka masu girma: WASIYYARSA
Wacce ta zama babbar qa'ida daga cikin qa'idodin addini, kuma ta zama ginshiqi
tushe wadda abinda ta qunsa yake bada kariya ga TAUHIDI DA IMANI, Ya zo daga Abdullahi
xan Abbas (رضي الله عنهما) yace:
Na
kasance a bayan Manzon Allah (S.A.W) wata rana sai yace da ni, “Ya kai
yaro! Zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah, sai ya kiyaye ka; ka
kiyaye Allah za ka same shi a gaba gare ka (yana yi maka jagora); idan zaka
roqa to ka roqi Allah; idan zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani,
da al’umma za su taru domin su amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanar da
kai komai ba , sai da abinda Allah ya rubuta maka. Idan kuma da al’umma za su
taru domin su cuce ka da wani abu, ba za su cuce ka ba, sai da abinda Allah ya
rubuta maka. An xauke alkaluma, takardun kuma sun bushe”.
Tirmiziy [2516] ya ruwaito shi, kuma yace hadisi ne mai kyau ingantacce.
Na'am!
Lallai
wannan wasiyya ce wacce a cikinta ta qunshi: Dashen girmama Allah a
cikin zukata, da bayanin cewa Shi ne wanda linzamin lamura gabaxayansu yake
hannunSa, kuma a wajenSa ne taskokin duniya suke, da mabuxan kowani abu.
(Allah) yana biyan buqatu, kuma yana amsa addu'oi. Halittu gabaxayansu mabuqata
ne zuwa gare shi (سبحانه),
kuma suna da lalurar bixar karamcinSa da kyautarSa da rahamarSa, "Wanene yake amsawa
mabuqaci idan ya roqe shi, ya ke kuma yaye mummuna?" [Namli:
62].
Kuma
"Idan Allah ya shafe ka da cuta to babu mai yaye maka face Shi, kuma
idan ya nufe ka da alheri to babu mai mayar da falalarSa, Yana samun wanda yake
so daga cikin bayinSa da shi, Kuma shi ne: Mai gafara Mai rahama"
[Yunus: 107].
Wasiyya ce daga
shugaban annabawa da manzanni wacce ta ke karantar da Musulmi cewa: A lokacin
neman biyan buqatu da yaye baqin ciki da musibu kada ya nufi wani face
MahaliccinSa mabuwayi da xaukaka, Allah ta'alah yana cewa:
"A kai kaxai mu ke yin bauta, kuma daga gare
ka kawai muke neman taimako" [Fatiha: 5].
Wasiyya
ce da take yin gargaxi wa Musulmi kan aukawa cikin sabbuban halaka madawwami,
da azaba na dindindin. Kuma (wasiyyar) tana yin kashedi ga halitta akan
fiskantar wanin Allah da addu'a, ko ya nemi agajinsa a cikin mawuyatan hali da
bala'oi, ko ya roqi wani koma-bayan Allah yaye cuta, ko jawo amfani da farin ciki,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne, duk wanda ya haxa Allah da wani
to haqiqa Allah ya haramta aljanna akansa, kuma makomarsa itace wuta" [Ma'ida:
72].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanda ya haxu da Allah baya haxa
Shi da komai ya shiga aljanna, Wanda kuma ya haxu da Shi yana yi masa shirka to
ya shiga wuta", Muslim ya ruwaito shi.
Ya zo cikin hadisin Abdullahi xan Mas'ud
"Wanda ya mutu alhalin yana roqan wani kishiya koma bayan Allah
ya shiga cikin wuta", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Wasiyya
ce da take taqaice maka –Ya kai Musulmi- bayanin karantarwar alqur'ani, da hadafinsa
da manufofinsa, da gayoyinsa cikin ababen da yayi umurni da waxanda yayi hani,
da labarun da suke cikinsa da qissosinsa; Waxanda suke nuna cewa: Duk wanda
ya rataya da Allah, ya saukar da buqatunsa zuwa gare shi, ya kuma fawwwala
al'amarinsa gare shi: To sai Allah ya isar masa a kowani lamari, ya kuma
sauqaqe masa kowace wahala, ya kusanto masa da duk wani abu na nesa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne Allah yana yin faxa saboda
waxanda suka yi imani" [Hajji: 38]. Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda yayi tawakkali ga Allah to
ya isar masa" [Xalaq: 3].
Wanda
kuma ya rataya zuciyarsa da wanin Allah, ya nitsu da shi = to sai a qyale shi da
shi, sai ya wayi gari cikin qasqanci da wulaqanci, sai kuma ya auka cikin
sharrace-sharrace da musibu masu raxaxi, Ya zo daga Muhammadu xan
Abdurrahman xan Abiy-Lailah, daga xan'uwansa Isah, Yace:
"Na shiga wa Abdullahi xan Ukaim don
na ziyarce shi, a tare da shi akwai ja
(wata cuta ce a jikin fata), Sai nace: Shin ba za ka rataya wani abu ba? Sai ya
ce: Mutuwa tafi hakan kusanci".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya ratawa wani abu, to
sai a qyale shi; a qi taimaka masa", Ahmad ya ruwaito shi, da
Attirmiziy.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Duk wanda wata buqata ta sauka a
gare shi, sai ya yi qoqarin sauke ta wa Mutane to lallai ya dace, kada
buqatarsa ta zama da sauqi. Wanda kuma ya sauke ta ga Allah, Sai Allah ya zo
masa da wani arziqi cikin gaggawa, ko da mutuwa ta nesa",
Ahmad ne ya ruwaito shi.
Sai
ka lazimta –Ya kai Musulmi- yin aiki da wannan wasiyyar, don kada
bidi'oi da soye-soyen zuciya su yi wasa da kai, sai ra'ayoyi mabanbanta (na
vata) suyi wurgi da kai! Saboda mutum bashi da wata kariya daga hakan, sai ta
hanyar bin turbar irin wannan wasiyyar mai haske wanda sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) suka tarbiyyantu akanta, har cikar
tauhidi wajen aikinsu da wannan wasiyar ya kai yadda Aufu xan Malik Al'ashja'iy
yake bamu labari, a inda yace:
"Mun kasance a wurin Manzon Allah mu
tara ko takwas ko bakwai, sai (Annabi) –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: Kada ku tambayi Mutane komai. Kuma haqiqa
na ga sashin waxannan Mutanen dorinar xayansu ta kan faxi, amma ba zai roqi
wani don ya miqo masa ita ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya zo daga Sauban, yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Wanene zai lamunce min cewa ba zai
roqi Mutane komai ba, Ni kuma na lamunce masa samun aljanna? Sai nace:
Nine. Sai (Sauban) ya kasance baya roqon wani mutum komai",
Abu-Dawud ya fitar da hadisin da Annasa'iy.
"Xa" ga Xan'uwan Al'ahnaf xan Qais
ya koka ciyon haqorin dasori, Sai shi Al'ahnaf yace da shi: Lallai ganin da
yake cikin idona ya tafi tun shekaru arba'in, amma ban tava faxa wa kowa ba.
To,
Ya kai Musulmi! Sai ka koma ka fake zuwa ga Allah, a lokutan tsanani, da
vacin rai. Kana mai rataya ranka da Allah maxaukaki shi kaxai; ba da waninsa
ba, a lokutan musibobi da tashin-tashina, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Idan baqin ciki ya samu xayanku, ko
bala'i to sai ya ce: Allah, Allah shine Ubangijina; kuma ba zan haxa shi da
komai ba…", Axxabaraniy a cikin littafin Al'ausax ya fitar da
wannan hadisin.
Kuma Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya kasance yana yin addu'a a lokacin
baqin ciki, ya kan ce: "LA ILAHA ILLAL LAHUL AZIM, LA ILAHA
ILLAL LAHU RABBIS SAMAWATI WAL ARDHI WA RABBIL ARSHIL AZIM –Ma'ana: Babu abin
bautawa face Allah mai girma, Babu abin bautawa sai Allah; Ubangijin sammai da
qassai, kuma Ubangijin al'arshi mai girma", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
Kuma
Maluma sun bada tabbaci cewa lallai duk wanda ya nemi taimako (isti'anah), ko
neman tsari (isti'azah), ko ya nemi agajin wata halitta da ta mutu, ko wacce
bata nan, ko agajin mai rai cikin abinda bashi da iko akansa face Allah
(istigasa), to waxannan shirka ne waxanda suke rushe aiyuka.
Ya ku Musulmai!
Lallai haqiqa
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
kwaxaitu wajen dasa bishiyar tauhidi a cikin zukata, kuma yayi jihadi cikin
da'awarsa zuwa ga wannan ginshiqin; Ya
nuna kwaxayi kan bada kariya wa vangaren tauhidi kariya cikakkiya, don kada
wata naqasa ta same shi, ko kuma tasgaro da cikas, ba a cikin zantuka ba, ko
aiyuka, ko manufofi da nufe-nufe; Saboda an tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) dangane da Mutum idan ya haxu da
xan'uwansa Shin zai yi masa durquso (ko ya sunkuyar da wuyansa a gare shi)? Sai
ya ce: A, a! Ahmad ya fitar da hadisin da Attirmiziy. Kuma yace: Hadisi
ne hasan. Wannan kuma ya kasance ne saboda hana qanqan da kai idan bag a Allah
Mai girma ba.
Kuma
Annabi (صلى الله عليه وسلم) Mai tausayi ya
karantar, kuma ya bada bayanin abinda zai tunkuxe waswasin Shexan da kaidinsa
da akircinsa; saboda Anas ya ruwaito cewa lallai wani Mutum ya ce:
Ya Muhammadu! Ya jagoranmu, xan jagoranmu, xan
mafi alkhairinmu, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
ce: Ya ku Mutane! Ku lazimci taqawarku, kada Shexan ya vatar da ku, Ni
Muhammadu ne, bawan Allah kuma manzonSa, bana son ku xaga ni fiye da matsayin
da Allah ya xora ni akansa", Annasa'iy ya fitar da hadisin da kuma
Ibnu-Hibbana.
Kuma ya zo a cikin Sahihul Bukhariy daga gare
shi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Kada ku qetare iyaka wajen yabo a
gare ni, kamar yadda Nasara suka qetare iyaka kan Isah xan Maryam, Kawai Ni
bawa ne, Sai ku ce: Bawan Allah da ManzonSa", Bukhariy ya fitar
da hadisin.
'Yan'uwa
cikin imani!!
Yana daga
ababen da suka bayyana kwaxayin Annabi (s.a.w) ga tauhidi, da cikakken kula da
ya bayar kan tabbatar da shi, Yadda ya toshe kowace hanya wanda Shexan zai iya
aukar da bayi cikin tavo ko tarkon shirka, da tatsuniyoyin jahiliyyah; Wannan
ne kuma ya sanya karantarwarsa (صلى الله
عليه وسلم) suka zo da hani kan fiskantar ma'abuta
qaburbura, da neman fakewa zuwa gare su, ko qanqan da kai a gaban itatuwan
qofar kabarin, ko neman agajin ma'abuta kaburburan, a lokutan tsanani ko vacin
rai, wanda har abada baya halatta sai ga wanda ya qagi qasa da samai, Ya zo
daga Abu-Hurairah (رضي الله عنه)
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Ya Allah! Kada ka sanya qabarina ya
zama gunki da ake masa bauta, Fushin Allah yayi tsanani akan mutanen da suka
riqi qaburburan annabawansu Masallatai", Ahmad ya fitar da shi, da
Malik a cikin littafin muwaxxa, da riwayar Axa'a xan Yasar.
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada kulawa mai girma ga lamarin
tauhidi, sai ya yi gargaxi kuma ya tsawatar kan bin hanyoyin Shexan, da
vatarwansa, ta hanyar fitinuwa da lamarin layu da guru, da lamarin rataya su ga
jikin rayuka ko dukiyoyi, da hujja ko da'awar cewa wai suna tunkuxe
sharrace-sharrace, wai kuma suna tafiyar da cutuka, suna kuma janyo alkhairori,
Ya zo a cikin "Musnad" cewa:
"Wanda ya rataya wata laya to lallai
yayi shirka", Alhakim ya fitar da hadisin .
Kamar
yadda Annabi (عليه الصلا والسلام) ya
tsawatar kan ruxuwa da masu suddabaru da rufa-ido, ko kuma bokaye maqaryata, a
inda yake cewa:
"Wanda ya je wajen boka, ko mai duba
sai ya gaskata shi kan abinda ya ke faxa to lallai ya kafirce da abinda aka
saukar zuwa ga Muhammadu –صلى الله
عليه وسلم-", Malamai huxu a cikin sunan
suka ruwaito shi, da Alhakim.
Kuma lallai an tambaye she aikin sihiri, don
warware sihiri, sai ya ce:
"Aikata hakan yana daga aiyukan
Shexan", Ahmad da Abu-Dawud da Albaihaqiy suka ruwaito shi.
Shi kuma hakan shine: Annushrah, wanda
kuma shine warware sihiri da wani sihirin kwatankwacinsa.
Ya
ku taron Musulmai!!
A matsayar
da Rai zata iya sanya Mutum aikata abinda bashi da kyau, ko abinda bai halatta
ba, wanda shinelokacin neman magani, A nan ma Annabi (s.a.w) yana tunatar da
al'ummarsa da lamarin tauhidi, da wajabcin bada kula mai girma ga hakan, ta
hanyar rataya rai da Allah, da neman mafaka ko fakewa a gare shi, da dogaro da
shi (tawakkali), da rashin waiwayawa sai izuwa gare shi, saboda A'ishah (r.a) ta
ruwaito cewa lallai Manzon Allah (s.a.w) ya kasance idan ya ziyarci maras
lafiya, ya kan ce:
"Ka tafiyar da cuta, ya Ubangijin
Mutane, ka bada waraka; don kai ne Mai bada waraka, babu waraka idan ba
warakarka ba, warakar da bata barin wata cuta", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma ya faxa wa Usman xan Abul-As, a lokacin
da ya koka wa Manzon Allah cutar da ta addabe shi a jikinsa, tun musuluntarsa,
Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce da shi: "Ka sanya hannunka a wurin da yake maka zogi ko raxaxi daga
jikinka, sannan ka ce: Bisillah, har sau uku. Sai kuma ka faxa sau
bakwai: A'uzu billahi wa qudratihi min sharri ma ajidu wa uhaziru, Ma'ana:
Ina neman tsarin Allah da qudurarSa daga sharrin abinda nake ji, da wanda nake
tsoro", Musli ya ruwaito shi.
'Yan'uwan
Musulunci!!
Yana
daga cikin misalai ko alamomin da Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya nunar wa mutane na kwaxayinsa kan
kaxaita Allah da tauhidi (har cikin laffuza), da himmatuwarsa wajen hakan ya
tabbatu a cikin rayuka: Karantarwarsa mai girma da ta zo cikin abinda ABdullahi
xan Abbas ya ruwaito; cewa: Lallai wani mutum yace: ما شاء الله وشئت ma'ana: Allah ya nufa, kaima ka nufa. Sai
Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace masa:
"Ka sanya ni kishiya ga Allah! A'a, ka
ce: Allah shi kaxai ya nufa", Ahmad da
Ibnu-Majah suka fitar da hadisin.
A cikin Huzaifah kuma daga
Annabi (s.a.w) ya ce:
"Kada ku ce:
Allah ya nufa, Wane shima ya nufa, Saidai ku ce: Allah ya nufa, Sa'annan sai
wane ya nufa", Ahmad da Abu-Dawud da Ibnu-Majah suka
fitar da hadisin.
Yana kuma daga cikin vangarorin da suke nuna kwaxaituwar
Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) don ganin al'ummarsa ta tsira: Faxakar da su da ya yi kan su
kiyayi duk abinda ke savawa haqiqanin tauhidi, ko ya ke rushe tushen tauhidi
daga asalinsa, ko rushe cikar tauhidi (na wajibi), Daga cikin haka akwai:
Saqonsa mai girma da ya fiskantar zuwa ga al'umma, cikin abinda Umar ya ruwaito
daga gare shi (صلى الله
عليه وسلم), ya ce:
"Ku saurara!
Lallai Allah yana hana ku yin rantsuwa da iyayenku; Duk wanda zai yi rantsuwa
to ya rantse da Allah, ko yayi shiru". Umar ya
ce: Ban yi rantsuwa da iyaye
bat un lokacin da na ji annabi, a adadin kaina, ko kuma ta hanyar hikaya. Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
A hadisin Abdullahi xan Umar
kuma, lallai Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yace:
"Duk wanda
ya rantse da wanin Allah to lallai ya kafirce ko yayi shirka", Ahmad da Abu-Dawud da Attirmiziy suka fitar da hadisin.
Ya ku, Musulmai!!
Ku sanya
tauhidin Mahalicci ya zama a gaba ga idanuwanku, ku rayu cikin bautar Mahalicci
da girmama shi, da rataya da shi cikin kowani sha'ani, ku kuma xaure rayuka da
zukata da Mahaliccinsu. Suma gabbai ku aikata abin da zai ya yardar da wanda ya
qage su = Sai alkhairi ya tabbata muku, sannan ku rabauta da lada mai girma,
"Lallai waxanda suka ce Ubangijinu shine Allah sa'annan suka tsayu,
to babu tsoro a tare da su kuma ba za su yi baqin ciki ba * Waxannan sune
ma'abuta aljannah suna masu dawwama a cikinta, sakamakon abinda suka kasance
suke aikatawa" [Ahqaf: 13-14].
Allah
ya sanya ni; Ni da Ku daga cikin masu tabbatar da tauhidi, masu tabbatar da
girmamawa da ta kai maqura ga Mahaliccinsu, kuma Mai azurta su (mabuwayi da
xaukaka).
Ina faxan wannan maganar, kuma ina neman
gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai, daga kowani zunubi, Sai ku nemi
gafararSa; saboda Shi ya kasance Mai gafara ne Mai Jin qai.
HUXUBA TA BIYU:
Ina yin
godiya wa Ubangijina kuma ina yin yabo a gare shi, kuma ina tuba zuwa gare shi
kuma ina neman gafararSa. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne. Ya
Allah ka yi qarin salati da sallama da albarka a gare shi, da kuma iyalansa da
sahabbansa.
Ya
ku Musulmai!
Yana
daga bada kariyar da Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya ke yi wa tauhidi, Yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya hana duk abinda mutum yake tunaninsa
na munanan tunani, da kuma zace-zace da zuciya take tunanowa, Ya zo cikin
hadisin Imran, "Baya cikinmu wanda ya yi canfi (shu'umi), ko aka yi masa canfi, ko
yayi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko yayi sihiri ko aka yi masa sihiri",
Albazzar ya fitar da hadisin kuma isnadinsa hasan ne.
Ya zo a cikin hadisin Mu'awuyah xan Alhakam
As-sulamiy, cewa: Ya Manzon Allah! Lamura ne da muka kasance muna aikata su a
zamanin jahiliyya; Mun kasance muna zuwa wurin bokaye, Sai ya ce: Kada ku je
wurin bokaye. Ya ce, Sai na ce: Mun
kasance muna canfa abubuwa? Ya ce: Wannan wani abu ne wanda xayanku ke jinsa
a cikin ransa, to amma kada ya hana ku ci gaba da aikata abin da kuka sa a
gaba". Muslim ya ruwaito shi.
Kuma y azo cikin abinda Ahmad ya ruwaito da
Abu-Dawud da Attirmiziy, daga hadisin Abdullahi xan Mas'ud, "Canfi
shirka ne".
Daga
qarshe, ka sani! Lallai dukkan lamura a hannun Allah maxaukaki suke, kuma
kowani abu yana aukuwa ne da qaddararSa da hukuntawarSa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Cuta bata da tasirin yaxuwa da
kanta, kuma canfi bashi da tasiri, haka canfin tsuntsun duji, kuma canfi da
watan Safar bashi da tasiri", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Sai ku bi -da rayukanku- hanyar alqur'ani, kuma
ku lazimta wa rayuwarku bin tafarki ko sunnar shugaban 'ya'yan qabilar adnan, wanda
mafificin salati da sallama suke qara tabbatuwa akansa…
Sannan, Lallai Allah ya umurce mu da wani
loamari mai girma, Wanda kuma shine: Yawaita salati da sallama ga wannan
Annabin Mai girma.
Ya Allah! Ka yi
salati da sallama ga annabinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai, Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikin da ke
tare da musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikin da ke
tare da musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikin da ke
tare da musulmai.
Ya Allah! Ka yaye wa 'yan'uwanmu da
suke qasar Yaman da siriya, da Iraqi da sauran qasashen Musulmai, ka yaye musu
dukkan wata cuta da mummunan lamari da abin qi.
Ya Allah! Ka dawo musu da aminci da zaman
lafiya.
Ya Allah! Ka saukar musu da aminci da
zaman lafiya.
Ya Allah! Ka rubuta buwaya da
jagoranci ga al'ummar musulmai, Ya ma'abucin xaukaka da yin kyauta.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza
da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bada waraka wa marasa
lafiyanmu da majinyatan musulmai.
Ya Allah! Ka bada waraka wa marasa
lafiyanmu da majinyatan musulmai.
Ya Allah! Ka bada waraka wa marasa
lafiyanmu da majinyatan musulmai.
Ya Allah! Ka shugabantar akan musulmai
zavavvunsu.
Ya Allah! Duk wanda ya yi makirci wa
musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka kama shi. Ya Allah! Ka sanya
halakarsa cikin tsare-tsaren makircin da ya ke yi, Ya ma'abucin xaukaka da
baiwa.
Ya Allah! Ka datar da shugaban
Musulmai na wannan qasar; Mai hidiman Masallatan harami biyu zuwa ga abinda
kake so, kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka datar da shi da masu
na'ibtansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, Ya ma'abucin
xaukaka da baiwa.
Ya Allah! Ka kasha wutar fitina wa
musulmai.
Ya Allah! Ka kasha wutar fitina wa
musulmai.
Ya Allah! Ka kiyaye rundunarmu a
ko-ina suke, Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu a ko-ina suke, Ya Allah!
Ka kiyaye jami'an tsaronmu a ko-ina suke, Ya Allah! Ka musu sakayyar
alkhairi kan abinda suke yi wa musulunci da musulmai. Ya Allah! Ka musu
sakayyar alkhairi kan abinda suke yi wa musulunci da musulmai.
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu da
qasashen musulmai daga dukkan mummuna da ababen qi.
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu da
qasashen musulmai daga dukkan mummuna da ababen qi.
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu da
qasashen musulmai daga dukkan mummuna da ababen qi.
Ya Allah! Lallai mu muna neman
tsarinka daga tsadar kaya, da annoba.
Ya Allah! Lallai mu muna neman
tsarinka daga tsadar kaya, da annoba.
Ya Allah! Lallai mu muna neman
tsarinka daga tsadar kaya, da annoba. Kuma muna neman tsarinka daga fitintinu
munana, waxanda suka bayyana daga cikinsu da waxanda suka vuya, Ya Rayayye,
Ya Tsayayye.
Ya Mawadaci ya Abun godiya, Ya Allah, Ya
Mawadaci, Ya Abun godiya! Ka shayar da garurrukanmu da gidajen musulumai.
Ya Allah! Ka shayar da garurrukanmu
da gidajen musulumai.
Ya Allah! Ka shayar da garurrukanmu
da gidajen musulumai.
Ya Allah! Ka shayar da mu, Ya
Allah! Ka shayar da mu, Ya Allah! Ka shayar da mu. Ya Allah! Ka
yi mana rahama (ka ji qanmu) saboda dabbobinmu.
Ya Allah! Ka ji qanmu saboda
dabbobinmu.
Ya Allah! Ka ji qanmu saboda dabbobinmu, Ya ma'abucin
girma da baiwa, Ya Mawadaci, Ya abun godiya, Ya mai rahama Ya Mai jin qai.
Bayin Allah!
Ku riqa ambaton Allah zikiri mai yawa.
Kuma qarshen Addu'armu itace:
الحمد لله رب العالمين