HALIN MAGABATAN KWARAI
A "WATAN AZUMI" (RAMADHANA)
-حال
السلف في رمضان-
TANADAR
VANGAREN ILIMI NA
"MADARUL WAXAN"
FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Xan'uwana musulmi, … 'yar'uwata musulma….
Amincin Allah da rahamarsa da albarkokinsa su
tabbata a gare ku…. Bayan haka:
Ina tura muku wannan wasiqar, wacce aka qunsa
mata bege da kuma gaishe-gaishe masu qamshi, zuwa gare ku, daga zuciyar da ta
take qaunarku don Allah, Kuma Allah muke roqon ya haxa mu a gidan karramawarsa
(aljannah), wacce take matattara ga rahamarsa.
A sakamakon shigowan watan azumi Nake gabatar
muku da taqaitacciyar kyauta. Ina fatan ba za ku raina ta ba, sannan kuma za ku
karve ta da yalwataccen zuciya. Tare da yi mini nasiha. Allah ta'alah ya kiyaye
ku ya baku kariya.
TA YAYA ZA MU FISKANCI WATAN AZUMI MAI ALBARKA?
Allah ta'alah yana cewa:
(شَهْرُ
رَمَضانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّناتٍ مِنَ
الْهُدى وَالْفُرْقانِ) [البقرة: 185ٍ]
Ma'ana: "Watan ramadhana wanda aka sauqar
da alqur'ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, da kuma bayanan shiriya da kuma
rarrabewa tsakanin gaskiya daga qarya" [185].
Xan'uwana mai karamci:
Lallai Allah ta'alah ya kevance watan ramadhana
akan sauran watanni (guda goma sha biyu) da wassu kevantattun abubuwa, da tarin
falaloli masu yawa, Daga cikinsu:
·
Warin da ke fita daga bakin
mai azumi daxinsa a wajen Allah fiye da qamshin turaren al-miski.
·
Mala'iku su kan yi ta neman
gafara ga masu azumi har zuwa lokacin da za su yi buxa baki.
·
A watan azumi ana sanya
shexanu a cikin sarqoqi da mari.
·
Ana bubbuxe qofofin aljanna
a watan azumi, kuma a rurrufe qofofin wuta.
·
A cikin watan ramadhana akwai
wani dare –lailatul qadari- wanda yafi watanni dubu alheri, Mutumin da aka
haramta masa samun alherin wannan daren lallai an haramta masa dukkan alheri
gabaxayansa.
·
Ana gafarta wa masu azumi a
daren qarshe na watan ramadhana.
·
Allah yana da bayin da yake
'yantar da su daga faxawa wuta, Wannan kuma ya kan kasance a cikin kowani dare;
daga cikin dararen ramadhana.
Ya kai xan'uwana mai
karamci:
Watan da ya kevanta da waxannan abubuwan na
falaloli, Da wani abu ne ya kamata mu fiskance shi?
Shin da shagalta da yin wargi ko kwanan zaune,
ko kuma muyi ta yin guna-guni kan shigowansa, tare da bayyanar da jin nauyinsa
akanmu? Allah ya tsare mu daga waxannan gabaxaya.
A'a… Lallai bawan Allah; nagari ya kan
fiskanci shigan wannan watan ne kawai da yin kyakkyawiyar tuba, da kuma qulla
azama ta gaskiya kan morar lokutan wannan watan, ta hanyar cike su da aikata
aiyuka nagari. Muna roqon Allah ya taimake mu wajen kyautata masa bauta.
XAN'UWANA MAI KARAMCI, GA WASSU AIYUKA NAGARI WAXANDA SUKE DA GIRMA A CIKIN WATAN
AZUMI (RAMADHANA):
1-
YIN AZUMI: Saboda
Annabi (r) yana cewa:
«كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ،
الْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا إِلَى سَبْعِ مِائَةِ ضِعْف، يَقُولُ اللَّهُ U: إِلَّا
الصّيام، فَإِنَّهُ لِي، وَأَنَا
أَجْزِي بِهِ، تَرَكَ شَهْوَتَهُ وَطَعَامَهُ
وَشَرَابَهُ مِنْ أَجْلِي، لِلــــــــــــصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَــــرْحَةٌ
عِنْدَ فِطْرِهِ، وَفَرْحَةٌ عِنْدَ لِقَاءِ رَبِّهِ،
وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ
مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ».
Ma'ana:
"Dukkan aiyukan xan adam nasa ne, kyakkyawa guda xaya za a ninnika masa
zuwa kwatankwacinsa sau goma, zuwa ninki xari bakwai. Allah mabuwayi da
xaukaka yana cewa: Saidai azumi, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi
sakayya akansa, ya bar sha'awarsa da abincinsa da abin shansa don Ni. Mai azumi
yana da nau'ukan farin ciki guda biyu, waxanda ransa take yin fari da su, farin
ciki xaya a lokacin buxa bakinsa, da wani farin cikin a lokacin ganawarsa da
Ubagijinsa. Kuma warin bakin mai azumi yafi daxi a wajen Allah fiye da qamshin
turaren al-miski".
[Bukhariy
da Muslim suka rawaito hadisin]. Ya kuma ce:
«مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا
غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana:
"Wanda yayi azumin ramadhana yana mai imani da neman lada an gafarta masa
abinda ya gabata daga zunubansa".
[Bukhariy
da Muslim suka rawaito shi].
Kuma babu
shakka lallai wannan lada mai yawa ba wai yana kasancewa ne ga wanda ya hanu
daga ci ko sha kaxai ba ne, saidai Annabi (r) yace:
«مَنْ لَمْ
يَدَعْ قَوْلَ الزُّورِ، وَالْعَمَلَ بِهِ، وَالْجَهْلَ، فَلَيْسَ لِلَّهِ حَاجَةٌ
أَنْ يَدَعَ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ».
Ma'ana:
"Wanda bai bar zancen qarya, da aiki da ita ba, to Allah bashi da buqatar
ya bar cin abincinsa da abin shansa".
[Bukhariy
ne ya rawaito shi]. Kuma Annabi (r) yana
cewa:
«وَالصّومُ
جُنَّةٌ، فَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ، فَلَا يَرْفُثْ وَلاَ يَفْسُقْ،
وَلاَ يَجْهَل، فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ فَلْيَقُلْ: إِنِّي امْرُؤٌ صَائِمٌ».
Ma'ana:
"Azumi garkuwa ne, Idan yinin azumin xayanku ya zo to kada ya yi batsa,
kuma kada ya yi fasiqanci, kada ya yi wauta, Idan kuma wani ya zage shi to sai ya
ce: Ni mutum ne da nake azumi".
[Bukhariy
da Muslim suka rawaito hadisin].
2-
SALLAR DARE: Saboda
Annabi (r) yana cewa:
«مَنْ قَامَ
رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana:
"Wanda ya yi tsayuwar ramadhana –sallar dare- yana mai imani da neman lada
an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". [Bukhariy da Muslim suka
rawaito hadisin].
{وَعِبَادُ
الرَّحْمَنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ
الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلَامًا * وَالَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمْ
سُجَّدًا وَقِيَامًا} [الفرقان: 63-64].
Ma'ana:
"Bayin mai rahama sune waxanda suke tafiya a bayan qasa da nitsuwa. Kuma
idan masu wauta suka yi musu magana sai su faxi: aminci. Kuma sune waxanda suke
kwana ga Ubangijinsu cikin sujjada da tsayuwa" [Alfurqaan: 63-64].
Kuma
lallai yin sallar dare (qiyamu allaili) xabi'a ce da Annabi (r) da sahabbansa suka saba
da ita, A'ishah (رضي الله عنها) tana cewa:
"لاَ تَدَعْ قِيَامَ اللَّيْلِ؛ فَإِنَّ رَسُولَ اللهِ
صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ لاَ يَدَعُهُ، وَكَانَ إِذَا مَرِضَ، أَوْ
كَسِلَ، صَلَّى قَاعِدًا".
Ma'ana:
"Kada ka bar yin sallar dare, saboda Manzon Allah -r- ya kasance baya barin yin
sallar dare, Kuma ya kasance idan ya yi rashin lafiya ko kasala to sai ya yi
sallar a zaune".
Kuma Umar
xan Al-khaxxab (t) ya
kasance ya kan yi sallar raka'oin da ya ga dama a cikin dare, har zuwa lokacin
da dare zai raba biyu, to sai ya tayar da iyalansa don su yi sallah, sa'annan
yace musu: Sallah! Sallah!! yana mai karanta musu:
{وَأْمُرْ
أَهْلَكَ بِالصَّلاَةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا لاَ نَسْأَلُكَ رِزْقًا نَحْنُ
نَرْزُقُكَ وَالْعَاقِبَةُ لِلتَّقْوَى} [طه:
132].
Ma'ana:
"Kuma ka umurci iyalanka da yin sallah, kuma ka jure akanta, ba za mu tambaye
ka wani arziqi ba, mune muke arzurta ka, kuma kyakkyawan makoma yana kasancewa
ne ga taqawa" [Xaha: 132].
Abdullahi xan Umar ya
kasance yana karanta wannan ayar:
(أَمَّنْ هُوَ قانِتٌ
آناءَ اللَّيْلِ ساجِدًا وَقائِمًا يَحْذَرُ الْآخِرَةَ وَيَرْجُوا رَحْمَةَ
رَبِّهِ) [الزمر:
9].
Ma'ana: "Shin wanda ya
kasance cikin dogon tsayuwa a tsakiyar dare yana sujjada, yana tsayawa, yana
tsoron lahira, yana fatan rahamar Ubangijinsa". Sai Abdullahi yace:
(ذَاكَ عُثْمَانُ
بْنُ عَفَّانَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْه).
Ma'ana: "Mai wannan
siffar shine Usman xan Affan (t)".
Ibnu-abiyhatim yace:
(وَإِنَّمَا قَالَ ابْنُ عُمَرَ ذَلِكَ، لِكَثْرَةِ صَلاةِ
أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ عُثْمَانَ بِاللَّيْلِ وَقِرَاءَتِهِ، حَتَّى إِنَّهُ
رُبَّمَا قَرَأَ الْقُرْآنَ فِي رَكْعَةٍ).
Ma'ana: "Kawai
Abdullahi xan Umar ya faxi haka ne saboda yawan sallar Amirulmuminina Usman da
daddare, da yawan karatunsa, har ma a wassu lokutan ya karanta alqur'ani
gabaxayansa a cikin raka'a guda xaya".
An rawaito daga Alqamah xan Qais, yace: Na kwana tare da
Abdullahi xan Mas'ud (t) a cikin wani dare sai ya
tashi a farkonsa, sa'annan ya sake tashi yana sallah, ya kasance yana karatu da
irin karatun limamin masallacin unguwarsa, na karatun tartili, baya tarji'i,
yana jiyar da waxanda suke gefensa, (yayi ta salla) har sai da ya zama babu
wani abu da ya rage na duhun qarshen dare, sai kamar abinda ke tsakanin kiran
sallar magriba, zuwa a idar da ita, sa'annan sai Abdullahi ya tashi yayi wutri.
Ya zo a cikin hadisin As-sa'ib xan Yazid yace:
«كَانَ الْقَارِئُ يَقْرَأُ
بِالْمِئِينَ، حَتَّى كُنَّا نَعْتَمِدُ عَلَى الْعِصِيِّ مِنْ طُولِ الْقِيَامِ،
قال: وَمَا كانو ينْصَرِفُون إِلَّا عند الْفَجْرِ».
Ma'ana: "Liman ya
kasance yana karanta surori masu ayoyi xari, har sai da muka zama muna dogara
akan sanduna saboda dogon tsayuwa, Yace: Kuma basu kasance suna idar da sallar
ba sai kusan asuba".
FAXAKARWA: Ya dace akanka –Ya kai
musulmi- ka tsaya a kammala sallar tarawihi da kai, a tare da liman, domin a
rubuta ka cikin mutanen da suka samu tsayuwar dararen azumi, saboda Annabi (r) yana cewa:
«مَنْ قَامَ مَعَ
إِمَامِه حَتَّى يَنْصَرِفَ كُتِبَ لَهُ قِيَامُ لَيْلَةٍ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
yi tsayuwar dare tare da limaminsa har ya gama, to za a rubuta masa ladan
tsayuwar dare cikakke" [Masu littafin sunan suka rawaito shi].
3-
YIN SADAKA: Manzon Allah (r) ya kasance shine wanda
yafi mutane yin kyauta, kuma ya kasance yafi yin kyautar tasa a cikin watan
ramadhana, saboda ya kan yi kyautar alkhairi fiye da iskar da aka turo (gabanin
saukar ruwa). Kuma yana cewa:
«أَفْضَلَ
الصَّدَقَةِ صَدَقَةٌ في رمضان...».
Ma'ana: "Mafificiyar
sadaka ita ce sadakar da aka yi ta a cikin watan ramadhana…" [At-tirmiziy
ya rawaito wannan hadisin daga Anas t].
Zaid xan Aslam, ya rawaito
daga Babansa, lallai shi yace:
(سَمِعْتُ عُمَرَ،
يَقُولُ: أَمَرَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ
نَتَصَدَّقَ، وَوَافَقَ ذَلِكَ مَالًا عِنْدِي، فَقُلْتُ:
الْيَوْمَ أَسْبِقُ أَبَا بَكْرٍ إِنْ سَبَقْتُهُ يَوْمًا،
فَجِئْتُ بِنِصْفِ مَالِي، فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «مَا
أَبْقَيْتَ لِأَهْلِكَ؟» ، قُلْتُ: مِثْلَهُ، وَأَتَى أَبُو
بَكْرٍ بِكُلِّ مَا عِنْدَهُ، فَقَالَ لَهُ: «يَا أَبَا بَكْرٍ، مَا أَبْقَيْتَ
لِأَهْلِكَ؟»
قَالَ: أَبْقَيْتُ لَهُمُ اللَّهَ وَرَسُولَهُ، فَقُلْتُ: لَا
أُسَابِقُكَ إلى شَيْءٍ أَبَدًا).
Ma'ana: "Na ji Umar,
yana cewa: Manzon Allah (r) ya umurce mu da cewa muyi
sadaka, sai hakan ya dace da wata dukiya da take wajena, Sai nace: Yau kam zan
riga Abubakar, tun da ban tava wuce shi ba da-xai. Yace: Sai na zo da rabin
dukiyata, Sai Manzon Allah (r) yace: Me ka bari wa
iyalanka? Yace: Sai nace: Kwatankwacinsa. Shi kuma Abubakar sai ya zo da dukkan
abinda ke wurinsa, Sai Manzon Allah (r) yace: Me ka bari wa
iyalanka? Yace: Na bar musu Allah da Mazonsa, Nace: Har abada ba zan sake neman
riga ka ga wani abu ba".
An rawaito daga Xalhat xan
Yahya xan Xalhat, yace: Kakata mai suna SU'UDIY 'yar Aufu al-murriyyah ta bani hadisi
–kuma ita ce mai warware wa Xalhat xan Ubaidullah kwarjalle; wato: matarsa-,
Tace: Wata rana Xalhat ya shigo wajena alhalin ransa a vace, Sai nace: Me yasa
naga fiskarka a turvune? Na sake cewa: Menene sha'aninka, shin wani abu ne kake
kokonto dangane da ni, sai in taimake ka? Sai yace: A'a! Madalla da ke a
matsayin matar mutum musulmi! Sai ta sake cewa: Menene sha'aninka? Sai yace:
«الْمَالُ الَّذِي
عِنْدِي قَدْ كَثُرَ وَأَكْرَبَنِي» قُلْتُ: وَمَا عَلَيْكَ اقْسِمْهُ، قَالَتْ:
فَقَسَمَهُ حَتَّى مَا بَقِيَ مِنْهُ دِرْهَمٌ وَاحِدٌ"،
قَالَ طَلْحَةُ بْنُ يَحْيَى: فَسَأَلْتُ خَازِنَ طَلْحَةَ: كَمْ
كَانَ الْمَالُ؟ قَالَ: أَرْبَعَمِائَةِ أَلْفٍ).
Ma'ana: "Dukiyar da
take wajena ne tayi yawa, sai hakan ya sanya ni cikin qunci. Tace sai nace:
Meye matsalarka, ka raba ta. Tace: Sai ya raba ta har sai da ya zama babu
dirhami xaya da ya wanzu a wajensa. Xalhat xan Yahya yace: Sai na tambayi mai taskance
dukiyar Xalhat, cewa: Nawa ne wannan dukiyar? Sai yace: Dubu xari huxu
ne".
Ya kai xan'uwana! Yin
sadaka a watan ramadhana yana da fifikon falala da muhimmanci, don haka, sai
kayi gaggawar aikata ta, kayi kwaxayin aiwatar da ita, gwargwadon halinka, Kuma
tana da misalai dayawa, Wassu daga cikinsu, sune:
a-
CIYAR DA ABINCI: Allah ta'alah yana cewa:
(وَيُطْعِمُونَ
الطَّعامَ عَلى حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا * إِنَّما نُطْعِمُكُمْ
لِوَجْهِ اللَّهِ لا نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزاءً وَلا شُكُورًا
* إِنَّا نَخافُ مِنْ رَبِّنا يَوْمًا عَبُوسًا قَمْطَرِيرًا *
فَوَقاهُمُ اللَّهُ شَرَّ
ذلِكَ
الْيَوْمِ وَلَقَّاهُمْ نَضْرَةً وَسُرُورًا * وَجَزاهُمْ بِما صَبَرُوا جَنَّةً
وَحَرِيرًا) [الإنسان: 8-12].
Ma'ana:
"Kuma suna ciyar da abinci alhalin suna sonsa wa miskini da maraya da
kamammen bawa * Lallai muna ciyar da ku ne don neman ganin fiskar Allah, bama
nufin samun sakayya daga wajenku, ko kuma godiya * Lallai mu muna tsoro daga
Ubangijinmu yini mai tsananin muni mai qunci * Sai Allah ya kare su daga
sharrin wannan yinin, ya kuma sadar da su da haske a fiska, da kuma farin ciki
* Ya kuma yi musu sakayya saboda haqurinsu da aljanna, da kuma tufafin
alharir" [Al-insaan: 8-12].
Kuma lallai magabata na kwarai
sun kasance suna kwaxayin ciyar da abinci, kuma suna qaddamar da shi akan
ibadodi dayawa, kamar qosar da mayunwaci, ko ciyar da xan'uwa salihi. Kuma
lallai ba sharaxi ba ne ga wanda za a ciyar ya zama faqiri, Manzon Allah (r) yana cewa:
«يَا أَيُّهَا النَّاسُ!
أَفْشُوا السَّلَامَ، وَأَطْعَمُوا الطَّعَامَ، وَصِلُوا الْأَرْحَامَ، وَصَلُّوا
بِاللَّيْلِ وَالنَّاسُ نِيَامٌ، تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ بِسَلَامٍ».
Ma'ana:
"Ya ku mutane! Ku riqa yaxa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da
zumunci, kuma ku yi salla da daddare alhalin mutane suna cikin barci, Sai ku
shiga aljanna da aminci".
[Ahmad
da Attirmiziy suka rawaito shi, Kuma Albaniy ya inganta shi].
Wani daga cikin magabatan
kwarai yana cewa:
(لأنْ أدعو عشرةً مِن
أصحابي فأطعمهم طعامًا يشتهونه أحبّ إلَيَّ مِن أنْ أُعتق عشرةً مِن ولد إسماعيل).
Ma'ana:
"Na gayyaci mutane goma daga cikin abokaina sai na ciyar da su abincin da
suke sha'awarsa yafi soyuwa a wurina fiye da na 'yanta bayi goma daga cikin
'ya'yan annabi Isma'il".
Kuma dayawa daga cikin magabatan kwarai sun kasance suna fifita
wassunsu da abin buxa bakinsu, alhalin suna azumi, Daga cikinsu akwai Sahabin
annabi (r) mai suna: Abdullahi xan
Umar (رضي الله
عنهما), da Dawud Axxa'iy, da Malik xan Diynaar,
da Ahmad xan Hanbal, Kuma Abdullahi xan Umar ya kasance baya buxa baki sai tare
da marayu da miskinai, Wata rana labari ya iske shi cewa wassu daga cikin
iyalansa sun kore su, don haka sai ya qi karyawa a wannan daren.
Kuma daga cikin magabata akwai waxanda suke ciyar da
'yan'uwansu, alhalin su kuma suna azumi, sai su zauna suna yi musu hidima, da
yi musu fifita, Daga cikinsu akwai: Alhasan (Albasariy) da Abdullahi xan
Mubarak.
Abus-siwaar al-adawiy yace: ((Wassu mutane daga qabilar
baniy-adiy sun kasance suna yin sallah a cikin wannan masallacin, Babu wani
daga cikinsu da ya ke buxa bakinsa shi kaxai; Idan ya samu wanda zai ci abinci
da shi sai ya ci, in kuma bai samu ba to sai ya fitar da abincinsa zuwa
masallaci don ya ci tare da mutane, suma su ci tare da shi)).
Kuma ibadar "ciyar da mutane abinci" tana haifar da
wassu ibadodin dayawa, Daga cikinsu: Neman soyayyar 'yan'uwanka da ka ciyar da
su, Sai hakan ya zama sababin shiga aljanna,
«لَا تَدْخُلُونَ
الْجَنَّةَ حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا».
Ma'ana:
"Ba za ku shiga aljanna ba face kun yi imani, Kuma ba za ku yi imani ba
face kun so junanku".
Kamar yadda take haifar da zama da mutane salihai, da kuma
neman ladan Allah cikin taimaka musu kan yi masa biyayyar da za su aikata
sakamakon qarfin aikata haka da ya samu a gare su saboda cin abincinka.
b-
SHAYAR DA MASU AZUMI: Annabi (r) yana cewa:
«مَنْ فَطَّرَ
صَائِمًا كَانَ لَهُ مِثْلُ أَجْرِهِ، غَيْرَ أَنَّهُ لَا يَنْقُصُ مِنْ أَجْرِ
الصَّائِمِ شَيْئًا».
Ma'ana:
"Wanda ya shayar da mai azumi abun buxa baki to yana da kwatankwacin
ladansa, ba tare da an tauye wani abu daga ladan mai azumin ba" [Ahmad da
An-nasa'iy suka rawaito shi, Kuma Albaniy ya inganta shi].
4-
YIN QOQARI WAJEN KARATUN
ALQUR'ANI: Xan'uwana
a nan zan tunatar da kai ne kan lamura guda biyu daga cikin halin magabatan
kwarai:
a. Yawaita
karatun alqur'ani.
b. Yin
kuka lokacin karatunsa, ko sauraronsa, tare da yin kushu'i wa Allah tabaraka
wa ta'alah da bayyanar da nitsuwa.
YAWAN KARATUN ALQUR'ANI: Watan ramadhana shine watan
alqur'ani, don haka ya dace ga bawa musulmi ya yawaita karanta shi, Kuma lallai
yana daga cikin halin magabatan kwarai kula da littafin Allah (alqur'ani, da
yawan karanta shi), Kuma Mala'ika Jibrilu ya kasance yana "darasun
alqur'ani" a cikin ramadhana tare da Annabi (r). Khalifah Usman (t) ya kasance yana yin
saukar alqur'ani sau xaya, a kowani yini.
Wassu daga cikin magabatan
kuma sun kasance su kan yi saukarSa a cikin sallolin kowani darare uku.
Wassu kuma cikin kowani
darare bakwai.
Wassu kuma cikin kowani
goma.
Kuma sun kasance suna yin
karatun alqur'ani a cikin sallah da wajenta.
Imam As-shafi'iy ya yi
saukar alqur'ani sau sittin a cikin watan ramadhana. Suna yin karatunsu har a
wajen sallah.
Shi kuma Qatadah
dimun-da'im ya kasance a rayuwarsa yana yin sauka duk bayan kwana bakwai, a
cikin watan azumi kuma duk bayan kwana uku, Idan aka shiga goman qarshe kuma ya
kan yi sauka xaya a kowane dare.
Imam Az-zuhriy shi kuma ya
kasance idan ramadhana ya shiga ya kan gudu ya bar karatun hadisi da zama da
ma'abota ilimi, sai kuma ya fiskanci tilawar alqur'ani daga
"Mus-hafi".
Sufyan As-sauriy shi kuma
ya kasance idan ramadhana ya shiga ya kan bar kowace ibada, sai kuma ya
fiskanci karatun alqur'ani.
Ibnu-rajab yace: Kuma hani
kan karanta alqur'ani cikin qasa da kwanaki uku ya zo ne, ga wanda ya ke son
dawwama akan haka, Amma a lokuta masu falala kamar watan ramadhana, da kuma
wurare masu alfarma kamar garin Makka ga wanda ya shige ta daga waxanda ba
mutanenta ba, to mustahabbi ne a yawaita tilawar alqur'ani a cikinta, domin
ribatar falalar lokaci, da wuri. Wannan kuma shine zancen Imam Ahmad da Is-haq,
da wassunsu daga cikin jiga-jigen maluma. Kuma aikin wassunsu yana nuna haka.
Kamar yadda ambatonsa ya gabata.
SHI KUMA YIN KUKA LOKACIN
TILAWAR ALQUR'ANI:
Lallai
baya daga cikin shiriyar magabatan kwarai saurin karatun alqur'ani irin yadda
ake karanta waqa, ba tare da tunani cikinsa ko qoqarin fahimtar saqon da yake
xauke da shi ba, A'a! magabatan kwarai sun kasance maganar Allah mabuwayi da
xaukaka ta kan yi tasiri akansu, kuma su kan girgiza zukata da shi, Ya zo
cikin littafin sahihul Bukhariy daga Abdullahi xan Mas'ud (t), yace: Manzon Allah (r):
«اقْرَأْ عَلَيَّ»
قُلْتُ: آقْرَأُ عَلَيْكَ وَعَلَيْكَ أُنْزِلَ؟ قَالَ: «فَإِنِّي أُحِبُّ أَنْ
أَسْمَعَهُ مِنْ غَيْرِي» فَقَرَأْتُ عَلَيْهِ سُــــــــورَةَ
النِّسَاءِ، حَتَّى بَلَغْتُ: {فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا
مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلاَءِ شَهِيدًا}
[النساء: 41] قَالَ:
«حَسْبُكَ» فَالْتَفَتُّ فَإِذَا عَيْنَاهُ تَذْرِفَانِ.
Ma'ana:
"Ka yi mini karatu. Sai nace: Zan yi maka karatu alhalin akai aka saukar?!
Sai yace: E, lallai ni ina son na ji alqur'ani daga wanina. Yace: Sai na
karanta masa suratun Nisa'i, har sai da nazo wannan ayar:
{فَكَيْفَ إِذَا
جِئْنَا مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلاَءِ شَهِيدًا}.
Sai yace: Ya ishe ka! Dana
juya sai ga idanunsa guda biyu suna kwallar hawaye".
Kuma
Albaihaqiy ya rawaito daga Abu-hurairah (t) yace: A lokacin da ayar
{أَفَمِنْ هَذَا
الْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ}
[النجم: 59-60].
Ta sauka, Sai waxanda ake
kira: Ahlus suffah suka yi ta kuka, har sai da hawaye ya gudana akan kumatunsu.
A yayin da Manzon Allah (r) ya ji haniniyarsu sai ya
yi kuka tare da su, sai sahabbai suka qara kuka da kukansa. Manzon Allah (r) sai yace:
"لَا يَلِجُ
النَّارَ مَنْ بَكَى مِنْ خَشْيَةِ اللهِ".
Ma'ana:
"Ba zai shiga wuta ba wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah".
Kuma
Abdullahi xan Umar ya karanta "suratu al-muxaffifina", har sai da ya
iso:
{يَوْمَ يَقُومُ
النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ} [المطففين: 6].
(Ranar da mutane zasu tsaya gaban Ubangijin halittu).
Sai ya kama kuka har ya
faxi, sannan sai ya tsaya daga karatun ayoyin da suke bayanta.
An
samo daga Muzahim xan Zufur, yace: Sufyanu As-sauriy ya yi mana sallar magriba,
sai ya yi karatu, har ya isa:
{إِيَّاكَ نَعْبُدُ
وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}.
Sai yayi ta kuka har sai da
karatunsa ya yanke, Sannan daga baya sai ya koma, ya fara karatu daga
"الحمد" .
An
samo daga Ibrahim xan Al-ash,as, yace: A wani dare Fudail yana karanta (suratu
Muhammadu) naji yana cewa, a halin kuka da maimata wannan ayar:
{وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ
حَتَّى نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ
أَخْبَارَكُمْ} [محمد: 31].
Ma'ana:
"Kuma lallai zamu jarrabe ku, har sai mun san masu jihadi daga cikinku, da
masu haquri, kuma lallai zamu binciki labarunku" [Muhammadu: 31]. Sai ya
riqa faxa yana maimaitawa:
(وَنَبْلُوَ
أَخْبَارَكُمْ)، وَيُرَدِّدُ: وَتَبْلُوَ أَخْبَارَنَا؛ إِنْ بَلَوْتَ
أَخْبَارَنَا فَضَحْتَنَا وَهَتَكْتَ أَسْتَارَنَا، إِنَّكَ إِنْ بَلَوْتَ
أَخْبَارَنَا
أَهْلَكْتَنَا وَعَذَّبْتَنَا. وَيَبْكِي".
Ma'ana:
"(Zamu binciki labarunku), Ya kuma maimaita: zaka binciki labarunmu,
Lallai idan har ka binciki labarunmu za ka kunyata mu, zaka kuma tona mana
asiri, Lallai idan har ka binciki labarunmu zaka halaka mu, ka kuma azabta mu.
Sai ya ci-gaba da kuka".
5-
ZAMA A CIKIN MASALLACI HAR
SAI RANA TA FUDO:
Annabi
(r) ya kasance idan ya yi sallar asuba, sai ya
zauna a gurbin da ya yi sallarsa har sai rana ta fudo [Muslim ya rawaito shi].
Kuma Attirmiziy ya rawaito daga Anas, daga Annabi (r) lallai shi yace:
«مَنْ صَلَّى
الْفَجْرَ فِي جَمَاعَةٍ، ثُمَّ قَعَدَ يَذْكُرُ اللَّهَ حَتَّى تَطْلُعَ
الشَّمْسُ، ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ، كَانَتْ لَهُ كَأَجْرِ حَجَّةٍ وَعُمْرَةٍ
تَامَّةٍ، تَامَّةٍ، تَامَّةٍ».
Ma'ana:
"Wanda ya yi sallar asuba a cikin jam'i, sannan sai ya zauna yana ambaton
Allah har rana ta fudo, sa'annan sai ya yi raka'oi guda biyu Yana da kamar
ladan hajji da umrah, cikakku! Cikakku!! cikakku!!!"[Albaniy ya inganta
shi].
Wannan falalar kuma ana
samunta a cikin kowani yini, yaya kuma idan a kwanankin azumi ne!
6- YIN
I'ITIKAAF: Annabi
(r) ya kasance yana yin
i'itikafin kwanaki goma a kowani watan azumi, A yayin da shekarar da aka karvi
ransa kuma ta zo sai ya yi i'itikafin kwanaki ashirin a cikinta [Bukhariy ya
rawaito shi].
Kuma
lallai i'itikaafi yana daga cikin ibadodin da ya tattara dangogin xa'a dayawa a
cikinsa, na daga tilawar alqur'ani da sallah da zikiri da addu'a da wassunsu.
Wanda bai tava jarraba yin i'itikafi ba zai iya zaton cewa yana
da matsanancin wahala ko wuya, alhalin kuma shi mai sauqi ne ga wanda Allah ya
sauqaqe masa shi, saboda duk wanda ya riqi niyya ta gari da kuma azama ta
gaskiya to sai Allah ya taimake shi. Kuma an qarfafa kasancewar i'itikafi ne a
kwanaki goman qarshe don fatan dacewa da "lailatul qadari". Kuma
i'itikafi shine kevewa da shari'a ta zo da shi; saboda mai yin i'itikafi ai ya
killace kansa ne kan yin biyayya wa Allah da ambatonsa, ya kuma yanke wa kansa
dukkan shagalin da zai shagaltar da shi ko ya kawar da shi daga ibada wa Allah,
yana mai taqaice tunaninsa da zuciyarsa da xaukacinsa ga Ubangijinsa da abin da
yake kusantar da bawa zuwa gare shi.
Don haka; mai i'itikafi
babu wani tunani da ya rage masa in banda Allah, da kuma abubuwan da zasu sa
Allah ya yarda da shi.
7- YIN
UMRAH A WATAN AZUMI: Ya
tabbata daga Annabi (r) lallai shi yace:
«عُمْرَة فِي
رَمَضَانَ تَعْدل حَجَّةً».
Ma'ana:
"Yin umrah a cikin watan ramadhana tana daidai da yin aikin hajji"
[Bukhariy ya rawaito shi da Muslim]. A wata riwayar kuma:
«حَجَّةً مَعِي».
Ma'ana: "Tana daidai
da yin aikin hajji tare da ni".
Abun a taya ka murna ne –ya
kai xan'uwana- ace ka samu falala ko ladar yin hajji tare da Annabi (r).
8- NEMAN
DACEWA DA DAREN "LAILATUL QADRI": Allah ta'alah yana cewa:
{إِنَّا
أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ القَدْرِ، وَمَا أَدْرَاكَ مَا لَيْلَةُ القَدْرِ، لَيْلَةُ
القَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ} [القدر: 1-3].
Ma'ana:
"Lallai mune muka saukar da alqur'ani a cikin daren qaddara * Me ya sanar
da kai abinda ake masa suna daren qaddara? Daren qaddara shi yafi alheri fiye
da watanni dubu" [Alqadari: 1-3].
Kuma Annabi (r) yace:
«مَنْ قَامَ لَيْلَةَ
الْقَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana:
"Wanda ya yi tsayuwan daren qaddara yana mai imani da neman lada to an
gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa" [Bukhariy ya rawaito shi da
Muslim]. Kuma Annabi (r) ya kasance yana kirdadon
dacewa da lailatul qadari, kuma yana umurtar sahabbansa da cewa su neme ta,
kuma Annabi a dararen qarshe na ramadhana ya kasance yana tayar da iyalansa
daga barci, don fatan dacewa ko riskar lailatul qadari, Ya zo cikin littafin
"Musnad" daga Ubadah (daga Manzon Allah r):
«مَنْ قَامَهَا
ابْتِغَاءَهَا ثُمَّ وَقَعَتْ لَهُ غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ وَمَا
تَأَخَّرَ».
Ma'ana:
"Wanda ya samu tsayuwanta yana nemanta, sa'annan sai ta auku masa, an
gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa da abinda ya jinkirta". Imam
An-nasa'iy shima ya rawaito kwatankwacinsa. Alhafiz (Ibnu-hajar) yace: Isnadin
hadisin yana kan sharaxin Bukhariy.
Kuma lallai ya zo daga
wassu; cikin magabatan kwarai na daga sahabbai da tabi'ai cewa sun kasance suna
yin wanka tare da shafa turare a waxannan dararen guda goma, saboda kirdadon
dacewa da lailatul qadari, wacce Allah ya xaukaka ta, ya kuma xaga darajarta,
wannan kuma saboda (lailatul qadari) ita kaxai tamkar tsawon rayuwa ne, tunda aiki a cikinta yafi
alheri fiye da watanni dubu; waxanda babu ita a cikinsu, Lallai duk wanda aka
haramta masa samun alherinta to lallai an haramta masa alheri.
Kuma ana samun ta ne a
cikin darare goma da suke qarshen watan ramadhana, a kuma mara daga cikin
dararensu (21, 23, 25, 27, da 29), kuma daren da aka fi sanya qaunar samunta a
cikinsa shine daren ashirin da bakwai (27), saboda abinda Muslim ya rawaito
daga Ubayyu xan Ka'ab (t):
(وَاللهِ إِنِّي
لَأَعْلَمُ أَيُّ لَيْلَةٍ هِيَ، هِيَ اللَّيْلَةُ الَّتِي أَمَرَنَا بِهَا
رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِقِيَامِهَا، هِيَ لَيْلَةُ
سَبْعٍ
وَعِشْرِينَ، وَأَمَارَتُهَا أَنْ تَطْلُعَ الشَّمْسُ فِي صَبِيحَتهَا
لَا شُعَاعَ لَهَا»
Ma'ana:
"Ina rantsuwa da Allah! Lallai ni na san a cikin wani dare take, Ita ce
daren da Manzon Allah (r) ya umurce mu da tsayuwan dare a cikinta, kuma
itace daren ashirin da bakwai". Kuma Ubayyu ya kasance yana rantsewa akan
haka, ya kan ce: Da alamar da Manzon Allah (r) ya bamu labari akanta
cewa: Lallai rana tana fudowa a safiyarta bata da zafi).
Kuma hadisi ya zo daga
A'ishah (رضي الله عنها)
tace: Ya ma'aikin Allah! In na samu dacewa da lailatul qadari me zan faxa? Sai
yace:
«قُولِي: اللَّهُمَّ
إِنَّكَ عَفُوٌّ، تُحِبُّ الْعَفْوَ؛ فَاعْفُ عَنِّي».
Ma'ana:
"Ki ce: Ya Allah lallai kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi mini afuwa"
[Ahmad da Attirmiziy suka rawaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi].
9- YAWAITA
ZIKIRI DA ADDU'A DA NEMAN GAFARA: Xan'uwana mai karamci, Yini da darare watan
ramadhana lokuta ne masu falala, sai kayi qoqarin ribatarsu ta hanyar yawaita
zikiri da addu'a, musamman a lokutan amsa addu'oi a cikinsu, Daga cikinsu:
v A lokacin buxa baki, saboda mai azumi a
lokacin buxa bakinsa in ya yi addu'a ba a mayar masa.
v A cikin kaso na uku na qarshen dare, a lokacin
da Ubangijinmu mabuwayi da xaukaka yake sauka (zuwa saman duniya), sa'annan
sai ya ce:
"هَلْ مِنْ
سَائِلٍ فَأُعْطِيَهُ؟ هَلْ مِنْ مُسْتَغْفِرٍ فَأغْفِرَ لَهُ".
Ma'ana:
"Wanene zai roqe ni sai na bashi, Wanene kuma zai nemi gafara ta sai na
gafarta masa".
v Neman gafara a lokacin yin sahur: Allah
ta'alah yana cewa:
{وَبِالْأَسْحَارِ
هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ} [الذاريات: 18].
Ma'ana:
"Kuma a lokacin sahur sun kasance suna neman gafara" [Zariyaat: 18].
DAGA QARSHE: Xan'uwana mai karamci..
Bayan zagaya dausayin aljanna da muka yi, muna masu hutawa a qarqashin inuwowin
aiyuka na kwarai, zan faxakar da kai wani lamari mai muhimmanci.. Shin ka san
menene shi?
Lallai shine yin ikhlasi
(yi don Allah), .. E, ikhlasi.. Saboda masu azumi dayawa babu wani abu da za su
samu daga azuminsu sai yunwa da qishi, kamar yadda masu sallah dayawa baza su
samu komai ba daga tsayuwarsu sai rashin barci da gajiya, Allah ya tsare mu da
kai daga haka. Wannan kuma shine ya sanya Annabi (r) ya qarfafa wannan lamari,
yace:
«إِيمَانًا
وَاحْتِسَابًا».
Ma'ana: "yana mai
imani da neman lada", Sai Manzon Allah ya sanya sakamako gafarar Allah ga
wanda ya yi azumi.
YIN WARGI A CIKIN WATAN
AZUMI: Xan'uwana..
Ina zaton na tsawaita wa'azina a gare ka, alhalin kuma ina kwaxaitar da kai
ribatar lokacinka ne.. wato na ci maka lokaci, Saidai ina son ka yi min izinin
mu duba wani abu mai matuqar hatsari a tare (ni da kai), musamman kuma a cikin
watan ramadhana. Lallai wannan shine: Lamarin vata lokaci, da yanke shi cikin
abinda ba biyayya ba ne ga Allah, Wannan kuma shine gafala, da juya baya ga
rahamomin Allah da kyautansa, Allah ta'alah yana cewa:
{وَمَنْ أَعْرَضَ
عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيامَةِ
أَعْمى * قالَ رَبِّ لِمَ حَشَرْتَنِي أَعْمى وَقَدْ كُنْتُ بَصِيرًا * قالَ
كَذلِكَ أَتَتْكَ آياتُنا فَنَسِيتَها وَكَذلِكَ الْيَوْمَ تُنْسى * وَكَذلِكَ
نَجْزِي مَنْ أَسْرَفَ وَلَمْ يُؤْمِنْ بِآياتِ رَبِّهِ وَلَعَذابُ الْآخِرَةِ
أَشَدُّ وَأَبْقى}، [طه: 124-127].
Ma'ana: "Lallai wanda
ya juya baya ga ambatona to yana da wata rayuwa mai qunci, kuma zamu tayar da
shi, a ranar alqiyamah yana makaho * Zai ce: Ya Ubangijina don me ka tayar da
ni makaho, alhalin na kasance ina gani * Sai Allah yace: Haka ayoyinmu suka zo
maka sai ka manta da su, to haka nan a yau za a manta ka * Haka muke sakanta ma
wanda ya qetare iyaka, bai kuma yi imani da ayoyin Ubangijinsa ba, Kuma azabar
lahira tafi tsanani da wanzuwa" [Xaha: 124-127].
Sau nawa kake jin raxaxi a ranka, zuciyarka ta zama kamar zata
yayyanke saboda ciyon abinda kake gani daga wajen samarin musulmai, waxanda
geffan hanya da titi da wuraren wasanni ya cika da su a cikin dararen ramadhana
masu falala.. Kuma nawa daga cikin abubuwan da Allah ya haramta, da sassava
masa ake bayyanar da aiki da su a cikin dararen ramadhana masu albarka.. Na'am!
Lallai musulmi zai yi kishin lokutan 'yan'uwansa musulmai, da kuma karsashin
samarinsu da ake tuntsurar da shi ba a cikin biyayya ga Allah ta'alah ba.
Saidai kuma... !! Ka kwantar da hankalinka.. Saboda hanyar
tsirarka da ta 'yan'uwanka ita ce kawai: Yin da'awah da addu'a, Na'am, Yin
wa'azi da da'awa ga wanda ya rafkana daga 'ya'yan musulmai tare da shiryar da
su hanya madaidaiciya, Da kuma yi musu addu'a a fake, da fatan Allah ta'alah ya
amsa, idan kuwa hakan ta faru to ba za mu tave ba har abada.
Almadinah
07/ramadhana/1436h,
daidai
da 24/06/2015m.
No comments:
Post a Comment