KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI
1-
Lallai cikin juyawar yini da dare, da saurin zamani da canzuwan halaye, da zuwan
sabin shekaru, da yadda ajali ke kokarin riskar ma'abutansa, dukansu dalili ne
akan al'amarin gushewa da makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da buri:
"Allah yana juyar da
dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
2- Mafi
alherinku shine wanda rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi
sharri kuma shine wanda rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni. Kuma daga
cikinku kowa za a tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da
samartakarsa ta yaya ya tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci, da mafi girman lokatai!
3-
Ku sani, lallai Allah ya zabi zababbu daga halittunSa, sai ya zabi manzanni
'yan aika daga cikin Mala'iku, suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga
cikin magana kuma ya zabi ambatonsa, a doron kasa kuma ya zabi masallatai, daga
cikin watanni kuma ya zabi watan Ramadhana da watanni masu alfarma, daga cikin
kwanaki kuma yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai
ku rika girmama abinda Allah ya girmama!
4-
Ku saurara! Lallai ga ku a farkon watan Muharram, kuma farkon shekarar
hijira, kuma lallai wannan watan yana cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda
Allah ya girmama su, ya ce: "Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha biyu, a
cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga cikinsu
akwai hudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku
zalunci kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
5-
Hakika Musulmai tun zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin
hijirar Annabi -SAW- daga garin Makkah zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi
da shekarar hijira, saboda Allah ya rarrabe tsakanin gaskiya da barna da al'amarin
hijira. Kuma
sahabbai sun fari kidayar shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya
tabbatu akan haka, kuma sai al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.
6-
An ruwaito daga Ibnu-Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –SAW– yana kirdadon yinin da ya
fifita shi akan waninsa ba, fiye da wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana
nufin watan Ramadhana", Bukhari da Muslim.
No comments:
Post a Comment