2019/09/18

د ثبيتي 21 المحرم 1441 إن الله لا يصلح عمل المفسدين Hudubar












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
I
(إن الله لا يصلح عمل المفسدين)
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh  AsSubaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: K, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Bayan haka:
Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye su a bayan kasa, na manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowan dukiya masu yawa, a karkashin kulawan Mutane domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].

Kuma dukkan umurni da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin su tabbatar ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma saboda kallafe-kallafen shari'a (umurni da hani)  suna komawa ne zuwa ga kiyaye manufofinta a cikin halittu. Wadannan manufofin kuma babu makawa sai an kula da su gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka rasa su maslahohin Duniya ba za su tsayu ba.
Musulunci ya rataya mafi tsananin narkon azaba, akan kawo barna a bayan kasa; kuma duk wanda ya kawo barna a bayan kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci ne.
Matsala zata iya samun Mutane saboda makircin masu makirci, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi, wannan kuma domin Allah ya jarrabi bayinsa Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewarsu su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan asalin tushensu.  Kuma hakikanin al'ummomi yana bayyana a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa, himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiyar tayu na rayuwa, a'a al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai musiba mai radadi wanda ya auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijratu Kharidh, kuma ya yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa da wannan al'ummar, aiki ne abin kyama, ya nuna wauta da jahilci da rashin hankalin wanda ya sanya ha'inci ya zama mazhabarsa, cin amana kuma dabi'arsa, makirci da yaudara kuma suka zama al'amarinsa. Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma ba za su samu muradinsu na barn aba, kuma da falalar Allah za su koma da asara mabayyaniya, haka kuma da fadakar jagororin al'amarin wannan kasa, da azamar jami'an tsaro da masu gadi iyakoki.
Kuma idan masu barna da 'yan rusau suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi ta'addanci akan mallakin al'umma, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin sanya iyaka ga wawayen hankula da makirce-makirce masu munanan manufofi da tottoshe kafofin masu makiya, da gyara abinda abinda ya karkace, sai amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasa da bunkasata ya cigaba.

Duk da wadannan musibun kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa aminci da zaman lafiya.

Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin a tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta, domin itace cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya masu aikin kawai su sani, lallai su ba za su iya rushe tsaron wannan kasa ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba, domin wannan kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana da tsananin fada da ta'addanci; domin alakokinta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar Allah ganuwa ne mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin kiyayewarsa, saboda tana daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune ginshikin hukuncinta, kuma mabubbugar shari'arta, kuma salon rayuwarta, kuma matabbata ga samun gindin zama, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shine zai sanya tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta al'amarin karfinsa, kuma rayuka suna fatan ganin bunkasarsa.

Danganta kai ga kasarka al'amari ne da aka dasa shi a jikin Mutane a al'adance, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro shi daga danganta kai ga addini, sai ya tafi tare da shi, Kuma yaya Mutum ba zai so kasar da yake rayuwa akantaba, ya taso aka turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da tarihinta? Kuma yaya Mutum ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki don hana masu ta'addanci a gare ta ba?

Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa lamarin tsaron kasar da dukkan nau'ukansa, sai ya samar kuma karfafa dangatakar 'yan kasan na cikin gida, wanda zai kare ta, daga wanda yake son kunno fitintinu da tashin-tashina a cikin kasar. Kuma yana daga abinda hakan yake hukuntawa:
Son kasarsa, da aiki tukuru dominta, da kada dan kasa ya zama kafa ga masu nufinta da sharri, ko duk wanda yake nufinta cutar da ita. Sannan ya yi kokari wajen duk wata maganar da zata kashe wata fitina, ko ta haifar kyakkyawan fata, ta kiyaye tsaro ta karfafa zaman lafiya, ta toshe kofar bala'i da tashin-tashina, ta rinjayar da maslahar kasa, ta karfafa alakokin al'umma. Wannan kuma yana hukunta kada ka amsa wa masu tsegumi da ma'abuta tutotin karya, wadanda nufinsu shine sace guiwa, da kawar da hadin kan jama'a da rushe abinda kasa ta samar kuma al'umma take girmamawa.

Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata shine hanyar samun nasara, da daukaka, kuma shine ginshikin samun karfi, tare da natsuwa da zaman lafiya, kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawar Allah yake raunata kulle-kullen makirci, yake dauke abu mai cutarwa.

Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, wato masarautar larabawa ta Saudiya, shine ginshikin amincin wannan al'umma (Musulmai), saboda Saudiya ita ce zuciyarta mai bugawa, kuma guzurinta mai tunkuda. Kuma lallai munana mata munana wa zaman lafiyar Musulmai ne (gaba daya). Kuma gangar jikin al'umma ba zai gushe ba yana cikin alheri matukar zuciyar tana bugawa, don haka, alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani kuma basu yankewa. Kuma hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasa da kare ta daga makircin makiya da kaidin masu kaidi abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumawa da wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma duk wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana hidima ne ga makiyan addinin Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako,Kuma duk yadda kiraye-kiraye barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare shi ya yawaita, to lallai barna gininsa mai girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].

Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk yadda masu kaidi suka kullo kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci, masu dakon ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai wanna kasar mai bada kariya ga harami biyu, tana nan da karfinta, madaukakiya, gagararriya, wanda ya nemi ya taba girmanta sai ya kaskanta, wanda ya yi adawa da ita zai fadi ya kaskanta, wannan kuma babu wata ruduwa a cikin haka, saboda Musulunci shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta mai karfi, kuma daukakanta yana karkashin bin addini, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi ya ce-: "Mu mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai Allah ya daukaka mu da Musulunci".

Da zaman dako (ribadin) zarata akan iyakoki, masu kiyaye addini da kasa, suna gwabzawa da makiya suna lankwame shi, kuma su basu girgiza, cikin kudurinsu, masu karfi da zamarsu da zukatansu, domin katse karshen masu ta'addanci, da bugu ga makaman barna.
Kuma muna yin jinjina kan gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasa, da wargaza tsare-tsarensu tun suna farko. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sais u yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Kuraish: 3-4].

Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Mumini a lokacin tsanani da fitintinu alakarsa da Ubangiji tana kara karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da Majibincinsa, ya nemi fakewa a mafakarSa, "Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa zuwa ga Allah, da nuna masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta. Kuma idan Musulunci ya bayyana bukatarSa ga Majibincinsa, to sai ya hada bukatarsa da aiki da kuma lazimtar addu'a, kuma lallai Allah yay i alkawarin amsawa duk wanda ya roke shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga Allah to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za ta samu gindin zama a zuciyarsa ba, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma zuwa gare shi ake mayar da lamura.

Kuma Al'ummar Musulmai za su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana has ashen zuwa lokaci nag aba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu da cika alkawarin Allah, Allah Ta'alah ya ce:   "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai" [Dalak: 3].


Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,




No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...