2015/06/25

HUDUBAR MADINA (1)








HUXUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN ANNABI (r)
9/RAMADHAN/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; ma'abocin girma da karramawa,    da mulkin da ba a cimmasa,    da kuma buwayar da bata qasqanta,  
Ina miqa godiyata ga Ubangijina akan manya-manyan ni'imomi,   
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,    mamallaki mai tsarki da kamala,   
Ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa,    Fiyayyen waxanda suka yi sallah da azumi,   
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa masu karamci.
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah a dukkan lokuta,    don ku rabauta da samun yardar Ubangijinku da aljannoni,   
Ya ku musulmai   
Ku kiyaye gafala da rafkana saboda suna halakarwa,    Sannan ku kiyaye jinkirta tuba, saboda munanan burace-burace suna vatarwa.
Kuma lallai Allah da falalarSa ya yi baiwa ga halittunSa na zahiri dana voye,    Amma su bayinSa muminai sai suka yi godiya akansu,    Yayin da su kuma maqiya Allah sai suka butulce masa,   
Allah ta'alah yana cewa:
"Wanda ya yi godiya to lallai ya yi godiya ne ga kansa. Wanda kuma ya butulce, to lallai Allah mawadaci ne abun godiya" [Luqman: 12].
            Kuma duk abubuwan da Allah  ya shar'anta na ibadodi da farilloli,    da duka abubuwan da Ya haramta na haram,    da waxanda ya tsawatar akansu na hani    =Ubangiji  ya yi su ne don karrama halittu masu hankali (mukallafai),     kuma don su zama tsarki da tsarkakewa,     kana su zama tanadar bawa da shirya shi domin ya dawwama a cikin aljannonin ni'ima,   
"tare da annabawa da siddiqai da shahidai da salihai,    Yayi kyau waxannan su zama abokan tafiya    **   Wannan kuma falala ce daga Allah,    Allah shine masani" [Nisa'i: 69-70].
           
Kuma lallai Allah mai tsarki ne,    Baya karvar aiki sai mai tsarki     Allah ta'alah yana cewa:
"Waxanda mala'iku suke xaukar rayukansu suna tsarkaka, suna cewa:     Aminci ya tabbata a gare ku,    ku shiga aljanna saboda abinda kuka kasance kuke aikatawa" [Nahli: 32].
Kuma Allah ta'alah yana cewa:
"Allah baya nufin qunci a gare ku,    Saidai yana nufin ya tsarkake ku,    Ya kuma cika ni'imominsa akanku,    tsammaninku zaku gode" [Ma'idah: 6].
Kuma Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma wanda ya nemi tsarkaka to lallai yana tsarkaka ne wa kansa"[Faxir: 18].
            Kuma Allah mabuwayi da xaukaka a cikin "hadisi qudusiy" yana cewa:
"Ya ku bayina!   Lallai waxannan aiyukanku ne nake qididdige muku su, sa'annan sai in cike muku sakayyarsu,   Duk wanda ya samu alheri to sai yayi godiya wa Allah,    Wanda kuma ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa" [Muslim ne ya rawaito shi, daga hadisin Abu-zarrin t].

            Su muminai aiyukansu sun zama tsarkaka Sai halayyansu da makomansu suka kyautata,     Allah ta'alah yana cewa:
"Wannan gidan lahira ne wanda muke sanya ta ga waxanda basa nufin girman kai a bayan qasa,     basa nufin varna,    kyakkyawar makoma tana tabbata ga masu taqawa" [Qasas: 83].

            Shi kuma kaxaita Allah ta'alah da tauhidi tatacce   shi ke tsarkake bawa, da aiyuka,     Kuma ya sanya aiyuka su inganta,   ya ninnika su,     ya tsarkake su.
            Kuma dukkan aiyuka ingantattu, karvavvu   suna bayan tauhidi ne    ( wato: kaxaita Allah ne a cikin bauta).
            Kuma duk wanda ya zalunci kansa ta hanyar yin shirka wa Allah a cikin bauta,    ko ta hanyar bidi'oi da suke karo da addinin Allah,    ko munafurcin voye; wanda ma'abocinsa ke qin hukunce-hukncen alqur'ani da sunnah     = to lallai waxannan mutanen aiki mai kyau ba zai amfanar da su ba,     kuma baza su shiga aljannah ba,    Saidai in sun tuba zuwa ga UbangijinSu maxaukaki,     Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai waxanda suka qaryata ayoyinmu, kana suka yi musu girman kai,     Baza a bubbuxe musu qofofin sama ba,     kuma ba za su shiga aljannah ba,     har sai raqumi ya shiga ta kafar allura,   Kuma da irin haka muke sakayya ga masu miyagun laifuka"[A'araf: 40].
Allah ya sake cewa dangane da munafiqai:
"Ku kawar da kai ku kyale su; lallai su dauxa ne,    Kuma makomarsu itace jahannama,     sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa" [Taubah: 95].
            An rawaito daga Abu-hurairah (t) yace: Manzon Allah (r) yace:
"Annabi Ibrahim (r) zai haxu da babansa a ranar qiyamah, alhalin a fiskar babansa akwai qura-qura na alamar qunci da qasqanci,      Sai yace masa:    Shin ban gaya maka KADA KA SAVA MINI BA!,    Sai ya ce: A yau kam ba zan sava maka ba!      Sai annabi Ibrahimu yace:    Ya Ubangijina, Shin baka min alkawarin cewa ba za ka kunyata ni ba,   Wani qasqancin ne yafi girma fiye da babana ya shiga wuta?     Sai Allah ta'alah yace:    Lallai ni na haramta shiga aljanna ga kafirai,    Sai annabi Ibrahim ya yawaita magana akan babansa wa UbangijinSa,     Daga nan; sai Allah ya shafe babansa ya rikixe ya dawo kura,     Sai ya juyo zuwa ga annabi Ibrahim,     Sai a ce masa:   Shin wannan shine babanka?    Sai yace:    A'a!    Sai ran annabi Ibrahim (u) yayi daxi,    to daga nan sai a kama qafofinsa a wurga shi cikin wuta" [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
            A kan wannan,    Ceto baya kasancewa sai ga masu tauhidi (musulmai), koda kuwa sashinsu sun aikata manya-manyan laifuka (kaba'irai).

            Su kuma ibadodi an shar'anta su ne don hikimomi masu girma, da manufofi maxaukaka,    Idan har waxannan ibadodin suka samar da hikimomi ko manufofin shar'anta su wa mutum mai hankali baligi (mukallafi) to sai su amfani ma'abocinsu da amfani mai girma.     Idan kuma ibadodin suka wofanta da tabbatar da hikimomin da aka shar'anta su don su to sai su zama hujja ga ma'abocinsu.
            Ibadar azumi an shar'anta ta ne don samar da taqawar Allah     da kyautata wa rai, da kuma kyautatawa halittu.
            Kuma lallai Allah –a cikin wannan wata na azumi mai albarka- ya haxa mana ninkin salloli na farilla,     da nafilfilin da ake yawaita su cikin dare da yini.       
            Da kuma yin zakkah ga wanda ya sanya watan ramadhana lokacin yin zakkar dukiyarsa,     da dangogin ciyarwa a qofofin alheri mabanbanta,    Ya kuma bubbuxe qofofin kyautatawa da yin sadakoki.
            Kuma Allah ya shar'anta yin umrah ga wanda hakan ya sauqaqa a gare shi,     kuma ita umrah ita ce "qaramar hajji".
            Kuma Allah ya kevance wannan watan da saukar da alqur'ani a cikinsa,     Ya kuma buxa qirazan bayi a cikin wannan watan don fahimtar alqur'ani da tunani a cikinsa,     Ya kuma sauqaqe yawaita karatunsa a cikin watan ga harsunan bayi.
            Kamar yadda ya kiyaye wannan al'ummar a cikin ramadhana daga shexanu masu taurin kai;    Basa iya isa zuwa ga abinda suka nufa na varna da fitina da sharri,   irin varnar da suke yi a waninsa.
            Kuma Allah a cikin wannan watan yayi falala ga masu azumi, ta fiskar amsa addu'oinsu,     An rawaito daga Ubadah xan As-samit (t), daga Annabi (r ) yace:
"Watan ramadhan ya zo muku,    watan albarka ne da Allah yake lulluve ku a cikinsa,    Sai ya saukar da rahama,    Ya kuma amsa muku addu'a a cikinsa,   Allah yana yin dubi zuwa ga rigayenku a cikinsa wajen aikata alheri,     Sai ya yi alfahari da ku wa Mala'ikunSa,    Sai ku nuna wa Allah alherin dake cikin kayukanku,    Saboda tavevve shine wanda aka haramta masa samun rahamar Allah a cikinsa", [Axxabaraniy ya rawaito shi, kuma maruwaitan hadisin amintattu ne].
            Kuma Ramadhan wata ne mai yawan albarka a cikin dukkan lokatansa,     Don haka, kada ka rafkana     -ya kai mai azumi-    kan cike dukkan awowin lokatansa da aiyuka kyawawa.
            Duk kuma abinda ya shuxe na lokaci to ba zai tava dawowa ba har abada.
           
Ka kuma yi hisabi wa kanka dangane da dukiyar da Allah mabuwayi da xaukaka ya baka,     sai ka nisantar da ita haramun da shubuha,     saboda abincin haram ya kan hana karvar addu'oi da aiyuka na kwarai.
            Sai ka tsarkake dukiyarka    –ya kai musulmi-     da fitar da zakka,     Saboda duk wanda bai bada zakkar dukiyarsa ba to zata zama azaba a gare shi da sharri,      Shi yana ta wahalar tattalata,     Waninsa kuma sai  ya ji daxinta a bayansa,     An rawaito daga Abu-hurairah (t), daga Manzon Allah (r) yace:
"Babu wani ma'abocin wata taskar dukiyar da baya bada zakkarta face an rikixar masa da ita zuwa ga macijiya, da zata riqa sararsa a muqamuqansa,    tana cewa: Nine dukiyarka, Nine taskarka" [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
            Kuma lallai ita zakka ibada ce ga Ubangiji maxaukaki,    Haqqi ne kuma na faqirai da baya faxuwa.      Su kuma ciyarwa na wajibi dana mustahabbi ana ninnika ladansu.
            Wace kyauta ce da falala tafi girma fiye da kyautar Allah da falalarsa; Allah shi ya baka dukkan abinda ka mallaka,     Sai kuma ya yarda ka bada wani xan gwargwado a matsayin zakka,     wanda kuma kaxan ne, da zaka fitar da shi daga dukiyarka;      Ma'ana: xaya bisa arba'in xinta 1/40   Misali a cikin miliyan xaya (1, 000000), za a bada zakkar dubu ashirin da biyar (25, 000) ne.      
Duk kuma abinda ya qaru akan miliyan ko ya ragu to za a bada zakkarsa ne gwargwadon lissafinsa,    
Allah ta'alah yana cewa:
"Duk abinda kuka ciyar na wani abu to Allah zai bada mayewansa, Kuma Allah shine mafi alherin masu azurtawa" [Saba'i: 39].
            Kuma da mawadata kowa-da-kowa daga cikinsu zai bada zakkar dukiyarsa to da baza a samu wani faqiri ba.

(Ya ku musulmai)  Damuwarku da yawaita ambaton Allah ta ana so ta kasance mai girma,      don yin zikiri shine aikin da yafi kowanne falala,   Shi kuma karatun alqur'ani a cikin nau'ukan zikiri shine yafi falala,    Kuma lallai Manzon Allah (r) ya kasance ya kan ware Qur'ani da yawaita tilawarsa a cikin watan ramadhana,     Kuma Mala'ika jibrilu a cikin watan azumi ya kasance yana yin darasun alqur'ani tare da annabi,      kamar yadda hakan ya tabbata a cikin "sahihul Bukhariy da Muslim".
            Kuma dangantakar da take tsakanin yawaita karatun alqur'ani a cikin watan azumi abu ne da yake a fili,    ga wanda ya yi tunani akanta;     Saboda kayan ci dana sha abinci ne na jiki,       Yayin da kuma Qur'ani da zikiri su kuma abinci ne na ruhi,      Shi kuma kamewa da yin azumi ya kan qarfafa ikon vangaren ruhi;      Sai musulmi yayi ta hauhawa cikin matakan ibada da falaloli   da yawaita karatun alqur'ani, da yin ambaton Allah.
            Sai ku yi gaggawa   -Allah ya muku rahama-   zuwa ga dukkan alkhairori, a cikin waxannan lokatan,     Kuma kada wani ya raina aikin alkhairi,    koda kaxan ne,    
Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai Allah baya yin zalunci daidai da kwayar zarrah,    In kuma ta kasance aiki ne mai kyau sai ya ninninka ta,    Ya kuma bayar daga wajensa lada mai girma" [Nisa'i: 40].
            Kuma kada mutum ya raina savo koda qarami ne,      saboda lallai Allah zai neme shi, kuma yana da littafin da ya kiyaye komai a wajensa,     Kuma sau dayawa mutum ya kan halaka saboda sakacinsa da qananan laifuka,    
Allah ta'alah yana cewa:
"Duk wanda ya aikata daidai da kwayar zarrah na alheri zai gan shi **   Wanda ya aikata daidai da kwayar zarrah na sharri zai gan shi" [Zalzalah: 7-8].
Kuma Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma kuyi rige cikin aikata alkhairori,     Zuwa ga Allah ne makomanku gabaxaya,    Sai ya baku labara kan abinda kuka kasance kuke savani a cikinsa" [Baqarah: 148].

            Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma!


HUXUBA TA BIYU
            Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ke karvar tuban bayinSa,     Ya kuma yi afuwa kan munana,      Wanda ya kwararo wa halittunSa daga taskokin kyautarSa abinda ba wanda zai iya qididdige shi sai Allah na alkhairori.     
Ina godiya wa Ubangijina,   Ina tuba zuwa gare Shi,    Ina kuma neman gafararSa,   
Ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,     Mahaliccin qassai da sammai.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne,      Wanda ya qarfafe shi da hujjoji da mu'ujizozi.
            Ya Allah kayi qarin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa waxanda suke rigaye zuwa ga aikata alkhairi.
            Bayan haka!
            Ku ji tsoron Allah ta hanyar aikata nagartattun aiyuka,    da qaurace wa abubuwan da aka haramta.
            Bayin Allah!
            Albishirinku !
            Kan irin abinda aka tanada wa wannan al'ummar na alheri gamamme, da kuma lada mai karamci,      a cikin wannan watan mai girma;
            Saboda;
Duk "Wanda yayi azumin ramadhana da imani an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa".     
Haka kuma Duk "Wanda ya yi tsayuwar ramadhana –sallar dare- da imani an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa",     
Sannan kuma Duk "Wanda ya yi tsayuwan daren qaddara da imani to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa".     Kamar yadda ingantattun hadisai suka nuna haka.
Allahu akbar !         Wa subhanallahi !!
Ka yi mamakin girman wannan ladan,     daga Allah mai mulki, mai karbar tuba,     Allah ta'alah ayana cewa:
"Rai bata san abinda aka voye mata ba na sanyin ido,    sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa" [Sajadah: 17].

            Saidai kuma tare da waxannan falalolin da suke faranta rai     Musulmi ransa ya kan vaci saboda abinda yake gani na rarrabuwar kai da savani, da kuma yawan qungiyoyin da suke munana wa musulunci,      suke kuma qoqarin jirkita kyakkyawiyar aqidarsa ingantacciya mai haske,   da caccanza hukunce-hukuncensa.    Saidai kuma  tavewa ne da qasqanci Allah ta'alah ya rubuta ga duk wanda ya ke yaqar addini.
            Sai kayi qoqarin sanin gaskiya     -Ya kai musulmi-  don ka gane su wanene suke kanta;    Sai ka kasance tare da su, Allah ta'alah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah,    Kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Taubah: 119].
            Ka kuma san varna da 'yan bidi'a don ka nisance su,    tare da tunkuxe  varnar da kuma bidi'oi.
            Kuma matsayin wannan al'ummar yana nan ne gwargwadon taimakonta ga gaskiya,       da kuma yadda take turbuxe varna..
Ya zo cikin hadisi:
"Wata jama'a daga cikin al'ummata ba zata gushe ba akan gaskiya, suna taimakakkeniya,   har sai lamarin Allah ya zo" [Muslim ya rawaito shi].

            Kuma wajibi ne akan al'umma suyi ta tuba zuwa ga Allah,    da komawa gare shi;    domin ya yaye  musu abinda ya dame su na bala'oi.

            Kuma wajibi ne ga kowani musulmi ya yi addu'a ta musamman ga musulmai gabaxayansu, da kuma jagororinsu,    Ya kuma riqa saka su cikin addu'oinsa lokacin da yake yin addu'oi wa kansa;   Saboda watan azumi yana daga cikin sabbuban xauke bala'i,    da kuma canza shi da alherori da abubuwan farin ciki.

Bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin…" [Ahzab: 56].

Addu'a ….
……………….
……………….

……………….

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...